Friday, 22 March 2019

 TASHIN HANKALI *
*Written by:Mmn Abduljalal*
*Fasaha Online Writers*
*3*
~A ladabce ta gaisheshi, ya amsa mata da kulawa yana tambayarta yanda ta kwana.
Tun ďazu take son ganinshi taji abunda zai ce game da komawarta gida.
Shiru tayi tana jiran jin abunda zai ce mata.
"Kinci abinci?"
Gyaďa mishi kai tayi ba tare da ta kalleshi.
Kallonta yayi na ďan lokaci kafin ya ce mata.
"Ya sunanki?"
"Deejah."
Babban sunanki kenan?"
Ya kuma tambaya.
"Hadiza."
Ta kuma cewa.
"Khadija kenan, Ina ne garinku?"
"Dorofi."
Maimaita sunan dorofin yayi, tun da yake bai tab'a jin sunan ba .
"Wani state kenan?"
"Taraba state."
"A wani local government."
"Sardauna local government, Gembu."
Shiru yayi yana tunani, shi dai yasan yana jin sunan taraba state, amma bai tab'a zuwa ba dan ba'a bashi wnn damar ba, kamar yanda ake hana sauran members ďinsu zuwa wasu states, saidai yana ganin a sanadiyyar ta zai karya dokar da aka kafa mishi na hanashi zuwa taraba state, da sauran states ďin da suke makwabtaka da ita.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace.
"Kinsan abunda nakeso dake yanzu,
Zaki ďan kara haquri zuwa wani ďan lokaci sbd zan ďanyi wani bincike kafin na mayar dake, ni nan da kika gani ban tab'a zuwa state ďinku ba balle wani local govt, shi yasa zan iya ce miki bansan ma ta inda zanbi inje ba, so ki ďan kara min lokaci kinji."
Dalla dalla yakeyi mata bayanin yadda zata fahimceshi dan ya fahimci cewa jin hausan nata ba sosai ba, da ya gane tayi karatu kuma yake ďan surka mata da harshen turanci snn kuma yakan haďa da ďan guntun fulatancin da ya iya na fulanin jos da kuma kwatance da hanu duk dan ta fahimceshi.
Kalloshi tayi da alamar rashin yarda a zcyrta tana tunanin ko shi ďinma cutar da ita yake sonyi shi yasa ya bullo mata ta wnn hanyar.
"Ya dai, baki yarda bane?"
Ya tambayeta tamkar yasan tunanin da takeyi.
Girgiza kanta tayi kawai batayi magana ba.
"Kinga, ni ba cutar dake zanyi, asalima gudun kada a cutar dake yasa na ďauko ki daga gidan scorpion dan nasan halinshi, taimakonki nakeson yi sbd Allah, bayan haka tun da na ganki nake jinki a raina tamkar 'yar uwata, ta jini, duk ni ďin bani dasu, sbd haka ki ďauke ni a matsayin hakan kema."
Ya karshe maganarshi a raunane, wanda hakan yasa taji ta yarda da maganganunshi har tana Immagining nan da kwanaki kaďan tana gidansu cikin danginta.
A hankali tace "Wani gari ne nan?"
"Jos, plateau state."
Jinjina kai tayi tana share kwallar da suka zubo mata sbd tunawa da tayi da gida ,babban damuwarta ma Yusufa da ta bari kwance cikin jini, Allah yasa dai babu abunda ya sameshi.
Adduar da take yawan kenan duk lokacin da ya fad'o mata.
Kaďan kaďan yake janta da hira yana kuma yi mata tambayoyi game da garinsu da familynta, tana bashi amsa a takaice, tun tana đari ďari har ta fara sakin jikinta.
Duk wani abin bukata ya tanadar mata, haka kuma sutura masu mutunci ya saya mata ba kamar scorpion da ya haďa ta da 'yan iskan kaya ba, duk english wears marasa mutunci, hakan ya kara mishi daraja da kima a idanunta har itama ta fara jinshi kamar ďan uwanta.
~Duk wani gidan member ďinsu da ya sani saida ya zaga yana bincikawa tare da taimakon Nass, amma ko alamar mai kamanta bai gani ba.
Sau biyu yana zuwa gidan Smart bisa shawarar Nas amma ko a fiska baiga alamun hakan daga shi smart ďinba, yayi binciken har ya gaji, saidai ya rasa dalilin da yasa zcyrshi ta kasa hakura da tunanin yarinyar.
~"Uncle smart."
Ta kira a hankali kamar yanda taji maaikatan gidanshi suke kiranshi.
tana buga hanun kujerar da yake kwance a kai.
Kaďan ya buďe idanunshi masu cike da bacci yana kallonta, daga bisani kuma ya waresu gaba ďaya sbd ganin yanda ta marairaice hawaye na sintiri kan fiskarta.
"Ya dai khadija, kukan me kikeyi?"
Kasa tayi da kanta tana so tayi mishi maganar gida sbd yau kwananta biyar kenan a gidanshi , ta kuma rasa ta inda zata fara.
Tashi yayi sosai ya zauna kan kujerar yana fiskantarta.
"Gida ko?"
Da sauri ta gyaďa kanta.
"Ina sane ban manta ba khadija, nima banso kikai har yanzu baki koma ba, sbd nasan hankalin iyayenki a tashe yake, saidai abun ne sai munbi a hankali, da dabara, a halin yanzu scorpion ya haukace yana nemanki, so yake ko ta halin yaya ki koma gareshi, ta iya yiyuwa ma ya baza mutane ta hanyar garinku sbd ke, bayan haka ni kaina nasan bai yarda dani ba, ya sa min ido sosai,shi yasa kika ga banyi gaggawar maida ki ba, bayan haka dole ne cikin sirri zan gudanar da bincike na sbd kada ya fahimci wani abu, sbd haka ki kwantar da hankalinki, ki kara hakuri, in Allah ya yarda kisa a ranki kin koma gidanku kin gama, ina fatar kin fahimta."
