Tuesday, 19 March 2019
March 19, 2019
Hausa Novels
No comments
* TASHIN HANKALI *
*Written by :Mmn Abduljalal*
*Fasaha Online Writers*
*1*
~Kai kawo sukeyi a kofar ďakin cikin tashin hankali, kowa da kalar addu'ar da yakeyi cikin zcyrshi wasuma a bayyane sukeyi ba matan ba mazan ba.
Sun ďau tsawon lokaci cikin wnn hali kafin nurse ďin dake cikin ďakin ta leko da kanta tana cewa a bata zani.
Cikin rawar jiki wacce ake kira da Dadayi ta ruga tayi cikin ďakinta ta ďauko ta zo mikawa nurse ďin.
Ba da jimawa ba ta umarci dadayi da ta shigo ďakin.
A tare suka gyara gurin da gurin tare da gyara 'yar matashiyar budurwar da ta haihu bayan dogon wahalar da tasha.
Tsab suka gyaresu tare da jinjirin, kato dashi fari tass, saidai ya galabaita sosai sbd wuyar da yasha shima.
Godiya suka rika kwararowa nurse ďin cikin harshen fullanci kasancewar shine yaren da sukeyi dukansu.
Duk da nurse ďin ba musulma bace amma tana jin fulatanci sosai saboda cuďanyar da takeyi da fulanin garin duk dai dukkan qabilun kauyen suna jin fullanci sosai.
Rige rigen shiga sukeyi bayan an kare gyarata har nurse ďin ta tafi dan ganin abinda aka haifa da kuma lfyr uwar.
Kwanciya tayi ta rufe idanunta ruff tamkar mai bacci duk bidirin da sukeyi cikin ďakin baisa ta buďe idanunta ba.
Maganganu ke tashi kala kala cikin matan ďaya ma kuka takeyi tana surutai.
"Kul, kul, Salamatu na hanaki sauri tsinuwa, ki daina, idan bazakiyi adduar shiriya ga mutum ba kiyi shiru da bakinki.
D'a na kowa ne, bakisan dalilin da yasashi cikin wnn halin ba kuma baki san kaddarar da ta jawo dalilin samuwar wnn ďan ba, kiyi mishi adduar shiriya kawai.
Share hawayenta tayi tana barin ďakin sbd maganar dattijon mijinta karyar mata da zcy kuma tasan idan tana tsaye wajen magana dole tayi shi dan cutarwar tayi yawa, sosai take jin bakin cikin abinda ya faru kan 'yar tasu, snn ko da yaushe ta tashi zagin macucin sai maigidanta ya taka mata birki da cewar adduar shiriya ya kamata tayi masa ba zagi, mummunan fata ko tsinuwa ba.
Itama kanta dadayi daurewa takeyi sbd zafi da zogin da takeji a ranta kuma ba damar magana.
Mika mata yaron sukayi suka fita daga ďakin, suka barta da mai jego.
Ta jima tsaye tana mata kallon tausayi kafin ta kwantar mata da yaron kusa da ita ta fita domin ďora ruwan zafin da zatayi ma mai jego wanka.
Tana fita ta tarar da har Salamatu wacce suke kira da adda ta ďora ruwan, ďayar matar da suke kira da Addamari tana share gidan, sbd tun safe basu samu sukunin yin aikin kirki ba dan tashin hankalin da suke ciki.
Sannu ta mata kafin ta tattari kayan da mai haihuwar ta b'ata ta zagaya ta baya dan wankewa.
Bayan fitarsu ba da jimawa ba ta buďe idonta a hankali ta tashi tana cije leb'e.
Kurawa yaron ido tayi tana mamakin kamannin da ta gani a tare dashi, duk da taji iyayenta sun tanka a kan hakan saidai batayi tsammani kamar ta fito har haka ba.
A hankali ta janyo filo ta ďora kan yaron da nufin ta danneshi ya mutu ta huta da abin kunya.
A take zcyrta ta mata tambaya "Kisan kai fa zakiyi, Laifin me ya miki shi kuma Deeja, me zaki cewa Ubangijinki ranar gobe qiyama?"
A sanyaye ta janye filon ta mayar mazauninta taci gaba da kallon jinjirin da ke kwance baya ko motsin kirki.
