Thursday, 4 April 2019

A* TASHIN HANKALI * *Written by :Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *4* *Dedicated to Mmn Buhari (Mama Deejah)* ~ Ciccib'anta yayi ya fita da ita ya kwantar a bayan motarshi ya shiga ya jata a guje ya ďauki hanyar barin gari. Bayan shuďewar wasu lokuta, smart ya dawo ya shiga da sallama, yana karawa da "Sorry sister, na b'ata miki lokaci ko?" Shirun da yaji baisa ya tuna komai ba tunda yasan ba lallai bane ta amsa. A yadda ya ajiye jakar haka ya sameta sbd haka ya ďauka yaje ya sakata cikin mota. Falon ya dawo yana kiran "Khadija fito mu tafi." Shi a tunaninshi ko ta koma cikin bedroom ne. Shirun da yaji yasashi leka ďakin, wayam bata nan, zama yayi yana tunanin ko tana toilet. Ya ďan ďauki lokaci zaune cikin ďakin sai duba agogon hanunshi yakeyi amma ko alamar motsinta baiji daga cikin toilet ďinba. Wani tunani ne ya ďarsu a zcyrshi lokaci guda ya mike zcyrshi na tsinkewa. "Khadija." Ya kwala kiran da ďan karfi. Jin shiru yasashi buďe kofar toilet ďin ya leka kamar a tsorace. Cikin tashin hankali ya fita ya leka ďakinshi, daga ya fara nema lungu da saqo na gidan. "Oh, no khadija badai guduwa kikayi ba, wa kika sani a garin jos, taya zaki koma garinku, bakya tsoron haďuwa da mugaye su cutar dake, dama baki yarda dani ba khadijah, ashe yafiyar da kikayi ba kai zuciya ba?" Surutai ya rika yi cikin tashin hankali. Kamar an tsikareshi ya tashi har ya kai bakin kofa ya tsaya ya tambayi gate man đin shi ko akwai wanda ya shigo gidan bayanshi. "Oga scorpion ne ya shigo kuma ya fita da wata yarinya kamar bata numfashi, inajin ba lafiya ne." Gate man ya bashi amsa. "Inna lillahi wa innaa ilaihi rajiuun." Ya dinga maimatawa yana juya kanshi take kuma ya fara jin kamar jiri na ďibanshi. Gefen bencin maigadi ya lalub'a ya zauna ya dafe kanshi take idanun shi suka rine da b'acin rai, ga wani irin tashin hankali marar misaltuwa da ya diro mishi. "Yallab'ai lafiya?" "Lafiya." Ya faďa a takaice tare da tashi ya bar wajen a sanyaye. Kofar falon ya tsaya yana kallon takalmanta dake zube a wajen. A hankali ya duqa ya ďauki takalman yana kallonsu tamkar khadijan zata b'ullo ta jikin takalman. "Why scorpion, why? Me yasa baka barni na cika mata burinta ba? Me yasa baka bani damar cika mata alkawarin da na ďaukar mata ba? Me yasa ka dage lallai sai ka cutar da ita, Laifin me tayi maka? Me yasa baza ka tausaya mata ba?" Haka yayi ta jerowa scorpion ďin da baya kusa tambayoyi har ya gaji ya mike da takalman a hanunshi ya je ya kwanta cikin kujeru, ya rungume takalman sbd yanda yakejin jikinshi ba nauyi kamar leda. Fiskarta ke mishi yawo a idon zuci, kawaicinta, kunyarta ,murmushinta, kukanta duk babu wanda baya tunawa, wata kila shi kenan ta rabu da danginta ta zama mara gata da dangi kamar shi, wata kila kuma ta halaka kanta kamar yanda tayi yunkurin yi lokacin da ya keta mata mutuncinta. kamar a mafarki yaji hawaye suna ziraro mishi, "Ya Allah ka tseratar da wnn baiwa taka daga cutarwar scorpion." Cikin zafin nama ya mike yaje ya ďauro alwala ya fara jero nafiloli da adduoi yana nema mata kariya a wajen Allah. Ko da wasa baiyi gigin neman scorpion ba sbd yasan bazai ma tsaya nan kusa da ita ba. ~Tafiya mai nisa sukayi, cikin ikon Allah ta farka amma kasala da nauyin jiki sun hanata motsawa, hakan yasa baisan cewar ta farka ba. Daga kwancen take ta kwararo adduoi a ranta sbd tunawa da shigowar scorpion da kuma nufarta da yayi, daga nan kuma bazata iya cewa ga abunda ya faru ba, saidai a yanzun tana da tabbacin dashi take tare dan kamshin turaren da take ji ba na uncle smart bane. Tafiya mai nisa sukayi, shi kanshi