"Uhmm."
Tace tana share hawayen fiskarta.
"Kin yarda yayanki bazai cuce ki ba,?"
Gyada mishi kai tayi.
"Ok, to smile let me see."
Murmusawan kuwa tayi yana tayata.
Kwana biyu tsakani, zuwa yanzu kam ta gama sawa ranta ta kusa komawa gida tunda uncle smart ya bata hujjojinshi kuma ta gamsu, bayan haka itama shaida ce kan zaryar da Scorpion yakeyi a gidan, shi yasa ko da wasa bata fita, saidai idan uncle smart yana gida nanma iyakarta falo, tana jin alamun taku kuma zata shige ďakin da aka sauketa.
~A gajiye ya shigo gidan sbd zirga zirgan da ya sha yau ba hutu kan sabon kampanin da ya buďe na sarrafa takalma da jakunkuna.
Wanka yayi ya ci abinci, har yayi shirin kwanciya ya tashi ya nufi ďakin ta sbd yau tun asubah ya fita basu haďu ba.
A hankali ya tura kofar ya shiga.
Baccinta takeyi haikan dan sai cikin kwanaki biyunnan take samu tayi bacci hankali kwance.
Ya jima tsaye yana kallonta yana jin wani abu na mintsinan zcyrshi game da ita.
Kawar da kai ya yi maida kallonshi ga agogon bangon dake cikin ďakin.
Karfe sha ďaya da mintuna ishirin da ďaya agogon ya juna.
Cikin sanyin jiki ya juya ya bar ďakin yana jin abu na mishi yawo a jiki wanda ko da wasa bai tab'a jin hakan game da ita ba.
Bathroom ya shiga ya sakarwa kanshi shower, ya jima a ciki snn ya fita ya sake shirin bacci, saidai me, baccin ya kauracewa idanunshi duk da sosai ďazu yake jinshi.
Babu abunda yake mishi yawo a ido sai surar ta, shaiďan kuma yana daďa kawata mishi kyaun
halittarta, dan tunda ta shigo gidan bai tab'a ganinta babu lullub'i ba sai yau.
Duk iya kokarin da yayi wajen aran dauriya ya yafawa kanshi da zcyrshi abun ya gagara, zcyrshi sai ingiza shi yake kan yaje ya sake kallonta.
Bin shawarar zcyrshi yayi ya koma ďakinnata, har yanzu tana kwance kamar yadda ya barta ďazu.
A hankali ya zauna a bakin gadon yana bin duk wani gab'a na jikinta da kallo, karshe ya sauke idanunshi kan kitsattsen sumarta baki kirin na fulanin asali.
Shafa kitson yayi yana lumshe idon shi kafin daga bisani ya maida hanunshi kan lips ďinta yana kewayawa da yatsarshi.
Motsin da tayi kamar zata tashi yasashi cire hanun, sai kuma ta koma ta ci gaba da baccinta.
A hankali ya matsa ya kwanta kusa da ita zcyrshi na daďa ingiza shi, wani irin feeling yakeji wanda zai iya cewa bai taba jin irinshi ba a rayuwarshi.
Bayanta ya ďaura hanunshi yana shafawa a hankali, itako sai daďa lafewa tayi a jikinshi tana baccinta hankali kwance.
Zarcewa yayi da tura hanunshi cikin rigarta hakan yayi sanadiyyar farkawarta.
A razane ta buďe ido jin bakon lamari a tare da ita, ganinshi yasata cikin inina tace "Un..un."
Kafin ta karasa ba ya haďe bakinsu hakan ya hana ta karasa abunda tayi niyyar faďa.
Wani irin rawa jikinta yakeyi tsoro da firgici suka mamayeta.
Yakushi da duka ta fara kai mishi a duk inda hanunta hakan kuma bai hana shi ida nufinshi akanta ba.
Tsabar azaba da razana suka bada gudunmawa wajen ďaukewar numfashinta.
Bai fahimci hakan ba saida hankalinshi ya dawo jikinshi.
Tattab'a jikinta yakeyi yana kiranta amma ina tayi nisa.
"Inna lillahi, na hana scorpion cutarki ni na cuceki."
Abinda ya faďa kenan rike da kanshi idanunshi suna tsiyayar da hawaye.
Yunkurin tashi yakeyi amma gaba ďaya ciwon da jikinshi yakeyi ya hana, wani irin ciwo mai zafi da raďaďi yakeji suke ratsa dukka gabb'an jikinshi.
Take zazzab'i mai zafi ya rufeshi wanda yasashi kwanciya nan kusa da ita yana jin haushi mamakin kanshi da ya kasa controlling kanshi har ya aikata abunda bai tab'a tunanin aikatawa ba.
Sai wuraren karfe huďu ta farfađo, kukan da takeyi ya tabbatar mishi da hakan.
"Kiyi hakuri khadija, am sorry, banyi da nufi ba."
Abinda yake faďa kenan cikin muryar marasa lafiya.
Lokaci guda ta fara rawar đari sbd azababben zazzab'in da ya rufe ta, hakoranta sai haďuwa sukeyi, tashi ya gagaresu dukansu biyu.
Saida gari yayi haske yasa mu ya ja jiki ya shiga wanka.
