Saturday, 6 April 2019

* TASHIN HANKALI * *Written by :Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *1* ~Kai kawo sukeyi a kofar ďakin cikin tashin hankali, kowa da kalar addu'ar da yakeyi cikin zcyrshi wasuma a bayyane sukeyi ba matan ba mazan ba. Sun ďau tsawon lokaci cikin wnn hali kafin nurse ďin dake cikin ďakin ta leko da kanta tana cewa a bata zani. Cikin rawar jiki wacce ake kira da Dadayi ta ruga tayi cikin ďakinta ta ďauko ta zo mikawa nurse ďin. Ba da jimawa ba ta umarci dadayi da ta shigo ďakin. A tare suka gyara gurin da gurin tare da gyara 'yar matashiyar budurwar da ta haihu bayan dogon wahalar da tasha. Tsab suka gyaresu tare da jinjirin, kato dashi fari tass, saidai ya galabaita sosai sbd wuyar da yasha shima. Godiya suka rika kwararowa nurse ďin cikin harshen fullanci kasancewar shine yaren da sukeyi dukansu. Duk da nurse ďin ba musulma bace amma tana jin fulatanci sosai saboda cuďanyar da takeyi da fulanin garin duk dai dukkan qabilun kauyen suna jin fullanci sosai. Rige rigen shiga sukeyi bayan an kare gyarata har nurse ďin ta tafi dan ganin abinda aka haifa da kuma lfyr uwar. Kwanciya tayi ta rufe idanunta ruff tamkar mai bacci duk bidirin da sukeyi cikin ďakin baisa ta buďe idanunta ba. Maganganu ke tashi kala kala cikin matan ďaya ma kuka takeyi tana surutai. "Kul, kul, Salamatu na hanaki sauri tsinuwa, ki daina, idan bazakiyi adduar shiriya ga mutum ba kiyi shiru da bakinki. D'a na kowa ne, bakisan dalilin da yasashi cikin wnn halin ba kuma baki san kaddarar da ta jawo dalilin samuwar wnn ďan ba, kiyi mishi adduar shiriya kawai. Share hawayenta tayi tana barin ďakin sbd maganar dattijon mijinta karyar mata da zcy kuma tasan idan tana tsaye wajen magana dole tayi shi dan cutarwar tayi yawa, sosai take jin bakin cikin abinda ya faru kan 'yar tasu, snn ko da yaushe ta tashi zagin macucin sai maigidanta ya taka mata birki da cewar adduar shiriya ya kamata tayi masa ba zagi, mummunan fata ko tsinuwa ba. Itama kanta dadayi daurewa takeyi sbd zafi da zogin da takeji a ranta kuma ba damar magana. Mika mata yaron sukayi suka fita daga ďakin, suka barta da mai jego. Ta jima tsaye tana mata kallon tausayi kafin ta kwantar mata da yaron kusa da ita ta fita domin ďora ruwan zafin da zatayi ma mai jego wanka. Tana fita ta tarar da har Salamatu wacce suke kira da adda ta ďora ruwan, ďayar matar da suke kira da Addamari tana share gidan, sbd tun safe basu samu sukunin yin aikin kirki ba dan tashin hankalin da suke ciki. Sannu ta mata kafin ta tattari kayan da mai haihuwar ta b'ata ta zagaya ta baya dan wankewa. Bayan fitarsu ba da jimawa ba ta buďe idonta a hankali ta tashi tana cije leb'e. Kurawa yaron ido tayi tana mamakin kamannin da ta gani a tare dashi, duk da taji iyayenta sun tanka a kan hakan saidai batayi tsammani kamar ta fito har haka ba. A hankali ta janyo filo ta ďora kan yaron da nufin ta danneshi ya mutu ta huta da abin kunya. A take zcyrta ta mata tambaya "Kisan kai fa zakiyi, Laifin me ya miki shi kuma Deeja, me zaki cewa Ubangijinki ranar gobe qiyama?" A sanyaye ta janye filon ta mayar mazauninta taci gaba da kallon jinjirin da ke kwance baya ko motsin kirki. Sallamar da taji yasa tayi saurin zamewa ta kwanta. "Sannu Hadiza am." Buďe idonta tayi ta kalleshi, kamar zata rusa kuka tace "Sannu Hamma am." "Zaki iya tashi?" Ya tambayeta da kulawa. kai ta gyaďa mishi ba tare da ta yarda sun sake haďa ido ba. A tsanake ta tashi ta zauna kanta a qasa. "Banishi in kalleshi." Kasa ta kuma yi da kanta. Tashi yayi daga inda yake zauna ya dawo baki gadon ya durkusa yana kallon yaron da baiga alamun zata mika mishi shi ba. "Ikon Allah, Hadiza kinga abunda na gani?" Ya tambaya cike da mamaki. Kwalla ta share tana gyaďa kai dan ta fahimci inda tambayarshi ta dosa. Shima share kwallar yayi yana mai tuna cewa yanzu da badon kaddara ta faďa musu ba da yanzu wnn ďanshine, gashi abin mamaki kuma yaron kama yake dashi tamkar shine ubanshi. Cikin sanyin jiki ya tashi ya ďauko ledar da ya shigo dashi ya ajiye mata ya fita. Ba da jimawa ba Dadayi ta shigo da kunun kanwa cikin kwanon sha ta ajiye kusa da ita tana ce mata. "Deeja tashi kisha da zafi zafinshi kada yayi sanyi." Tana maganar tana buďe ledar da ta gani kusa da ita. Balangu ta gani cikin ledar hakan yasa ta fita ta ďau kwano ta juye mata tana umartarta da taci maza ta fito ayi mata wanka. Fitowarta daga wanka ta samu adda zaune rike da yaron tana kallonshi shi kuwa sai tsala kuka yakeyi itama addan sharar kwalla takeyi kaďan kaďan. Zuwa yanzu shima yaron anyi mishi wanka an suturta shi da kayan sanyi mai k'auri an kuma lullub'e shi ruff, ga kuma gaushin da aka haďa a kasko yana ďuma ďakin sbd sanyin dake garin. "Maza zo ki bashi abincin shi yunwa ke sashi wnn kukan." Cewar adda tana mika mata yaron. Saida ta zura riga snn ta ja kujera 'yar tsuguno ta zauna ba tare da ta kalli addanba. Kan cinyarta ta ajiye mata shi ta fice daga ďakin dan tasan ba bashi zatayi a gabanta ba. Sosai ta kure yaron da ido tana kallon tsantsar kamar da sukayi da Hamma Shehu. Tunani ta fara na yadda kaddara ta afka musu ana saura sati biyu ďaurin aurenta da Hamma Shehu. *Tuna Baya* Cikin motar haya suke zaune a hanyarsu ta zuwa kauyen kawunanta sunkani daga asalin qauyen mahaifanta Dorofi dake cikin Gembu, domin ta kai musu ziyara kafin tayi aure. Ita da kaninta mai bi mata sukayi wnn tafiyar. Surutu ake ta zubawa cikin motar babu kakkautawa, wasu da harshen fillanci wasu da Mambilanci, wasu Hausa. Sunyi nisa a tafiyar har Deejah ta fara gyangyaďi, kasancewa kusa da kaninta take zaune, ta kwantar da kanta kan kafaďarshi. Bugu yake shirin kai mata sbd ya gaji , har ya ďaga hanu kafin ya isar yaji qarar bindiga tauu wanda ya haddasawa driver taka birkin da bai shirya, yawancin passengers suka wuntsila gaba suka sake komawa mazauninsu da karfi wasu har suna karo da juna wasu ko suna gwara kansu da jikin motar. A razane ta ďago tana kallonshi. "Yusufa menene?" Daga masu salati a motar sai masu kiran jesus, sai masu cewa Yesu kristi, haka motar ta cika da hayaniya. Kafin ya bata amsa Tauu, suka kuma jin wata karar, tsitt kakeji cikin motar tamkar babu mai rai a ciki. Gamm Deeja ta damke kaninta yusufa sai zare idanu takeyi, shi kuwa sai faman lekawa yake ko zai ga abunda yake faruwa. Wata murya mai tsoratarwa ta ratsa dodon kunnensu inda ake umartarsu da duk su fito. Take jikin Deeja ya ďau b'ari tuni ta fara hawaye dan tasan yau kam saita Allah, sbd ta fahimci 'yan fashin da takejin labarine itama yau tayi karo dasu. A tsorace suke fitowa daga motar har aka zo kan deejan dake kankame da kaninta gamm jikinta sai rawa yakeyi. Kallo ďaya ta musu ta sadda kai qasa, dukkansu biyar sanye suke da face mask. Umartarsu akayi da su kwanta, ba tare da bata lokaci ba daga driver har passengers suka mimmike flat a qasa. Deeja kam da kaninta a jere suke kwance kuma har yanzu bata sake shi ba. Bincikar motarsu suka shigayi suka kwashi abunda zasu kwasa suka koma lalubar aljifai. Suna nan kwance deeja taji ansa hanu an ďago ta, ba shiri ta sake tamke kaninta wanda shima ya tashi a firgice ya rikota riko mai kyau kuwa. Ďaya daga cikin 'yan fashinne ya ďagota, ganin yanda suka rike juna, ya sashi fara b'anb'arar hanun deeja daga jikin yusufa. Cikin tashin hankali ya kare damkarta yana bada hakuri dukansu kuka sukeyi. Da karfin tsiya ya rabasu ya janye deeja daga wajen, ya fara nufar cikin daji da ita, hakan yasa suka kwalla kara a tare da yusufa, a guje kuma ya je ya rikota yana dađa bada hakuri. Ganin zai b'ata musu lokaci yasa ďan fashin kwaďa mishi gindin bindiga sai da ya faďi kasa, ya jata yayi gaba da ita. Dishi dishi yusufa ya fara gani sbd yanda jini yake fitowa daga kanshi, jakan kuma bai hanashi yunkurin tashiba saidai kuma a halin yanzu bashi da wani karfi sbd jiri dake ďibarshi, saidai mika mata hanu da yakeyi yana kiranta. Itama kuma waigenshi takeyi tana mika mishi hanun tare da gursheken kuka sbd ganin suna ji suna gani za a rabasu. Dafe kanshi yayi ya zube a wajen ganin sun b'acewa ganinshi. Kuka takeyi tana kiran Yusufa har muryarta ta dishe. Sunyi nisa sosai cikin dajin kafin suka isa inda suka b'oye motocinsu guda biyu. Cikin mota ya turata ya shiga gefen driver ya zauna tare da kulle motar. Buga gilashin motar takeyi tana kuka da disasshiyar muryarta har saida ya gaji ya daka mata gigitacciyar tsawar da ya tilasta mata haďiye kukanta. Saida suka qare operation ďinsu kafin suka iso suka samesu a gurin. Uku daga ciki suka shiga waccar motar sukayi gaba, sai ďaya da ya shiga motar su deeja suka take musu baya. Tafiya mai nisa sukayi, deeja duk ta gaji da zaman ko ina na jikinta ciwo yake mata ga idanunta duk sun kumbura sbd kukan da tasha ba kaďan ba, har yanzu kuma bata bar zubar da hawaye ba, baranma idan ta tuna halin da tabar Yusufanta ciki. A can kuma, 'yan fashin suna tafiya sauran jama'an suka yo kan Yusufa da jini ya wanke wa fiska har jikinshi. Ba b'ata lokaci aka tattareshi aka karasa dashi asibitin dake garin Bali dan shi yafi kusa dasu. Tashin hankali ba kaďan ba iyaye da 'yan uwa suka shiga lkcin da suka samu labarin Yusufa yana asibiti nanma dan an ce musu hatsari suka samu basu san ainihin abunda ya faru ba. Hamma shehu da kaninshi Ali suka fara zuwa asibitin, sun samu an sa mishi karin jini yana bacci, saidai basu ga alamar Deeja cikin asibitin ba. Ko da suka tambayi likitocin suka tabbatar musu da cewa shi kaďai aka kawo. Haka suka zauna suna jiran farkawarshi cikn rashin kwanciyar hankali. ~ Cikin gudu na tashin hankali Allah ya isar dasu lfy. Wani tamfatsetsen gida motar ta shiga a guje dan sun raba hanya da ďaya motar. Umartarta sukayi da ta fito, suka nufi wani tangamemen falo wanda yasha kayan alatu na more rayuwa. Suna shiga suka umarceta da ta zauna kada kuma tayi gigin fita dan akwai karnuka masu haďari a gidan. Cusa kanta tayi cikin cinyoyin ta ta dasa wani sabon kukan, har suka fita bata sani ba, saida wata dattijuwar mata ta kawo mata abinci tana mata magana, jin muryar mace 'yar uwarta yasata ďago nan tasan basa ma cikin falon. Cikin tausayawa matar take kallonta, "Sannu yarinya." Gyaďa mata kai kawai tayi batayi magana ba." "Ci abinci yarinya, kinji." "Mama ka taimakeni ka fitar dani a gidannan." Ta faďa da muryarta da bata fita sosai wasu sabbin hawaye suna daďa surnano mata. "Ci abinci to sai musan yanda zamuyi." Ta fađi hakanne kawai dan ta kwantar mata da hankali, amma ita kanta tasan bata isa ta kub'utar da ita saidai idan Allah ne yaso hakan, tunda itama tana ji tana gani aka rabo ta da 'ya'yanta da danginta, tazo tana musu bauta babu kuma hanyar kub'uta. ~Sun jima zaune a gun kafin ya farka da kiran Adda Deeja, da iyakan karfin muryarshi yana mika hanu. Rikon da suka mishine yasashi bud'e idanunshi, ganin yayyunshi ke rike dashi ya fara yunkurin tashi suka maidashi. "B'e dillidi be mako." Ma'ana :Sun tafi da ita. Yake maimaitawa yana girgiza kanshi cikin tashin hankali. Sai kuma yayi saurin rike kan ya rintse idanun shi sbd wani irin ciwo da yaji kan yana mishi. Mayar dashi Ali yayi ya kwantar yayin da dukkansu hankali tashe suke tambayarshi da wa aka tafi. "Adda Deeja." Ya amsa musu cikin matsanancin kuka. A kiďime Ali yace "Su waye suka tafi da ita." Kafin ya bada amsa sai karar faďuwar Hamma shehu suka ji. Sake Yusufa yayi ya koma kan Hamma shehu yana jijjigashi amma ina, yayi nisa. Cikin b'acewar baseera da dabara ya dab'ashe a wajen ya fashe da wani irin kuka mai tab'a zuciya....... * TASHIN HANKALI * *Written by :Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *2* ~Sai dare wajen karfe tara suka dawo, lokacin tana cikin ďakin da aka bata, taci kuka ta koshi, hawayen har sun kafe, tana zaune kan đan kwalinta da tayi sallah, ba abunda takeyi sai tunanin gida da halin da kaninta yusufa yake ciki. Turo kofar da akayi ya haddasa mata faďuwar gaba. Bata ďago ba har ya qaraso ya tsuguna yana kare mata kallo. "Yar fulani, kinci abinci?" Gyaďa mishi kai kawai tayi. "Wanka fa?" Qasa tayi da kai ba magana. "Ga wnn, ki shiga kiyi wanka kizo ki canza." Duk da ba jin hausan sosai takeyi ba amma tana fahimtar abinda yake cewa dan tana tsintar daďďaya. Fitar da kayan ya fara yi yana nuna mata su, ya ware mata na bacci daban, da na sawa a cikin gida, sai kayan kwalliya da turaruka, sai takalma guda biyu flat shoes. Kallon kayan takeyi amma sam bata fahimtar abunda yake faďa sbd nisan da hankalinta yayi. Sai da ya tab'ota ta kalleshi a firgice sai kuma tayi saurin dukar da kai . "Nace ki tashi kije kiyi wanka,." Ya faďa a ďan kausashe. Da saurinta ta tashi ta shige ban ďakin. Kasancewar matannan ta nuna yanda zata yi amfani da komai bata wani sha wahala ba tayi wankan, ta maida kayan da ta cire. Ta jima tana tsaye cikin toilet ďin, duk a tunaninta ko yana cikin ďaki. Daga karshe ta gaji da tsayuwar ta ďan bude ta leka. Ganin baya ciki yasa ta saurin fitowa. Zama ta kuma yi ta jingina da jikin bango ta lumshe idanunta da suke mata wani irin tsami. Shigowarshi yasa ta bud'e idanun tana mishi kallon kasan ido sbd sam bata so yasan ma tana kallonshi. "Ya kika maida kayan?" Bata ce mishi qala ba, dan bata da abun cewa. D'aya daga cikin rigunan baccin ya ďauka ya mika mata ya daďa ďaure fiskarshi tamau. "Wannan zaki saka kafin ki kwanta, oya." Karb'a tayi tana jujjuya rigar, ganin haka yasa shi fita. Ware rigar tayi dakyau tana kallo, doguwace silk tana da kauri, saidai hanun vest ce da ita. Sauri sauri ta cire rigar jikinta ta zura shi, ta ďau hijabinta ta saka ta ci gaba da zama a wajen, a hakan har bacci b'arawo ya sureta ta b'ingire kan carpet. ~Jinya biyu aka komayi cikin asibitin, ga yusufa ga Hamma shehu, iyayen suma saida suka iso suka ji labarin babban tashin hankalin da ya samesu na b'atan Deejah. Babanta kam karfin addu'a ne ya hanashi samun tab'in hankali, dan itace mafi soyuwa a cikin 'ya'yanshi, kasancewar mahaifiyarta ta rasu tun tana jinjira. Adda kuwa Mahaifiyarsu Hamma shehu jin b'atan Deejah saida dad'add'en hawan jininta ya tashi itama aka kaita babban asibitin dake cikin Gembu. Kakarsu kam in banda kuka da surutai babu abunda takeyi, sai cewa take aje a nemo mata jikarta. Kowa dai ka gani a gidan ya zama abun tausayi babu mai rarrashin wani kowa ta kansa yakeyi. ~Kwananta biyu a gidan ,duk ta rame ta zama wata iri, suk da kulawar da take samu ta fannin abinci da sutura da duk wani abun bukata, saidai ita duk ba wnn ne a gabanta ba, kullum sai ta roki matarnan da taimaka mata ta fitar da ita, ita kuwa kullum cikin rarrashi da kwantar mata da hankali takeyi da cewa nan ba da daďewa ba za a fitar da ita ta koma gidansu. Takan ďan sake su tab'a hira da matar duk da dai ba iya hausa sosai tayi ba. Zaman ďakinne ya isheta ganin masu gidan basa nan sai wnn matar take ta kai kawo ya sa ta fito tazo ta zauna kan corridor tana kallon yanayin gidan. Tayi nisa cikin tunani bata ankara ba tagansu su biyu sun tunkaro inda take zaune dan ta hanyar zasu bi su shiga falo. Qasa tayi da kai tana wasa da yatsunta dan sam bata son ganinsu. Dukansu biyu tsura mata ido sukayi suna kallonta daga bisani bakon ya ďauke kai ya shige cikin falon. "Ina fata ba planning na guduwa kikeyi ba kam?" Taji tambayar kamar saukar aradu. Girgiza kai kawai tayi alamun a'a ba tare da tayi magana ba. Har ya wuce zai shiga sai ya dawo da baya yace "Zaman me kikeyi anan?" Kafin tace wani abu saiga dattijuwarnan ta rike warmers na abinci tana mishi sannu da dawowa. "Baba me yasa baki kunna mata TV ba?" Cikin ladabi baba tace "Na kunna mata ta gaji da zaman cikinne ta fito shan iska." Ciki ya shige ba tare da ya sake cewa komai ba, baba ta rufa mishi baya.. Saida ta qare zirga zirgarta ta dawo wajen Deeja, tace mata "Yace ki shigo kici abinci." A hankali ta tashi ta shiga dan bata ma son ya sake zuwa ya mata magana. Ciki ciki tayi sallama sai taji kamar an amsa mata, duk da daibmai amsawar ma a hankali ya amsa. D'ago idon da zatayi idanunta ya sarqe da bakon da suka shigo tare dashi. Lokaci guda taji wani irin faďuwar gaba ya ziyarceta har ta ďan daburce. Shima kuma ta gefenshi haka abun yake dan zai iya cewa bai tab'a jin irin wnn faďuwar gaban ba. Kawar da kanshi yayi hakan ya bata damar shigewa da sauri tamkar ana korinta. "Ina ka samo wnn kuma scorpion." Ya jefawa abokin nashi tambaya. "Farautota nayi." "Wato dai baka bar halin ba, ina gaya maka wata rana xaka farauto abunda yafi qarfin ka." "No ba haka bane, kaima kasan na daina, wnn is different, da ka dubeta da kyau zaka fahimci abunda nake nufi, very young, beautiful, and innocent, ba irin 'yan matan da kake tunani bane." Jinjina kai kawai yayi ya share maganar suka shiga wata chapter. *Dorofi* ~Gida kam ya zama tamkar gidan makoki, gaisuwa kashi biyu ake zuwa yi, ga na jajen b'atan Deeja, ga kuma na marasa lafiya har guda huďu. Hamma shehu, yusufa, Adda, sai 'Yar uwarta kuma kawarta Fa'i kanwarsu Hamma shehu.. Sauran mutan gidanma duk a sanyaye suke komai Manyan mazanne masu taurin zcy suka dukufa da addua Allah ya bayyanata ya kuma kareta a duk inda take. Kakarta madai gata nan ne kawai bata da magana sai na Deeja. Sunyi reporting ana kan bincike saidai fatar Allah yasa a dace. ~Tun da suka rabu da scorpion ya koma gida tunanin yarinyar da ya gani a gidanshi ya addabe shi, haka kawai yaji yana son ya taimaka mata ya kub'utar da ita daga zalincin scorpion dan yasan halinshi sarai, bashi da kyau. Sai ya buďe mata ido ya lalata mata rayuwa ya sata a mummunar hanya karshe ya yi dumping ďinta a wulakance. Tabbas kamar yadda ya faďa hakan take, young, beautiful and innocent. Juyi yake tayi ya gagara bacci sai innocent face ďinta yake mishi yawo a idon zuci. Dakyar ya samu barci ya kwasheshi saidai mafarkanta ne kawai suka cika mishi baccin. Washe gari haka ya wuni da tunanin mafita, duk abinda yakeyi hankalinshi da tunaninshi suna wajenta har scorpion yazo ya sameshi ya kuma isar musu da sakon ogansu yana nemansu. "Smart baka tambayeni labarin beauty na ba." "Waye kuma beautynka?" Ya tambayeshi tamkar baisan abunda yake nufi ba. "Kaifa ďan iska ne wlh, jiya jiya muje kaga yarinya kuma kana tambaya wacece beauty." "Mtsseew wnn ai kasan matsalar kace ba tawa ba, meye haďina da ita da zan tambayeka labarinta, afterall ni gaba ďaya ma na mance da maganar ta idan ba yanzu da ka tuna min ba." Ya qarashe zancenshi yana daquna fiska irin abin bai dameshi ba ďinnan. Gyara zama scorpion yayi Yace "You know what smart, ina bala'in burin son ganin lucky ladyn da zatayi nasarar sace maka zuciya, gaskiya da sai nayi mata kyauta." "Da yake ance maka na zama kai namamajo ba." Ya bashi amsa cikin nuna halin ko in kula, snn ya kamo wata hirar daban. 