Sallamar da taji yasa tayi saurin zamewa ta kwanta.
"Sannu Hadiza am."
Buďe idonta tayi ta kalleshi, kamar zata rusa kuka tace "Sannu Hamma am."
"Zaki iya tashi?"
Ya tambayeta da kulawa.
kai ta gyaďa mishi ba tare da ta yarda sun sake haďa ido ba.
A tsanake ta tashi ta zauna kanta a qasa.
"Banishi in kalleshi."
Kasa ta kuma yi da kanta.
Tashi yayi daga inda yake zauna ya dawo baki gadon ya durkusa yana kallon yaron da baiga alamun zata mika mishi shi ba.
"Ikon Allah, Hadiza kinga abunda na gani?"
Ya tambaya cike da mamaki.
Kwalla ta share tana gyaďa kai dan ta fahimci inda tambayarshi ta dosa.
Shima share kwallar yayi yana mai tuna cewa yanzu da badon kaddara ta faďa musu ba da yanzu wnn ďanshine, gashi abin mamaki kuma yaron kama yake dashi tamkar shine ubanshi.
Cikin sanyin jiki ya tashi ya ďauko ledar da ya shigo dashi ya ajiye mata ya fita.
Ba da jimawa ba Dadayi ta shigo da kunun kanwa cikin kwanon sha ta ajiye kusa da ita tana ce mata.
"Deeja tashi kisha da zafi zafinshi kada yayi sanyi."
Tana maganar tana buďe ledar da ta gani kusa da ita.
Balangu ta gani cikin ledar hakan yasa ta fita ta ďau kwano ta juye mata tana umartarta da taci maza ta fito ayi mata wanka.
Fitowarta daga wanka ta samu adda zaune rike da yaron tana kallonshi shi kuwa sai tsala kuka yakeyi itama addan sharar kwalla takeyi kaďan kaďan.
Zuwa yanzu shima yaron anyi mishi wanka an suturta shi da kayan sanyi mai k'auri an kuma lullub'e shi ruff, ga kuma gaushin da aka haďa a kasko yana ďuma ďakin sbd sanyin dake garin.
"Maza zo ki bashi abincin shi yunwa ke sashi wnn kukan."
Cewar adda tana mika mata yaron.
Saida ta zura riga snn ta ja kujera 'yar tsuguno ta zauna ba tare da ta kalli addanba.
Kan cinyarta ta ajiye mata shi ta fice daga ďakin dan tasan ba bashi zatayi a gabanta ba.
Sosai ta kure yaron da ido tana kallon tsantsar kamar da sukayi da Hamma Shehu.
Tunani ta fara na yadda kaddara ta afka musu ana saura sati biyu ďaurin aurenta da Hamma Shehu.
*Tuna Baya*
Cikin motar haya suke zaune a hanyarsu ta zuwa kauyen kawunanta sunkani daga asalin qauyen mahaifanta Dorofi dake cikin Gembu, domin ta kai musu ziyara kafin tayi aure.
Ita da kaninta mai bi mata sukayi wnn tafiyar.
Surutu ake ta zubawa cikin motar babu kakkautawa, wasu da harshen fillanci wasu da Mambilanci, wasu Hausa.
Sunyi nisa a tafiyar har Deejah ta fara gyangyaďi, kasancewa kusa da kaninta take zaune, ta kwantar da kanta kan kafaďarshi.
Bugu yake shirin kai mata sbd ya gaji , har ya ďaga hanu kafin ya isar yaji qarar bindiga tauu wanda ya haddasawa driver taka birkin da bai shirya, yawancin passengers suka wuntsila gaba suka sake komawa mazauninsu da karfi wasu har suna karo da juna wasu ko suna gwara kansu da jikin motar.
A razane ta ďago tana kallonshi.
"Yusufa menene?"
Daga masu salati a motar sai masu kiran jesus, sai masu cewa Yesu kristi, haka motar ta cika da hayaniya.
Kafin ya bata amsa
Tauu, suka kuma jin wata karar, tsitt kakeji cikin motar tamkar babu mai rai a ciki.
Gamm Deeja ta damke kaninta yusufa sai zare idanu takeyi, shi kuwa sai faman lekawa yake ko zai ga abunda yake faruwa.