Falo ya koma yayi sallah, kafin ya dawo ďakin ya taimaka mata, duk da shima ďin juriya kawai yakeyi, dakyar da lallashi da ban hakuri, dan madai bata da wani karfi ne, da ko da wasa baza ta sake yarda da daďin bakinshi ba.
A zaune tayi sallah, ya kawo mata brkfast nanma da kyar taci tasha magani, sai tsine mishi takeyi a ranta.
Ba abunda ya ke bata mamaki irin yanda yake nuna kamar kunyarta yakeji wanda ita a matsayin munafurci ta ďauki hakan.
~Kwana uku kenan yanzu yana binta da rokon ta gafarceshi ba da niyya yayi ba amma ko uffan bata ce mishi.
Kamar kullum yauma haka ya shigo ya qaraci ban hakurinshi harda kukanshi, tayi burus dashi kamar bata cikin ďakin.
"Khadija idan na maidaki gidanku zaki yafe min?"
Ai a tamanin ta gyaďa mishi kanta hakan yasa ya bata tabbacin gobe asubanci zasuyi su kama hanya.
Duk da ba gama yarda tayi dashi ba amma fiskarta ta nuna alamun taji daďin maganarshi.
Da asubah kuwa suna idar da sallah ya shigo da shirin tafiya, itama hakan take a wajenta, tana zaune kan sallaya da jakarta a gabanta.
Saida yace ta tashi su tafi, ta gaisheshi.
Kusa da ita yazo ya durkusa tayi saurin ja da baya.
"Khadija, kafin mu fita inaso na sake rokon gafararki a karo na ba adadi, ki yarda dani wlh ba da nufi nayi ba, sharrin shaiďan ne, ki yarda dani ba halina bane, asalima kyamar mai aikata hakan nakeyi, nasan na cuceki na cuci rayuwarki, saidai inaso ki ďauki hakan a matsayin kaddara da ta hau kanmu dukanmu biyu, ki yafemin khadija."
Tunda ya fara magana ta durkushe a gurin tana kuka, ga dama ta samu zata koma gida saidai zata koma da mummunan tabo . har saida ya kare, ita ma cikin kukan tace "Na yafe maka uncle smart."
"Na gode, nagode khadija, thank u so much, Allah ya saka miki da mafificin alkhairi."
A tare suka mike, ya sa hanu ya ďauki jakarta suka fito daga ďakin.
Sun kai kofar falo zasu fita yana gaba tana biye dashi a baya, dab da zasu fita wayarshi tayi qara.
Picking yayi a kagauce.
"Hello Billy ya ne?"
Daga ďaya bangaren aka ce mishi "Boss ne yakeson ganinka yanzunnan."
"Oh goshh."
Ya faďa yana dafe goshinshi.
"Ok, gani nan zuwa."
Ya kashe wayar.
"Khadija kiyi hakuri barinje in dawo yanzu zamu tafi."
"
Gyaďa mishi kai tayi a sanyaye duk ta qagara ta ganta a hanyar garinsu.
Da sassarfa ya fita ita kuma ta koma ta zauna cikin ďaya daga cikin kujerun falon ta buga tagumi.
Bata daďe da zama sosai ba taji alamun shigowar mutum.
Juyawan da zatayi sukayi ido huďu da scorpion yana kallonta yana murmushin da zata iya kiranshi na mugunta.
A tsorace ta mike tana ja da baya, kafin tayi wani yunkurin kirki har ya karaso inda take ya shaqa mata abu a hanci, take ta zube a wajen yarafff....

Wednesday, 20 March 2019


.* TASHIN HANKALI *
*Written by :Mmn Abduljalal*
*Fasaha Online Writers*
*2*
~Sai dare wajen karfe tara suka dawo, lokacin tana cikin ďakin da aka bata, taci kuka ta koshi, hawayen har sun kafe, tana zaune kan đan kwalinta da tayi sallah, ba abunda takeyi sai tunanin gida da halin da kaninta yusufa yake ciki.
Turo kofar da akayi ya haddasa mata faďuwar gaba.
Bata ďago ba har ya qaraso ya tsuguna yana kare mata kallo.
"Yar fulani, kinci abinci?"
Gyaďa mishi kai kawai tayi.
"Wanka fa?"
Qasa tayi da kai ba magana.
"Ga wnn, ki shiga kiyi wanka kizo ki canza."
Duk da ba jin hausan sosai takeyi ba amma tana fahimtar abinda yake cewa dan tana tsintar daďďaya.
Fitar da kayan ya fara yi yana nuna mata su, ya ware mata na bacci daban, da na sawa a cikin gida, sai kayan kwalliya da turaruka, sai takalma guda biyu flat shoes.
Kallon kayan takeyi amma sam bata fahimtar abunda yake faďa sbd nisan da hankalinta yayi.
Sai da ya tab'ota ta kalleshi a firgice sai kuma tayi saurin dukar da kai .
"Nace ki tashi kije kiyi wanka,."
Ya faďa a ďan kausashe.
Da saurinta ta tashi ta shige ban ďakin.
Kasancewar matannan ta nuna yanda zata yi amfani da komai bata wani sha wahala ba tayi wankan, ta maida kayan da ta cire.
Ta jima tana tsaye cikin toilet ďin, duk a tunaninta ko yana cikin ďaki.
Daga karshe ta gaji da tsayuwar ta ďan bude ta leka.
Ganin baya ciki yasa ta saurin fitowa.
Zama ta kuma yi ta jingina da jikin bango ta lumshe idanunta da suke mata wani irin tsami.