12:30 suka shirya zasu haďu domi fita wani operation, hakan yasa ya kare duk wani shirinshi tun 12:00. Saida ya tabbatar da duk suna can ta bakin wani abokinsu Nas, snn ya shiga mota ya kama hanyar gidan Scorpion. A ďan nesa yayi parking motarshi ya qarasa da qafa, fiskarshi sanye da face mask da suke sakawa idan zasu fita operation. Tura karamin gate ďin yayi ya shiga bs tare da yayiwa gate man magana ba, duk da yana tayi mishi barka da shigowa, hanu kawai ya ďaga mishi ya shige ciki. Babu kowa a falon, ya leka ďakin Baba tana kwance tana ta sharar baccinta. Face mask ďin ya cire ya karasa kofar da yaga ta shiga ďazu. A hankali ya tura kofar. Tana zaune ta jinginu da jikin bango a haka bacci ya kwasheta. Gabanta yaje ya tsuguna yana karewa fiskarta kallo, zcyrshi tana daďa kwaďaita mishi son taimakonta. Gyaran murya yayi tayi firgigit ta buďe ido tana kallonshi, ga dukkan alamu a tsorace take. Tausayinta ta daďa ratsa shi , cikin saukar da murya yace "Kina buqatar taimako?" Gyaďa mishi kai tayi. Ya kuma cewa zaki bini na maida ke gida?" Jin ya ambaci gida batasan sanda murmushi ya sub'uce mata ba. Shima murmusawan yayi yana mai jin daďin ganin fara'a a fiskarta. Da hanu ya mata alamar ta tashi ta biyo shi, ba gardama ta mike, sbd haka kawai taji hankalinta yafi kwanciya dashi. Tafe yake tana binshi a baya har suka fita daga gidan suka qarasa gurin motarshi. Buđe mata yayi ta shiga, shima ya zagaya ya shiga. Da gudu ya figi motar ya bar wajen. Har kofar ďakin ya rakata ta shiga sum sum kamar munafuka. Sauri sauri gudu gudu ya fita daga gidan ya sake figar motar domin zuwa wajen meeting đinsu. ~Basu suka dawo ba saida asuba. Daga scorpion har Baba babu wanda ya fahimci cewar Deeja bata gidan, har Baba ta kai mata abinci. Rashin ganinta kuma baisa ta tuna komaiba dan a zatonta ko tana cikin ban ďaki ne. Saida ya shigo dubata yaga wayam, toilet ya leka nanma haka. Cikin tashin hankali ya fara kwalawa Baba kira. A tamanin ta shigo ta rusuna, "Gani yallab'ai." "Ina yarinyar nan ta shiga?" Ya tambaya yana muzurai. "Nima dai Yallab'ai ban ganta ba nayi tunanin ko ta zaga nema shi yasa banyi magana ba." "Bull shit." Ya faďa cikin karaji tare da kaiwa bango naushi. Da sauri kuma ya fita sai gurin gate man. A tsawace yake mishi tambayar da ta rikita mishi kwakwalwa ta kuma kaďa mishi 'ya'yan hanji. Cikin inina yace "O..oga tun.. tun jiya da kazo ka fita da ita ban sake ganinta ba." "What?" Ya faďa da karfi saida gateman yaji kamar fitsari yana neman kub'uce mishi. Cakumar wuyarshi yayi a tsawace kuma "Dan uban ubanka yaushe na fita da ita?" Cikin rawar murya yace "Bayan fitanku kaďan dasu oga Nas naga ka shigo kun fita tare." "You must be very stupid Sule, niďinne baza ka ba gane har wani zai shigo cikin gidannan ya sace mutum ya tafi dashi kace nine? Fuck u, Idiot." Ya hankaďa shi da karfi saida ya bugu da gate, shi kuma ya koma cikin gida. Tamkar tab'abb'e ya koma yana nuna Baba da yatsa yace "I swear idan yarinyar nan bata fito ba, zaku ga d other side of me." Ya zari wayarshi ya fice. Tab'e baki baba tayi tace "Ni nasan maka wani aswa, da oda sadami, yaran musulmai duk kun maida kanku kamar kafurai, sai zalunci. Allah yasa ma ta samu mai cetonta ne ta koma hanun iyayenta, Allah amin." Ta karasa adduar tana shafawa a fiskarta. Saida ya daidaita zamanshi cikin motarshi snn ya ďaga waya ya kira Nas, ya shaida mishi abunda ya faru. "Ka tambayi smart?" Abunda ya fara ce mishi kenan. "Kaima kasan smart baya wannan harkar dan ko jiya ma da na kawo mishi maganarta ce min yayi in daina damunshi dan shi ba wnn ne a gabanshi ba. "Hakane kam, saidai inaga duk wanda yayi aikinnan sananne ne ya sanka kasanshi ya kuma san sirrin gidanka." "Sosai ma, dole nayi bincike sbd har kaima bazan barka ba mutum ba abun yarda bane." "Hahaha, dat's gud namiji nima zan tayaka binciken." "And what's funny guy?" Ya faďa a kufule. "Nothing sha." Nas ya faďa tare da datse kiran yana dariyar yanda abokinshi ya ruďe akan yarinya k'arama. * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *3* ~A ladabce ta gaisheshi, ya amsa mata da kulawa yana tambayarta yanda ta kwana. Tun ďazu take son ganinshi taji abunda zai ce game da komawarta gida. Shiru tayi tana jiran jin abunda zai ce mata. "Kinci abinci?" Gyaďa mishi kai tayi ba tare da ta kalleshi. Kallonta yayi na ďan lokaci kafin ya ce mata. "Ya sunanki?" "Deejah." Babban sunanki kenan?" Ya kuma tambaya. "Hadiza." Ta kuma cewa. "Khadija kenan, Ina ne garinku?" "Dorofi." Maimaita sunan dorofin yayi, tun da yake bai tab'a jin sunan ba . "Wani state kenan?" "Taraba state." "A wani local government." "Sardauna local government, Gembu." Shiru yayi yana tunani, shi dai yasan yana jin sunan taraba state, amma bai tab'a zuwa ba dan ba'a bashi wnn damar ba, kamar yanda ake hana sauran members ďinsu zuwa wasu states, saidai yana ganin a sanadiyyar ta zai karya dokar da aka kafa mishi na hanashi zuwa taraba state, da sauran states ďin da suke makwabtaka da ita. Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace. "Kinsan abunda nakeso dake yanzu, Zaki ďan kara haquri zuwa wani ďan lokaci sbd zan ďanyi wani bincike kafin na mayar dake, ni nan da kika gani ban tab'a zuwa state ďinku ba balle wani local govt, shi yasa zan iya ce miki bansan ma ta inda zanbi inje ba, so ki ďan kara min lokaci kinji." Dalla dalla yakeyi mata bayanin yadda zata fahimceshi dan ya fahimci cewa jin hausan nata ba sosai ba, da ya gane tayi karatu kuma yake ďan surka mata da harshen turanci snn kuma yakan haďa da ďan guntun fulatancin da ya iya na fulanin jos da kuma kwatance da hanu duk dan ta fahimceshi. Kalloshi tayi da alamar rashin yarda a zcyrta tana tunanin ko shi ďinma cutar da ita yake sonyi shi yasa ya bullo mata ta wnn hanyar. "Ya dai, baki yarda bane?" Ya tambayeta tamkar yasan tunanin da takeyi. Girgiza kanta tayi kawai batayi magana ba. "Kinga, ni ba cutar dake zanyi, asalima gudun kada a cutar dake yasa na ďauko ki daga gidan scorpion dan nasan halinshi, taimakonki nakeson yi sbd Allah, bayan haka tun da na ganki nake jinki a raina tamkar 'yar uwata, ta jini, duk ni ďin bani dasu, sbd haka ki ďauke ni a matsayin hakan kema." Ya karshe maganarshi a raunane, wanda hakan yasa taji ta yarda da maganganunshi har tana Immagining nan da kwanaki kaďan tana gidansu cikin danginta. A hankali tace "Wani gari ne nan?" "Jos, plateau state." Jinjina kai tayi tana share kwallar da suka zubo mata sbd tunawa da tayi da gida ,babban damuwarta ma Yusufa da ta bari kwance cikin jini, Allah yasa dai babu abunda ya sameshi. Adduar da take yawan kenan duk lokacin da ya fad'o mata. Kaďan kaďan yake janta da hira yana kuma yi mata tambayoyi game da garinsu da familynta, tana bashi amsa a takaice, tun tana đari ďari har ta fara sakin jikinta. Duk wani abin bukata ya tanadar mata, haka kuma sutura masu mutunci ya saya mata ba kamar scorpion da ya haďa ta da 'yan iskan kaya ba, duk english wears marasa mutunci, hakan ya kara mishi daraja da kima a idanunta har itama ta fara jinshi kamar ďan uwanta. ~Duk wani gidan member ďinsu da ya sani saida ya zaga yana bincikawa tare da taimakon Nass, amma ko alamar mai kamanta bai gani ba. Sau biyu yana zuwa gidan Smart bisa shawarar Nas amma ko a fiska baiga alamun hakan daga shi smart ďinba, yayi binciken har ya gaji, saidai ya rasa dalilin da yasa zcyrshi ta kasa hakura da tunanin yarinyar. ~"Uncle smart." Ta kira a hankali kamar yanda taji maaikatan gidanshi suke kiranshi. tana buga hanun kujerar da yake kwance a kai. Kaďan ya buďe idanunshi masu cike da bacci yana kallonta, daga bisani kuma ya waresu gaba ďaya sbd ganin yanda ta marairaice hawaye na sintiri kan fiskarta. "Ya dai khadija, kukan me kikeyi?" Kasa tayi da kanta tana so tayi mishi maganar gida sbd yau kwananta biyar kenan a gidanshi , ta kuma rasa ta inda zata fara. Tashi yayi sosai ya zauna kan kujerar yana fiskantarta. "Gida ko?" Da sauri ta gyaďa kanta. "Ina sane ban manta ba khadija, nima banso kikai har yanzu baki koma ba, sbd nasan hankalin iyayenki a tashe yake, saidai abun ne sai munbi a hankali, da dabara, a halin yanzu scorpion ya haukace yana nemanki, so yake ko ta halin yaya ki koma gareshi, ta iya yiyuwa ma ya baza mutane ta hanyar garinku sbd ke, bayan haka ni kaina nasan bai yarda dani ba, ya sa min ido sosai,shi yasa kika ga banyi gaggawar maida ki ba, bayan haka dole ne cikin sirri zan gudanar da bincike na sbd kada ya fahimci wani abu, sbd haka ki kwantar da hankalinki, ki kara hakuri, in Allah ya yarda kisa a ranki kin koma gidanku kin gama, ina fatar kin fahimta." "Uhmm." Tace tana share hawayen fiskarta. "Kin yarda yayanki bazai cuce ki ba,?" Gyada mishi kai tayi. "Ok, to smile let me see." Murmusawan kuwa tayi yana tayata. Kwana biyu tsakani, zuwa yanzu kam ta gama sawa ranta ta kusa komawa gida tunda uncle smart ya bata hujjojinshi kuma ta gamsu, bayan haka itama shaida ce kan zaryar da Scorpion yakeyi a gidan, shi yasa ko da wasa bata fita, saidai idan uncle smart yana gida nanma iyakarta falo, tana jin alamun taku kuma zata shige ďakin da aka sauketa. ~A gajiye ya shigo gidan sbd zirga zirgan da ya sha yau ba hutu kan sabon kampanin da ya buďe na sarrafa takalma da jakunkuna. Wanka yayi ya ci abinci, har yayi shirin kwanciya ya tashi ya nufi ďakin ta sbd yau tun asubah ya fita basu haďu ba. A hankali ya tura kofar ya shiga. Baccinta takeyi haikan dan sai cikin kwanaki biyunnan take samu tayi bacci hankali kwance. Ya jima tsaye yana kallonta yana jin wani abu na mintsinan zcyrshi game da ita. Kawar da kai ya yi maida kallonshi ga agogon bangon dake cikin ďakin. Karfe sha ďaya da mintuna ishirin da ďaya agogon ya juna. Cikin sanyin jiki ya juya ya bar ďakin yana jin abu na mishi yawo a jiki wanda ko da wasa bai tab'a jin hakan game da ita ba. Bathroom ya shiga ya sakarwa kanshi shower, ya jima a ciki snn ya fita ya sake shirin bacci, saidai me, baccin ya kauracewa idanunshi duk da sosai ďazu yake jinshi. Babu abunda yake mishi yawo a ido sai surar ta, shaiďan kuma yana daďa kawata mishi kyaun halittarta, dan tunda ta shigo gidan bai tab'a ganinta babu lullub'i ba sai yau. Duk iya kokarin da yayi wajen aran dauriya ya yafawa kanshi da zcyrshi abun ya gagara, zcyrshi sai ingiza shi yake kan yaje ya sake kallonta. Bin shawarar zcyrshi yayi ya koma ďakinnata, har yanzu tana kwance kamar yadda ya barta ďazu. A hankali ya zauna a bakin gadon yana bin duk wani gab'a na jikinta da kallo, karshe ya sauke idanunshi kan kitsattsen sumarta baki kirin na fulanin asali. Shafa kitson yayi yana lumshe idon shi kafin daga bisani ya maida hanunshi kan lips ďinta yana kewayawa da yatsarshi. Motsin da tayi kamar zata tashi yasashi cire hanun, sai kuma ta koma ta ci gaba da baccinta. A hankali ya matsa ya kwanta kusa da ita zcyrshi na daďa ingiza shi, wani irin feeling yakeji wanda zai iya cewa bai taba jin irinshi ba a rayuwarshi. Bayanta ya ďaura hanunshi yana shafawa a hankali, itako sai daďa lafewa tayi a jikinshi tana baccinta hankali kwance. Zarcewa yayi da tura hanunshi cikin rigarta hakan yayi sanadiyyar farkawarta. A razane ta buďe ido jin bakon lamari a tare da ita, ganinshi yasata cikin inina tace "Un..un." Kafin ta karasa ba ya haďe bakinsu hakan ya hana ta karasa abunda tayi niyyar faďa. Wani irin rawa jikinta yakeyi tsoro da firgici suka mamayeta. Yakushi da duka ta fara kai mishi a duk inda hanunta hakan kuma bai hana shi ida nufinshi akanta ba. Tsabar azaba da razana suka bada gudunmawa wajen ďaukewar numfashinta. Bai fahimci hakan ba saida hankalinshi ya dawo jikinshi. Tattab'a jikinta yakeyi yana kiranta amma ina tayi nisa. "Inna lillahi, na hana scorpion cutarki ni na cuceki." Abinda ya faďa kenan rike da kanshi idanunshi suna tsiyayar da hawaye. Yunkurin tashi yakeyi amma gaba ďaya ciwon da jikinshi yakeyi ya hana, wani irin ciwo mai zafi da raďaďi yakeji suke ratsa dukka gabb'an jikinshi. Take zazzab'i mai zafi ya rufeshi wanda yasashi kwanciya nan kusa da ita yana jin haushi mamakin kanshi da ya kasa controlling kanshi har ya aikata abunda bai tab'a tunanin aikatawa ba. Sai wuraren karfe huďu ta farfađo, kukan da takeyi ya tabbatar mishi da hakan. "Kiyi hakuri khadija, am sorry, banyi da nufi ba." Abinda yake faďa kenan cikin muryar marasa lafiya. Lokaci guda ta fara rawar đari sbd azababben zazzab'in da ya rufe ta, hakoranta sai haďuwa sukeyi, tashi ya gagaresu dukansu biyu. Saida gari yayi haske yasa mu ya ja jiki ya shiga wanka. Falo ya koma yayi sallah, kafin ya dawo ďakin ya taimaka mata, duk da shima ďin juriya kawai yakeyi, dakyar da lallashi da ban hakuri, dan madai bata da wani karfi ne, da ko da wasa baza ta sake yarda da daďin bakinshi ba. A zaune tayi sallah, ya kawo mata brkfast nanma da kyar taci tasha magani, sai tsine mishi takeyi a ranta. Ba abunda ya ke bata mamaki irin yanda yake nuna kamar kunyarta yakeji wanda ita a matsayin munafurci ta ďauki hakan. ~Kwana uku kenan yanzu yana binta da rokon ta gafarceshi ba da niyya yayi ba amma ko uffan bata ce mishi. Kamar kullum yauma haka ya shigo ya qaraci ban hakurinshi harda kukanshi, tayi burus dashi kamar bata cikin ďakin. "Khadija idan na maidaki gidanku zaki yafe min?" Ai a tamanin ta gyaďa mishi kanta hakan yasa ya bata tabbacin gobe asubanci zasuyi su kama hanya. Duk da ba gama yarda tayi dashi ba amma fiskarta ta nuna alamun taji daďin maganarshi. Da asubah kuwa suna idar da sallah ya shigo da shirin tafiya, itama hakan take a wajenta, tana zaune kan sallaya da jakarta a gabanta. Saida yace ta tashi su tafi, ta gaisheshi. Kusa da ita yazo ya durkusa tayi saurin ja da baya. "Khadija, kafin mu fita inaso na sake rokon gafararki a karo na ba adadi, ki yarda dani wlh ba da nufi nayi ba, sharrin shaiďan ne, ki yarda dani ba halina bane, asalima kyamar mai aikata hakan nakeyi, nasan na cuceki na cuci rayuwarki, saidai inaso ki ďauki hakan a matsayin kaddara da ta hau kanmu dukanmu biyu, ki yafemin khadija." Tunda ya fara magana ta durkushe a gurin tana kuka, ga dama ta samu zata koma gida saidai zata koma da mummunan tabo . har saida ya kare, ita ma cikin kukan tace "Na yafe maka uncle smart." "Na gode, nagode khadija, thank u so much, Allah ya saka miki da mafificin alkhairi." A tare suka mike, ya sa hanu ya ďauki jakarta suka fito daga ďakin. Sun kai kofar falo zasu fita yana gaba tana biye dashi a baya, dab da zasu fita wayarshi tayi qara. Picking yayi a kagauce. "Hello Billy ya ne?" Daga ďaya bangaren aka ce mishi "Boss ne yakeson ganinka yanzunnan." "Oh goshh." Ya faďa yana dafe goshinshi. "Ok, gani nan zuwa." Ya kashe wayar. "Khadija kiyi hakuri barinje in dawo yanzu zamu tafi." " Gyaďa mishi kai tayi a sanyaye duk ta qagara ta ganta a hanyar garinsu. Da sassarfa ya fita ita kuma ta koma ta zauna cikin ďaya daga cikin kujerun falon ta buga tagumi. Bata daďe da zama sosai ba taji alamun shigowar mutum. Juyawan da zatayi sukayi ido huďu da scorpion yana kallonta yana murmushin da zata iya kiranshi na mugunta. A tsorace ta mike tana ja da baya, kafin tayi wani yunkurin kirki har ya karaso inda take ya shaqa mata abu a hanci, take ta zube a wajen yarafff.... * TASHIN HANKALI * *Written by :Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *4* *Dedicated to Mmn Buhari (Mama Deejah)* ~ Ciccib'anta yayi ya fita da ita ya kwantar a bayan motarshi ya shiga ya jata a guje ya ďauki hanyar barin gari. Bayan shuďewar wasu lokuta, smart ya dawo ya shiga da sallama, yana karawa da "Sorry sister, na b'ata miki lokaci ko?" Shirun da yaji baisa ya tuna komai ba tunda yasan ba lallai bane ta amsa. A yadda ya ajiye jakar haka ya sameta sbd haka ya ďauka yaje ya sakata cikin mota. Falon ya dawo yana kiran "Khadija fito mu tafi." Shi a tunaninshi ko ta koma cikin bedroom ne. Shirun da yaji yasashi leka ďakin, wayam bata nan, zama yayi yana tunanin ko tana toilet. Ya ďan ďauki lokaci zaune cikin ďakin sai duba agogon hanunshi yakeyi amma ko alamar motsinta baiji daga cikin toilet ďinba. Wani tunani ne ya ďarsu a zcyrshi lokaci guda ya mike zcyrshi na tsinkewa. "Khadija." Ya kwala kiran da ďan karfi. Jin shiru yasashi buďe kofar toilet ďin ya leka kamar a tsorace. Cikin tashin hankali ya fita ya leka ďakinshi, daga ya fara nema lungu da saqo na gidan. "Oh, no khadija badai guduwa kikayi ba, wa kika sani a garin jos, taya zaki koma garinku, bakya tsoron haďuwa da mugaye su cutar dake, dama baki yarda dani ba khadijah, ashe yafiyar da kikayi ba kai zuciya ba?" Surutai ya rika yi cikin tashin hankali. Kamar an tsikareshi ya tashi har ya kai bakin kofa ya tsaya ya tambayi gate man đin shi ko akwai wanda ya shigo gidan bayanshi. "Oga scorpion ne ya shigo kuma ya fita da wata yarinya kamar bata numfashi, inajin ba lafiya ne." Gate man ya bashi amsa. "Inna lillahi wa innaa ilaihi rajiuun." Ya dinga maimatawa yana juya kanshi take kuma ya fara jin kamar jiri na ďibanshi. Gefen bencin maigadi ya lalub'a ya zauna ya dafe kanshi take idanun shi suka rine da b'acin rai, ga wani irin tashin hankali marar misaltuwa da ya diro mishi. "Yallab'ai lafiya?" "Lafiya." Ya faďa a takaice tare da tashi ya bar wajen a sanyaye. Kofar falon ya tsaya yana kallon takalmanta dake zube a wajen. A hankali ya duqa ya ďauki takalman yana kallonsu tamkar khadijan zata b'ullo ta jikin takalman. "Why scorpion, why? Me yasa baka barni na cika mata burinta ba? Me yasa baka bani damar cika mata alkawarin da na ďaukar mata ba? Me yasa ka dage lallai sai ka cutar da ita, Laifin me tayi maka? Me yasa baza ka tausaya mata ba?" Haka yayi ta jerowa scorpion ďin da baya kusa tambayoyi har ya gaji ya mike da takalman a hanunshi ya je ya kwanta cikin kujeru, ya rungume takalman sbd yanda yakejin jikinshi ba nauyi kamar leda. Fiskarta ke mishi yawo a idon zuci, kawaicinta, kunyarta ,murmushinta, kukanta duk babu wanda baya tunawa, wata kila shi kenan ta rabu da danginta ta zama mara gata da dangi kamar shi, wata kila kuma ta halaka kanta kamar yanda tayi yunkurin yi lokacin da ya keta mata mutuncinta. kamar a mafarki yaji hawaye suna ziraro mishi, "Ya Allah ka tseratar da wnn baiwa taka daga cutarwar scorpion." Cikin zafin nama ya mike yaje ya ďauro alwala ya fara jero nafiloli da adduoi yana nema mata kariya a wajen Allah. Ko da wasa baiyi gigin neman scorpion ba sbd yasan bazai ma tsaya nan kusa da ita ba. ~Tafiya mai nisa sukayi, cikin ikon Allah ta farka amma kasala da nauyin jiki sun hanata motsawa, hakan yasa baisan cewar ta farka ba. Daga kwancen take ta kwararo adduoi a ranta sbd tunawa da shigowar scorpion da kuma nufarta da yayi, daga nan kuma bazata iya cewa ga abunda ya faru ba, saidai a yanzun tana da tabbacin dashi take tare dan kamshin turaren da take ji ba na uncle smart bane. Tafiya mai nisa sukayi, shi kanshi tafiya yake ya rasa takamemmen inda ya kamata ya kaita sbd gudun sharri smart, yasan halinshi sarai, kamar yadda suke kiranshi smart haka yake ya amsa sunan, zai iya yin komai cikin dabara da aiki da hankali har ya gano inda suke. Saida ya shiga Nasarawa state ya samu bakin hanya ya gangara ya tsayar da motar, ya juya yana kallonta kafin daga bisani yakai hanu ya shafi fiskarta,, "Sleep well my beauty, barin samo miki abunda zakici kafin ki farka." Luff tayi tamkar baccin takeyi da gaske. Saida ta tabbatar ya fita ta ďago kanta ta leka ta glass. Bayan shi ta hango ya shiga wani restaurant. A hankali tasa hanu ta buďe kofar. Ganin bai kulle ba yasa tayi karfin halin tashi ta ja jiki ta fita daga cikin motar ta fara tafiya tana waige. Tana matsawa daga wajen wani da yazo wucewa yaga kofar mota a buďe ya tura ya rufe yayi gaba abinshi. Wani shago ta shiga, mai shagon yana binta da kallo sbd ganinta da yayi a galabaice. "Baiwar Allah lafiya." "Ki taimakeni ki b'oye ni wani ya mini sata ne." " Waye ya yi miki sata kuma satan me ya miki?" Ya tambaya yana wurga ido ta inda yaga take kallo." Jan kafarta tayi ta shiga ciki sosai ta zauna dab'as a kasa yanda na waje bazai hango ta ba kafin tace. "Ya mini sata a garinmu ya kawoni a nan." Ta sake faďa idanunta suna faman rufewa. "Ina ne garinnaku?" "Gembu." Ta bashi amsa sai tayi luu ta kwanta. "Ikon Allah, da alama fa sato yarinyar akayi." Ya faďa yana kallonta. ~Manyan ledoji guda biyu ya dawo dasu ya buďe mota ya saka ya zagaya ya zauna ba tare da ya kalli bayan motan ba. A guje ya sake figar motar ya kunna kiďa yana yana bi cikin nishaďi har ya qarasa cikin abuja. Slowing tukin yayi ya waiga bayanshi yana cewa "Har yanzu baki tashi .... Maganar tashi ce ta katse sbd abinda idanunshi suka gane mishi. "mafarki ko gaske?" Ya tambayi kanshi. Wani irin wawan birki yaci. Da azama ya buďe kofar motar yaje buďe baya yana leka kasan motar da kyau. Ja da baya yayi a tsorace "Mutum ko aljan." Ya kuma cewa. "Ko dai smart ya biyoni ne?" Take ya ciro wayarshi ya kira Nass ya tambayeshi labarin Smart. Har gidan yaje ya kuwa sameshi kwance kan sallaya yana bacci. Take ya kirashi ya shaida mishi. ~Sauri yayi ya rufe shagonshi ya fita sai police station, nan ya shaida musu abunda yarinya ta sanar dashi tare da basu tabbacin yarinya tana cikin shagonshi a kwance. Tare sukazo da police uku, maxa biyu mace ďaya suka ďauketa sai asibiti. ~Shawara zcyrshi ta bashi da ya koma inda ya tsaya a nasarawa state ko zaiji labarin an ganta, yana kuma mamakin yanda akayi ta samu karfin fita daga motar. Haka ya koma ya karaci bilayinshi bai samu wani kwakkwaran labari ba, karshe anan garin ya kwana washe gari kuma ya koma jos. Gidan Smart ya fara zuwa yana jin takaicin rasata da sukayi dukansu biyu, shi bai bar mishi ita ba ,gashi shima ya rasata. Kallo kallo suka fara yiwa juna, wanda shi smart kallon tsana karara yake yiwa abokin nashi. "Smart, ta b'ata, ta gudu ban ganta ba." "Rubbish, ka daina faďa min maganar banza, ina kakai 'yar mutane?" Ya faďa a tsawace yana huci. "I swear ta b'ata, ban ganta ba nima, mun rasata dukanmu biyu, dana san zata b'ata da na hakura na bar maka ita, Saida Billy yace in bar maka ita, she must be the lucky lady da nake faďa naki yarda, gashi mun rasata gaba ďaya. Shako kwalar rigarshi smart yayi cikin ďaga murya yace. "Wa ya faďa maka sonta nakeyi, taimakonta nayi dan in kub'utar da ita daga sharrinka, maidata gidansu cikin danginta nakeso inyi, but now, kaga abinda ka jawo, ka rabata da familynta, kazo kana gaya min baka san inda take ba." Sai kuma ya sassauta rikon da ya mishi ya kuma sassauta muryarshi. "Scorpion, yanzu a wani hanu kake tunanin zata faďa? me yasa baka da tausayi da imani? why are you so heartless scorpion?" A hankali ya zame hanunshi daga rikon da ya mishi ya kuma nunashi da yatsa. "Ka sani duk abunda ya faru da khadija, Allah bazai barka ba, Allah sai ya kama ka, alhakin yaran da kake cutarwa bazai barka ba scorpion sai Allah ya kamaka." Murza yatsunshi yayi ya juya ya shige cikin bedroom ya barshi nan tsaye jiki a sanyaye, bai san mai yasa yau maganganun smart sukayi tasiri a kanshi ba duk da ba yau ya fara faďa mishi hakan ba, baisan me yasa b'atan yarinyar ya ďaga mishi hankali ya sanyayar mishi da jiki ba. "Am sorry friend, i missunderstood u, rashin sani ne, da na barka ka maidata garinsu, am sorry once again. " Shi kaďan shi ya karaci surutanshi ya fita daga gidan gaba ďaya yana jin zcyrshi ba daďi. ~ kwananta biyu a asibiti ta warware hankalinta ya gama dawowa jikinta, tambayoyi kam tasha su, daga bisani aka hađa ta da 'Yan sanda biyu a rana ta uku suka rakata garinsu. Mikakkiyar tafiya sukayi zuwa jalingo, cin abinci da sallah yake tsayar dasu. Daga nan suka ci gaba da tafiya zuwa Baruwa, suka isa karfe takwas da 'yan mintoci. Cikin baruwan suka kwana sbd haurawan hawan biyu da sisi, da zasuyi. Sai washegari suka haura Gembu wuraren karfe goma na safe, daga can suka sauka suka hau machine mai kafa biyu, suka haye kogin wukari suka karasa dorofi, da misalin karfe sha biyu na rana. Duk zumuďin da takeyi na zuwa garinsu suna isa taji gabanta na faďuwa. Mutane sai binsu da kallo sukeyi yayinda ita kuma ta ja lullub'inta ta rufe fiskarta dashi. 