Wata murya mai tsoratarwa ta ratsa dodon kunnensu inda ake umartarsu da duk su fito.
Take jikin Deeja ya ďau b'ari tuni ta fara hawaye dan tasan yau kam saita Allah, sbd ta fahimci 'yan fashin da takejin labarine itama yau tayi karo dasu.
A tsorace suke fitowa daga motar har aka zo kan deejan dake kankame da kaninta gamm jikinta sai rawa yakeyi.
Kallo ďaya ta musu ta sadda kai qasa, dukkansu biyar sanye suke da face mask.
Umartarsu akayi da su kwanta, ba tare da bata lokaci ba daga driver har passengers suka mimmike flat a qasa.
Deeja kam da kaninta a jere suke kwance kuma har yanzu bata sake shi ba.
Bincikar motarsu suka shigayi suka kwashi abunda zasu kwasa suka koma lalubar aljifai.
Suna nan kwance deeja taji ansa hanu an ďago ta, ba shiri ta sake tamke kaninta wanda shima ya tashi a firgice ya rikota riko mai kyau kuwa.
Ďaya daga cikin 'yan fashinne ya ďagota, ganin yanda suka rike juna, ya sashi fara b'anb'arar hanun deeja daga jikin yusufa.
Cikin tashin hankali ya kare damkarta yana bada hakuri dukansu kuka sukeyi.
Da karfin tsiya ya rabasu ya janye deeja daga wajen, ya fara nufar cikin daji da ita, hakan yasa suka kwalla kara a tare da yusufa, a guje kuma ya je ya rikota yana dađa bada hakuri.
Ganin zai b'ata musu lokaci yasa ďan fashin kwaďa mishi gindin bindiga sai da ya faďi kasa, ya jata yayi gaba da ita.
Dishi dishi yusufa ya fara gani sbd yanda jini yake fitowa daga kanshi, jakan kuma bai hanashi yunkurin tashiba saidai kuma a halin yanzu bashi da wani karfi sbd jiri dake ďibarshi, saidai mika mata hanu da yakeyi yana kiranta.
Itama kuma waigenshi takeyi tana mika mishi hanun tare da gursheken kuka sbd ganin suna ji suna gani za a rabasu.
Dafe kanshi yayi ya zube a wajen ganin sun b'acewa ganinshi.
Kuka takeyi tana kiran Yusufa har muryarta ta dishe.
Sunyi nisa sosai cikin dajin kafin suka isa inda suka b'oye motocinsu guda biyu.
Cikin mota ya turata ya shiga gefen driver ya zauna tare da kulle motar.
Buga gilashin motar takeyi tana kuka da disasshiyar muryarta har saida ya gaji ya daka mata gigitacciyar tsawar da ya tilasta mata haďiye kukanta.
Saida suka qare operation ďinsu kafin suka iso suka samesu a gurin.
Uku daga ciki suka shiga waccar motar sukayi gaba, sai ďaya da ya shiga motar su deeja suka take musu baya.
Tafiya mai nisa sukayi, deeja duk ta gaji da zaman ko ina na jikinta ciwo yake mata ga idanunta duk sun kumbura sbd kukan da tasha ba kaďan ba, har yanzu kuma bata bar zubar da hawaye ba, baranma idan ta tuna halin da tabar Yusufanta ciki.
A can kuma, 'yan fashin suna tafiya sauran jama'an suka yo kan Yusufa da jini ya wanke wa fiska har jikinshi.
Ba b'ata lokaci aka tattareshi aka karasa dashi asibitin dake garin Bali dan shi yafi kusa dasu.
Tashin hankali ba kaďan ba iyaye da 'yan uwa suka shiga lkcin da suka samu labarin Yusufa yana asibiti nanma dan an ce musu hatsari suka samu basu san ainihin abunda ya faru ba.
Hamma shehu da kaninshi Ali suka fara zuwa asibitin, sun samu an sa mishi karin jini yana bacci, saidai basu ga alamar Deeja cikin asibitin ba.
Ko da suka tambayi likitocin suka tabbatar musu da cewa shi kaďai aka kawo.
Haka suka zauna suna jiran farkawarshi cikn rashin kwanciyar hankali.
~ Cikin gudu na tashin hankali Allah ya isar dasu lfy.