tafiya yake ya rasa takamemmen inda ya kamata ya kaita sbd gudun sharri smart, yasan halinshi sarai, kamar yadda suke kiranshi smart haka yake ya amsa sunan, zai iya yin komai cikin dabara da aiki da hankali har ya gano inda suke. Saida ya shiga Nasarawa state ya samu bakin hanya ya gangara ya tsayar da motar, ya juya yana kallonta kafin daga bisani yakai hanu ya shafi fiskarta,, "Sleep well my beauty, barin samo miki abunda zakici kafin ki farka." Luff tayi tamkar baccin takeyi da gaske. Saida ta tabbatar ya fita ta ďago kanta ta leka ta glass. Bayan shi ta hango ya shiga wani restaurant. A hankali tasa hanu ta buďe kofar. Ganin bai kulle ba yasa tayi karfin halin tashi ta ja jiki ta fita daga cikin motar ta fara tafiya tana waige. Tana matsawa daga wajen wani da yazo wucewa yaga kofar mota a buďe ya tura ya rufe yayi gaba abinshi. Wani shago ta shiga, mai shagon yana binta da kallo sbd ganinta da yayi a galabaice. "Baiwar Allah lafiya." "Ki taimakeni ki b'oye ni wani ya mini sata ne." " Waye ya yi miki sata kuma satan me ya miki?" Ya tambaya yana wurga ido ta inda yaga take kallo." Jan kafarta tayi ta shiga ciki sosai ta zauna dab'as a kasa yanda na waje bazai hango ta ba kafin tace. "Ya mini sata a garinmu ya kawoni a nan." Ta sake faďa idanunta suna faman rufewa. "Ina ne garinnaku?" "Gembu." Ta bashi amsa sai tayi luu ta kwanta. "Ikon Allah, da alama fa sato yarinyar akayi." Ya faďa yana kallonta. ~Manyan ledoji guda biyu ya dawo dasu ya buďe mota ya saka ya zagaya ya zauna ba tare da ya kalli bayan motan ba. A guje ya sake figar motar ya kunna kiďa yana yana bi cikin nishaďi har ya qarasa cikin abuja. Slowing tukin yayi ya waiga bayanshi yana cewa "Har yanzu baki tashi .... Maganar tashi ce ta katse sbd abinda idanunshi suka gane mishi. "mafarki ko gaske?" Ya tambayi kanshi. Wani irin wawan birki yaci. Da azama ya buďe kofar motar yaje buďe baya yana leka kasan motar da kyau. Ja da baya yayi a tsorace "Mutum ko aljan." Ya kuma cewa. "Ko dai smart ya biyoni ne?" Take ya ciro wayarshi ya kira Nass ya tambayeshi labarin Smart. Har gidan yaje ya kuwa sameshi kwance kan sallaya yana bacci. Take ya kirashi ya shaida mishi. ~Sauri yayi ya rufe shagonshi ya fita sai police station, nan ya shaida musu abunda yarinya ta sanar dashi tare da basu tabbacin yarinya tana cikin shagonshi a kwance. Tare sukazo da police uku, maxa biyu mace ďaya suka ďauketa sai asibiti. ~Shawara zcyrshi ta bashi da ya koma inda ya tsaya a nasarawa state ko zaiji labarin an ganta, yana kuma mamakin yanda akayi ta samu karfin fita daga motar. Haka ya koma ya karaci bilayinshi bai samu wani kwakkwaran labari ba, karshe anan garin ya kwana washe gari kuma ya koma jos. Gidan Smart ya fara zuwa yana jin takaicin rasata da sukayi dukansu biyu, shi bai bar mishi ita ba ,gashi shima ya rasata. Kallo kallo suka fara yiwa juna, wanda shi smart kallon tsana karara yake yiwa abokin nashi. "Smart, ta b'ata, ta gudu ban ganta ba." "Rubbish, ka daina faďa min maganar banza, ina kakai 'yar mutane?" Ya faďa a tsawace yana huci. "I swear ta b'ata, ban ganta ba nima, mun rasata dukanmu biyu, dana san zata b'ata da na hakura na bar maka ita, Saida Billy yace in bar maka ita, she must be the lucky lady da nake faďa naki yarda, gashi mun rasata gaba ďaya. Shako kwalar rigarshi smart yayi cikin ďaga murya yace. "Wa ya faďa maka sonta nakeyi, taimakonta nayi dan in kub'utar da ita daga sharrinka, maidata gidansu cikin danginta nakeso inyi, but now, kaga abinda ka jawo, ka rabata da familynta, kazo kana gaya min baka san inda take ba." Sai kuma ya sassauta rikon da ya mishi ya kuma