'Yar yayanta wanda yake ďan Baffanta ne, wacce bata wuce shekaru biyar ba ta dawo daga makaranta zata wuce gidansu ta gansu. Tsayawa tayi tana kallon 'yansandan kafin ta maida dubanta ga Deejah. "Goggo Deejah oyoyo." Take faďa da tsattsamar muryarta tana tsalle. Rige rige matan gidan sukeyi wajen fita daga gidan sbd tabbatar da abunda kunnuwansu suka jiyo musu. Rike da hanun Ummi ta doso gidan suka ci karo da matan gidan. Adda, Mmnsu Hamma shehu ce tayi saurin rungumeta sai kuma suka fashe da kuka a tare . Sauran matan ma riketa suka yi suna kukan. Kan kace me tuni makwabta sun fara taruwa ana taya murna, sai daga baya hankulansu yaje kan Jami'an tsaron da suka rakota. D'akin Hamma shehu aka buďe musu suka shiga daga nan aka fara hidima dasu dama ga mutanen dorofi ba dai iya karrama bako ba. Kan kace me gida ya cika da jama'a 'yan taya murna , tuni labari ya isa ga iyayenta maza da suke wajen kasuwancinsu, shima Hamma shehu da yake cikin kamaru tuni aka nemi gurin service aka kirashi, dan ba ko ina ake samun service a garin ba. Yusufa dake makaranta sai gashi ya shigo a guje yana "Ina adda Deejan?" Ai a guje ta tashi ta rungumeshi ta kuma fashewa da kuka, a haka iyayensu suka dawo suka samesu. A takaice ranar farin cikin baya misaltuwa ga ahalin wnn gida, baranma Hamma Shehu da baki yaki rufuwa, kannenta kuwa daga kan Yusufa yayi kasa suna makale da ita , Fa'i kuwa kamar zasu shige cikin juna. Godiya suka rika yiwa jami'an tsaronnan ba adadi bayan sun basu labarin yanda akayi aka samota. Saida 'yan barka suka lafa, snn iyaye da yayyu aka haďu nan take basu labarin bayan rabuwansu da yusufa saidai ta gagara sanar dasu fyaďen da Uncle smart ya mata, amma sunsha labarin kyautatawar da ya mata kam, harda yunkurin da yayi na dawo da ita gida scorpion ya zoya sake ďauketa. Addua sukayi ta mishi na alkhairi shi da mutumin da ya taimaka mata a nasarawa state. Sai washegari polisawan suka kama hanyar komawa bayan yan uwanta sun cika su da goma ta arziki.... * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *5* *Dedicated to Mmn Buhari (Mama Deejah)* ~'yan uwa da abokan arziki dake ciki wasu kauyuka dake makwabtaka dasu duk sai zuwa taya murna sukeyi dan kamar yadda labarin batanta ya bazu hakama dawowarta. 'Yan uwansu dake cikin Jalingo da dangin mamanta na sunkani duk ba a barsu a baya ba wajen zuwa taya murna. Gata kam ta ganshi, daga gun dangi,kakarta da ma makwabta sai nan nan sukeyi da ita, wani lokaci har kuka abun yake sata. Babban damuwarta a yanzu bai wuce mummunan tabo da smart ya mata ba, gashi ta gagara sanar da kowa. Wani lokacin sai tayi yunkurin sanar da matar Babanta (Mmn su Yusufa) da yake akwai fahimtar juna tsakaninsu, riko na tsakani da Allah take mata, ko kuma 'yar uwarta kawarta Fa'i, sai kuma taji nauyin bayyana maganar , a haka ta bar abun a zuciyarta. Wata biyu kenan yanzu take nema da dawowa, zuwa lokacin an fara shirye shiryen bikinta da Hamma shehu. Wani irin azababben mura mai shegen taurin kai take fama dashi, anyi maganin na asibiti da na gida, duk a banza. Ga wani ciwon kan da yake takurata har yakai ga bata son hayaniya kusa da ita. Hakan yasa a yanzu ko da yaushe tana gidan kakarta dake bayan gidansu kaďan, wani lokacinma a can take kwana. Yawan bacci da yawan kasala da ya sata a gaba, tun Hajja Inna (Kakarta) tana ganin kamar na muranne har ta ga abin ya wuce misali. Dalili kenan da wani zargi ya fara ďarsuwa a ranta. Nazarinta ta shiga yi sosai karshe ta zo ta sameta gurin da take kwance bayan ta fito wanka dan ko mai bata shafa ta ďale gadon 'yasr tsohuwa ta mimmike tana lumshe idanu. "Deejatu, Umma joďa." (Tashi ki zauna.) Ta umarceta. Tashin tayi tana zumbura baki irin an takuratan nan. Kwayar idanuta ta tsurawa idanu daga bisani ta kama idon ta kwaye, hanunta ta sake kamowa ta jima tana kallo mai cike da nazari, saiga 'yar tsohuwa ta fashe da kuka. "Hajja inna Jam bo?" (Lafiya kuwa?" Take tambayarta cikin kiďima. "Deejatu, wa ya cucemu ya lalata miki rayuwa, cikin shege a zuri'armu." Tsohuwa ta faďa cikin kuka tana fyace majina da bakin zaninta. Dumm taji kirjinta ya buga kamar zai b'alle. "Ciki?" Ta maimaita a hankali tana dafe kirjinta. Fita Hajja inna tayi cikin matsanancin tashin hankali. Ita kuwa Deejah, nan ta kwanta ta fara rusa kuka tamkar ranta zai fita. Can jimawa sai ga iyayenta maza dukansu uku, Babanta wanda yake shine qarami a cikinsu, sai baban Hamma shehu, sai kuma wansu babba. Salati suka ďauka gaba ďayansu lokacin da mahaifiyarsu ta sanar dasu, sai kuma ďakin ya ďauki shiru. Gyaďa kai babban wansu ya shiga yi, "Babu shakka azzaluman da suka ďauketa ne suka lalata mata rayuwa dan sunsan halin 'yarsu bata da hayaniya, snn basu tab'a ganinta da wani a matsayin saurayinta ba idan ba Shehu đan uwanta wanda zata aura ba." Mahaifin shehunne ya amshe da cewa "Ba banza ba tunda ta dawo ta kara zama wata shiru shiru, har iyayenta mata suna yawan faďin tana saka tunani a ranta, sbd yawan zama guri ďaya da takeyi tayu jiguum kamar bata da isasshen lafiya." Babanta kam ba magana zaune yake kawai kamar an dasashi a gurin, zuciyarshi dai harbawa takeyi, Yau Hadizanshi da ciki, cikinma na shege, wanda ba a san ubanshi ba, kuma zaiyi wuya a sani ďin har abada. Tabbas wnn duka yana cikin kaddarar rayuwarsu, gwara itama da sauki da aka samu ta dawo. Tabbas wnn wata jarrabawa ce da Allah ya jarabcesu shida ďan uwanshi, Allah ya basu ikon cinye wnn jarabawar. "Yaya za ayi da cikin nan gashi biki saura kwanaki kaďan." Hajja inna ta tambaya tana bin yarannata da kallo da jajayen idanunta da suka sha kuka. "Babu yanda za ayi dashi, barin shi zamuyi ta haife shi, wnn al'amari ne na ubangiji bai kamata muyi mishi wani shisshigi a ciki ba, fatanmu dai Allah ya bata lafiya ya kuma rabata dashi lafiya." Cewar babban wansu. Shirune ta ratsa wajen na wani lokaci, zuciyoyi duka babu daďi. "Ko ku yaya kuka gani? Ya tambayi sauran yan uwannashi." "Yanda ka faďan haka za ayi." Suka hađa baki wajen faďa. Baban Hamma shehu ya qara da "Allah ya takaita mana wnn al'amari hakanan." "Amin." suka amsa dukansu har da Hajja Inna. Koda labari ya riski Hamma shehu hauka ne kawai baiyi ba,amma saida ya kwanta ciwo, dakyar aka shawo kanshi da nasiha, addua da ban baki. Suma kansu iyaye matan dagewa sukayi sai an zubar da cikin, amma su Mazan suka ki amincewa. Adda Mmn su Hamma shehu kam kuka ne tayishi har ta godewa Allah, Tabbas azzalumai sunyi mata tabon da zai tab'a gogewa a zcyrta shi yasa duk lokacin da matsala irin haka ta taso ko ta tuno da shuďedďen al'amari sai tayi kuka har ta kwanta ciwo. Duk lokacin da ta buďi baki zatayi mummunan addua garesu kuwa sai mijinta ya taka mata birki, saidai idan baya wajen. Da haka taci gaba da rainon cikinta cikin rashin kwanciyar hankali da sukuni, farin ciki ya qaurace mata, walwala ya nisanta gareta, fara'a ya gushe a fiskarta, duk da iyayenta suna iya kokarinsu wajen ganin ta saki jiki ta koma kamar da. Shima Hamma shehu kokarin da yakeyi kenan, burin shi yaga ta koma Hadizanta ta da. Ana haka naquda ya kama ta cikin dare babu wanda ta faďawa har gari ya waye, haka tayi ta fama, dan ita a lokacin bataki sanadiyyar haka ta mutu ba da taga ta haifa ta rike. Fa'i ma da suke tare bata sani ba har ta shirya ta tafi makaranta, saida abun yafi qarfinta nanma matar babanta ne ta shiga duba ta ta sameta cikin mawuyacin hali, nan ta sanar da sauran mutanen gida, daga nan aka kira nurse ďin dake karb'a musu haihuwa a qauyen. Tasha baqar wahala har hankulan kowa na gidan ya tashi kafin daga bisani cikin ikon Allah ta haifo ďanta namiji. *Mu koma Labari* Kulawa sosai take samu daga ko wani b'angare, amma har yanzu bata bar damuwa ba, baranma idan taga Hamma shehu ya tasa yaron a gaba yana kallo duk sai taji wani iri. Ga makwabta da na nesa da suka sansu sai zuwa barkan haihuwa sukeyi wanda wasu kam gulma ke kawo su. Ranar suna yaro yaci suna Mahmud, wan babanta ya yi yanka. Sunyi rawar gani sosai wajen haďa mata kayan suna ita da mahmud, kowa da kalar bajintarshi. Washegarin suna kanwar babansu dake aure a Nguroje ta tafi da ita, a cewarta watakil dan tana tare da mutanen da ta sani a garin da aka santa sosai shi yasa take takura kanta. Ba laifi kafin tayi arba'in ta fara sakewa dan tana samun kulawa sosai daga wajen goggonta, kuma yaran goggon suna iyakar kokarinsu na ganin sun ďebe mata kewa. Duk kwana biyu Hamma shehu yake kai mata ziyara saidai idan yayi tafiya sarin kaya, a kano ko a kamaru. Hakama yusufa duk weekend ya ke zuwa wani lokacin har da Fa'i da sauran kannenta. ~Kwance yake sanye da 3quater da singlet,ya shige cikin kujera idanunshi a rufe, duk tsayuwar da sukayi a kanshi na tsawon lokaci baisa ya buďe idanunshi ba, bacci yakeyi haikan. Tab'a shi Billy yayi motsi kamar zai tashi sai kuma ya gyara kwanciyarshi. Murmushi ya fara yi sai suka ga yana mika hanu kamar yana so ya kamo wani abu. "Khadijah." Yace da karfi, sai kuma ya sassauta murya "Tsaya kiji pls." Kallon juna sukayi dukansu suka murmusa. "Banza get up, wani irin bacci ne wnn kamar mace." Nass ya faďa daidai lokacin da ya ďaka mishi duka. A firgice ya tashi ya share fiskarshi ya ďaga ido ya bisu da kallo dukansu uku kafin yaja dogon tsaki. "Wani iskancinne yasa kuka tsaya min akai kamar babu gurin zama." Ya faďa cikin jin haushinsu dan gani yayi kamar sunyi mishi shamaki da ita ne da suka tasheshi. Kusan ko yaushe ya kwanta kwanannan sai yayi mafarkin khadija rike da wani cute baby boy tana mika mishi, da zaran ya mika hanu zai karb'e shi kuma sai ta b'ace, yau kuma bata b'acen ba matsawa baya take tayi, yana kokarin tsaidata suka tasheshi, gashi yaron ba karamin shiga ranshi yayi ba, snn ganinta cikin mafarkin yana nuna mishi cewar tana raye cikin koshin lafiya, saidai ganinta da yaronne ya rasa gane me hakan yake nufi. Yana tsoron gaskata abunda zcyrshi yake raya mishi. Kallonsu yayi a karo na biyu ya banka musu harara kafin yace "Get seated u fools, three idiots, kuna sa kaina yana juyawa." Tab'e baki scorpion yayi yace "Khadija dai ta saka kanka juyawa tunda ka gagara kamota." Dariya suka kwashe mishi dashi kowa ya zauna. Scorpion da ke zaune kusa dashi yace "Who is she?" "Ina ruwanka magulmaci." "Seriously smart ka ture batun wasa "Who is khadijah?" "The lucky lady." Su Nass da Billy suka haďa baki wajen bashi amsa suna dariyan shakiyanci. ""Kuna da matsala wlh, ya faďa yana yunkurin tashi daga gurin. Rikoshi Scorpion yayi ya maidashi yace "Yaufa sai ka faďa mana matsalarka , mun gaji da ganinka cikin damuwa, ka koma smart đinka da muka sani ,kuma sai ka faďa mana wacece khadijah idan ba haka ba saidai mu kwana zaune nan gurin, ba ci, ba sha, ba sallah, ba kashi, ba fitsari, ba.." "Enough parrot." Ya faďa yana ďagawa Scorpion hanu. "Ehen, We are all ears." Scorpion ya faďa yana kama kunnenshi.... Wa nake dashi da zanyi sharing problems ďina dashi idan ba ku ba. Ya ayyana hakan a ranshi, amma can kasan zuciyarshi yana shakkun fađa musu takamammen damuwarshi. "Smart, don't forget we are brothers, we share our problems to each other, we cry together, we smile together, and we unite to solve each others problem, then ,why the sudden change.?" Cewar Billy da serious face. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauqe kafin yace "The problem is..is..all about.. Sai kuma yayi shiru. Dukansu sun bada hankulansu dan jin mene matsalar ďan uwansu. "That girl." Ya faďa yana shafa kanshi." "Which girl?" Suka tambaya a tare.... "Yarinyar da ta b'ata a hanunka last year." Ya faďa yana kallon scorpion. "What about her?" "I think she is alive n healthy and i need to see her." "Malam go straight to the point." Nass ya faďa cikin nuna gajiyawa da kwana kwanan da yake musu. Cikin nitsuwa ya fara zayyane musu tun yanda yaji game da ita tun ranar da ya fara ganinta, ďauko ta da yayi irin zaman da sukayi har karshe rabuwarsu da kuma mafarkin da yake yawan yi da ita. Bai b'oye musu komai ba. "Me yasa ka yarda da Smart hundred percent scorpion, smart ba mutum bane ?ko an ce maka bashi da zuciya ne, ?A tunaninka bashi da feelings ne? Ko kana ganin haka zai tabbata a rayuwa a baiga macen da ta mishi ba? Common be wise scorpion, smart is also a human being like u. Maganganun da Nass ya faďa mishi ne lokacin da yake tuhumarsu kan ďauke khadija daga gidanshi ,while ya ware smart kan cewa bazai aikata ba, maganganun ne suka dawowa scorpion kamar yanzu Nass yake faďa mishi. "I think mafarkinka na maka nuni da cewa tsautsayin da ya gifta tsakaninku an samu rabo." Billy ya faďa cikin nuna alamun tabbatar da abunda zcyrshi ya tuna mishi, hakan ya katse wa Scorpion tunaninshi. "Me yasa baka nemeta ba Smart?" Scorpion ya tambaya a sanyaye. "Naje state ďinsu na shiga lcl govt ďinsu kuma na bi qauyukansu amma ban sameta ba, in fact i went there almost four times." Ya faďa cikin tausayawa kanshi. Dafashi scorpion yayi "Don't worry friend, i promise u zamu nemeta kuma zamu sameta indai tana raye....." TASHIN HANKALI * *Written by: Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *6*to8 *Dedicated to My lovely sister, Haleema Auwal (Mmn Ayshat)* ~"Really?" Ya tambaya yana binsu da kallo. "Seriously, mun damu da damuwarka smart, we can do anything to make u happy, so don't be surprise idan nace zamu nemo maka ita, what are friends for?" Jinjina kai yayi, a take kuma suka mike suka haďa hanu sukayi taken da suka saba idan zasu haďa kai suyi wani abu mai muhimmanci. *"United we stand, but devided we fall, we are one, no going back."* "Thank u friends." "Never mind." Scorpion ya fad'a yana buga kafađarshi. "Saidai dai da zamu san takamammen sunan kauyensu binciken zaifi yi mana sauki." Bayan wuyanshi ya shafa yana kallon kasa alamun tunani, "Gaskiya da nake zuwa kauyukan da aka lissafa min suna da yawa, sai jiya na tuna ta tab'a gaya min sunan kauyensu, i think Dorokin or Dofrofi, tsakanin biyunnan dai.Sardauna local govt." "Ok, zakaji feedback idan mun shirya." Nan suka yi hand shake suka tafi suka barshi yana addu'ar Allah yasa a dace. ~Zuwa yanzu Mahmud ya kai wata biyar yayi wayau, har ya fara koyon rarrafe, yarone mai shiga rai, gashi kullum tsaftsaf dashi. Sosai yayi sabo da Hamma shehu, da ya ganshi sai yayi ta mika hanu yana dariya. Itama yanzu ta cire damuwa a ranta sai ďan abunda baza a rasa ba, mahmud kuma jinshi takeyi har cikin ranta, baranma da ya ďauko kamannin 'yan gidansu dan kusan zance ita ce ta fita daban cikinsu ta yo kamannin mahaifiyarta. ~Ba tare da saninshi ba suka tafi Gembu tunda scorpion yana ganin zai ganeta in har ya ganta. Ba karamar wuya suka ci ba kafin suka samu haurawa Gembu har suka gane dorofi, sbd suma kwab'a sunan kauyen dorofin kamar yadda smart yayi tayi. Saidai duk uban zagayen da sukayi a dorofi ko mai kama da ita basu gani ba, sunyi tambayar khadijah har bakinsu yayi tsami, amma ba a samu wanda yace ya santa. Kwanansu uku a can suka yanke shawarar bincika sauran kauyukan, kamarsu, Mbamga, tamnya, mai samari, mayo ndanga, Yarimaru, karshe suka yada zango a nguroje dake kan hanya. Kwanansu biyu a gurin suka yanke shawarar komawa, dama gudun hakan yasa basu sanar dashi ba kada yasa rai. Ko jiya da ya kira scorpion yana nemanshi ce mishi sukayi sun fita aikin da baya so ne, wato fashin kan hanya. Nan kuma yake shaida musu yana gidanshi na Bauchi kan wani Alhaji da yake bibiya daga jos, so su zama ready kafin ya kuma kiransu. A ranar da sukayi shirin komawa sun fito har sun fara tafiya scorpion ya dakatar dasu. "Ku dakata kamar itace a can." Ya faďi yana nuna wasu mata biyu ďayar da yaro rike a hanunta shi kuma yaron yana ta zillewa yana mikawa ďayar hanu yanaso ta karb'eshi. Dakatawa sukayi har suka zo suka wucesu, scorpion ya tabbatar lallai itance kafin suka bi bayansu a hankali. Rakiya tayi ďayar ta shiga mota ita kuma ta karb'o ďanta ta juyo tana tafiya a tsanake. Haka sukayi ta binta har ta koma gida. a ranar dai kusan wuni sukayi ta arean gurin suna gadinta dan su tabbatar da nanne gidansu. Har dare basu ga fitowarta ba hakan ya basu tabbacin nan take. Masaukinsu suka koma zcyoyinsu fal farinciki. Sai cikin dare kafa ya ďauke suka fito da shirinsu na tafiya suka doshi gidan. Cikin bacci taji kamar an haskata da toci. Buďe idanunta tayi sai taji shiru hakan yasa ta koma baccinta. A hankali Billy yasa hanu ya ďauki Mahmud wanda hakan yayi daidai da sake farkawarta. Da karfi ta tashi ta cafki hanunshi zatayi ihu scorpion yayi hanzarin toshe mata baki, ya ďagata cak suka fita dasu sai wuntsila kafafu takeyi babu damar ihu. Habibatu da suke kwana tare alamun fitar mutum taji ta tashi tana yiwa Deeja magana. "Adda Deeja jirani muje tare." Tace dan ita tayi tsammanin deeja ce zata fita fitsari. Jin shiru yasa ta daďa ware idanunta tana lalub'an lantern. Jin kamar motsi a kofar gida yasa ta tashi ta tsaya ta kunna lantern ďin da hanzari sai ganin kofarsu tayi a hangaďe. " Adda Deejah." Ta đan ware muryarta ta kira hakan yayi daidai da fitowar Babansu dan shima yaji motsin. Kofar gidansu suka gani a buďe, ya koma ďakinshi a guje ya ďauko sandar goranshi. Tashin mota sukaji dan dama Nass yana ciki a mazaunin driver yana jiransu, suna shigowa kuma yaja suka bar wajen a guje, sun taki sa'a kuma gidan a bakin hanya yake, basu samu wahalar hawa da gangara, ko wani gargada ba. Da gudu babansu ya fita amma ina sunyi nisa. "Babu Adda Deeja, babu Mahmudu." Habibatu ta faďa cikin kiďima kuma da karfi wanda Hakan ya tashi Mmn Habiban da sauran yaran gidan daga bacci. Babansu kam da ya leka ďakin yaga basanan bayan gida ya nufa nanma wayam, gaba ďaya jikinshi rawa yakeyi bakinshi kuma yana jero duk adduar da ta zo mishi. Wani irin razannannen ihu goggon Deeja ta saki hanunta a kai wanda yayi sanadiyyar fitowar makwabtansu suka fara ďuruwa cikin gidan ba mazan ba ba matanba. Sauran yaran gidan kowa kuka yakeyi, Habibatu harda birgima, sai basu hakuri akeyi. Washegari da sassafe sukayi sammakon tafiya Dorofi, goggon Deeja da mijinta, aka bar Habibatu ta kula da yara. Aiko suna isa ta fasa ihun kuka sbd yanda abun yake mata raďaďi a zcyrta. Lokaci guda mutanen gidan suka taru a kanta suna tambayar wa ya mutu? "Deejah, Mahmudu, Deejah", take ta maimaitawa cikin matsanancin kuka. "Me ya samesu? Adda da Hajja Inna suka tambaya a tare. Itakam matar babanta tuni har ta fara kuka, ďayar matar baffanta kuwa daskarewa tayi a wajen tana kallonta kawai ta gagara magana. "Sun sake ďauketa ,cikin dare suka biyo ta suka ďauketa." Ta faďa dakyar numfashinta kamar zai ďauke. Cakk, Hamma shehu ya tsaya, ya kasa ďaga kafarshi, take yaji kamar numfashinshi yana tafiya. Mijin goggonsu ne dake zaune ya dafe kai da hanu bibbiyu idanunshi sunyi ja kamar garwashin wuta ya lura dashi. Zuwa yayi ya kama shi yana girgizashi "Shehu, shehu." Sam shehu bai ma san yanayi ba dan kwakwalwarshi ta daina aiki. Zaunar dashi yayi yana bashi baki, ko kallonshi baiyi ba , gu ďaya kawai ya kurawa idanu. Adda kam sulalewa tayi ta zube a wajen babu numfashi a jikinta. A sukwane Hajja inna ta juya tayi cikin gidanta ko kallon adda batayi ba, tsabar rikicewa sai da ta ďaura zannuwa har guda huďu kan zanin da ke jikinta, ta ďauko ďaya ta yafa, ta fito babu ko takalmi a kafarta, tana cewa sai taje ta karb'o deejatunta, wnn karo ba za a cutar mata da jika ba. Ya'yanta da aka kira isowarsu kenan suka tareta, sai a lokacin ta samu ta fashe da kuka tana cewa, itafa yau sai ta nemo 'yan fashinnan ta karb'o Deejah. Dakyar suka sha kanta suka shiga da ita gida. Dakyar aka samo kan adda ta farfaďo amma fa karshe asibiti aka nufa da ita. Yusufa kam da ya dawo yaji labari kulle kanshi yayi a ďakinsu yaci kuka ya koshi, yana tsinewa waďanda suka ďauke mishi 'yar uwa. Tashin hankali dai baya misaltuwa a wnn gidan dan mahaifinta duk dauriyarshi da ya iso yaji labari zubar da hawaye yayi tayi. ~Bauchi suka kaita, taci kuka har ta gode Allah, Mahmud rungume a jikinta. Idan yana kuka saidai ta zuba mishi ido itama tana kwararar da hawaye, Scorpion dake kusa da ita shi ke karb'arshi ya rarrashe shi, ita har ta ma manta ana bawa yaro nono, saida scorpion ya tunatar da ita. Duk yanda suka bita taci abinci ki tayi sai kuka take yi, yanzu kam ta riga ta sawa ranta ta rabu da iyayenta tunda aka zo har gida aka ďauketa. Tambayar kanta takeyi ita kuwa me tayi wa mutanennan suke bibiyar rayuwarta. Sai kusan magriba suka isa garin bauchi, direct gidan smart na bauchi suka nufa. Dialing nambarshi scorpion yayi dan basu sameshi a gida ba. "Kana ina ne munzo bamu sameka ba?" Abinda yace mishi kenan lokacin da yayi picking call ďin. "Zuwa ba sanarwa kenan, ku jirani ina zuwa ai kasan inda nake ajiye key, ka ďauka ka buďe muku. "ok." Yace, ya karasa wajen da yasan yana ajiye keys đinshi ya ďauka ya buďe kofar falo. Tasata sukayi a gaba har cikin falon kafin, suka fita suka kulleta ta waje. Saida suka fita ya sake kiranshi yace, "munyi ajiya mai muhimmanci a gidanka ya kamata ka dawo da sauri dan mu zamu wuce Jos." "Wani irin ajiya?" "Sai ka zo ka gani amma ka zo da sauri pls, kada kazo kanayi mana korafi." Yana gama faďin haka ya kashe wayar. Tunanin wani irin ajiya sukayi masa yasashi canza shawara, duk da baiyi niyyar dawowa nan kusa ba haka ya kamo hanya. A hanya yayi sallar Magriba kafin ya qaraso. Tana zaune sai sauke ajiyar zuciya takeyi ga ciwon kan da ya addabeta ga kuma yunwa. Mahmud yana kwance yayi bacci a jikinta, tuni duhu ya mamaye ďakin. Buďe kofa taji anayi hakan ya daďa tsananta bugun zcyrta. Kunna wutan ďakin akayi wanda ya haske ďakin tarr. Mamaki ne da tsoro ya rufesu lokaci guda, da karfinta ta mike har Mahmud yana faman faďuwa daga hanunta tayi saurin tallabeshi. "Khadijah." Ya kirata cike da mamaki da tsoro. "Laifin me na maka uncle smart ka sake raboni da iyayena, in kasheni kukeson yi ku kasheni in huta dan Allah, na gaji, na gaji." Ta faďa cikin kuka mai tab'a zcy. Hannayenshi ya ďaga duka biyu. "Bani bane Khadija, wlh ba ni bane, bansan zasu kawoki ba, bani nasa su kawoki ba." Komawa tayi ta zaune taci gaba da kukanta wanda yayi sanadiyyar tashin Mahmud, ya fara raba ido yana kallon hasken ďakin, daga bisani kuma ya fashe da kuka ganin mamanshi tana kuka. "Kinga kin sa ya tashi yana kuka." Ya faďa yana matsowa kusa dasu. Sa hanu yayi zai dauki Mahmud ta janyeshi, "Kar ka tab'a min yaro." "Yaronki ko yaronmu?" Ya faďa yana bin yaron da kallo. "Ta ina ya zama naka yaro da Ubanshi." "Waye ubannashi?" "Mijina mana." Ta bashi amsa kufule. "Kina so kice min kenan kinyi aure?" "Banyi aure ba taya zaka ganni da yaro?" Ta sake faďa cike da jin haushinshi. "Karya kikeyi, wnn yaro d'anane jininane." Ya faďa a tsawace saida suka razana daga ita har Mahmud. Fashewa ta daďa yi da wani kukan wanda ya qara tsananta kukan Mahmud. Da sauri yasa hanu ya ďauki Mahmud yana jijjigashi, "Sorry my lovely son, na tsorata ka ko, am so sorry my boy." Durkusawa yayi a gabanta rike da mahmud da yayi luff a jikinshi yana sauqe ajiyar zcy. "Khadija, ko ki so ko ki ki wnn yaro nawane jininane dan naji hakan a jikina, na jima ina ganinshi a mafarkina, najima ina jinshi cikin raina, Allah ya jarabceni da qaunarshi tun ban tab'a ganinshi ba." Ya karashe maganar kamar zaiyi kukan shima. Cikin kuka tace ..... *F.O.W* [8/22, 9:54 PM] +234 806 071 2446: * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *7* *Dedicated to Hauwa S.Zaria. (Mmn Uswan.)