Shigowarshi yasa ta bud'e idanun tana mishi kallon kasan ido sbd sam bata so yasan ma tana kallonshi.
"Ya kika maida kayan?"
Bata ce mishi qala ba, dan bata da abun cewa.
D'aya daga cikin rigunan baccin ya ďauka ya mika mata ya daďa ďaure fiskarshi tamau.
"Wannan zaki saka kafin ki kwanta, oya."
Karb'a tayi tana jujjuya rigar, ganin haka yasa shi fita.
Ware rigar tayi dakyau tana kallo, doguwace silk tana da kauri, saidai hanun vest ce da ita.
Sauri sauri ta cire rigar jikinta ta zura shi, ta ďau hijabinta ta saka ta ci gaba da zama a wajen, a hakan har bacci b'arawo ya sureta ta b'ingire kan carpet.
~Jinya biyu aka komayi cikin asibitin, ga yusufa ga Hamma shehu, iyayen suma saida suka iso suka ji labarin babban tashin hankalin da ya samesu na b'atan Deejah.
Babanta kam karfin addu'a ne ya hanashi samun tab'in hankali, dan itace mafi soyuwa a cikin 'ya'yanshi, kasancewar mahaifiyarta ta rasu tun tana jinjira.
Adda kuwa Mahaifiyarsu Hamma shehu jin b'atan Deejah saida dad'add'en hawan jininta ya tashi itama aka kaita babban asibitin dake cikin Gembu.
Kakarsu kam in banda kuka da surutai babu abunda takeyi, sai cewa take aje a nemo mata jikarta.
Kowa dai ka gani a gidan ya zama abun tausayi babu mai rarrashin wani kowa ta kansa yakeyi.
~Kwananta biyu a gidan ,duk ta rame ta zama wata iri, suk da kulawar da take samu ta fannin abinci da sutura da duk wani abun bukata, saidai ita duk ba wnn ne a gabanta ba, kullum sai ta roki matarnan da taimaka mata ta fitar da ita, ita kuwa kullum cikin rarrashi da kwantar mata da hankali takeyi da cewa nan ba da daďewa ba za a fitar da ita ta koma gidansu.
Takan ďan sake su tab'a hira da matar duk da dai ba iya hausa sosai tayi ba.
Zaman ďakinne ya isheta ganin masu gidan basa nan sai wnn matar take ta kai kawo ya sa ta fito tazo ta zauna kan corridor tana kallon yanayin gidan.
Tayi nisa cikin tunani bata ankara ba tagansu su biyu sun tunkaro inda take zaune dan ta hanyar zasu bi su shiga falo.
Qasa tayi da kai tana wasa da yatsunta dan sam bata son ganinsu.
Dukansu biyu tsura mata ido sukayi suna kallonta daga bisani bakon ya ďauke kai ya shige cikin falon.
"Ina fata ba planning na guduwa kikeyi ba kam?"
Taji tambayar kamar saukar aradu.
Girgiza kai kawai tayi alamun a'a ba tare da tayi magana ba.
Har ya wuce zai shiga sai ya dawo da baya yace "Zaman me kikeyi anan?"
Kafin tace wani abu saiga dattijuwarnan ta rike warmers na abinci tana mishi sannu da dawowa.
"Baba me yasa baki kunna mata TV ba?"
Cikin ladabi baba tace "Na kunna mata ta gaji da zaman cikinne ta fito shan iska."
Ciki ya shige ba tare da ya sake cewa komai ba, baba ta rufa mishi baya..
Saida ta qare zirga zirgarta ta dawo wajen Deeja, tace mata "Yace ki shigo kici abinci."
A hankali ta tashi ta shiga dan bata ma son ya sake zuwa ya mata magana.
Ciki ciki tayi sallama sai taji kamar an amsa mata, duk da daibmai amsawar ma a hankali ya amsa.
D'ago idon da zatayi idanunta ya sarqe da bakon da suka shigo tare dashi.
Lokaci guda taji wani irin faďuwar gaba ya ziyarceta har ta ďan daburce.
Shima kuma ta gefenshi haka abun yake dan zai iya cewa bai tab'a jin irin wnn faďuwar gaban ba.
Kawar da kanshi yayi hakan ya bata damar shigewa da sauri tamkar ana korinta.
"Ina ka samo wnn kuma scorpion."
Ya jefawa abokin nashi tambaya.
"Farautota nayi."
"Wato dai baka bar halin ba, ina gaya maka wata rana xaka farauto abunda yafi qarfin ka."
"No ba haka bane, kaima kasan na daina, wnn is different, da ka dubeta da kyau zaka fahimci abunda nake nufi, very young, beautiful, and innocent, ba irin 'yan matan da kake tunani bane."
Jinjina kai kawai yayi ya share maganar suka shiga wata chapter.
*Dorofi*
~Gida kam ya zama tamkar gidan makoki, gaisuwa kashi biyu ake zuwa yi, ga na jajen b'atan Deeja, ga kuma na marasa lafiya har guda huďu.
Hamma shehu, yusufa, Adda, sai 'Yar uwarta kuma kawarta Fa'i kanwarsu Hamma shehu..
Sauran mutan gidanma duk a sanyaye suke komai
Manyan mazanne masu taurin zcy suka dukufa da addua Allah ya bayyanata ya kuma kareta a duk inda take.
Kakarta madai gata nan ne kawai bata da magana sai na Deeja.
Sunyi reporting ana kan bincike saidai fatar Allah yasa a dace.