sassauta muryarshi. "Scorpion, yanzu a wani hanu kake tunanin zata faďa? me yasa baka da tausayi da imani? why are you so heartless scorpion?" A hankali ya zame hanunshi daga rikon da ya mishi ya kuma nunashi da yatsa. "Ka sani duk abunda ya faru da khadija, Allah bazai barka ba, Allah sai ya kama ka, alhakin yaran da kake cutarwa bazai barka ba scorpion sai Allah ya kamaka." Murza yatsunshi yayi ya juya ya shige cikin bedroom ya barshi nan tsaye jiki a sanyaye, bai san mai yasa yau maganganun smart sukayi tasiri a kanshi ba duk da ba yau ya fara faďa mishi hakan ba, baisan me yasa b'atan yarinyar ya ďaga mishi hankali ya sanyayar mishi da jiki ba. "Am sorry friend, i missunderstood u, rashin sani ne, da na barka ka maidata garinsu, am sorry once again. " Shi kaďan shi ya karaci surutanshi ya fita daga gidan gaba ďaya yana jin zcyrshi ba daďi. ~ kwananta biyu a asibiti ta warware hankalinta ya gama dawowa jikinta, tambayoyi kam tasha su, daga bisani aka hađa ta da 'Yan sanda biyu a rana ta uku suka rakata garinsu. Mikakkiyar tafiya sukayi zuwa jalingo, cin abinci da sallah yake tsayar dasu. Daga nan suka ci gaba da tafiya zuwa Baruwa, suka isa karfe takwas da 'yan mintoci. Cikin baruwan suka kwana sbd haurawan hawan biyu da sisi, da zasuyi. Sai washegari suka haura Gembu wuraren karfe goma na safe, daga can suka sauka suka hau machine mai kafa biyu, suka haye kogin wukari suka karasa dorofi, da misalin karfe sha biyu na rana. Duk zumuďin da takeyi na zuwa garinsu suna isa taji gabanta na faďuwa. Mutane sai binsu da kallo sukeyi yayinda ita kuma ta ja lullub'inta ta rufe fiskarta dashi. 'Yar yayanta wanda yake ďan Baffanta ne, wacce bata wuce shekaru biyar ba ta dawo daga makaranta zata wuce gidansu ta gansu. Tsayawa tayi tana kallon 'yansandan kafin ta maida dubanta ga Deejah. "Goggo Deejah oyoyo." Take faďa da tsattsamar muryarta tana tsalle. Rige rige matan gidan sukeyi wajen fita daga gidan sbd tabbatar da abunda kunnuwansu suka jiyo musu. Rike da hanun Ummi ta doso gidan suka ci karo da matan gidan. Adda, Mmnsu Hamma shehu ce tayi saurin rungumeta sai kuma suka fashe da kuka a tare . Sauran matan ma riketa suka yi suna kukan. Kan kace me tuni makwabta sun fara taruwa ana taya murna, sai daga baya hankulansu yaje kan Jami'an tsaron da suka rakota. D'akin Hamma shehu aka buďe musu suka shiga daga nan aka fara hidima dasu dama ga mutanen dorofi ba dai iya karrama bako ba. Kan kace me gida ya cika da jama'a 'yan taya murna , tuni labari ya isa ga iyayenta maza da suke wajen kasuwancinsu, shima Hamma shehu da yake cikin kamaru tuni aka nemi gurin service aka kirashi, dan ba ko ina ake samun service a garin ba. Yusufa dake makaranta sai gashi ya shigo a guje yana "Ina adda Deejan?" Ai a guje ta tashi ta rungumeshi ta kuma fashewa da kuka, a haka iyayensu suka dawo suka samesu. A takaice ranar farin cikin baya misaltuwa ga ahalin wnn gida, baranma Hamma Shehu da baki yaki rufuwa, kannenta kuwa daga kan Yusufa yayi kasa suna makale da ita , Fa'i kuwa kamar zasu shige cikin juna. Godiya suka rika yiwa jami'an tsaronnan ba adadi bayan sun basu labarin yanda akayi aka samota. Saida 'yan barka suka lafa, snn iyaye da yayyu aka haďu nan take basu labarin bayan rabuwansu da yusufa saidai ta gagara sanar dasu fyaďen da Uncle smart ya mata, amma sunsha labarin kyautatawar da ya mata kam, harda yunkurin da yayi na dawo da ita gida scorpion ya zoya sake ďauketa. Addua sukayi ta mishi na alkhairi shi da mutumin da ya taimaka mata a nasarawa state. Sai washegari polisawan suka kama hanyar komawa bayan yan uwanta sun cika su da goma ta arziki....