* ~"Me kuke so dani?" "Yarona nakeso." Ya bata amsa ba tare da fargaban komai ba, dan ya riga ya tabbatarwa kanshi ďanshine. "Ka cuceni Uncle Smart, ka rabani da farin cikina, ka sani rainon ciki da goyon shege, abokinka ya wargaza bikina da ake shirinyi saura sati biyu ya ďaukeni, kazo ka cutar min da rayuwa, gashi yanzu ka sake wargaza auren da ake shirin yi nan da wata ďaya." "Enough." Kada ki kara sheganta min ďa, da ubanshi da gatanshi, bana so." Ya faďa cike da b'acin rai. Sai kuma ya sassauta murya. "Khadijah, rabon haihuwan wnn yaro ya sa scorpion ďaukeki, snn ya tabbata rabon nine mahaifinshi yasa scorpion bai miki komai ba, har na ganki naji baxan iya barinki wajenshi ba, rabon wnn ďan yasa na kusanceki ba tare da na shirya hakan ba, wlh khadija ba halina bane, i regrated everything, but, kaddara ta riga fata, dama can Allah ya kaddari akwai rabon haihuwa tsakaninmu, so kema ki sa hakan a ranki . Marairaice fiska tayi "Yaushe zan koma gida." "zaki koma amma nan zaki barmin yarona ko?" Zaro ido tayi ta shiga girgiza kanta, kafin tayi magana yace "Kinyi sallah?" Shiru tayi tana tunanin, shi wnn wani irin mutumne, gashi yana tare da 'yan iska 'yanfashi, kuma tana tunanin sana'arsu ďaya ne, amma wani lokacin halayenshi na mutanen kirki." "Ga ďaki akwai toilet a ciki kije kiyi alwala." Ya katse mata tunaninta. Kallon jikinta tayi ta daďa b'ata fiska, "To a haka zanyi sallan?" Shima kallonnata yayi daga sama har qasa, sai yaga ta ďan rame ba kamar yanda ya santa na, sanye take da zani da kuma Karamar bakar riga, top, sai bakar hular da ta rufe kanta dashi. "Oh, sorry, gashi bansan zaki zo ba da na taho miki da kayanki daga jos. Shiru tayi tana binshi da kallo har yanzu bata daina mamakin halayenshi ba. A hankali ya kwantar da Mahmud da ya koma baccinshi kan kujera, fitsari har ya fara jika mishi kayanshi,dan pampers ďin ta cika tapp. "Ina zuwa." Ya faďa lokacin da yake mikewa. Har ya fita bata bar binshi da kallo ba. Bata san me yasa kalamanshi suke kashe mata jiki ba, bata me yasa take jinshi kamar wani ďanuwanta ba, hankalinta yafi kwanciya dashi akan su scorpion duk da abinda ya mata kuwa. Tana nan zaune har ta fara gyangyaďi ya shigo da manyan ledoji a hanunshi ya ajiye mata, ya tashi ya shiga kitchen, ba da jimawa sosai ba ya fito da ruwan zafi a rubber bucket, ya shige ďakin da ya nuna mata. Tana ďan gyangyaďinta taji yana cewa " Tashi kije kiyi wanka kiyi sallah. Sum sum ta tashi ta shige ta barshi tsaye yana kallon mahmud. Ruwa masu ďumi ta samu ga soso, sabulu, brush, maclean, tsaf tayi wankanta, tana fitowa kuma taga leda kan matrass dake cikin ďakin ta buďe, nan taga dogayen riguna guda uku, da hijabai biyu, sai sleeping dresses ma biyu,undies da pampers, sai kayan mahmud masu kyau, sai mayukan shafawa, da turaruka. Ďaya daga cikin rigunan ta ďauka ta saka ta hau kan sallayan da ta gani a shimfiďe ta fara jero sallolin da ake binta. Baccine yake neman fin karfinta ga idanunta tsami, haka ta idar da sallar ko addua bata samu tayi ba ta fito dan ta ďauki mahmud. Nan ta samu smart kan sallaya zaune ya ďaga hanunshi yana addua. "Ko adduar me yake yi, oho, ko kunyar Allah ma baya ji. Ta ayyana hakan a ranta. Kawar da kanta tayi daga kallonshi tasa hanu zata ďauki Mahmud. "Ga abinci nan kici kafin ya tashi." Ya faďa yana nuna mata ledar take away da yayi mata. "Na koshi." Tace a hankali, duk da yunwan takeji sosai da sosai. "Khadijah bakison komawa gida, da alama kin fi so mu zauna tare, indai zaki rika yimin gardama kuma ki ka sakin jikinki, saidai muyi ta zama a haka, baza ki koma gida ba." A hankali ta ďauki ledar abincin da plate ďin da ya ajiye mata ta koma ďakin da ta fito, taci tayi nakk, kafin ta tattaro sauran da plate ďin ta fito dasu. Har yanzu yana zaune kan sallayar,saidai ganin ta fito yasashi mikewa ya karb'i kayan hanunta ya kai kitchen, yana cewa " tsaya a haďa ruwa shima ki mishi wanka." Ruwan zafi ya sake fitowa dashi yaje ya surka kafin ya umurceta taje tayi mishi wanka. Tana tub'e mishi kaya ya farka, sbd haka ta shiga tayi mishi wanka ta shirya shi cikin wani overall mai laushi daga cikin kayan da ya kawo. Nono ta bashi, yana sha tana tunanin yanzu idan da gaske yakeyi zai mayar da ita gida ta bar mishi Mahmud yaya zatayi. Yaro yana koshi ya saki nono ya dasa suruntai irin na yara, yana yi yana cilla kafafu, itako har idanunta sun fara rufewa daga zaunen. "Khadijah." Taji shi yana kiranta daga falo. Bata amsa saidai ta tashi taje rike da mahmud a hanunta har wani rinjayarta yakeyi sbd tsalle tsallen da yakeyi, gashi ita kuma bacci yana neman yaci karfinta. "kawo shi kije ki kwanta." Ya faďa yana karb'anshi daga hanunta. Bar mishi shi tayi taje tayi kwanciyarta, tun tana jin yana mishi wasa har barci ya kwasheta. Bata ma san lokacin da ya shigo dashi ba,saida ya kwankwasa mata kofa ta tashi tayi sallar asubah ta ganshi kwance kusa da ita. Tana idar da sallah nan kan sallayar ta kwanta taci gaba da baccinta, ba ita tashi ba saida tajishi kamar a mafarki yana cewa. "Mummy a tashi a bamu abinci." A hankali ta buďe idanunta, taga guri ysyi haske tarr, mamaki ya sata ware idanu, wnn wani irin baccine, idan satar yaron yayi niyyar yi ma ya saceshi har suyi nisa bata sani. Wata zcyr tace mata, aikin banza, kema da hankalinki da wayonki da girmanki, aka sace ki balle ďan wnn jinjirin." "Tunanin me kikeyi haka khadijah, yaro yana jin yunwa." Karb'anshi tayi ta sauke kai kasa, shi kuwa ya harďe hanu ya tsaya yana kallonta. "Bashi mana." Ya ce ganin mahmud yana ta lalub'an abincinshi itako tayi mirsisi. "ka fita mana toh." Ta faďa tana turo bakinta. Murmusawa yayi ya juya ya fita daga ďakin. Sai can jimawa ya leko yace ta fito ta karya. Tea mai kauri ya haďa mata, da chips da kwai, ya kuma kara ce mata idan bata saki jikinta tana ci ta koshi ba komawa gida. Shigewa ciki yayi ya barta ta karya dan yaga alamar bazata sake taci a gabanshi ba. Wankanshi ya sheko ya fito da shirin fita, kamshin turarenshi ya buďaďe ko ina. ta gama ta tattara gurin tana zaune ta ajiye Mahmud kusa da ita yana ta jan jiki yana koyon rarrafe. "Ku shiga kuyi wanka, ni zan fita sai zuwa anjima zan dawo, ga wnn idan akwai abunda kike bukata ki kirani." Ya faďa yana ajiye waya kusa da ita. "Ki kula min da my boy." Ya faďa tare da pecking ďin Mahmud a goshi. Ba tare da tace komai ba ta ďaukeshi ta shige cikin ďakin dan suyi wanka. Wayarshi ce tayi ringing, ya lalub'o daga aljihun suit đinshi. Ganin scorpion ne yasa ya murmusa tare da karawa a kunne. "Kaida ďan iska ne smart, irin wnn babban kyauta shine ba kira balle godiya?" Abinda ya fara ce mishi kenan. "Sorry friend, I was confused ne, wlh." "Confussion? Why." "Saboda banyi expecting ganinta cikin sauki haka ba." "Ubanka, shege, kai ka ganta cikin sauki mu kam saida muka ci ubanmu har munyi give up kafin muka ganta. "Sorry." Ya kuma cewa yana shafa sajenshi yana ďan murmusawa. "So ya kaga yaronmu?" "Very cute wlh, i love him." Dariya ya sheqe dashi yace "Daga na ganshi nasan wnn smart junior ne, shege smart Ustazun karya, what u guys are doing is not gud, is not fair, kai da ka tashi sai kayi mai gaba ďaya har ka riga mu ganin magaji." Ya karasa yana dariyar shaqiyanci. Dariyan yake tayashi kasa kasa, yace "Ko yanzuma ďauko ta da mukayi is not fair, dan bai kamata mu zauna gida ďaya tare ba." "I see, so bakayi appreciating effort namu ba kenan?" "No nayi appreciating, dan baka ji daďin da nakeji ba da na gansu, kamar an sauqe min wani nauyi a kaina nakeji, saidai ina tausayawa yarinyar da parents ďinta ne." "Look smart, kasan bazai yiyu ka kai kanka gidansu yarinyar nan ba dan kanaso ka ganta kaga yaronka, dan wnn tonuwar asirinmu ne gaba ďaya, best solution shine ďaukota da mukayi, so is left to you kayi kokari kayi wining heart ďinta, ka aureta, so that ka kula da yaronka, idan kuma yaron kakeso ba ita ba sai taci gaba da kula maka dashi idan ya girma sai ka karb'i yaronka ka sallameta ko ya ka gani." "Thank u friend, i will think about it, ina Billy da Nass?" "Suna can suna huce gajiyar hawa da sauqan da mukayi tayi a Gembu, kuma zakaci ubanka a gunsu idan baka yi musu bangajiya ba, ni ďinma dan bani da zcy ne." "Sorry, kaima zan kirka ai my friend." "Banza, idan kaso kada ka kirani, ba ka samu abinda kake nema ba." Yana gama faďin haka ya yanke call ďin ya barshi da murmushi yana girgiza kai. "Scorpion." Ya kira sunan a hankali,a ranshi yana tunanin hali irin na abokinshi, idan yaga dama kirki ne dashi idan kuma ya juye sai yafi kunama harbi. ~zaune take a tsakiyar falon babu abinda take tunani sai iyayenta da 'yan uwanta, hakika mutanennnan ba karamin ďaukar alhakinsu sukeyi ba. Tunani take yaya rayuwarta zata kasance nan gaba, shin zata sake ganin iyayenta ko ta rabu dasu kenan. Tunanin gwada guduwa tayi ta tashi tayi nufin buďe kofa ta fita ta jita a kulle. Jinta takeyi wata iri, kamar an ďaure ta. gata zaune guri ďaya, ita ba aiki ba ita ba fita ba. Ko wani hali Hamma shehu yake ciki yanzu, ta tuna hakan lokacin da ta kallo mahmud kwance yana ta ja da ciki. Da d'add'aya take tunosu daga iyaye, yayyu da kannenta tana sharar kwalla. Buďe kofar taji anyi tayi saurin goge hawayenta, abinci yazo ya ajiye mata tare da yiwa mahmud wasa ya sake sallamarsu ya fita. Sai dare ya sake dawowa da kaya niki niki. Tana cikin ďakin ya kwankwasa mata kofa. Buďewa tayi ta fito ta tsaya tana kallonshi. "Ba ko sannu da zuwa khadijah." Shiru tayi tana jin kamar ta rusa kuka. "Ina my boy?" "Yayi bacci." Tace mishi. "Zo ki gani." yace mata yayin da ya fara tafiya. Bayanshi tabi yana zaune kan kujera ta zauna a kasa. Manyan jakunkunan da ya dawo dasu ya fara buďewa. Suturane kala kala, nata, kama daga zannuwa, arabian gowns, english gown, takalma da sauransu,da kayan mahmud, ga jibgin kayan wasa suma kala kala. Kuka ta fara yi sosai sbd ganin kayan ya tabbatar mata da cewa zaman din din din, zatayi a gidan. "Khadijah kukan me kikeyi?" Ya faďa a tausashe yana kallonta. "Uncle smart shikenan na rabu da iyayena , kaji tausayina ka mayar dani gida, wlh bana son kayan." Ta faďa cikin kuka. Kusa da ita ya dawo ya zauna tare da tankwashe kafafu, Shima kamar zaiyi kukan yace. "Khadijah ko kađan bani da niyyar cutar dake, tun da na fara ganinki tausayinki ya ďarsu a zcyta nake kuma jinki tamkar wata b'angare na jikina, asalima wnn ďaukokin da akayi bani nace a ďaukoki ba, damuwar rashin ganinki ne yayi min yawa, ga kuma ďana danake yawan gani a mafarki suka taru suka min yawa, har su nass suka gane ina cikin matsala, har suka nemi sanin damuwata, ni kuma na sanar dasu. A rayuwata ban tab'a shiga damuwa kan mace ba sai a kanki, shi yasa abokai na suka yanke shawarar ďauko min ke ba tare da na sani ba dan su faranta min. "Khadijah kin bani farin ciki a rayuwa duk da ba ta hanyar aure na sameshi ba, bani da kowa bani da gata sai wnn yaro da kika haifa min, dashi nake gadara, shi kaďai ne jinina da na sani a duniya, shi kaďai zan kalla inji farin ciki, shine jinina, dangina, shine abin alfaharina. Khadija idan ban muku gata ba wa kike tsammanin zanyi wa, wlh zan iya mallaka muku duk a bunda na mallaka in dai zan faranta muku ke dashi. Khadijah ki bani dama inji ďumin yarona a tare dani shi ma yaji na mahaifinshi, ki taimakeni ki bani wnn daman, ni kuma nayi miki alkawarin zan maida ke gurin iyayenki." Wani irin tausayinshi taji yana ratsata, to ina iyayenshi, idan mutuwa sukayi ai ko yaya tasan bazasu rasa wasu dangin ba." "Ina iyayenka to?" Ta tambayeshi tana mishi kallon tausayi. Shi kuwa ganin kalamanshi sunyi tasiri akanta yasashi daďa Marairaicewa. "Ban sani ba khadijah, nima haka na tashi na ga kaina bani da kowa, sai .... Shiru ya ďanyi kafin yace "Khadijah zaki barmin shi." "Cabb, in bar maka shi shima ya girma ya zama ďan fashi." Ta tuna hakan aranta." "Uhm, khadijah, kinyi shiru." Girgiza kanta ta shiga yi kafin tace. "Bazan iya ba, nima ina sonshi, ina son zama dashi." Wani irin murmushine ya sub'uce mishi. "Babanshi fa?" Ya tambaya yana yi mata kallon cikin ido." Kasa tayi da kanta tana mai jin kunyar cewa da tayi tana son mahmud a gabanshi.. *F.O.W* [8/22, 9:59 PM] +234 806 071 2446: * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *8* *Dedicated to Maryam A.I Gital* ~Leka fiskarta yayi yana 'yar dariya "Ana son ďa ba a son uba anya kuwa hakan mai yiyuwa ne?" Jin tayi shiru yace. "Share hawayenki muyi magana." Sharewan tayi burinta bai wuce taji yace ga ranar da zata koma gida ba. "Baki faďa min sunan yarona ba." "Mahmudu." Tace dashi kanta a kasa. Waro idanunshi yayi yana kallonta. "Mahmud." Ya maimaita, yana murmushi, yace "Very nice." Wa ya raďa mishi sunan?" "Baffana, baban Hamma shehu." "Waye Hamma shehu?" "Yayana ne, kuma shine...?" Sai tayi shiru,tana matsar kwalla. "Ko shine dama zaki aura?" Gyaďa mishi kai kawai tayi, hawaye suna daďa zubo mata. Tsura mata idanu yayi kafin daga bisani yace "To ki bar kukan mana." Share hawayen ta shigayi, a ranta tana adduar Allah yasa ya tausaya mata ya maida ta gidansu. ~"Hamma shehu, kaci abincin mana." Habibatu dake zaune tun ďazu tana kallon Hamma shehu da aka kawo mishi abinci amma ko kallo ďaya baiyiwa abincin ba, tace. Ko kallonta baiyi ba balle tasa ran zai amsa mata. Fita tayi daga ďakin ta sanar da Baban Deeja da yanzu shima bai cika fita ba sbd baijin daďin jikinshi. Cikin faďa ya fara mishi magana. "Haba shehu, me kakeso ka maida kanka ne, yau kwana uku kenan kana nan, ba ci, ba magana, anya rayuwa zata tafi a haka. Musulmin kwarai an sanshi da yarda da kaddara, idan har ka ďauki wnn mataki hakika ka butulcewa Allah ne da ya maka ni'imomi da dama waďanda bazasu lissafu ba. Shin hakan da kakeyi shi zai dawo da ita, ko kana tunani zai canza wani abu daga littafin kaddara da Allah ya rubuta mata. Ganin hawaye na shatata daga idanunshi yasashi sassautowa. "Hakuri zamuyi shehu, haka Allah ya kaddara mata ya tsara mata rayuwarta, kowani mutum da ka gani da akwai kalar jarabtar da Allah yake masa ,mu kuma irin tamu jarabawarmu kenan, sai muyi kokarin cinyewa ta hanyar fawwalawa Allah al'amarinmu. Allah daya kub'utar da ita daga farko shi zai sake bayyanar mana da ita indai muna da rabon sake ganawa da ita, kayi haquri shehu, ga mahaifiyarka can tana kwance, kai ya kamata a matsayinka na babba ka rika kwantar mata da hankali ba kuma kaima kayi ta sawa kanka damuwa ba. Addua ya kamata mu bi ta dashi, Addua bata faďuwa kasa banza, da yardar Allah zamu ga ribar hakurinmu." Gyaďa kanshi yakeyi cikin gamsuwa da kalaman baffannashi. "Na gode Baffa." "Yauwa, Usmanu, Allah ya maka albarka. ~Yau kwananta huďu kenan a gidan, duk wani kulawa da ta dace yana bata domin ganin ta kwantar da hankalinta, kuma yana kokarin janta a jiki ko dan su samu fahimtar juna amma sam har yanzu taki sakin jikinta dashi, gani takeyi kamar abunda ya faru wancan karo zai sake faruwa. Ko da wasa bata yarda ta yi zama na tsawon lokaci dashi, haka ko yaya bata yarda ta bawa Mahmud nono a gabanshi ,kamar yanda bata yarda taci abinci a kusa dashi. A wnn lokacinne kuma ya kammala aikin da ya kawo shi ya sanar da abokan hulďanshi. Su shida sukazo, bayan nass, scorpion, billy, sai kuma wasu arna guda uku, Sam, Emeka, da Chris. Tana daga cikin ďaki tana jin hayaniyarsu, Mahmud sai kiriniya yakeyi yanaso ya fita sai rirrikeshi takeyi, ita dai addu'a takeyi Allah ya kareta daga sharrinsu. Tana jin lokacin da yake cewa kada su nemeshi shi ya gama aikinshi, suyi nasu kawai sai sun haďu a Jos. Washegari kuwa babu yadda baiyi da ita ba su koma jos tare taki yarda. Fita sukayi ya kaisu guraren shakatawa, Super market, har saloon. Sosai taji dađin fitannasu dan ta ga gari gari ya ganta, dama kuma zaman guri ďayan ya isheta. Ko da yace zai kawo mai tayata zama da yi mata aiki , sai cewa tayi bata so, dan ita duk a tunaninta sato watan zasuyi su kawo mata, sbd haka tace zata iya aikin da kanta, sai mai wanki da dama yana nan sai kuma mai kula da tsaftar gidan, sai gate man. Duk abinda ake buqata na abinci ya tanadar mata ya kuma nuna mata yanda zatayi amfani da kayan kitchen. Ita dai sai kallon ikon Allah takeyi yadda gidan yake kamar na wani mai mata. Ba don yaso ba haka ya tafi ya barsu nan Bauchi, bayan ya koya mata yanda zata yi amfani da babbar waya, da kuma electronics na falon, dan ďebe kewa, snn kuma ya ja musu kunne sosai kan kada suyi kuskuren barinta ta fita. Sati guda da barinshi Bauchi amma gaba ďaya gidan jinshi take ya mata faďi, gwara mata yana shiga da fita tana ganinshi ko da ba wani sakewa dashi takeyiba, hakan yafi mata. Ga dai komai na jin daďi an tanadar mata amma jinta take tamkar marainiya. Duk da kuwa kullum sai ya kira sau biyu sau uku sun gaisa ya tambayi lafiyarta dana mahmud. Tasha trying layin Hamma shehu da na Babanta sam basa shiga kasancewar garin akwai matsalar rashin service dole sai in su suka nemi gurin service suka kira mutum. Kwananshi goma ya dawo Bauchi, zuwan cikin dare yayi sbd haka bata ma san yazo ba. Fitowarta kenan daga ďaki zata shiga kitchen dan samawa kanta abun karyawa ta ganshi zaune kan carpet sanye da farar jallabiya, hanunshi rike da casbaha yana ja. Ja da baya tayi da sauri tana mishi kallon mamaki dan sam batayi tsammanin ganinshi ba tunda bsi sanar da ita zai zo ba. 