~Tun da suka rabu da scorpion ya koma gida tunanin yarinyar da ya gani a gidanshi ya addabe shi, haka kawai yaji yana son ya taimaka mata ya kub'utar da ita daga zalincin scorpion dan yasan halinshi sarai, bashi da kyau.
Sai ya buďe mata ido ya lalata mata rayuwa ya sata a mummunar hanya karshe ya yi dumping ďinta a wulakance.
Tabbas kamar yadda ya faďa hakan take, young, beautiful and innocent.
Juyi yake tayi ya gagara bacci sai innocent face ďinta yake mishi yawo a idon zuci.
Dakyar ya samu barci ya kwasheshi saidai mafarkanta ne kawai suka cika mishi baccin.
Washe gari haka ya wuni da tunanin mafita, duk abinda yakeyi hankalinshi da tunaninshi suna wajenta har scorpion yazo ya sameshi ya kuma isar musu da sakon ogansu yana nemansu.
"Smart baka tambayeni labarin beauty na ba."
"Waye kuma beautynka?"
Ya tambayeshi tamkar baisan abunda yake nufi ba.
"Kaifa ďan iska ne wlh, jiya jiya muje kaga yarinya kuma kana tambaya wacece beauty."
"Mtsseew wnn ai kasan matsalar kace ba tawa ba, meye haďina da ita da zan tambayeka labarinta, afterall ni gaba ďaya ma na mance da maganar ta idan ba yanzu da ka tuna min ba."
Ya qarashe zancenshi yana daquna fiska irin abin bai dameshi ba ďinnan.
Gyara zama scorpion yayi Yace "You know what smart, ina bala'in burin son ganin lucky ladyn da zatayi nasarar sace maka zuciya, gaskiya da sai nayi mata kyauta."
"Da yake ance maka na zama kai namamajo ba."
Ya bashi amsa cikin nuna halin ko in kula, snn ya kamo wata hirar daban.
12:30 suka shirya zasu haďu domi fita wani operation, hakan yasa ya kare duk wani shirinshi tun 12:00.
Saida ya tabbatar da duk suna can ta bakin wani abokinsu Nas, snn ya shiga mota ya kama hanyar gidan Scorpion.
A ďan nesa yayi parking motarshi ya qarasa da qafa, fiskarshi sanye da face mask da suke sakawa idan zasu fita operation.
Tura karamin gate ďin yayi ya shiga bs tare da yayiwa gate man magana ba, duk da yana tayi mishi barka da shigowa, hanu kawai ya ďaga mishi ya shige ciki.
Babu kowa a falon, ya leka ďakin Baba tana kwance tana ta sharar baccinta.
Face mask ďin ya cire ya karasa kofar da yaga ta shiga ďazu.
A hankali ya tura kofar.
Tana zaune ta jinginu da jikin bango a haka bacci ya kwasheta.
Gabanta yaje ya tsuguna yana karewa fiskarta kallo, zcyrshi tana daďa kwaďaita mishi son taimakonta.
Gyaran murya yayi tayi firgigit ta buďe ido tana kallonshi, ga dukkan alamu a tsorace take.
Tausayinta ta daďa ratsa shi , cikin saukar da murya yace "Kina buqatar taimako?"
Gyaďa mishi kai tayi.
Ya kuma cewa zaki bini na maida ke gida?"
Jin ya ambaci gida batasan sanda murmushi ya sub'uce mata ba.
Shima murmusawan yayi yana mai jin daďin ganin fara'a a fiskarta.
Da hanu ya mata alamar ta tashi ta biyo shi, ba gardama ta mike, sbd haka kawai taji hankalinta yafi kwanciya dashi.
Tafe yake tana binshi a baya har suka fita daga gidan suka qarasa gurin motarshi.
Buđe mata yayi ta shiga, shima ya zagaya ya shiga.
Da gudu ya figi motar ya bar wajen.
Har kofar ďakin ya rakata ta shiga sum sum kamar munafuka.
Sauri sauri gudu gudu ya fita daga gidan ya sake figar motar domin zuwa wajen meeting đinsu.
~Basu suka dawo ba saida asuba.
Daga scorpion har Baba babu wanda ya fahimci cewar Deeja bata gidan, har Baba ta kai mata abinci.
Rashin ganinta kuma baisa ta tuna komaiba dan a zatonta ko tana cikin ban ďaki ne.
Saida ya shigo dubata yaga wayam, toilet ya leka nanma haka.
Cikin tashin hankali ya fara kwalawa Baba kira.
A tamanin ta shigo ta rusuna, "Gani yallab'ai."
"Ina yarinyar nan ta shiga?"
Ya tambaya yana muzurai.
"Nima dai Yallab'ai ban ganta ba nayi tunanin ko ta zaga nema shi yasa banyi magana ba."
"Bull shit."
Ya faďa cikin karaji tare da kaiwa bango naushi.
Da sauri kuma ya fita sai gurin gate man.
A tsawace yake mishi tambayar da ta rikita mishi kwakwalwa ta kuma kaďa mishi 'ya'yan hanji.
Cikin inina yace "O..oga tun.. tun jiya da kazo ka fita da ita ban sake ganinta ba."
"What?"
Ya faďa da karfi saida gateman yaji kamar fitsari yana neman kub'uce mishi.
Cakumar wuyarshi yayi a tsawace kuma "Dan uban ubanka yaushe na fita da ita?"
Cikin rawar murya yace "Bayan fitanku kaďan dasu oga Nas naga ka shigo kun fita tare."
"You must be very stupid Sule, niďinne baza ka ba gane har wani zai shigo cikin gidannan ya sace mutum ya tafi dashi kace nine? Fuck u, Idiot."