Wani tamfatsetsen gida motar ta shiga a guje dan sun raba hanya da ďaya motar.
Umartarta sukayi da ta fito, suka nufi wani tangamemen falo wanda yasha kayan alatu na more rayuwa.
Suna shiga suka umarceta da ta zauna kada kuma tayi gigin fita dan akwai karnuka masu haďari a gidan.
Cusa kanta tayi cikin cinyoyin ta ta dasa wani sabon kukan, har suka fita bata sani ba, saida wata dattijuwar mata ta kawo mata abinci tana mata magana, jin muryar mace 'yar uwarta yasata ďago nan tasan basa ma cikin falon.
Cikin tausayawa matar take kallonta, "Sannu yarinya."
Gyaďa mata kai kawai tayi batayi magana ba."
"Ci abinci yarinya, kinji."
"Mama ka taimakeni ka fitar dani a gidannan."
Ta faďa da muryarta da bata fita sosai wasu sabbin hawaye suna daďa surnano mata.
"Ci abinci to sai musan yanda zamuyi."
Ta fađi hakanne kawai dan ta kwantar mata da hankali, amma ita kanta tasan bata isa ta kub'utar da ita saidai idan Allah ne yaso hakan, tunda itama tana ji tana gani aka rabo ta da 'ya'yanta da danginta, tazo tana musu bauta babu kuma hanyar kub'uta.
~Sun jima zaune a gun kafin ya farka da kiran Adda Deeja, da iyakan karfin muryarshi yana mika hanu.
Rikon da suka mishine yasashi bud'e idanunshi, ganin yayyunshi ke rike dashi ya fara yunkurin tashi suka maidashi.
"B'e dillidi be mako."
Ma'ana :Sun tafi da ita.
Yake maimaitawa yana girgiza kanshi cikin tashin hankali.
Sai kuma yayi saurin rike kan ya rintse idanun shi sbd wani irin ciwo da yaji kan yana mishi.
Mayar dashi Ali yayi ya kwantar yayin da dukkansu hankali tashe suke tambayarshi da wa aka tafi.
"Adda Deeja."
Ya amsa musu cikin matsanancin kuka.
A kiďime Ali yace "Su waye suka tafi da ita."
Kafin ya bada amsa sai karar faďuwar Hamma shehu suka ji.
Sake Yusufa yayi ya koma kan Hamma shehu yana jijjigashi amma ina, yayi nisa.
Cikin b'acewar baseera da dabara ya dab'ashe a wajen ya fashe da wani irin kuka mai tab'a zuciya.......
Related Posts:
tashin hankali page 3 TASHIN HANKALI **Written by:Mmn Abduljalal**Fasaha Online Writers**3*~A ladabce ta gaisheshi, ya amsa mata da kulawa yana tambayarta yanda ta kwana.Tun ďazu take son ganinshi taji abunda zai ce game da komawarta gida.… Read More
TASHIN HANKALI HAUSA NOVEL complete * TASHIN HANKALI * *Written by :Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *1* ~Kai kawo sukeyi a kofar ďakin cikin tashin hankali, kowa da kalar addu'ar da yakeyi cikin zcyrshi wasuma a bayyane sukeyi ba matan ba mazan ba. Su… Read More
TASHIN HANKALI PAGE 2 .* TASHIN HANKALI **Written by :Mmn Abduljalal**Fasaha Online Writers**2*~Sai dare wajen karfe tara suka dawo, lokacin tana cikin ďakin da aka bata, taci kuka ta koshi, hawayen har sun kafe, tana zaune kan đan kwalinta da … Read More
Tashin Hankali Page 1 * TASHIN HANKALI * *Written by :Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *1* ~Kai kawo sukeyi a kofar ďakin cikin tashin hankali, kowa da kalar addu'ar da yakeyi cikin zcyrshi wasuma a bayyane sukeyi ba matan ba mazan ba. S… Read More
TASHIN HANKALI episode 4 A* TASHIN HANKALI * *Written by :Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *4* *Dedicated to Mmn Buhari (Mama Deejah)* ~ Ciccib'anta yayi ya fita da ita ya kwantar a bayan motarshi ya shiga ya jata a guje ya ďauki hanyar bari… Read More
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
0 comments:
Post a Comment