'Ya dai Khadijah ba dai tsorata ki nayi ba." Ya faďa fiskarshi ďauke da fara'a dan ba karamin farin ciki ganinta ya sashi ba. "Sannu da zuwa ta mishi da sassanyar muryarta snn tayi saurin komawa ciki kasancewar sleeping dress ne a jikinta riga da wando masu tsantsi." Zani ta ďaura ta sanyo hijabi daga cikin hijaban da ya saya mata kafin ta fito. Har kasa ta duka ta gaisheshi tana mishi ya hanya kafin ta tashi zata shiga kitchen." "Amm, nace ba." Juyowa tayi tana kallonshi, idanunsu suka sarke da juna take taji abu na tsirga mata, gabanta ya hau faďuwa kaďan kaďan. "Ina Mahmud?" A daburce tace "Yana bacci." Tayi saurin barin gurin sbd irin kallon da yake binta dashi. Tana cikin kitchen taji shi a bakin kofa yana cewa "A haďa breakfast ďin da ni, mummy, ko bazan samu ba?" "Zaka samu." Tace idonta na kan abinda takeyi. Ya jima tsaye a wajen yana kallon yanda take ayyukanta cikin natsuwa da tsafta. "Ko inzo in tayaki." Ya sake tambaya. "Kaji min mutum da neman magana. kamar irin kullum shi yake tayani nnan. Ta faďi hakan a zcyrta, a bayyane kuma tace. "A'a na gode." Ba tare da ta kalleshi ba. A ranar kam kusan wuni Mahmud yayi a hanunshi dan babu inda yaje, yana makale da ďanshi, tsakaninta dashi sai in yaji yunwa. Ita kuwa takura kanta ta shiga yi da zaman cikin ďaki girki kawai yake fito da ita. Kwananshi uku da zuwa Bauchi, Mahmud ya fara wani zazzafan zazzab'i cikin dare. Cikin bacci tajishi yana nishi sama sama. A tsorace ta tashi tana tattab'a jikinshi, taji zafi rau, baranma ta kanshi. Jikinshi duk ya b'aci da amai. Kafin tayi wani yunkuri taga ya fara wani kakarin aman, tun yanayi abu na fita har ya koma sai kakarin kawai yake yi. "Mahmudu me ya sameka." Ta faďa cikin kuka tana tub'e mishi riga. Ganin idanunshi na neman juyewa gaba ďaya ta rikice ta rasa abinda zatayi mishi. Kwantar dashi tayi ta fita a guje cikin tashi hankali tunowa da tayi ba ita kaďai ne a cikin gidan ba. Kwankwasa kofar takeyi kamar zata b'alla, tana kiran " Uncle smart." A razane ya farka ya zo ya buďe kofar yana kallon ta cike da tsoron jin,abunda ya hargitsata cikin dare haka. Hanunshi ta riko cikin tashin hankali tana cewa "Zai mutu ya barni, uncle smart." A razane yace "Waye." "Mahmudu ta faďa tana daďa rike hanunshi tare da tsalle tana doddoka kafa tamkar maijin fitsari. A tamanin ya fizge hanunshi ya faďa ďakin ya nufi inda Mahmud yake kwance. Duk ya gama galabaita cikin ya d'akale tamkar babu kayan ciki, nishin ma yanzu kaďan kaďan yake fitarwa. Bai tsaya b'ata lokaci ba ya zareshi ya fita da sassarfa daga cikin ďakin, ya shige nashi ya ďau keyn mota ya fita a guje, ya shiga motarshi tare da danna horn da karfi, wanda ya razana gate man yayi saurin wangale gate . Bin bayanshi tayi tana kuka, kafin ta karasa tuni ya ja mota yayi gaba, hakan yasa ta kara fashewa da kuka tare da jifa da hijabin da ta ďauko, dan sai taji haushi ďauko hijabin da ta tsaya yi. Yana isa asibiti yayi sa'an samu wani doctor, ya karb'eshi. "Me kuka tsaya yi har saida jikinshi yayi zafi haka kuka kawo shi asibiti, irin wnn zuwa anjima kaďan zaka yaro ya fara suma azo ana shiga tashin hankali, alhali laifinku ne tunda yafara ta kamata ku kawoshi, snn idan jikin yaro yayi zafi haka shafa mishi ruwan sanyi ya kamata a rikayi ko da ďan towel zaiji relief, amm.... "And what are waiting for? Ka duba min yaro ka bashi taimakon da ya kamata ba surutan banza nace kayi min ba, aikin banza kawai, believe me idan wani abu ya samu yaronnan u will be in for it idiot ." Ya faďa a fusace cikin tsantsan bacin rai saida doctor ya tsorata da yanayinshi. Take ya maida hankalinshi kan yaron yana bashi taimakon gaggawa, shiko yana tsaye kamar wani soja sai huci yakeyi, idonshi kan Mahmud. Bashi ya samu nitsuwa ba saida yaga numfashin yaronya daidaita an basu gado aka ďaura mishi drip. Nurse ce ta tambaye maman yaro sai a snn ya tuna da ya barta a gida, yanzu tana can cikin *Tashin hankali* Rokon nurse ďin yayi da ta kula mishi da yaron zaije gida ya taho da mamanshi. Gudu yake tsulawa yana zullumin halin da take ciki tunawa da yanda ta rikice lokacin da take sanar dashi maganar ciwon mahmud. A kofar gida yayi parking ya shiga cikin gida, tun daga tsakiyar gidan yaga hijabinta a yashe a kasa, ya duka ya ďauka zcyrshi na harbawa yana tunanin kada dai tayi karambanin binsu a yanda take hankali a tashe. A balcony ya sameta tana zaune a kasa ta hađa kai da gwiwa. Kusa da ita ya tsuguna cikin tausayawa yasa hanu ya shafa kanta dake buďe babu hula ba ďankwali. D'agowa tayi sauri ganin shine tayi saurin mikewa tana kallonshi cikin kullewar kan rashin ganinshi tare da Mahmud. Kallon idanunta ya tsaya yi ganin yanda idanun sukayi luhu luhu da gani tasha kuka ba kaďan bama. Kallon da yake mata ne ya daďa tsoratata take taji jiri na ďibanta. Baya tayi zata faďi yayi saurin tarota ta faďo jikinshi. A kiďime yace "menene Khadijah?" "Ya mutu ko? Nasan ya mutu." Ta faďa cikin kuka. Buga bayanta ya shiga yi a hankali yace mata "Ki kwantar da hankalinki, Mahmud bai mutu ba yana asibiti kuma jikin da sauki." D'agowa tayi tana kallon idonshi dan son gaskata abunda ya faďa." "Da gaske?" Ta sake tambaya a sanyaye. "Believe me, yana raye bai mutu ba." Gam ta rike hanunshi "Ka kaini in ganshi Uncle smart." * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *9*&10 ~Lumshe idanunshi yayi na secs, goma snn ya waresu a fiskarta, daga sama har kasa ya kalleta, ya matse hanunta dake cikin nashi da ďan karfi kafin yace. "Amma dai ba a haka zaki je bako?" Kallon jikinta tayi, doguwar rigar baccine a jikinta, peach colour, daga ciki akwai karama mai hanun vest wacce da kaďan ta wuce gwiwarta sai na saman da ya sauka har qasa,mai yalwar hanu, shi kuma gaban a buďe yake. Kunya ce ta rufe ta tayi saurin zame hanunta ta ruga tayi ciki da gudu. ,"Ga hijabinki." Ya faďa yana dariyar gudunnata. Ko kallonshi bata tsaya yi ba ta arce. Har suka koma Mahmud yana bacci bai tashi ba, nan suka zauna dukansu biyu suka tsura mishi idanu, kaďan kađan Deeja take sharar kwalla sbd gani take kamar zata rasa shi. Shi ko smart kallon su kawai yakeyi a ranshi yana tunanin irin karfin soyayyar dake tsakanin ďa da uwa, kamar ba akanshi ranar take mishi kukan ya cuceta ya sata goya ciki da haifan shege ba, ji yanzu yanda duk tabi ta rikice, take kuka duk da taga yanyin jikinnashi da sauki ba kamar yanda suka bar gida ba. Wani abu sai uwa, shi kuwa ko wacece tashi uwar?Tana raye ko tana mace ? Allah masani. Kallonta ya kuma yi yaga ta kifa kanta kusa da kan Mahmud. Gyaran murya yayi yace "Khadija hau gadon ki kwanta mana." Girgiza mishi kai tayi takuma maida kanta ta kifa. A haka har drip ďin ya qare aka cire mishi, sai da sukayi sallar asubah ya farka. jikin kam da sauki sosai, saidai idan yasha nono yana amayarwa, hakan yasa aka rubuta musu magunguna har da na amai. Kwana uku sukayi a asibiti aka sallamesu, cikin kwanaki ukunnan tare suke wuni su kwana gurinshi, cikinsu sai ka rasa gane wa yafi wani son Mahmud wa kuma yafi bashi kulawa, duk da kawaici da kunya da take kokarin nunawa na fulani, amma hakan bai hana idanunta bayyana irin qaunar da takewa Mahmud ba. Wnn karo sosai yayi ta zagayawa dasu cikin garin bauchi, Sabo sukayi sosai, ba karamar shakuwa sukayi da Mahmud ba, har ya zamanto da ya ganshi sai ya fara tsalle yana dariya tare da mika mishi, wani lokacinma zata shiga ta barsu a falo nan barci zaiyi awon gaba dasu dukansu biyu. Wani lokacin har goyashi yakeyi yace ta sa mishi zani, abun mamaki yake bata ba kaďan ba, wani lokacin kuma sai tsoro ya shigeta ganin yanda yake daďa manna Mahmud a jiki, anya zai barta ta koma, in kuwa ya barta ta koma ba lallai ya barta ta tafi da Mahmud ba dan shaquwar tayi yawa, ya kwallafa ranshi sosai akanshi. snn kuma ritsata yakeyi dole sai ta koya mishi fulatancin garinsu, gaba ďaya yace su daina magana da hausa ba turanci kuma sai fulatanci, duk da cewa yawanci kwab'awa yakeyi tayi ta mishi dariya kafin ta gyara mishi, hakan ya dage kuma yana picking sosai. Kwanaki tara ya qara yace zai koma jos, yana da ayyuka a can dan yanzu ma sbd su yazo Bauchi, ita kuma ta ce bazata bishi jos ba, ta raba mishi hankalinshi gida biyu. Ita dai tana shiru bata ce komai ba, saida ya tambayeta ko zasu bishi ne? Nan kuma tace "A,a" Duk da dai wancan karon da ya tafi gidan bai mata daďi ba, amma tana ganin gwara suna rage kusancin da ke tsakaninsu sbd gudun fađawa tarkon shaiďan, Allah ma yasa ta lura shi ďin mai tausayi da kirki ne ba irin su scorpion ba da komai gaba gaďi yakeyi ba tausayi babu tausasawa. Kwananshi huďu a jos ya sake zuwa don yi musu sallama zaiyi tafiya zuwa Umuahia. Tunda ya faďa mata maganar tafiyar taji Hankalinta ya tashi gabanta ya shiga faďuwa, duk yadda taso ta b'oye saida ya fahimta. "Menene khadija ko ba kya so inje ne, sai in fasa?" Ya tambaya bayan ya kare nazarin yanayinta. Saita kanta tayi kafin tace "Ni na isa." "Kin isa mana har kin wuce ma, idan kince kada inje sai in fasa kawai." "Da zan iya da nace kada kaje ." Ta ayyana hakan a ranta. "Me kike tunanine haka?" "Ba komai." Tace kafin kuma ta cikin in.ina tace. "Nikam har yanzu baka gama ganin mahmudun bane, ka maida mu gida?" Dariya yayi mai sauti har jerarrun fararen hakoranshi masu ďauke da ďan siririn wushirya suka bayyano. Rass taji zcyrta ya tsinke, kullum tana ganin akwai wasu abubuwan da idan yayi yana mata yanayi da Hamma shehu, amma yau ganin kamannin tsarin hakoransu yatsoratata, kasancewar bata tab'a zuba mishi ido ta kalleshi da kyau kamar na yau ba, balle har tace ga yanayin dariyarshi, duk da dai bai cikayin dariyar ba yafi yin murmushi, saidai yawanci idan yana wasa da Mahmud takanji sautin dariyarshi. "Kin gaji da ganina ne Khadija?" Ya tambayeta yana langab'e kai. Shiru tayi tayi qasa da kanta. "Ni kuma gashi ban gaji da ganinku ba, a kullum kwanan duniya so na naganni tare daku dan kune sanyin idaniyata, kune farin cikina." Rau rau tayi da idanunta kamar zatayi kuka, da alama duk kokarin da tayi wajen sakin jikinta dashi baiyi tasiri ba, tunda har yanzu baida niyyar maidata gida." Katse mata tunaninta yayi da cewa "Da farko ina tunanin ko Mahmud kika bar min is ok, amma yanzu ina ganin rashin mummyn mahmud ma zai iya zama babban gib'i ga rayuwata. Any way ki kara hakuri barin je in dawo zan duba in gani." Daga haka dukansu suka yi shiru kowanensu da tunanin da yakeyi a ranshi. Sayayya sosai ya musu, kama daga kayan abinci, kayan sawa da duk wanin abun amfani, ita abinma har mamaki yake bata kamar baisan zafin kuďi ba. Washegari yana idar da sallah ya sallameta tare da ajiye mata kuďi masu yawa yana cewa. "Ga wannan ko akwai abinda zaki buqata dan bansan iya adadin kwanakin da zanyi ba nima, sai na samu na gama abinda ya kaini zan dawo, ki kula min da kanki, ki kula min da Mahmud. Jikinta ne yayi sanyi, bata tab'a jin haka idan zaiyi tafiya ba sai wnn karo, kasa kallonshi tayi, sai harbawa zcyrta keyi ta rasa dalili. Tashi yayi ya shige ďakinta ya duka ya sumbaci Mahmud, tare da cewa "Sai na dawo swtheart." Inda ya barta nan ya dawo ya sameta, tana zaune duk jikinta yayi sanyi. "Khadijah, zan tafi , nasan zanyi kewarku sosai, Allah ya sada mu da alkhairi." D'aga mata hanu yayi ya rataya travelling bag ďinshi ya fara tafiya, har yakai bakin kofa ya dawo. "Khadija bakiyi min addu'a ba." "Addu'a." Ta maimaita hakan aranta. "To ince Allah ya bada sa'a, ya tsare." "Sa'an sata kenan zan roka mishi ko meye." kallonshi tayi taga shi ďinma ita yake kallo amma kamar tunani yakeyi. Haka kawai ta samu kanta da ce mishi "Allah wartire jam." (Allah ya dawo dakai lafiya.) "Miyetti khadija." (Na gode khadija." Ya faďi cike da jin daďin addu'ar da tayi mishi. "I'm going to miss u." Ya faďa kafin ya juya ya fita. Tun da ya tafi take jin zcyrta ba daďi, sai tunani takeyi ba mamaki fashi zasu je yi, idan sunyi sa'a su dawo lafiya, idan babu sa'a kuma a kama su ko ma a kashesu. Take taji wasu hawaye masu ďumi suna gangaro mata, ita kanta ta rasa gane dalilin dake sata damuwa kan tafiyarshi. "Allah ya tsare ta faďa a bayyane." Gurin mahmud ta koma ta zauna ta tsura mishi ido sai kallonshi takeyi ita kanta bata san tunanin me takeyi ba. Zuciyarta ce ta tambayeta , me yasa tun tuni bata tab'a yi mishi addu'ar shiriya ba, take tasawa ranta duk lokacin da tayi sallah zata rika yi mishi addu'ar Allah ya shiryeshi. Wnn karon kam tasan cewa ba karamar shakuwa sukayi da uncle smart ba dan sosai rashinshi ya daketa, duk da yana kiransu yaji lafiyarsu, kullum sai ta tambayeshi yaushe zai dawo, shi kanshi har mamakin hakan yakeyi. Addu'a kuma ta dage duk lokacin da tayiwa kanta tayiwa iyayenta sai tayi mishi. Satinshi biyu a gurin yace mata zai dawo washegari. Tun da safe da ya kirata bai kuma kiranta ba, tun tana basarwa har abin ya fara damunta ganin ba haka ya saba ba gashi yamma tayi. Kasa daurewa tayi ta fara neman layinshi, amma switch off ake ce mata, wasa wasa har washegari babu bshi bbu dalilinshi. Haka tayi ta zama cikin zullumi da tunanin ko me ya faru dashi, k'arshe dai zcyrta ta fara raya mata an kasheshi ne kawai. Haka take tasa Mahmud a gaba tayi ta kuka baranma idan ta tuna irin syyyr da yake nunawa Mahmud. Duk yanda take marmarin ta fita daga hanunshi ta koma gida yanzu babu, burinta bai wuci taji koda labarin halin da yake ciki bane. Kwance take bacci ya gagareta sai tunani takeyi, ko wani hali yake ciki yanzu. Yau kwana goma sha bakwai kenan rabon da ta jishi. Gajiya tayi da tunanin ta mike taje ta ďauro alwala tazo ta fara jera nafilfilu ko wani sujada da tayi sai tayi mishi addu'a. Tana cikin haka taji tsayuwar mota cikin gidan, da sauri ta lalub'o wayarta ta kunna, karfe biyu da mintuna goma sha shida na dare. Zaro idanunta, "Allah dai yasa lafiya. Tashi tayi ta yaye labulen ďakin tana lekawa ta window. Mutum uku ta gani sun fito daga cikin motar, ďaya na tsakiyar su yana ďingisa kafa. Zuba ido tayi sosai ta kare musu kallo, tabbas uncle smart ne, da scorpion sai ďayan da bata tantance ko waye shi ba. Da sauri ta nufi kofar fita daga ďakin sai kuma ta koma ta tsaya. Kwankwasa kofa taji anayi, tayi saurin zura hijabinta ta fito . Hanunta na rawa ta buďe kofa, ta matsa baya. Kutsa kansu sukayi, scorpion a gaba Smart na biye da shi sai ďayan a karshe. Kallon juna suka tsaya yi yayin da su scorpion suka karasa cikin falo suka zauna. Magana takeson yi amma bakinta ya gagara buďuwa, ba karamin rama ta ga yayi ba, da ganinshi babu lafiya. Take kwalla suka ciko idanunta tayi saurin juyawa ta shige ďakinta da gudu ta faďa kan katifa ta fashe da kukan da ita kanta bata san dalili ba. D'an murmushi yayi yana binta da kallo kafin daga bisani ya bi bayanta. "Khadijah kukan me kikeyi?" Ci gaba tayi da kukanta. Hakan yasa yayi kneeling kusa da katifar. "Khadijah." Muryar da yayi amfani da ita wajen kiran sunanta yasa ta ďago tana kallonshi fiskarta sharkaf da hawaye. "Kiyi haquri, bakijini ba na lokaci mai tsawo, nayi rashin lafiya ne." Kallonshi ta ci gaba dayi cikin tausayawa tace "Me ya sameka." Kafarshi ya nuna mata wanda yasha ďinki da plaster "accident nayi a hanyata ta dawowa." Kallon kafar tayi kamar zatayi kuka ta rasa ma abinda zata ce mishi, sai tace "Sannu." "Me ya hanaki bacci?" Ya sake tambaya yana kallonta. Kwab'a fiskarta tayi "Ba kaine ba ,ina ta neman wayarka bana samu." "Sorry dear, wayar ma ban san yanda tayi dan ko motar ma kaca kaca tayi, Allah nema yasa nima ina da rabon sake numfashi a duniya da sai kiji mummunar labari. Bata san sanda tace "Allah ya kiyaye." Saida ta faďa kuma kunya ya kamata ta kawar da kanta gefe. "Allah na gode maka, ashe haka aka damu dani ban sani ba." "Akwai abunda kake buqata ne?" Ta tambaya cikin son basar da zancenshi. "Ba komai, kwanta ki huta tunda me hanaki baccin ya dawo." Kifa kanta tayi kan katifa dan ta boye fiskarta ganin yana maganar yana kallon fiskarta. Gurin Mahmud ya koma ya sumbaceshi yace "ur daddy is back swthrt." "swt dreams mummyn Mahmud." Har ya fita yaja mata kofar bata ďago ba. A ďaki ya samu su scorpion har sun fara bacci sbd haka shima shirin baccin kawai yayi ya kwanta, yana mai jin daďin yanda ta nuna damuwarta karara a kanshi. *F.O.W* [8/22, 10:09 PM] +234 806 071 2446: * TASHIN HANKALI * *Written by :Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *10* *Dedicated to Maryam Mazad (Mmn Tawa.)* ~Bacci mai daďi ne ya kwasheta irin wanda ta daďe batayi ba. Ko da tayi sallar asubah ma nan kan sallayan ta kwanta saida taji motsin Mahmud ta tashi. Kitchen ta shiga bayan ta shayar da Mahmud tayi mishi wanka ta goyashi ta haďa brkfast. Ciki ta koma ganin babu wanda ya fito daga cikinsu, tayi wanka kafin ta sake fitowa. Tana jera musu brkfast suka fito dukansu uku. Gaishesu tayi tayi musu ya gajiyar hanya, shi kuma smart ta kara da ya jiki kafin ta gabatar musu da abin karyawa ta koma ciki. Talle keyarshi scorpion yayi bayan ta shige yace "Wnn kallo haka sai kasa ta faďi ai." "Kai wai ina ruwanka da nine?" "Ina guje maka ne kada kazo kana ce mana tsautsayi ya gifta ne Ustazu." "Dan iskan kawai." Yace mishi tare da kai mishi duka. Gocewa yayi yana dariya yace "To ai gaskiya na fađa." Karyawa sukayi suka sallameshi tare da addu'ar Allah ya bashi lafiya suka tafi. Bayan tafiyarsu ta fito ta tattara kayan da suka karya, yana zaune yana kallon T.V amma sam hankalinshi ba kan T.Vn yake, kallonta yakeyi a kaikaice. Mahmud ne ya fito daga cikin ďaki da rarrafe yana gwalab'enshi na yara. Da sauri ya tashi ya ďingisa ya ďaukoshi yana cewa "Oyoyo Yaron daddynshi." Shi ko tuni ya b'angale baki yana dariya. "Iye har da hakora huďu mukayi ashe." Kwanciya yayi ya ďorashi kan cikinshi yana ta zuba surutu kamar mai magana da babban mutum, tana daga kitchen tana jinshi ,wani abun idan ya fađa har dariya takeyi. "My Mahmud kayi missing ďina kamar yadda mummy tayi?" Ya faďa yana satar kallon ta daidai lokacin da ta fito daga kitchen. Kamar bata jishi ba tazo ta wuce. "Zo mana khadijah." Da baya ta dawo ta zauna tace "gani." "D'an matso mana yanda zakiji abunda zance." kaďan ta qara matsawa. "Bani labarin abunda ya faru da bana nan." "Babu abinda ya faru." "Ni nasan akwai abunda ya faru, zaki faďa da kanki ko in faďa?" "Ka faďa." Tace, tana kawar da kanta daga kallonshi. "Da bana nan, kikayi ta tunani, babu Uncle smart babu wayarshi, me ya faru dashi, ko ba lafiyane, ko mutuwa yayi, kika shiga yin kuka, bacci ya kauracewa idanunki, karshe ma cin abinci gagararki yakeyi, sai tausayawa Mahmud kikeyi ya rasa daddynshi, ko ba haka ba?" "Ni kam ina cin abinci." "Kuma shine duk kika rame haka, mummy, dubi idanunki fa yadda suka koma, sun kankance sunyi ja, duk dan rashin bacci." Shiru tayi kamar bata wajen. Tashi yayi ya zauna ya hada goshinshi da na Mahmud yace "Mahmud ba kayi min albishir daddy ya yi kasuwa ba, we have to celebrate my son." Kallonshi takeyi yanda ya dage yake ta zuba bayani, cikin farin ciki. Ko wani irin ciwo ne ya ramar dashi haka?" Ta tuna hakan a ranta, sai kuma ta tsinci kanta da tambayarshi. "Me ya sa ka rame haka? "Tunanin Mahmud da mummynshi suka ramar dani." Ya bata amsa kai tsaye. Tashi tayi ta bar mishi wajen shi kuma ya bita da kallo yana dariya. Custard taje ta damawa mahmud ta kawo ta ajiye kusa dasu. "Yauwa mummy sannu da aiki, je ki kwanta ki rama baccinki dan kinsan ba'a cin bashinshi." "Hmm, kawai tace ta wuce, dan kam da gaskiyarshi, tana bukatar baccin sbd rashin baccin da bata samuba 'yan kwanankin. Saida ya warke tsaf snn yace zai koma jos. Ga mamakinshi sai yaji tace suma zasu je. Daďi yaji sosai, ko ba komai yasan yanzu gudanar da al'amuranshi hankali kwance, kuma ga dukan alamu akwai Improvement sosai daga gareta. Kwanansu huďu da komawa jos, ranan cikin dare haka kawai taje jin jikinta babu daďi ga bacci yaki zuwa mata. Gajiya tayi da juyejuyen da takeyi ta tashi ta nufi falo, ita kanta baza tace ga dalilin fitowarta falon ba. Turuss ta tsaya ganinshi rike da piston yana jujjuyawa, sanye yake da bakaken kaya daga sama har kasa, bata haufi akan shi ďinne domin a yanzu ko cikin duhu ta ganshi zata ganeshi, balle kuma falon akwai haske da ya ratso ciki daga security light na waje. Da sauri taja da baya zcyrta yana harbawa, duk da tasan sana'ar su ďaya dasu scorpion amma ganinshi a haka ya tsoratata. A sanyaye ta koma cikin ďakin ta zube nan tsakiyar ďakin tana maida numfashi kamar wacce tayi gudun famfalaki, daga bisani kuma ta fashe da kuka. Yau ita ke rayuwa da b'arawo ďan fashi cikin gida ďaya, har da rabon haihuwa a tsakaninsu ba tare da aure bama. Wani kukan ta kuma rushewa dashi mai tsuma zcyr mai saurare. A b'angarenshi kuwa ba karamin kaďuwa yayi ba da ya ganta a wnn lokaci, sbd ko kaďan baiyi tsammani ba, to me ya fito da ita a wnn lokaci? Ko bata da lafiya ne, ko Mahmud ne?" Duk wađannan tambayoyi ya tsaya yake yiwa kansa ba tare da ya san amsoshinsu ba. Take yaji fitar ya fita ranshi, da sassarfa ya koma cikin ďakinshi ya adana bindigar. Dole nema yaji dalilin fitowarta a wnn lokaci idan ba haka ba hankalinshi bazai tab'a kwanciya ba. Kofar ďakinta ya nufa har ya sa hanu zai buďe, yaji kukanta. Tsayawa yayi cakk jikinshi duk yayi sanyi, yana tunanin ta ina zai fara. Har cikin ranshi yake jin kukan A hankali ya jinginu da jikin kofar ya rintse idanunshi, zcyrshi na daďa ingiza shi da ya shiga ya ji dalilin fitowarta. Karfin hali yayi ya tura kofar ya buďe ya shiga. A tsorace ta ďago ta kalleshi sai kuma ta fara ja da baya tana girgiza mishi kanta. "Na shiga uku." Yace a zcyrshi. A bayyane kuma sai yace. "Calm down khadijah, tsoron me kikeji?" Kallonshi ta tsaya yi, ta kuma had'iye kukan, a yanzu babu bindigar a hanunshi amma duk da haka a tsorace take dashi. Ganin yanda duk tabi ta tsorata ya sashi tsayawa ďan nesa da ita yace. "Me ya fito da ke da darennan?" "Ba komai." Tace muryarta na rawa. "Khadijah pls idan akwai damuwa ki faďa min." Ya faďa cikin sanyin murya. Girgiza