Ya hankaďa shi da karfi saida ya bugu da gate, shi kuma ya koma cikin gida.
Tamkar tab'abb'e ya koma yana nuna Baba da yatsa yace "I swear idan yarinyar nan bata fito ba, zaku ga d other side of me."
Ya zari wayarshi ya fice.
Tab'e baki baba tayi tace "Ni nasan maka wani aswa, da oda sadami, yaran musulmai duk kun maida kanku kamar kafurai, sai zalunci.
Allah yasa ma ta samu mai cetonta ne ta koma hanun iyayenta, Allah amin."
Ta karasa adduar tana shafawa a fiskarta.
Saida ya daidaita zamanshi cikin motarshi snn ya ďaga waya ya kira Nas, ya shaida mishi abunda ya faru.
"Ka tambayi smart?"
Abunda ya fara ce mishi kenan.
"Kaima kasan smart baya wannan harkar dan ko jiya ma da na kawo mishi maganarta ce min yayi in daina damunshi dan shi ba wnn ne a gabanshi ba.
"Hakane kam, saidai inaga duk wanda yayi aikinnan sananne ne ya sanka kasanshi ya kuma san sirrin gidanka."
"Sosai ma, dole nayi bincike sbd har kaima bazan barka ba mutum ba abun yarda bane."
"Hahaha, dat's gud namiji nima zan tayaka binciken."
"And what's funny guy?"
Ya faďa a kufule.
"Nothing sha."
Nas ya faďa tare da datse kiran yana dariyar yanda abokinshi ya ruďe akan yarinya k'arama.

Tuesday, 19 March 2019


* TASHIN HANKALI *
*Written by :Mmn Abduljalal*
*Fasaha Online Writers*
*1*
~Kai kawo sukeyi a kofar ďakin cikin tashin hankali, kowa da kalar addu'ar da yakeyi cikin zcyrshi wasuma a bayyane sukeyi ba matan ba mazan ba.
Sun ďau tsawon lokaci cikin wnn hali kafin nurse ďin dake cikin ďakin ta leko da kanta tana cewa a bata zani.

Cikin rawar jiki wacce ake kira da Dadayi ta ruga tayi cikin ďakinta ta ďauko ta zo mikawa nurse ďin.
Ba da jimawa ba ta umarci dadayi da ta shigo ďakin.
A tare suka gyara gurin da gurin tare da gyara 'yar matashiyar budurwar da ta haihu bayan dogon wahalar da tasha.
Tsab suka gyaresu tare da jinjirin, kato dashi fari tass, saidai ya galabaita sosai sbd wuyar da yasha shima.
Godiya suka rika kwararowa nurse ďin cikin harshen fullanci kasancewar shine yaren da sukeyi dukansu.
Duk da nurse ďin ba musulma bace amma tana jin fulatanci sosai saboda cuďanyar da takeyi da fulanin garin duk dai dukkan qabilun kauyen suna jin fullanci sosai.
Rige rigen shiga sukeyi bayan an kare gyarata har nurse ďin ta tafi dan ganin abinda aka haifa da kuma lfyr uwar.
Kwanciya tayi ta rufe idanunta ruff tamkar mai bacci duk bidirin da sukeyi cikin ďakin baisa ta buďe idanunta ba.
Maganganu ke tashi kala kala cikin matan ďaya ma kuka takeyi tana surutai.
"Kul, kul, Salamatu na hanaki sauri tsinuwa, ki daina, idan bazakiyi adduar shiriya ga mutum ba kiyi shiru da bakinki.
D'a na kowa ne, bakisan dalilin da yasashi cikin wnn halin ba kuma baki san kaddarar da ta jawo dalilin samuwar wnn ďan ba, kiyi mishi adduar shiriya kawai.
Share hawayenta tayi tana barin ďakin sbd maganar dattijon mijinta karyar mata da zcy kuma tasan idan tana tsaye wajen magana dole tayi shi dan cutarwar tayi yawa, sosai take jin bakin cikin abinda ya faru kan 'yar tasu, snn ko da yaushe ta tashi zagin macucin sai maigidanta ya taka mata birki da cewar adduar shiriya ya kamata tayi masa ba zagi, mummunan fata ko tsinuwa ba.
Itama kanta dadayi daurewa takeyi sbd zafi da zogin da takeji a ranta kuma ba damar magana.
Mika mata yaron sukayi suka fita daga ďakin, suka barta da mai jego.
Ta jima tsaye tana mata kallon tausayi kafin ta kwantar mata da yaron kusa da ita ta fita domin ďora ruwan zafin da zatayi ma mai jego wanka.
Tana fita ta tarar da har Salamatu wacce suke kira da adda ta ďora ruwan, ďayar matar da suke kira da Addamari tana share gidan, sbd tun safe basu samu sukunin yin aikin kirki ba dan tashin hankalin da suke ciki.
Sannu ta mata kafin ta tattari kayan da mai haihuwar ta b'ata ta zagaya ta baya dan wankewa.
Bayan fitarsu ba da jimawa ba ta buďe idonta a hankali ta tashi tana cije leb'e.
Kurawa yaron ido tayi tana mamakin kamannin da ta gani a tare dashi, duk da taji iyayenta sun tanka a kan hakan saidai batayi tsammani kamar ta fito har haka ba.
A hankali ta janyo filo ta ďora kan yaron da nufin ta danneshi ya mutu ta huta da abin kunya.
A take zcyrta ta mata tambaya "Kisan kai fa zakiyi, Laifin me ya miki shi kuma Deeja, me zaki cewa Ubangijinki ranar gobe qiyama?"