Related Posts:

  • TASHIN HANKALI episode 4 A* TASHIN HANKALI * *Written by :Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *4* *Dedicated to Mmn Buhari (Mama Deejah)* ~ Ciccib'anta yayi ya fita da ita ya kwantar a bayan motarshi ya shiga ya jata a guje ya ďauki hanyar bari… Read More
  • TASHIN HANKALI HAUSA NOVEL complete * TASHIN HANKALI * *Written by :Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *1* ~Kai kawo sukeyi a kofar ďakin cikin tashin hankali, kowa da kalar addu'ar da yakeyi cikin zcyrshi wasuma a bayyane sukeyi ba matan ba mazan ba. Su… Read More
  • Tashin Hankali Page 1 * TASHIN HANKALI * *Written by :Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *1* ~Kai kawo sukeyi a kofar ďakin cikin tashin hankali, kowa da kalar addu'ar da yakeyi cikin zcyrshi wasuma a bayyane sukeyi ba matan ba mazan ba. S… Read More
  • TASHIN HANKALI PAGE 2 .* TASHIN HANKALI **Written by :Mmn Abduljalal**Fasaha Online Writers**2*~Sai dare wajen karfe tara suka dawo, lokacin tana cikin ďakin da aka bata, taci kuka ta koshi, hawayen har sun kafe, tana zaune kan đan kwalinta da … Read More
  • tashin hankali page 3  TASHIN HANKALI **Written by:Mmn Abduljalal**Fasaha Online Writers**3*~A ladabce ta gaisheshi, ya amsa mata da kulawa yana tambayarta yanda ta kwana.Tun ďazu take son ganinshi taji abunda zai ce game da komawarta gida.… Read More

0 comments:

Post a Comment

BTemplates.com

Popular Posts