mishi kai tayi. "Baki da lafiyane?" "A'ah." "Mahmud fa?" Girgiza kanta ta sakeyi. Kaarasawa yayi kusa da mahmud ya tattab'a jikinshi, ya koma kusa da ita, duk yadda taga jikinta je karkarwa saida yasa hanu ya tab'a wuyarta, da goshinta. Jin babu alamun zafi ya sake cewa cikin kulawa. "Ko cikinki ne yake ciwo?" "Um um." Ta kuma cewa, duk ta gama tsurewa, amma kuma cikin ranta tana mamakin yanda yake abu cikin sanyi. "Je ki kwanta to." "Bana jin bacci." Ta fad'a kamar zata rushe da kuka. "Me yasa?" Shiru tayi mishi. "Mummy pls je ki kwanta in dai lfyrki qlau, ko sai nazo na sake checking." Da sauri ta matsa kusa da mahmud ta kwanta tare da rungumeshi gam a jikinta kamar za a kwace mata shi. Kallonta ya tsaya yi cikin tausayawa, yana jin muguwar tsanar sana'arshi na shigarshi. Vibration ďin da wayarshi yakeyi ne ya sashi fita daga ďakin, dan yasan masu kiranshi. Falon ya zauna yayi recieving call ďin, "Am not feeling fine, Billy, bazan samu zuwa ba, zan baku description na wurin." Scorpion ne ya kwace wayar, "Ina fata ba 'yar fulani ce ta hana ka zuwa ba." "Count her outta dis, bata san komai akai ba ďan banza masharranci." "Share banza smart turo mana description ďin dama aikin mune ai, see u tomorrow." "Dat's my guy shi yasa nake sonka akwaika da saurin fahimta." "Mu kuma da ba'a sonmu a kona mu a huta daganinmu." Cewar Nass. Yana 'yar dariya yace "Ban isa ba ai." Kwatance ya musu ta yadda zasu fahimta, duk da dai sunso suje tare dashi dan shi yasan sirrin komai amma hakan suka haqura. A nan ya zauna ya jingina da kujera, sai saka da warwara yakeyi har akayi kiran farko na asubah, ya tashi ya ďauro alwala ya fara nafilfili kafin ya tafi masallaci. Kwance tayi tana kuka kasa kasa dan ma kada yaji ya sake shigowa har bacci ya sureta amma ba mai daďi ba. Waashegari kuwa sai ga kira daga members ďinsu, cewa jiya anyi attacking ďinsu, an kashe biyu daga cikinsu, Billy da Emeka, Scorpion kuma an harbeshi a qafa, sai Nass da Uche da suka jijji ciwo garin gudun ceton rai. Sosai mutuwar Billy ya dakeshi dan tare suka taso, kuma yana ďaya daga cikin abokanshi da yake ji dasu, kusanma yafi Nass da Scorpion saukin kai. ~Kwana uku kenan yau suna wasan b'uya bata yarda sam su haďu, duk yanda yayi kaucewa haďuwarsu takeyi. Idan tajishi zai shigo da sauri take shiga banďaki ta kulle kanta. Tana jinshi zai karaci surutanshi da Mahmud har gaji ya fita. A yanzu shi ďinma ba wani zama sosai yakeyi a gidan ba gaba ďaya ya zama so busy. Haka kuma duk lokacin da murtuwar su Billy ya faďo mishi sai ya daďa tabbatar wa kanshi cewa Khadijah alkhairi ce a rayuwarshi, ba dan ita ba shi kuma baisan abunda zai faru dashi ba a ranar, a ranshi yana ji akwai wani babban dalili da yasa Allah ya haďashi da ita. Kwana biyar da faruwar al'amarin taji ya tara duk ma'aikatan dakwe gidn ya sallamesu tare da yi musu kyauta mai tsoka, sai godiya suke zuba mishi. "To me zai faru da ita kuma,Sallamar zaizo kanta ne ko kuwa su ďinne kawai suka taki sa'a?" Ta tambayi kanta. Tsit taji gidan yayi babu kowa, hakan yasa ta lekawa cikin sanďa ta fito falo , tsabar hankalinta na waje bata lura dashi a wajen ba, saida ta gama leke lekenta ta juya suka haďa ido dashi yana zaune kasan carpet ya jingina bayanshi da jikin kujera. Da sassarfa tayi nudfin komawa ciki ya dakatar da ita da cewa "Dan Allah khadija ki tsaya zamuyi magana." A ranta tace Allah yasa nima zai sallameni na koma gida ne. Niko da nake makale a gefe nace "Da yake ance miki haukan sallama ne ya kamashi ba. D'an nesa da shi ta zauna ta snkuyar da kai, shi kuwa ya tsura mata idanu yana kallonta amma can cikin zcyrshi tunani yakeyi . "Khadijah me yasa kike guduna?" Shiru tayi a ranta tace ďan fashi kam abun gudu ne ai. "Khadija, na yanke shawarar maidake gida cikin 'yan kwanakinnan." D'ago kai tayi ta kalleshi da sauri suka haďa idanu, tayi saurin sadda kanta qasa zcyrta na harbawa da sauri sauri. Gyaran murya yayi kafin yace "Kamar yanda kika sani ina da tarihi mai muni a rayuwata,ina nufiin sana'ar da nakeyi, Fashi. Bayan haka a yadda kika ganni bani da iyaye bani da kowa sai abokaina da kika sanni dasu. A haka muka taso muka tsinci kanmu cikin wnn sana'a... Wnn suna da kikaji ake kirana dashi *Smart* ya samo asaline tun muna primary schl wani malaminmu ya sa min, daganan sunan ya bini, amma asalin sunana *MAHMUD* shi yasa naji mamaki kwarai da kika faďa min sunan mahmud har na tambayeki wanda ya raďa mishi sunan. Ainihin sunan scorpion *Umar* ne sai Nass, *Nasir* sai kuma Billy *Bilyamin* Ba iya mu kaďai bane , muna da yawa, akwai musulmai a cikinmu snn akwai waďanda ba musulmai ba. amma dukanmu muna amfani da sunan mutum ďaya a matsayin surname wato *Adam* wanda shine Boss ďinmu, duk da cewa daga baya mun fahimci ba shine mahaifinmu ba. Akwai wađanda suka girmemu akwai kuma sa'o'inmu kuma akwai waďanda basu kaimu ba. a hanunshi muka taso, shi ya sakamu a makaranta, ya samar mana masu dafa mana abinci da kula damu har muka girma ya saka mu a wnn harka wato sata, fashi da makami..... TASHIN HANKALI * *Written by: Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *11*&12 *Dedicated to Amina sale muri (My kakus)* ~Ina da role na musamman danake playing a cikin harkar, wanda ya zama special shi yasa na kasance special a wajen boss ďinmu, haka kuma kasona special ne. Nisawa yayi kafin ya ci gaba da cewa, na kasance mutum mai dabara da iya mu'amala da mutane ta fiska mai kyau da kamala ta yadda har zan gama bincikena kan mutum bazai fahimci ina tare dashi da wata manufa bane. Ina shiga cikin jama'a ta fiskar da kowa yake min ganin mutumin kirki, hakan yasa nake hulďa da manyan mutane kuma nake sanin duk wani sirrin arxikinsu ba tare da sun ankare da hakan ba. Sallah wnn da kika gani da na munfurci nakeyi dan babu yadda za'a yi lokacin sallah tazo ta wuce banje nabi jam'i ba, hakan yasa mutane suke mutuntani, amma daga baya cikin iko da hikima ta ubangiji sai yasa min son yin ibada tsakani da Allah ba dan wani dalili ko dan ganin idon mutane, ya zamanto duk abinda nakeyi kuma duk inda nake indai lokacin sallah yayi banyi shi ba bana jin daďi da kwanciyar hankali har sai nayi. Haka kuma nakan shiga cikin manyan mutane ďaukan karatu duk da na munafurci ne amma ina ďaukan karatun, kuma yawan zama cikin masallaci da kuma guraren ďaukan karatu yasa min tsoron Allah da hanani aikata munanan ayyuka, irin su shaye shaye, da neman mata. Bazan boye miki ba a da ni mashayi ne, amma daga baya naji sam bana sha'awar halin. Haka kuma soyayya tun na yaranta na secondry sch. da nayi na daina. Shi yasa kika ji su scorpion suke kirana da ustaz. Bayan haka bana fashin kan hanya, ni dai aiki na na binciko sirrin gidan mai kuďi nayi directing members ďinmu zuwa gidan ko ma'aikata. Nayi aiki a ma'aikatu da dama, da kamfanoni amma sam babu wanda ya tab'a gano sana'ar da nakeyi. Daga mun kare sec. Sch. Ake barinmu mu ďauki nauyin kanmu da kanmu, inda kika ganni nan har masters nayi, amma yawancin abokai 'ya'yan masu kuďi ne, sosai nake shiga jikinsu, nasan sirrin gidan su da arxikin mahaifansu karshe na tura members ďinmu, haka kuma idan kinga anje satan dani tofa gidan ko ma'aikatar akwai kwakkwarar tsarone, wanda idan ba da ni da nasan kan gidan ko ma'aikatar ba zasu wahala kafin su samu abunda suke nema. Na tara arziki da yawa ta hanyar sata, kuma na tara ta hanyar nema da gumi na. Sbd mutunta kuďin da na samu da gumina da nakeyi yasa na buďe account na musamman nake waresu na sasu ciki, snn na haram kuma ina nufin na sata account ďinsa daban, batan haka duk wasu qadarori da nake saya da kuďin haram nake saya, su kuwa na halal suna killace cikin account. Wlh, wlh, duk wani hidima da kikaga nake yi muku ke da mahmud da halaliyana nake yi muku shi sbd ko kaďan banaso Mahmud yaci daga haramun. Sau da dama nakan zauna nayi tunani yaya Mahmud zaiji idan ya girma yasan cewa mahaifinshi ďan fashi ne. "Khadijah, bani da babban buri da ya wuce in san su waye mahaifana in koma garesu in bar wnn harka in nemi gafarar ubangiji, saidai saninsu zaiyi min wuya dan tunda muka taso da su Nasir mukayi wayo muke tambayar ina mahaifanmu, amma kullum amsar ďayace *Tsinto mu akayi* Sai daga baya muka gane ta yanda aka samomu kasancewar muna ganin yanda Boss da mutanenshi suke farauto mutane manya da yar, har wasu daga cikinmu sukayi adopting wnn hali, misali, scorpion, kinga a wajen farautarshi ya farautoki, to hakan sukeyi, idan sunga mace tayi musu, ko suka kakkarfan saurayi su sato shi, har da yara kanana wani lokacin harda wađanda suka manyanta kamar Baaba kenan me aikin gidan scorpion. wanda Allah ya kub'utar ya gudu ya koma gun danginshi. Wani kuma idan aka kamashi zai gudun sai a kasheshi kawai sbd ya nuna bazai bada haďin kai ba, kuma zai iya tona musu asiri. Shiru tayi ta bashi dukkan hankalinta, labarinshi kuma yana tab'ata haka kawai taji ya bata tausayi sbd rashin sanin iyayenshi da yace. "Khadija, kinji takaitaccen tarihi na, sai kuma wani abu da nake so in sanar dake a yanzu shine. Nayi niyyar barin sata kuma zan koma inda ba'a sanni ba in sake sabon rayuwa in nemi gafarar mahaliccina. D'agowa tayi da sauri ta kalleshi, sai ta saki murmushi tana kuma sharar kwalla. "Khadijah, nayi alkawarin barin wnn sana'a domin Allah, saidai nasan ke da Mahmud kune sanadi." Tasowa yayi ya durkusa a gabanta. "Khadijah, zaki aureni?" Wani irin dumm taji, saukar maganarshi cikin kunnenta tajishi kamar saukar aradu, kirjinta sai bugawa yakeyi, take ta fara haďa zufa duk da a.cn dake cikin falon. "Aure kuma?" Tayi tambayar a ranta. "ta ya auren zai kasance kenan, yana nufin suje inda ba a sansun ba tare suyi aure ko kuwa?" Kamar yasan tunanin da takeyi yace "Yace ki kwantar da hankalinki khadijah, bazan tilastaki aurena ba. Kuma koda kin amince sai na maidake gida gurin danginki na nemi aurenki, idan Allah yasa ina da rabo su bani, idan sun hanani kuma zan jira Mahmud ya girma na karb'eshi ya zamemin dangina da gatana, sai dai abunda na sani shine, duk tsawon rayuwar da zanyi zanyishine da sonki da qaunarki ne cikin zcyta, bazan tab'a mantawa dake ba khadijah." "Khadijah, nasan rayuwata tana cikin hatsari muddin mutanenmu sukasan cewa na bar kungiyarsu, nasan cewa duk inda nake zasu nemoni kuma zasu kasheni, shi yasa na yankewa kaina shawarar kai kaina ga hukuma. Kallonshi ta kumayi da jajayen idanunta da suka sha kuka kuma still hawayen basu bar fitowa daga idanunta ba. "Eh, khadijah, dole na kai kaina ayi min duk hukuncin da ya dace dani, idan ina da rabon rayuwa zan dawo in nemi aurenki in kin amince, idan baki amince ba zanzo in karb'i mahmud, idan kuma ni ba mai rayuwa bane kuma, ina rokonki ki yafemin , idan Allah ya raya Mahmud kice ya yafe min." "Na shirya tafiyanmu gobe zan mayar dake, na gama sayar da duk wata kadara da nake dashi kamfanina kawai na bari sai gidannan, da kuma mota guda ďaya,ita ďinma ďazu na canza ta dan an sanni da saura. saidai zanyi farin ciki idan kika furta kalmar so a gareni amma nafison ya fito daga zcyrki ba abaki kawai ba." Kukanta ne ya tsananta, sbd tunanin abu biyu, ita kanta tasan a yanzu ta kamu da sonshi, kuma zatayi farin ciki da barin shi harkar sata, saidai yaya iyayenta zasu ďauki al'amarin, snn ya zatayi da Hamma shehu. Bayan haka bata da tabbacin shin mutanenshi zasu barshi a raye ko zasu kasheshi, gashi kuma yace zai kai kanshi ga hukuma, to yaya al'amarin zai kasance. "Khadijah, ki daina kukannan ki faďa min abinda ke ranki game dani, in har na rayu nayi miki alkawarin zanyi iya kokarina iyayenki su bani ke, sai dai kinsan dole sai da haďin kanki hakan zai kasance." "Khadijah, zaki aureni?" Ya kuma tambaya a karo na biyu. Gyaďa mishi kai ta shigayi alamar ta amince saidai har yanzu bata bar kukan ba. "Alhamdulillah, Alhamdul.... Maganarshine ya yanke sakamakon ganin wulgawan mutum da yayi. Take yaji zcyrshi ya tsinke, jikinshi ya bashi cewa tabbas akwai wadda yaji hirarsu da khadija, inko hakane akwai babban matsala, dan zasu iya halakasu dukansu uku, sbd rufuwan asirinsu, yasan halin kungiyarsu komai zasu iya aikatawa. Deejah bata fahimci halin da yake ciki ba sbd kukan da taji Mahmud yanayi daga ďaki, tayi sauri ta tashi taje wajenshi. Baiyi yunkurin lekawa ba sbd kada mutumin ya gane ya ganshi. Shiga ďakinshi kawai yayi ya haďa kayanshi da duk wani abu mai amfani, yaje nasu deejah ma ya kama haďa nasu kayan ba tare da ya ce mata wani abuba, itama kuma bata tambaya ba, dan damuwa da tunanin da suka mata zcy ma kaďai sun isheta. Tsaff ya gama hađa komai, ya haďa ya ďurasu cikin mota, yanayin komaine cikin kwanciyar hankali. Dawowa yayi ya karb'i mahmud ya ďanyi mishi wasa kafin ya mishi wanka da kanshi, ya canza mishi kaya. Kiran sallar magriba da akayi yasashi ce mata zai fita amma tana idar da sallar magriba tayi wanka ta saka kayan da ya ajiye mata kafin ya dawo akwai inda zasuje. Sai bayan sallar Isha'i ya dawo musu da abinci, har cikin ďakin ya kai mata ya fito ya ci nashi kafin ya umarceta da ta tashi su tafi, yayin da ya ďauki Mahmud ya sab'ashi a kafaďa. Barin unguwar sukayi saida sukayi nisa kafin yace mata Bauchi zasu je su kwana. Shiru yaďan biyo baya kafin daga baya tace, "Uncle ina neman wata alfarma, in zan samu." "In har baifi qarfina ba." "Ka taimaki mama dan Allah itama ka kub'utar da ita daga gidan scorpion." Shiru ya ďanyi kafin juya kan motar yana cewa "Kiyi min addu'ar samun sa'a." Sun jima a tsaye nesa da gidan kaďan saida kafafu suka ďauke snn ya yaja motar ya karasa kofar gidan ya danna horn gate man ya buďe. Direct ya shige cikin gidan, nesa da gateman yayi parking ya fito. Tura kofar falon yayi ya kutsa kanshi cikin falon gidan kasancewar a buďe ba a kulleta ba. Kwankwasa kofar Baba yayi ta zo ta buďe tana murza idanu. "Yallab'ai sannu da dawowa." Ta faďa cikin muryar bacci. Qasa yayi da muryarshi "Ba shi bane, Baba,kiyi sauri ki biyoni in fitar dake daga gidannan kafin kafin ya dawo." Kamar zatayi gardama sai kuma tayi tunanin watakil add'uartace ta karb'u ta samu mai kub'utar da ita. Da sauri ta juya ta ďauki lullub'inta tabi bayanshi har wajen motar ya buďe mata baya ta shiga. Har suka fita mai gadi baisan wainar da ake toyawa ba. Saida suka fita Deeja ta ďaga mata gaisuwa a ladabce, itama ta amsa tana mai jin natsuwa da ganin yanayinsu dukansu biyu, da alama ba masu cutarwa bane, ta faďi hakan a ranta. Hayaki suka hango ya turnuke ta hanyar gidan shi, hakan yasa ya nufi ta wajen bayan ya rage tafiyar motar. Hayaniya ne ya karade wajen jama'a na ta kokarin kashe wutar amma sai kara ci wutar takeyi. Tabbas gidanshi aka kona, wato shirin da sukayi kenan su biyo cikin dare su kona su. Kallonshi ya mayar kan Deeja da ta toshe bakinta idanunta sun firfito sai zubar hawaye sukeyi, a ranta godewa Allah takeyi da suka fita kafin wutan ya kama.... A high speed yaja motar suka bar wajen a ranshi yana godewa Allah da ya bashi daman fita kafin suzo. Saida suka ďanyi nisa da tafiya ya sake kallonta. "Mummy pls bar kukannan haka." Haďiye kukan tayi amma zcyrta fal tsoro gani take kamar zasu iya biyosu su halaka su. "Baaba ina zamuje?." "Zaria." Ta bashi amsa tana fatar Allah ya nuna mata taga danginta, zcyrta fal farin ciki, saidai har yanzu bata gane ko waye bane yakeson taimakonta. Cikin daren suka kaita zaria, saida suka isa Baba ta ganesu. Har gidanta ya kaita, dake gidansu family house ne lokaci guda aka haďu kamar rana ana ta murnar dawowarta. Saida sukayi sallar asubah suka kama hanya, suka barta da danginta sai sa musu albarka sukeyi. sallah da cin abinci ke tsaida su, har dare suka isa jalingo a gajiye. Hotel ya kama musu ďakuna biyu suka kwana, washegari suka kama hanyar Gembu. "Dofrofi zamuje ko? Ya tambayeta lokacin da suka kusa isa gembu. Dariyace ta sub'uce mata jin yadda ya kira sunan dorofin har shima ta bashi dariya. "Dariyar me kikeyi, ni dai nasan ban manta sunan garinku ba." Tana murmushi tace mishi "Nguroje zamu tsaya, zan karasa dorofin daga baya, dan shiga ciki akwai wahala, kaga kuma dare ya farayi." Dafe kanshi yayi da hanu ďaya "Oh, nayi mistaking sunan ko?" "A'ah, kayi kokari ma ai." Ta faďa tana 'yar murmushi. Suna karasawa Nguroje ta fara nuna mishi hanya yana bi har suka isa. Suna doso kofar gidan goggonta taji gabanta ya fara faďuwa, zcyrta na tsananta bugawa, lokaci guda ta shiga *Tashin hankali* mara misaltuwa ..... *F.O.W * [8/22, 10:20 PM] +234 806 071 2446: * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *12* ~Na farko, rabuwar da zasuyi take tunawa, gashi kuma yace zai kai kanshi ga hukuma, na biyu tana tunanin yanda rayuwarta zata kasance a matsayinta na wacce b'arayi suka sace tahar sau biyu, bama kamar yanzu da ta zauna gurinsu na tsawon lokaci, anya ba za a zargeta ba? Na uku tunanin yanda zata cika mishi alkawarinshi na aure duk da basu da tabbacin za a barshi da rai ko a'a. "Mummy tunanin me kikeyi ina ta magana kinyi shiru." Firgigit tayi ta kalleshi ta kalli hanya kafin tace "Uncle mun wuce fa." Samun guri yayi yayi parking ya juyo gaba ďaya yana kallonta. Kafin yayi magana tace "Uncle smart, dan Allah ka kwana anan sai gobe ka tafi." "Anya kuwa khadijah?" Ya faďa cikin tantama yana kallonta. Rau rau tayi da ido kamar zatayi kuka tace "Dan Allah fa nace." "Wa kenan zakice musu a gida, D'an fashin da ya sace ki? Baban Mahmud? Ko yaya?" "Ni dai nasan abunda zance." Shiru yayi kamar mai tunani. Hanunshi ďaya ta kama ta rike, hakan yasa ya ware idanu yana kallon ta, Sai kuma ya sauke idanunshi kan hannayensu da ke haďe gu ďaya. Kallo hannayen nasu tayi, tayi saurin ďauke hanunta ta sunkuyar da kanta a kunyace. Kokarin buďe kofar motar ta farayi yayi saurin mika mata hanu tare da cewa "Bani yarona kar kije garin murna ku kada min shi." Mika mushi mahmud da yayi nisa da bacci tayi ta fita ta koma baya kaďan kafin ta isa kofar gidan. Ta jima a tsaye tana saka da warwara kafin tayi karfin halin kwađa sallama tare da kokarin tura kofar gidan kaďan. Suna cikin ďaki kofofinsu a rufe suna cin abinci sbd sanyin da ake kwaďawa a garin. Da sauri goggonta ta mike tana amsa sallamar kafin tace muryar wa nakeji kamar ta Deejah. Ai tun bata karasa ba Habiba ta mike tayi hanyar waje. Kicib'is sukayi ita tana shigowa Habiba na fita. Kasancewar akwai hasken farin wata tarr suke kallon juna. Wani wawan tsalle Habiba tayi ta rungumeta tana ihun murna tana cewa "Wlh, ďun hanko, Adda deejah warti." Sauran yaran ma da masu ďan girman da kananan duka suka nufosu a guje suna ihu, suka kakkamata kamar zasu kadata, sai da Habiba ta ja mata su snn ta samu sukunin karasawa cikin gida. A tsaye goggonta take kamar an dasata a gurin sai tasbihi takewa Ubangiji da ya nuna mata wnn rana. A sukwane Deejah ta karasa ta rungume ta, Kamar jira take ta rungume deejah kamkam tare da rushewa da kukan farin ciki. Saida suka natsa kafin kafin goggo ta tambayeta ina Mahmudu. "Yana waje." Ta bata amsa. "Shi da waye?" Goggon ta sake tambayarta. "Suna tare da wanda ya dawo damu." Ai da sauri Goggo ta mike tana cewa, "Haba deejah, ya zakizo da bako ki barshi a waje baki sanar ba." Sallamar mijintace ta katse mata faďan da takewa deejah. A tare suka amsa masa. Cikin farinciki yake cewa "Ina Deejan takene?" "Gani Baffa." Ta amsa tana yar fara'a. "Ma sha Allah, Alhamdulillah, Allah shine abin godiya, Allah mun gode maka, Ya Allah ka taqaita mana wnn al'amari haka nan." Abinda yake ta maimaita wa kenan cikin tsantsan farinciki hannayenshi duka biyu a sama snn ya shafa ,har Deejah taji tausayinsu ya rufeta. Ita tana can cikin kwanciyar hankali duk da dai tunaninsu na cikin ranta, su kuwa suna nan cikin tashin hankalin rashinta. "Malam tare fa suke da baqo a waje ta barshi bata fađa ba." "A, to, toh." Da sauri ya fita, can ya hango motarshi ya karasa, cikin mutunta juna suka gaisa tare da mishi godiya da nuna mishi jin daďinshi game da taimakon da yayiwa deejah. D'akin babban ďansu dake kofar gida yayi mishi masauki snn ya karb'o mahmud ya shigo dashi. Tarba aka mishi na musamman wanda har mamakin karamcinsu yakeyi, duk yaran gidan saida suka je suka gaisheshi, har da goggon Deejah. Tun da daren ya fito da kayakinta da na Mahmud ya bawa yara su shigo dasu. Mamakin yawan kayakin ne yasa goggonta ta kasa hakura tambayeta inda ta samesu. Rass rass taji zxyrta ya tsinke ta fara tunanin abinda zata faďa musu su yarda da ita sbd gudun zargi. Can dai ta daure tace musu shi wanda ya dawo da itanne ya saya musu ita da Mahmud. Shiru goggonta tayi naďan lokaci kafin ta kuma tambayarta , yanda akayi suka haďu dashi. Nanfa ake yinta, deejah ido ya raina fata, to me zata ce musu tsakaninta da uncle smart, ko kaďan bata so ta faďi abunda zaisa suga laifinshi, nan dai ta karkace ta fara shirya musu abinda yazo cikin ranta. Taimakonsu yayi ita da wata mata lokacin da ya gansu sun fito daga gidan yan fashin da suka sace su suna neman wajen tsira. Shi ya taimaka musu ya kaisu wani gida ya b'oyesu, kasancewar barayin sunga lokacin da ya ďaukesu suka bisu dakyar ya samu suka tsira. sanadiyyar haka ya canza motarshi sbd