A sanyaye ta janye filon ta mayar mazauninta taci gaba da kallon jinjirin da ke kwance baya ko motsin kirki.
Sallamar da taji yasa tayi saurin zamewa ta kwanta.
"Sannu Hadiza am."
Buďe idonta tayi ta kalleshi, kamar zata rusa kuka tace "Sannu Hamma am."
"Zaki iya tashi?"
Ya tambayeta da kulawa.
kai ta gyaďa mishi ba tare da ta yarda sun sake haďa ido ba.
A tsanake ta tashi ta zauna kanta a qasa.
"Banishi in kalleshi."
Kasa ta kuma yi da kanta.
Tashi yayi daga inda yake zauna ya dawo baki gadon ya durkusa yana kallon yaron da baiga alamun zata mika mishi shi ba.
"Ikon Allah, Hadiza kinga abunda na gani?"
Ya tambaya cike da mamaki.
Kwalla ta share tana gyaďa kai dan ta fahimci inda tambayarshi ta dosa.
Shima share kwallar yayi yana mai tuna cewa yanzu da badon kaddara ta faďa musu ba da yanzu wnn ďanshine, gashi abin mamaki kuma yaron kama yake dashi tamkar shine ubanshi.
Cikin sanyin jiki ya tashi ya ďauko ledar da ya shigo dashi ya ajiye mata ya fita.
Ba da jimawa ba Dadayi ta shigo da kunun kanwa cikin kwanon sha ta ajiye kusa da ita tana ce mata.
"Deeja tashi kisha da zafi zafinshi kada yayi sanyi."
Tana maganar tana buďe ledar da ta gani kusa da ita.
Balangu ta gani cikin ledar hakan yasa ta fita ta ďau kwano ta juye mata tana umartarta da taci maza ta fito ayi mata wanka.
Fitowarta daga wanka ta samu adda zaune rike da yaron tana kallonshi shi kuwa sai tsala kuka yakeyi itama addan sharar kwalla takeyi kaďan kaďan.
Zuwa yanzu shima yaron anyi mishi wanka an suturta shi da kayan sanyi mai k'auri an kuma lullub'e shi ruff, ga kuma gaushin da aka haďa a kasko yana ďuma ďakin sbd sanyin dake garin.
"Maza zo ki bashi abincin shi yunwa ke sashi wnn kukan."
Cewar adda tana mika mata yaron.
Saida ta zura riga snn ta ja kujera 'yar tsuguno ta zauna ba tare da ta kalli addanba.
Kan cinyarta ta ajiye mata shi ta fice daga ďakin dan tasan ba bashi zatayi a gabanta ba.
Sosai ta kure yaron da ido tana kallon tsantsar kamar da sukayi da Hamma Shehu.
Tunani ta fara na yadda kaddara ta afka musu ana saura sati biyu ďaurin aurenta da Hamma Shehu.
*Tuna Baya*
Cikin motar haya suke zaune a hanyarsu ta zuwa kauyen kawunanta sunkani daga asalin qauyen mahaifanta Dorofi dake cikin Gembu, domin ta kai musu ziyara kafin tayi aure.
Ita da kaninta mai bi mata sukayi wnn tafiyar.
Surutu ake ta zubawa cikin motar babu kakkautawa, wasu da harshen fillanci wasu da Mambilanci, wasu Hausa.
Sunyi nisa a tafiyar har Deejah ta fara gyangyaďi, kasancewa kusa da kaninta take zaune, ta kwantar da kanta kan kafaďarshi.
Bugu yake shirin kai mata sbd ya gaji , har ya ďaga hanu kafin ya isar yaji qarar bindiga tauu wanda ya haddasawa driver taka birkin da bai shirya, yawancin passengers suka wuntsila gaba suka sake komawa mazauninsu da karfi wasu har suna karo da juna wasu ko suna gwara kansu da jikin motar.
A razane ta ďago tana kallonshi.
"Yusufa menene?"
Daga masu salati a motar sai masu kiran jesus, sai masu cewa Yesu kristi, haka motar ta cika da hayaniya.
Kafin ya bata amsa
Tauu, suka kuma jin wata karar, tsitt kakeji cikin motar tamkar babu mai rai a ciki.
Gamm Deeja ta damke kaninta yusufa sai zare idanu takeyi, shi kuwa sai faman lekawa yake ko zai ga abunda yake faruwa.
Wata murya mai tsoratarwa ta ratsa dodon kunnensu inda ake umartarsu da duk su fito.
Take jikin Deeja ya ďau b'ari tuni ta fara hawaye dan tasan yau kam saita Allah, sbd ta fahimci 'yan fashin da takejin labarine itama yau tayi karo dasu.
A tsorace suke fitowa daga motar har aka zo kan deejan dake kankame da kaninta gamm jikinta sai rawa yakeyi.
Kallo ďaya ta musu ta sadda kai qasa, dukkansu biyar sanye suke da face mask.
Umartarsu akayi da su kwanta, ba tare da bata lokaci ba daga driver har passengers suka mimmike flat a qasa.
Deeja kam da kaninta a jere suke kwance kuma har yanzu bata sake shi ba.
Bincikar motarsu suka shigayi suka kwashi abunda zasu kwasa suka koma lalubar aljifai.
Suna nan kwance deeja taji ansa hanu an ďago ta, ba shiri ta sake tamke kaninta wanda shima ya tashi a firgice ya rikota riko mai kyau kuwa.
Ďaya daga cikin 'yan fashinne ya ďagota, ganin yanda suka rike juna, ya sashi fara b'anb'arar hanun deeja daga jikin yusufa.
Cikin tashin hankali ya kare damkarta yana bada hakuri dukansu kuka sukeyi.
Da karfin tsiya ya rabasu ya janye deeja daga wajen, ya fara nufar cikin daji da ita, hakan yasa suka kwalla kara a tare da yusufa, a guje kuma ya je ya rikota yana dađa bada hakuri.
Ganin zai b'ata musu lokaci yasa ďan fashin kwaďa mishi gindin bindiga sai da ya faďi kasa, ya jata yayi gaba da ita.
Dishi dishi yusufa ya fara gani sbd yanda jini yake fitowa daga kanshi, jakan kuma bai hanashi yunkurin tashiba saidai kuma a halin yanzu bashi da wani karfi sbd jiri dake ďibarshi, saidai mika mata hanu da yakeyi yana kiranta.
Itama kuma waigenshi takeyi tana mika mishi hanun tare da gursheken kuka sbd ganin suna ji suna gani za a rabasu.
Dafe kanshi yayi ya zube a wajen ganin sun b'acewa ganinshi.
Kuka takeyi tana kiran Yusufa har muryarta ta dishe.
Sunyi nisa sosai cikin dajin kafin suka isa inda suka b'oye motocinsu guda biyu.
Cikin mota ya turata ya shiga gefen driver ya zauna tare da kulle motar.
Buga gilashin motar takeyi tana kuka da disasshiyar muryarta har saida ya gaji ya daka mata gigitacciyar tsawar da ya tilasta mata haďiye kukanta.
Saida suka qare operation ďinsu kafin suka iso suka samesu a gurin.
Uku daga ciki suka shiga waccar motar sukayi gaba, sai ďaya da ya shiga motar su deeja suka take musu baya.
Tafiya mai nisa sukayi, deeja duk ta gaji da zaman ko ina na jikinta ciwo yake mata ga idanunta duk sun kumbura sbd kukan da tasha ba kaďan ba, har yanzu kuma bata bar zubar da hawaye ba, baranma idan ta tuna halin da tabar Yusufanta ciki.
A can kuma, 'yan fashin suna tafiya sauran jama'an suka yo kan Yusufa da jini ya wanke wa fiska har jikinshi.
Ba b'ata lokaci aka tattareshi aka karasa dashi asibitin dake garin Bali dan shi yafi kusa dasu.
Tashin hankali ba kaďan ba iyaye da 'yan uwa suka shiga lkcin da suka samu labarin Yusufa yana asibiti nanma dan an ce musu hatsari suka samu basu san ainihin abunda ya faru ba.
Hamma shehu da kaninshi Ali suka fara zuwa asibitin, sun samu an sa mishi karin jini yana bacci, saidai basu ga alamar Deeja cikin asibitin ba.
Ko da suka tambayi likitocin suka tabbatar musu da cewa shi kaďai aka kawo.
Haka suka zauna suna jiran farkawarshi cikn rashin kwanciyar hankali.
~ Cikin gudu na tashin hankali Allah ya isar dasu lfy.
Wani tamfatsetsen gida motar ta shiga a guje dan sun raba hanya da ďaya motar.
Umartarta sukayi da ta fito, suka nufi wani tangamemen falo wanda yasha kayan alatu na more rayuwa.
Suna shiga suka umarceta da ta zauna kada kuma tayi gigin fita dan akwai karnuka masu haďari a gidan.
Cusa kanta tayi cikin cinyoyin ta ta dasa wani sabon kukan, har suka fita bata sani ba, saida wata dattijuwar mata ta kawo mata abinci tana mata magana, jin muryar mace 'yar uwarta yasata ďago nan tasan basa ma cikin falon.
Cikin tausayawa matar take kallonta, "Sannu yarinya."
Gyaďa mata kai kawai tayi batayi magana ba."
"Ci abinci yarinya, kinji."
"Mama ka taimakeni ka fitar dani a gidannan."
Ta faďa da muryarta da bata fita sosai wasu sabbin hawaye suna daďa surnano mata.
"Ci abinci to sai musan yanda zamuyi."
Ta fađi hakanne kawai dan ta kwantar mata da hankali, amma ita kanta tasan bata isa ta kub'utar da ita saidai idan Allah ne yaso hakan, tunda itama tana ji tana gani aka rabo ta da 'ya'yanta da danginta, tazo tana musu bauta babu kuma hanyar kub'uta.
~Sun jima zaune a gun kafin ya farka da kiran Adda Deeja, da iyakan karfin muryarshi yana mika hanu.
Rikon da suka mishine yasashi bud'e idanunshi, ganin yayyunshi ke rike dashi ya fara yunkurin tashi suka maidashi.
"B'e dillidi be mako."
Ma'ana :Sun tafi da ita.
Yake maimaitawa yana girgiza kanshi cikin tashin hankali.
Sai kuma yayi saurin rike kan ya rintse idanun shi sbd wani irin ciwo da yaji kan yana mishi.
Mayar dashi Ali yayi ya kwantar yayin da dukkansu hankali tashe suke tambayarshi da wa aka tafi.
"Adda Deeja."
Ya amsa musu cikin matsanancin kuka.
A kiďime Ali yace "Su waye suka tafi da ita."
Kafin ya bada amsa sai karar faďuwar Hamma shehu suka ji.
Sake Yusufa yayi ya koma kan Hamma shehu yana jijjigashi amma ina, yayi nisa.
Cikin b'acewar baseera da dabara ya dab'ashe a wajen ya fashe da wani irin kuka mai tab'a zuciya.......

BTemplates.com

Popular Posts