bibiyarshi da sukeyi. Snn kuma gudun kada suyi saurin ganoshi yasa baiyi gaggawar fito dasu daga gidan ba saidai ya samar musu abubuwan bukata ita da matar da kuma suturan sawa har da na Mahmud. Sosai sukayi mamakin kokarinshi suka kuma yabawa kirkinshi sai addu'a da fatar alkhairi suke ta mishi. ~Kusan kwana yayi yana tunanin makomar rayuwarshi ga kuma rabuwa da khadijanshi da kuma gudan jininshi mahmud. Ita kuwa Deejah baccinta tayi hankali kwance, har mafarkin mutanen gidansu na dorofi takeyi. Washegari tun sallar asubah ta tashi ta shiga taya Habiba da goggo aiyukan gida, dukda suna tace mata ta bari ta je ta kwanta ta kara hutawa amma sam taki, Alla Alla take gari ya gama yin haske taje taga uncle smart. Saida suka gama haďa breakfast suka kimtsa snn ta ďuma ruwa ta shiga wanka. Cikin ďakin tayi wa Mahmud wanka ta shiryashi cikin kayan sanyi masu nauyi kasancewar su a can sosai ake sanyi dan itama saida ta ďora rigar sanyi kan atamfar da ta saka. Sau uku tana lekawa yana kwance yana ta sharar baccinshi kasancewar bai samu bacci sosai ba jiya da dare. Some fewa minutes past eleven ta sake lekawa nan ta samu ya tashi har yayi breakfast. Gaisheshi tayi yayi shiru tamkar bai jita ba. "Uncle smart." Ta kira tana kallonshi ganin irin shariyar da ya mata. "Nifa fushi nake dake mummy idan baki sani ba." Zaro idanunta tayi ta dafe kirji. "Me nayi uncle." "Baki san laifinki ba kenan." "Ban sani ba uncle." Ta faďa cikin sanyin murya. Kallonta yayi na ďan lokaci itako sai sunkuyar da kai takeyi. "Khadija daga dawowa gida sai ki manta dani ko kizo ki min good night hakafa kika barni na kwana da tunaninki, dan Allah ki faďi gakiya ke haka nake yi miki a can." Qasa ta daďayi da kanta tana wasa da yatsun hanunta a kunyace tace "Uncke naga kuna tare dasu bappa ne ni kuma kunya nakeji." "Ba wani nan, kin dai nuna min mantawa zakiyi dani idan na tafi." "A'a Wlh bazan manta da kai ba." Ta faďa cikin sauri tana girgiza kanta. Sosai furucinta yayi mishi daďi. Ya kuma cewa offence number two. Me yasa tun da safe bakizo mun gaisa ba sai yanzu past eleven." "Sau uku na shigo fa uncle kana bacci, su bappa ma su leka ku gaisa baka tashi ba." Ta faďa tana nuna mishi yatsunta uku. "To ai ke kika hanani bacci da wuri kikasa ina ta tunaninki har bansan dare ya tsala sosai ba." Ya faďa yana mariraice fiska. Jin tayi shiru batace komaiba ya kuma cewa. "Me yasa baki tasheni ba bayan kinsan ya kamata inyi sammako in tafi." Da alama wnn magana yake nema da ita, ta ayyana hakan a ranta. A bayyane kuma sai tace "Naga ka gaji ne kana bukatar hutu shi yasa ban tasheka ba, kuma ya kamata ka ďan kara hutawa zuwa gobe sai ka tafi." "Gobe kuma?" Ya fađa bayan ya waro idanunshi. "To ai kaga su bappa ma sun fita bakuyi sallama ba kuma ba yanzu zasu dawo ba." Ta faďa tana marairaice fiska." D'an jimm yayi yana tunani, tabbas yaso ya tafi yau saidai shi kanshi baya jin tafiyar a jikinshi ko dan yana tunanin rabuwa dasune?" "Kawo min sweetheart ďina idan yace in kwana zan kwana amma idan bai amsa ba tafiya ta zanyi." Mikewa tayi taje ta ďauko mahmud ta kawo mishi, yaro yana ganin ubanshi ya fara mika hanu yana tsalle da dariya. Shima dariyan yakeyi yana cewa "Oyoyo my boy kaima kayi missing ďina ko?" Karb'arshi yayi yana mishi wasa shi kuma sai b'abb'aka dariya yakeyi, ita kuwa tana kallonsu gaba ďaya tausayin kanta da Mahmud ďinne ya rufeta. Fita tayi ta shiga ban ďaki ta wanke shi tass snn ta haďa mishi ruwan wanka ta kai mishi kafin tazo ta sanar dashi. Karb'ar mahmud tayi ta fita dan ya samu yayi wankan, saida ya shiga wanka ta dawo ta kimtsa ďakin tsaf tare da fesa room freshner da dama yana cikin ďakin, snn ta sake zubo garwashi cikin kasko ta haďe da turaren wuta kađan ta ajiye cikin ďakin sbd ya ďumama ďakin. Tsab ta samu Habiba ta karasa dafa white rice da suka ďora kan wuta har ta zuba cikin foodflask da za a sa mishi abinci. Already Deeja ta gama haďa stew da naman kajin da bappa yasa aka yanka mishi tun safe rabi kuma ta soyesu. Saida ta jira zuwa lokacin da tasan ya gama komai suka kai mishi abincin tare da Habiba, haďe da flask na ruwan lipton da yasha kayan kamshi, sai Ayaba da peer da suka kasance cimarsu ne a can gasunan birjik. Zaune suka sameshi yana bin ďakin da kallo yana jinjina tsabta irinnasu, gashi dai kauyen jar kasa ne dasu amma suna kokari sosai wajen ganin sun gyara muhallinsu. Gaisheshi Habiba tayi tana tambayarshi ya yaji sanyin garinsu. "Akwai sanyi sosai kam." Ya bata amsa yana maida kallonshi ga Deejan dake wasa da bakin gyalenta. "Yauwa kanwata zan samu ganin Hamma shehu, akwai maganar da nakeso muyi dashi." Ya tambayi Habiba. Dumm deeja ta ji gabanta ya faďi, to me zai faďawa Hamma shehun. Dariya Habiba tayi itama a kunyace tace mishi Hamma shehu ba a garin yake ba yana dorofi, kuma dorofinma yanzu da wuya a sameshi dan ya fi zama a can camaroon yanzu. Jinjina kai yayi, yace "Naso kam in ganshi, amma ba laifi next time." Habiban da bata san me ake ciki ba tace barin je in gwada kiran layinshi idan ya shiga zan kawo ku gaisa idan baka ganni ba kuma bai shiga ba kenan." "To na gode kanwata." "Habiba sunanta." Deejah ta fad'a duk ta gama tsarguwa gani take kamar habiba ta gano tsakaninsu. "Toh haj. Habiba na gode." Yace lokacin da takai bakin kofa. "Me zaka cewa Hamma shehun?" Ta jefo mishi tambayar bayan fitar Habiba. "Bai shafekiba tsakanina da ďan uwanane." Ya bata amsa yana maida kallonshi kan abincin da suka kawo mishi. "Wnn duka nawa ni kaďai, lallaifa ni ďin ďan gata ne." Shiru tayi ta faďa kogin tunani. "Khadijah." Ya kirata ina serious tune." "Na'am." Ta amsa tare da kalloshi kaďan sai kuma ta kawar da kanta, dan batason suna yawan had'a ido dashi. "Naso in tafi yau, amma Allah baiyiba, saidai gobe in sha Allah zan kama hanya." Da damuwa fal a fuskarta tace "Yanzu jos ďin zaka koma?" Murmusawa yayi kafin yace "Jos kam ai yanzu sunana matacce, bauchi ma kusan haka ne, na yanke shawarar abuja zan wuce direct inyi reporting." Wani irin bugawa zcyrta tayi, lallai fa akwai aiki a gabanta. Tamkar zata rusa kuka tace "Nikam dole ne reporting ďin? Tunda ka riga ka barsu ka nemi wani wajen ka koma mana, ko nan cikin gembu ba sai ka zauna ba tunda babu wanda ya sanka a wajen, kuma kaga cikin gembu ba kamar nan kauye bane, sai ka samu gida ka zauna ka kama sana'a." Kallonta yakeyi cikin jin daďin yanda ta nuna damuwarta karara a kanshi, saida ta kare maganarta ya sauke ajiyar zcy kafin yace. "Khadija reporting ya zama dole gareni, ko don hakkin jama'a dana tarawa kaina, ina fatan gamawa da duniya lafiya, ina kwaďayin gafara da jin kain ubangijina, ina so nayi kyakkyawan karshe, kuma in samu makoma mai kyau. Wa ya sani ma ko ta dalilin haka Allah ya bayyana min iyayena." Ya karashe maganarshi cikin rauni. * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *13*&14 ~Wani irin tausayinshi taji yana ratsata, a sanyaye tace. "Allah ya biya maka dukkan buqatunka na alkhairi, Allah ya kare ka daga sharrin dukkan abin ki." "Amin, mummyn mahmud." Ya faďa cikin jin daďin addu'o'inta gareshi, har itama ta fahimci hakan. Tashi yayi ya buďe jakar kayanshi ya ďauko wata envelope yazo ya zauna. Mika mata yayi tasa hanu ta karb'a da alamar tambaya a fiskarta. "Buďa ki gani." Kuďi ta gani masu yawa a ciki sai credit card da kuma wani case. Karb'a yayi ya fito da credit card ďin yana nuna mata. "Wnn na account na kuďina wanda na mallaka da gumi nane, zaki ajiye min idan Allah yasa na dawo zaiyi min amfani, idan kuma ban dawo ba ko kuma ta Allah ta kasance a kaina ki bawa Mahmud idan Allah ya raya shi. Snn kuďaďen cikin nan kuma nakune ke da Mahmud kuyi amfani dashi. Wnn kuma, ya fitar da case ďin daga cikin file ďin. "Karb'i wnn." Ya sake faďa yana mika mata. A sanyaye tasa hanu ta karb'a dan maganganunshi ba karamin tab'ata sukayi. "Kyautace wanda nayi niyyar yiwa Mummyn mafi soyuwa a wajena a duniya, ina fatar kyautar zata faranta ranki. Jujjjuya battan takeyi jiki a mace, 'yan kunne da sarkar gwal ne masu ďankaren kyau a ciki. Bata gama kallo ba ya sake miko mata wata 'yar karamar batta. Yace "ga wnn." A sanyaye ta sake karb'a tana kallo. Zoben gwal ne a ciki shima mai kyau. "Mummy." D'agowa tayi ta kalleshi a sanyaye. "In har kin amince dani da soyayyata, kin kuma amince idan na dawo zaki aureni inaso ki saka wnn zobe a yatsar ki yanzu, sbd inaso ki rika ganina a jiki bayan bana nan." Kallonshi ta kumayi taga ya kafeta da kaifafan idanunshi, hakan yasata sauke nata da sauri. Buďewa tayi a hankali ta fito da zoben ta saka a yatsarta mabi da na karshe. Sosai zoben yayi mata kyau, ya matso yana kallon yanda zoben ya zauna mata a yatsar. "Woww, kinga yanda yayi miki kyau kuwa Khadijah?" Share hawayen da tayi ne yasashi dakatar da maganar shi yana kallonta. "Haba, mummy kuka kuma? Mahmud kuma yayi yaya, ko so kike nima nayi kukan?" Girgiza kanta tayi tana dađa share hawayen da suke zubo mata ba kakkautawa. "Look, khadijah, you have to be strong , for me, for mahmud, and for ur self. Dafa hanunshi yayi kan heart ďinshi yace. *Heart is not a basket for keeping tension and sadness.* *It's a golden box for keeping roses of happiness and sweet memories.* Khadijah bai kamata sa wa zcyrki damuwa har ta kaiki ga ki karya min zuciya ba, kamata yayi ki karfafa min gwiwa ki bini da addu'a, idan kina haka gaskiya zakiyi discouraging ďina, dan Allah ki taimakeni kada kisa damuwa a ranki kinji my Khady." Gyaďa mishi kai kawai tayi amma kam tana jinjina rabuwa dashi da kuma kewarshi da zatayi. "Yauwa dear, ni kuma me zaki bani?. "Me kakeso?" Ta tambayeshi a sanyaye bayan taja hanci. "Wnn nakeso ki bani." Ya faďa yana nuna zoben azurfan dake yatsar hanunta na dama. Babu gardama ta cire ta mika mishi, duk da tasan cewa Hamma shehu ne ya saya mata a wani tafiya da yayi zuwa cameroon, amma bata jin zata iya hana shi kan wnn dalili. "Thank u so much Mom Mahmud." Ganin taki sakin jikinta yasa ya ďauko wata chapter, "Yauwa mummy jiya me kika ce musu tsakaninmu." D'an murmushi tayi da tuno karyar da ta shera musu jiya, nan ta fara bashi labarin abunda ta faďa. "Laa'ilah, ashe haka kika iya karya mummy." Dariya takeyi kasa kasa ganin yanda ya rike hab'a kamar mace. "Karfa ki koyawa sweet heart ďina ." "In zuba maka abinci?" Ta tambaya da kawar da zancen. "A,ah wnn zaki bani." Ya faďa yana nuna fruits ďin da suka ajiye mishi. Wuka ta ďauka ta tsattsaga peer guda uku manya ta hađa da ayaba ta tura mishi tare da cewa "Bismillah." Saida ya ďauki ayaban ya b'are kamar zai kai baki sai ya fasa. "Amma ban yarda dake bafa." "Me nayi?" "Nima ban sani ba saidai ina kokwanton ko kinsa maganin bacci a ciki in kwanta inyi tabacci in makara." Yadda taga yake magana da serious face yasata cewa "wlh ban sa komai ba." "taya kike tsammanin zan yarda bayan bakici na gani ba." "Kawo inci ka gani." ta faďa da sauri tana mika mishi hanunta. "Ban yarda ba kar kimin ojoro." Ya faďa yana kai ayaban bakinta da hanunshi. Kadan ta gutsura ta sunkuyar da kai a kunyace, har ta haďiya snn ta kalleshi. "Baki gama ba ai saura wnn." Ya faďa yana sake mika mata b'arin peern da ya cire. Karb'a nanma tayi ta taune ta haďiye kafin tace "ka gani babu abinda nasa." "Na yarda ai." Yace yana dariya. "Amma kinsan bazanyi wahalar banza bako?" Kallon rashin fahimta tayi mishi . Ya ďage girarshi ďaya yana murmushi. "Kema sai ki bani a baki yanda na baki." Ai a tamanin ta mike ta runtuma a guje tayi waje tana dariya, sai yanzu ta fahimci dabara ya mata. Shima dariyar yake mata sbd rashin gano shi da batayi da wuri ba. Cikin gidan ta shiga, sai lokacin kunyar jimawar da tayi a wajenshi ya kamata. Kallon Habiba tayi tace "Ke kuma ana ta jiranki ki kira nambar Hamma shehu shiru." "Ayya adda deejah ai nace idan baku ganni ba bai shiga bane." Shiru tayi dan bata da abin cewa. Daga masallaci ya ďan fita ya zaga yana kallon yanayin garin, kowa ka gani da ďirkekiyar rigar sanyi. "No wonder basa rabuwa da garwashin wuta a ďaki, snn ruwan zafi shine ruwan shansu dan shi tun jiya da yazo basu barshi yayi amfani da ruwan sanyi ba, na sha ma da suka kawo mishi ďazu da ya kurb'a saida ruwan ya kashe mishi hakora. Sai yamma su bappa suka dawo, sosai suka sake dashi sukayi ta hira kamar dama sunsan juna. Tare suka je masallaci sukayi sallar magrib da isha'i, tare kuma suka ci abinci. Daga nan Basharu babban ďan goggo ya tada gen suka shiga kallon ball, shi kuma Bappa ya shiga gida ya barsu. Shidai zaune yake yana tayasu kallon amma sam hankalinshi ba ga kallon yake ba. Tunanin kewarsu kadijah da mahmud da zaiyi yakeyi, sai kuma tunanin yadda rayuwarshi zata kasance gaba. Suna nan zaune aka kawo musu damammiyar fura da nono daga cikin gida. Wnn d'abi'arsu ce, shan fura da nono da dare, dan tun da rana ake damawa a zuba sugar isasshe a ajiye sai dare lokacin hira a sha ana hira, dake garin da sanyi sosai kuma sai kaji kamar daga fridge aka fito dashi. Sosai yasha dan ya mishi daďi ba kaďan ba, su Bashar kuma burgesu yakeyi yanda ya saki jiki dasu yake kuma cin cimarsu ba tare da raini ko nuna kyamata ba. ~ Tun bayan dawowarsu daga masallaci ya gama shirin tafiyarshi. Bappa ne ya fara shigowa sukayi sallama yana daďa yi mishi godiya. Snn su Bashar ma suka shigo. Saida gari ya ďan fara haske Bashar ya rakashi cikin gidan suka gisa da goggonta itama sukayi sallama tana ta zuba mishi godiya. Tun da ta jiyoshi yana sallama da goggo zcyrta ta dinga bugawa da qarfi, gaba ďaya tsoro da fargaba sun mamayeta. Shi kenan yau kam, zasu rabu . Allah ne yasan ko zasu sake haďuwa ko kuma rabuwan kenan. Nonon ayaba manya uku da peer cikin babbar bakar leda goggo ta bawa yara suka kai wajen da aka adana mishi motarshi. Habiba ce ta fito da kwanukan samiru sabbi dal ta juye naman kajin da khadija ta soya jiya. Sai soyayyar miyar da ta zuba cikin karamar samiran ta rufe ta saka su cikin leda sai babban ledan bread ta rike a ďayan hanunta ta kai mishi. Godiya sosai ya musu harda kyautar kuďi, dakyar ta karb'a itama har wani iri takeji kamar wacce tayi sabo dashi. Saida goggo tayi magana kafin Deejah ta fito. "Ke baza kije kuyi sallama bane kin kunshe kanki a ďaki." A tsanake ta juya ta ďauki mahmud da yanzu ta gama shirya shi dan tashinsa ma tayi daga bacci sbd sanin babanshi zaiso ya ganshi kafin ya tafi. Tafiya takeyi kamar wacce kwai ya fashewa a ciki. Daga can gun motarsa ya hango ta hakan yasa shi karasowa gurin da take da sauri suka karasa ďakin Bashar. Tun bata karasa shigowa ba ya karb'i Mahmud ya ďaga shi sama ya cab'e kafin yayi pecking goshinshi kumatunshi da bakinshi. Maida dubanshi yayi kan Deejah da kanta ke kasa. "Khadijah na gode da karramawar da kukayi min, gaskiya danginki suna da kirki, ina fatar haďa zuri'a dasu cikin aminci. Ki taya ni addu'a Allah yasa hakan ta kasance." "Khadijah." Ya sake kiranta jin tayi shiru. D'agowa tayi tana kallonshi idanunta fal qwalla saidai kokarin maidasu takeyi. "Zan tafi, saidai kafin nan akwai abunda na ke so ki sani game dani wanda ba kowa ya sani ba sai makusanta na. Ina son kisan asalin kamannin Mahmud Adam, ba smart ba." Mamaki kalamanshi suka bata. Wani irin kamanni kuma bayan wanda tasanshi dashi. Bata gama tunaninta ba sai gani tayi ya sa hanu ya kwaye fiskarshi wata fiskar ta bayyana. Abu biyu ne suka tsoratata suka tsananta bugun zuciyarta. Ko a labari bata tab'ajin inda mutum ya cire fiskarshi ba. Snn kamannin da ya bayyana kan fiskarshi wanda ya matukar razana ta har ta rasa yanda zata kwatanta abun. Kallonshi takeyi baki sake, mamaki kwance kan fiskarta, sai kuma ta maida kallon kan Mahmud. Murmushin kwantar da hankali ya mata snn cikin taushin murya yace. "Wnn fiska da kika ga na cire, fiska ne wanda muke sawa sbd b'adda kama a cikin mutane, ba kowa ne ya sammu da asalin fiskar mu ba sai mu ya mu." Ganin yanda har yanzu take binshi da kallon tsoro ya kuma cewa. "Kiyi hakuri mummy, kada hankalinki ya tashi, yadda kika ganinnan shine asalinni ďin, na kuma bayyana miki ne saboda gaba dan indai Allah yayi zan dawo a matsayin Mahmud baban Mahmud zan dawo ba a matsayin Smart ba, ina fata kuma kada ki manta da kamannin. Taya zan manta da wnn kamanni. Ta tuna hakan a ranta ba tare da furta komai ba. "Am leaving khadijah, ki kulamin da ku, Allah ya sada mu da alkhairi." Yana gama faďin haka ya fita mahmud na rike a hanunshi dan shi kanshi baiyi tsammanin jin wani abu daga gareta ba, duba da shock ďin da ta shiga sbd ganin ainihin fiskarshi. A sanyaye take binshi a baya har ta karasa gun motarshi, shigo tuni ya shiga ya zauna yana rungume da Mahmud tamkar kar su rabu yakeji. Sun jima a gurin shiru babu mai magana kowannensu da tunanin da yakeyi, daga bisani ta sa hanu ta karb'i Mahmud. A sab'ule tace "Allah ya tsare ." "Amin." ya amsa yana mata murmushi. *I hope and pray someday, we live together forever.* Kamar bayaso ya tada motar tare da ďaga mata hanu, cikin dauriya yaja motar ya fara tafiya. Tsaye take kamar an kafata a gurin saida taga b'acewarshi snn ta sauke ajiyar zuciya ta maida kallonta ga Mahmud.... *Barkanmu da sallah, da fatar kowa yayi sallah cikin koshin lafiya.* *Allah ya maimaita mana.* *F.O.W* [8/24, 5:39 PM] +234 814 058 5795: * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *14* *Dedicated to my friendy Lubabatu kyauta (Mmn Ukhty.)* ~Ta jima nan tsaye zcyrta a cunkushe tama rasa kalar tunanin da zatayi. A sanyaye ta koma cikin gidan tana jin zcyrta da gangar jikinta duk sun sauya kamar ba nata ba. A ranar suka shirya tafiya dorofi ita da goggonta. Tsoffin kayanta da ta bari dama can babu wanda ya tab'a mata su. Su ta tattara ta zubasu cikin travelling bag ďinta ta bar duk kayayyakin da smart ya saya mata a nguroje, sai kuďi da sarka da 'yan kunnen da ya bata, sai kuma kayan Mahmud, suma ba duka ba. Tsohuwar wayarta ta karb'a ta b'oye wanda smart ya bata, dan ita kam batasan bayanin da zatayi musu ba a gida idan an ganta da babbar waya. D'okin ganin mutanen gidansu ya ďan mantar da ita halin da take ciki game da smart har Allah ya kaisu lafiya. Murna gurin ahalin gidan a ranar basai na tsaya zayyane muku ba dan b'ata lokacine, masu kukan farin cikin sun koka, masu dariya sun dara ,sai nan nan sukeyi da ita da Mahmud, Adda kam Mmn Hamma shehu kamar ta haďiye Mahmud dan Allah ya sa mata son yaron sosai. Hamma shehu ne kawai basu samu ba, dan yana kano. Take mahaifin Hamma shehu, ya sa aka kwantar da rago aka yanka akayi raba sadaka da naman, mahaifnta kuma kaji biyar, Hajja inna kuwa fura da nono ta rika damawa tana rabawa yara sadaka dan nuna godiyarsu ga Allah. Duk wnn abinda akeyi hankalinta na ga smart, so take taji muryarsa taji ya yake ta kuma rasa ta yadda zata fara. Duk hirar da Fa'i take zuba mata ba ko wanne takeji ba dan ita hankalinta ya ďauku ga son gane takamammen sabon kamannin da ta gani tattare da uncle smart a safiyar yau. Tambayar kanta takeyi, shin da gaske ne abunda ta gani ko kuma kallon tsoro tayi mishi, to ta yaya ma hakan zai kasance. Ta yarda da cewa da yayi saka fiska yayi, dan munafuki more especially masu harka irin tasu babu abunda bazasu iya aikatawa ba . amma wnn sabon kamannin fa da yaya zata fassara shi, anya ya kamata ta sashi cikin jinsin mutane? Ba wasa da hankalinta yakeso yayi ba kuwa?" Tunawa da tayi da Mahmud jikinta ya daďa yin sanyi. Tunani iri daban daban ta rikayi karshe kuma sai ta kwantarwa kanta hankali da cewar kallon tsoro kawai tayi wa sabuwar fuskarshi. Dabara ce ta faďo mata ta bawa yusufa waya ya kai mata caji. Sai yamma ya karb'o ya kawo mata, lokacin shige da ficen da jama'a sukeyi dan taya murna ya ragu. Sulalewa tayi kamar zataje gidan Hajja inna, ta tafi wajen da tasan sukan samu service idan zasuyi kira can ďan nesa da gidansu. Dialling sabuwar nambarshi da ya canza bayan sun baro Jos tayi kasancewar ta haddace nambar tass a kanta. "Hello." Taji ya faďa bayan ya ďaga wayar. "Assalamu alaikum." Take ya gane muryarta. Cikin zumuďi ya amsa mata sallamar ya kara da cewa. "Haba mummy, ya tun ďazu ina ta nemanki ban sameki ba, kin san yanda na damu kuwa?" "Munje dorofi ne, kuma babu service, yanzu ma saida na je wani gu na samu service." "Alhamdulillah, ai kin tsoratani nayi tsammanin kina so ki shafe babin uncle smart ne a rayuwarki." Kawar da maganar tayi da cewa "Ya hanya." "Alhamdulillah." "Kana ina yanzu?" "Ina jalingo, sai gobe zan kama hanya." "Sannu." Tace a takaice tayi shiru. "Ina my boy, nayi missing naku sosai, fiye da yanda kike zato." "Yana gurin Adda." Saida yayi shiru na ďan lokaci kamar mai tunani, can kuma yace. "Wacece Adda." "Mamanmu, itace Mmn Hamma shehu." "Yanzu hankalinki a kwance kina cikin 'yan uwanki ko?" Ya tambaya a sanyaye. "Hmm." Kawai tace a ranta kuma cewa take, gani dai cikinsu duk da naji daďin ganinsu amma hankali yaki kwanciya. "Mummy." Taji ya kirata cikin wata kasalalliyar murya. "Na'am uncle." "I miss u." Yace mata kamar mai raďa. Wani iri taji a jikinta ta kuma kasa buďe baki tayi magana." Kamar wacce aka tilasta tace "Uncle zan koma gida kar a nemeni." "Thank u mom Mahmud, sai yaushe?" "Zan kira zuwa gobe idan na sake fitowa." "Sai na jiki, shafa min kan Mahmud, kice masa daddynshi yayi missing ďinshi, and he loves u both." Kashe wayar tayi ba tare da ta sake magana ba, ta kurawa wayar ido kamar shi đin take kallo, wani irin kewarshi take ji kamar tayi tsuntsuwa ta ganta kusa da shi. Saida ta biya ta gidan Hajja inna ta ďan zauna kafin ta shiga gidansu. Washegari ma haka bayan sunyi breakfast ta shiga ta gaida Hajja inna daga can ta wuce ta samu ta kirashi, suka gaisa, nan yake sanar da ita cewa asubanci yayi yanzu haka yana hanyar Abuja. Saida taji tsinkewar zcy duk da tasan dole hakan ta kasance. Karshe suka rabu akan zata sake kiranshi anjima in ta sake samun fita. Haka ranar ta wuni zirga sam bata da sukuni , har adda da dadayi suna mata faďan taki ta zauna gu ďaya ta huta. Ba ta kwantar da hankalinta ba saida ta kirashi kusan Magriba yace mata ya isa lafiya. Cikin fara,'arta ta dawo gida, tana isa kofar gida suka ci karo da Hamma shehun da bai jima da dawowa daga tafiya ba yaji labarin dawowarta shine ya fito da zumuďinshi zaije gidan Hajja inna dan can aka ce mishi ta shiga. Cikin tsantsan farin ciki suke kallon juna , a lokacin Hamma shehu ji yayi kamar ya rungumeta ya b'oyeta cikin jikinshi ya hana ko wani ďan iska samun ganinta balle har yayi tunanin sake ďauke mishi ita. "Hadiza." Ya faďa cikin rawar murya, ga hawaye na zuba daga idonshi, ga kuma murmushi kwance kan fiskarshi. "Hamma." Itama ta faďa tana sharar kwalla. Allah ya sani tana son Hamma shehu da zcy ďay, saidai yanzu zata iya cewa son 'yan uwantaka take yi mishi ba kamar na da ba, zcyrta kam yana ga Uncle smart. Yanzu haka ma ganinshi da tayi abubuwa da dama ne suka shiga gifta mata cikin kwakwalwarta game da shi da Uncle smart. "Allah ne abun godiya Hadiza, Allah ya karb'i addu'armu ya dawo mana dake a lokacin da har mun fara tunanin mun rabu dake kenan, Alhamdulillah, Alhamdulillah." Ya faďa fiskarshi na bayyana tsantsan farin cikin da yake ciki. Itama farin cikin ne fal fiskarta saidai magana ya gagareta sai gyaďa kai da ta keyi. Kusa dab da ita ya karaso yana daďa kallonta. "Hadiza me suke baki haka naga kin kara girma da haske da kyau, ji kamar baki da wata damuwa." Ya faďa yana bin fiskarta da kallo. Waigawa tayi kaďan ta dubi gefe da gefenta ta ďan matsa baya kaďan gudun kada wani ya gansu ya zamo musu abun magana. Bakinta ta rufe da tafin hanunta tana 'yar dariya, tare da tunanin yanda mutanen gidansu ma sukayi ta fađin hakan har Hajja inna cewa tayi "Wai deejatu meye 'yan iska mara sa tsoron Allahnnan suke baku ke da Mahmudu kuka canza haka?" Tana cikin tunanin taji yace. "Shikenan dai bari inje masallaci idan na dawo ki bani labari." Da haka ya wuce masjid zcyrshi k'al, itako ta shige cikin gida. Kwana tayi da zullumin abunda zai faru gobe sbd sanar da ita da uncle smart yayi kan goben zai mika kanshi. Sosai abun yake ďaga mata hankali sbd tunanin wani irin hukunci za a mishi. Yauma saida suka karya ta saci jiki ta fita dan ta kirashi. Daga muryarta ma ya gane tana cikin damuwa. Sai tambayarshi takeyi yaushe zai je shi kuwa sai basarwa yakeyi yana janta da hira. Karshe dai ce mishi tayi ya fasa zuwa a ranar ya bari sai ya huta. "Me za a fasa mum mahmud, duk ďaya ne, ni nafi marmarin in kai kaina in san matsayin da nake ko in fara lissafin shekaru ko watannin da zan ganku." Ai batasan sanda kuka ya sub'uce mata ba, wato har ma shekaru, lallai akwai kalubale mai girma a gabanta. Har yaushe za a barta tayi shekaru tana zaman jiranshi shi da babu wanda yasan da zancenshi a gidansu. "Mummy bar kukannan muyi magana kinji." Taji ya faďa a tausashe. Shima kanshi ya rasa kalmar da zai yi amfani wajen kwantar mata da hankali. "Khadijah, pls ki zama mai fawwalawa Allah al'amarinki, sawa kai damuwa da kuka basa maganin matsala saidai su kara, ki kwantar da hankalinki, ku ďauka kamar tsakanin yau da gobe ne komai zai wuce kamar ba'ayiba, kinga ni nan daďi nakeji da Allah ya ganar dani har zanje in kai kaina a kin hukunci daidai da laifukana tun ina raye. Ke kuma kin sa zcyrki cikin damuwa instead of ki kwantar da hankalinki ki tayani addu'a Allah ya yafe min laifukana, ko kinfi son in jira in karb'i hukuncin lahirane khadijah?" Girgiza kanta takeyi kamar yana ganinta, sai daga bisani tace "Um um." Kamar wacce aka shaqe. "Ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru sai alkhairi kinji." "Allah yasa." Ta faďa a shake." "Amin dear, ina yarona." "Yana gida gurin adda." "Kai amma addannan tana sonmu sosai Allah ya biyata." "Amin." "Ammafa da kin fita da shi muyi magana inji muryarshi ko bai fara magana bane?" "Kai uncle yaushe muka rabu da kai har zai fara magana?" "ya kusa shekara ai mummy ko?" Ya sake jefo mata tambaya. "Uncle, kwana biyunne shekara?" "Au, sorry sai yamin fa kamar mun shekara da rabuwa." Ji tayi kamar ta rushe da dariya sbd immagining ďinshi da takeyi ya rufe baki ya waro idanunshi in a funny way, dan tasan da tana kusa dashi hakan zaiyi." "Amma yana tafiya ai ko?" Ya sake mata tambayar da yanzu ta gama ďaukanshi a matsayin na ganganci. "Har da gudu ma." Yana dariya yace "thank God, yarona ya girma saura aure." Bata san sanda dariya ya sub'uce mata sbd tunawa da tayi ubanshi ma yaushe yayi auren balle shi. Shi kuwa dama haka yakeso dan ya shashantar da wancan maganar da sukeyi, ya kuma wanke mata damuwar da take ciki. Haka yayi ta janta da hira cikin raha, daga karshe sukayi sallama kan zata sake nemanshi anjima. Tana komawa gida kuwa tun kan ta shiga ta aiki yaro ya saya mata recharge card, kafin ta shiga ciki. Fa'iza da Yusufa ne suka sa ta gaba sai bata labarin halin da suka shiga lokacin da aka sake ďauketa sukeyi, da kuma labari suman da adda tayi da kuma ciwon da tayi tayi wanda dakyar aka samu ta dawo dadai, sai kuma labari halin da Hamma shehu ya shiga shima, ba ci ba magana har saida ya yi jinya shima, tsabar tausayi har kuka tayi. A yanzu ba karamin tausayin Hamma shehu takeji ba, dan gani take kamar bata kyauta mishi ba shi yana mutuwa akanta, ita kuma ta bawa waninshi zuciyarta, ko yaya abun zai kasance. Tun daga ranar da sukayi magana da uncle smart bata sake samunshi a waya ba. Hakan ya tabbatar mata da cewa yana hanu, ya riga ya kai kanshi kenan. Kamar yadda yace haka ta dage da addu'a, Allah ya tabbatar da alkhairi, ya kaďe fitina da sharri. Hamma shehu yana iya kokarinshi na ganin ya kyautata mata ta kuma saki jiki dashi kamar da, sbd ya fiskanci akwai abinda yake damunta, wanda duk nacinshi taki sanar dashi, kullum amsar ďaya ce "Ba komai." Yaso a tada maganar aurensu a karo na uku, amma aka ce ya hakura sai ta yaye Mahmud sai a barwa adda shi sbd yanda ta shaqu da yaron. Mahmud kuwa tsakaninshi da Mmnshi sai yaji yunwa, nanma ba ko da yaushe ba sbd yanzu yana cin abinci yana shan kunu, yawanci sai dare yake shan mama. Watanta guda da dawowa Hamma shehu ya sallamesu kan zai je sarin kaya, wnn karo Aba zaije saro yadunan hijabai da materials. Kwana biyu da tafiyarshi wani kanin Adda, mahaifiyarshi da ke zaune da iyalinshi cikin jalingo ya zo. Isowan cikin dare yayi sbd haka ya samesu dukansu iyaye mazan a gida. Bayan an marabce shi yaci abinci ya huta ya fara gabatar da makasudin zuwanshi wanda yayi bala'in gigitasu da tayar musu da hankali. Take Bbn Deeja ya mike yana girgiza kai cikin halin kiďima da tashin hankali yake fad'in....... TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *15*&16 *Dedicated to Jamila Usman Nyaja (Mmn Al-mustafa.)* *Wohoho, ashe haka tashin hankali ya tashi hankalin mutane, ashe haka Deejah da Hamma shehu ke da masoya.* *Kuyi hakuri da jina shiru da kukayi, wayarce ta samu matsala, nayi typing ya goge, amma in sha Allah komai ya daidaita.* *Uncle smart, Deejah da Hamma shehu suna godiya da soyayya.* ~Wani shehun kake nufi Uba, badai shehu usman namu ba, kai ba ma shi bane. Usmanu cikin 'yan fashi? Ina ka sake magana, nasan shehu bazai aikata hakan ba. Duk maganganun da yakeyi da ka ganshi zaka san ba cikin hayyacinshi yake yinsu ba. Su kuwa sauran'yan uwanshi banda Inna lillahi babu abunda suke jerawa. "Ku yarda dani, kun san bazan taso daga jalingi har nan dan in shirya karya in faďa ba, naga Usman ganin ido na a network news an nuna shi cikin 'yan fashi jiya da daddare kuma, jibi za a shiga dasu kotu ,gashi na tambayeku kunce baya nan yayi tafiya, hakan ya nuna da gaske shi ďinne kenan." "Kai dallah gyara maganarka, saidai idan mai kama da usmanu ka gani badai shehu namu ba, yaro mai hankali da hangen nesa. Ya karashe yana huci kamar zai haďiye kawun shehun. Yayansu ne ya jawo shi ya zaunar da shi. "Ka nitsu Umaru mu saurareshi mu fahimci maganar dan musan yanda zamu b'ullowa al'amarin tun da wuri." Baban shehunne yayi magana a karo na farko yace. "Abinda ban fahimta ba anan shine, shin an kama 'yan fashinne sun saci shehun shima ko kuwa..." Tun bai kare magana ba, bbn deeja ya daďa matsowa kusa ďan uwanshi kamar zai shige cikinshi, cikin saurin baki yace "Yauwa, nima abunda nakeso na sani kenan, sace sukayi shima kamar yanda suka sace 'yan uwanshi?" Haba wnn wani irin musiba ne, daga wnn sai wnn? Kai , abun yayi yawa." "Nitsu Umaru, kada kaje kayi sab'o, babu abinda zai samu bawa ba tare da sanin Allah ba." Jinjina kai sukayi dukansu tare da cewa "Wnn kam hakane." Bbn deejah ya kara da "Astagfirullahi wa atuubu ilaihi." "Kai muke sauraro uba, kayi mana bayani yanda zamu fahimta." Cikin nitsuwa ya sake yi musu bayani yanda zasu gamsu da cewa tabbas shehu ya gani cikin 'yan fashi a ntwrk news jiya, an nuno su, shima dai bayanin yakeyi amma sam hankalinshi ba a kwance yake ba. Dakyar suka nutsu suka yanke shawarar dole suje su gani da idon su dan su tabbatar, kuma kada a sanar da kowa a cikin gidan gudun *Tashin hankali* snn ko dan ciwon adda mahaifiyar shehu ya kamata su b'oye maganar. Washegari haka duka suka kama hanya da sunan zasu je wani t'aziyya ne, daga can kuma zasu wuce ďaurin aure, ta yiwu su kwana biyu kafin su dawo. Wnn shine maganar da suka shirya a tsakaninsu dan su sanar da iyalan sbd kar a samu matsala, dan ko yaya basa haďuwa suyi tafiya dukansu, dole a bar koda ďayane wanda zai jagoranci gidan kafin sauran su dawo. Sati guda sukayi a tafiyarsu suka dawo harda tsaraba sukayi, lokacin kuma Hamma shehu kwananshi uku da dawowa. ko da wasa kuma basu nuna alamun akwai wani damuwa ba. Bayan wata guda, Baban deejah suka kuma tafiya tare da Hamma shehu, daga nan dai idan an ďan kwana biyu ďaya daga cikin iyayen zasu yi tafiyar tare da Hamma shehu ko kuma shi Hamma shehun suje da babban wansu ďan baffansu Atiku, amma duk abunda akeyi mutanen cikin gida basu sani ba. Duk wannan lokaci da aka ďauka daidai da rana ďaya Deejah bata tab'a manta Smart da kuma soyayyarshi ba, wani lokaci haka zata tasa Mahmud a gaba cikin dare tayi ta kallonshi tana sharar kwalla, snn duk neman da zatayi mishi a waya bata samun shi. Moments ďinsu na farin ciki da suka yi sharing a jos da Bauchi suna abun tunawarta. Guraren shakatawa da yake kaita, guraren sayayya, parks, duk babu wanda bata tunawa. Addu'a kuma kullum yinshi take bata fasa ba, wani lokacin tsabar tunanin da take sawa kanta har muryarshi take ji kamar yana mata magana, ko kuma taji kamar ya kirata yanda ya saba (Mummy, ko Khadijah.) Haka kuma sosai take jinjina soyayyar Hamma shehu gareta sbd duk waďannan abubuwa da suka faru da ita basu sa ya nuna canji ko kađan, ko wani abu na soyayyarta ya ragu a zcyrshi ba, wanda ita a tunaninta tana ganin in wani ne tun saceta da akayi na farko ta kuma da ciki zata canji, balle kuma da aka sake ďauketa wnn karo har daďewa tayi kuma shi da kanshi yake magana canzawar da tayi alamun ko da aka ďauketa bata cikin matsala, amma duk da hakan baisawa ranshi zarginta ba, tabbas Hamma shehu ya cika masoyi na kwarai. A kwana a tashi ba wuya yanzu tayi wata biyar rabonta da uncle smart, zuwa lokacin Mahmud ya girma yayi wayo, yana tafiya, har gwalab'en surutu yanayi Irinna yara. Takanji a ranta inama da Uncle smart zaizo yaga ďanshi da yakeji dashi yadda ya girma, yayi wayo. Yayeshi da tayi ya sata komawa nguroje, sbd kukan dare da yakeyi yana neman abincin shi, da rana sam baya damuwa sai dare yayi barci ya farka sai ya fara lalub'e, rashin samun abunda yake so yake sashi tsala musu kuka, ita kuma jin kukan takeyi har cikin ranta, ga wani irin tausayinshi da take ji, kuma kunyar nuna hakan takeyi a gaban iyayenta shi yasa ta koma nguroje. Saidai duk da hakan tunanin yaron da kewarshi su suka bi suka addabeta, hakan yasa ta zamo wata sukuku da ita. Gashi komawarta gurin ya zafafa mata tunanin smart, duk lokacin da zata leka kofar gida sai taga kamar zata ga ya fito daga ďakin Bashar. Ga kuma jibgin kayanta wanda shi ya saya mata, har yanzu ta gagara tab'asu, illa zobe da ta sa a yatsarta. Duk lokacin da ta ďaga hanunta ta kalli zobennan sai ta tuno lokacin da ya ke ce mata, saka zobennan yana nufin ta amshi soyayyarshi ne, kuma ta amince zata aureshi. To ta yaya auren zai kasance?" Tambayar da takeyiwa kanta da kanta kenan sbd tasan dai tunda Hamma shehu yana kan bakarshi na aurenta babu fashi sai anyi, gashi ta gagara faďawa kowa damuwarta balle a bata shawara. Sati biyu da komawarta can goggonta ta sanar da ita ansa bikinsu ita da Fa'iza sati biyu masu zuwa, sbd haka nan da sati su shirya zasu tafi dorofi sbd shirye shiryen biki. A ranar Hamma shehu ma yazo mata da zancen biki, sosai kuma yake nuna farin cikinshi kan hakan. Tun lokacin da goggo ta sanar da ita maganarbikin ta shiga *Tashin hankali mara misaltuwa, sai dai tana iya kokarinta dan ta danne kada a gane. Cikon dare take tashi taci kukanta ta gode Allah, ta kuma yi nafilfilita roki Alllah, ya cire mata son smart ya dawo mata da son Hamma shehunta kamar da. A ranar da suka koma suka tarar da gida a cike, ga saniya da aka yanka ana ta sarrafa naman, ana kuma raba sadaka Gida dai kamar ana wani babban biki. Tun tana tunanin ko bikinnasu ne ya tarasu daga yanzu, har abun ya koma bata mamaki tana fara ganin abin ba haka bane. Hayaniyan Jama'a yasata barin gidan ta koma gidan Hajja inna tayi zamanta. Anan ta aika aka ďauko mata Mahmud. Tana nan har dare, bayan sallar isha'i tana cin abinci ta kwanta tare da ďanta a nan ďakin Hajja. Washegari tun da asubahi ta tashi tayi sallah ta sake kudundunewa cikin bargo bacci ya sake kwasanta, Mahmud ma Hajja inna ce ta ďauke shi ta mayar dashi gurin adda. Wajen karfe goma na safe ta tashi ciki duk yunwa bata ga hajja inna ba, ta kare dubedubenta kuma bataga abinci ba. Tana fitowa kofar gida sukayi kicibis da Fa'i tana shigowa rike da Mahmud, fiskarta fal fara'a. "Ina zakije haka kike sauri?" Deejah ta tambayeta da mamaki ganin yanda ta kwashi sauri har suka kusa cin karo. "Zo muje deejah, ana ta murna kina barci." D'an tab'e baki tayi tace "Ni yunwa ma nakeji fa'i." Cikin ďoki tace muje ki karya kisha labari. Langab'ar da kanta tayi tace "ayya fa'i kawo min abincin anan da wani kaya in canza kafin mu shiga gidan, wlh kaina juyawa yakeyi idan na shiga cikin jama'a." Da sauri fa'i ta juya tana cewa "Bari inje in dawo kisha labari." "Yauwa fa'ina, kawo shi dan ki dawo da wuri wlh sosai nakejin yunwan." Ta faďa tana karb'ar mahmud daga hanun fa'i. Tare suka dawo da Habiba, tana karyawa tace Habiba ta ďora mata ruwan wanka a wuta. "Labarin me kikace zaki bani?" Ta tambayi fa'i da tun dazu murmushi yaqi ďaukewa kan fiskarta. "Hmm, adda deejah labari mai daďi da ban mamaki kuwa." Habiba ma ta faďa cikin fara'a. "To ku faďa min mana." Ta faďa cikin zakuwa. "Ina yayanmu ďan farin adda da ake bamu labari ya b'ata tun ba'a haifemu ba?" "Eh, tace da sauri tana daďa matsawa kusa da fa'i. "To ya dawo jiya, an gano shi." "Wayyo Allah, dan Allah dai f'ai?, a ina aka ganoshi?, ina yake?" Ta jero wa fa'i tambayar bayan ta mike a zabure." Maida ita fa'i tayi ta zauna suna mata dariya da Habiba. "Jiya da daddare ya dawo, Hamma shehu da kawu Uba, suka dawo dashi, har yanzu ba'a sanar damu inda aka ganoshi ba." "Ina adda, yaya tayi da ta ganshi?" Ta sake tambaya a kagauce. "Ai na gaya miki jiya anyi abu, suna shigowa da Hamma shehu inda kikasan tagwaye dadayi ce ta haskesu da fitila tana tambayar Hamma shehu shi da waye, dan su yaya Ali duk sun dawo lokacin suna gida. Ai bata kare maganar ba ta haďiye sbd ganin kammani, adda kuwa take ta tashi ta tsaya jiki na karkarwa ta nufeshi tana kare mishi kallo, kafin ayi mata wani bayani kawai sai muka ga ta yanki jiki ta faďi. Saida ta farfaďo kafin su Baba suke gaya mana cewa yayanmu ne wanda ya b'ata ake nema." "Yanzu ina yake, muje na ganshi." Ta fada tana zura takalmanta. "Allah, adda deejah ko kinje baza ki samu ganinshi ba, ko yanzu ma da muka wuce jama'a ne cike a ďakin Hamma shehu, sai shiga da fita akeyi. Muma tun ganinjiya da dare da mukayi mishi ba mu sake sashi a ido ba, ki bari idan jama'a sun ragu sai muje mu ganshi. "Alhamdulillah, take ta maimaitawa har ta juye ruwan wankanta taje tayi, ta dawo ta canza kaya suna zaune suna jiranta. Hajja Innace ta shigo ta ďirka mata dundu a baya tana cewa "Sarauniyar 'yan bacci, jiya ina ta tashinki kije kiga abin farin cikin da ya samemu sai barcinki kikeyi har da minshari, kafafu a sama." "Kai, hajja." Ta faďa a shagwab'e, suko sai dariya suke musu." "Ai baccin naki ne abun haushi, shi yasa yauma na fita ban tasoki , ni kam ko baki samun bacci a gida Ramatunne, ko kuma laushin gadona ya saki wnn bacci haka." "Mu tafi nikam ko zan samu in ganshi." Hajja inna dake rataye mayafinta kan kyauren kofarta tace "Ahab, ai wnn ko shugaban kasa iyakaci, a yanzu kam bazaki samu ganinshi ba dan nima saida na yi bushewar ido na samu na kutsa na ganshi, bare ke kuma da idon mutane biyu ma zai zubar dake a kasa." A haka suka fita suka koma gida, kamar yadda Hajjan ta faďa kuma hakanne basu samu ganinshi ba. Gida kam gashi a cike 'yan taya murna sai shigowa sukeyi, wasu ma daga wasu kauyukan suke shigowa,dakyar ta samu ta shiga gurin adda ma ta rungumeta tana murna da barka. Ita dai adda bata iya amsawa sbd wai kunyar ďan fari, amma kam fiskanta ya gagara b'oye farin cikin da take ciki, shekara ashirin da bakwai ba wasa bane, har ta cire rai da sake ganin đanta Allah ya bayyana mata shi cikin hikima da buwayanshi. Har saida suka dawo daga sallar la'asar Hamma shehu ya aiko yusufa aka kirawo ta ganin mutane sun ragu. Da sauri ta ďauko gyalenta ta yafa ta saka takalmanta ta kira Habiba da fa'i suka tafi tare. A kofar ďakin suka haďu da Hamma Atiku suka gaishesu, ya fita ya basu hanya su shiga. Tunda ta kutsa kai ciki taji wata irin mummunar faďuwar gaba. Hakan ta daure ta qarasa ciki, su Fa'i suna biye da ita. Gaisuwar da tayiwa Hamma shehu ne ya sashi juyowa daga kwancen da yake, a take kuma ya mike tsaye a zabure yana kallonta ko kiftawa babu. Mikewan tayi itama cikin zafin nama lokacin da tayi ido huďu dashi, buďe baki tayi da niyyar yin magana amma ta kasa, sai kawai ta tafi luuu. Kafin takai kasa su Fa'i suka tarota ta zube a jikinsu sumammiya.... *F.O.W* * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *16* *Dedicated to all Fasaha group writers, Allah ya qara muku baseera da fasaha.* ~Cikin tashin hankali da kullewar kai yake binta da kallo, zcyrshi na matsanancin bugu, saidai ya gagara yin ko wani irin yunkuri akan halin da ta shiga. Hamma shehu ne ya ďebo ruwa mai sanyi ya yayyafa mata a fiska, saida ya yayyafa a karo na uku kafin ta farka. Buďe idanunta tayi ta sauke kanshi, shima ďin ita yake kallo cikin wani irin yanayi da bazai fasaltu ba. D'akin yayi tsit sai kallon kallo akeyi, su Hamma shehu kuwa sai su kalli wannan su juya su kalli wannan. Dukansu babu wanda yayi magana balle su fahimci abunda yake faruwa. Runtse idanunta tayi hawaye na gangarawa ta gefensu. Shi kuwa da baya da baya ya koma ya zauna kan katifar da ya tashi ya kuma rintse idanunshi sbd jirin da yake neman ka da shi. Dakyar Hamma shehu ya buď baki yace musu su shiga gida kada mutane su shigo su samesu a haka. A sanyaye suka kamata ta mike, ba tare da ta sake kallonshi ba suka fita. Shiru ya biyo bayan fitarsu, Hamma shehu dai nazarinshi yakeyi, shi kuwa kanshu ne ya kulle ya ma rasa irin tunani da zaiyi, ga wani irin sarawa da kanshi yakeyi, ga kuma dokawa da zcyrshi keyi. Ganin halin da yake ciki ne yasa Hamma shehu ya gagara yi mishi magana, ya sa kai ya fita tare da rufo mishi kofa sbd yasan zai bukaci kaďaicewa, duk da baisan menene matsalar ba, saidai yasan zaiyi wuya ya ji a yanzu. Gidan Hajja ya nufa da niyyar ya aika a kira mishi deejah, sai ko yayi sa'ar samunsu a can cikin ďakin Hajja innan, sai surutu take musu da alama haushi suka bata. "Kai shehu me ya samu deejatu sun fita nan da murna suka dawo dukansu kamar kajin da aka tsoma a ruwa." "Kanta ne ya ke ciwo." Ya bata amsa a takaice. Tab'e bakinta tayi tace "Shine kuma ina ta magana sukayi min shiru kamar masu ciwon baki, dan 'yar uwar ku bata da lafiya sai duk ku bi ku kashe jiki. Wnn ba sai kusa taji ciwonma ya karu ba, wawayen yara kawai." Ta karashe tare da gutsira goronta taci gaba da taunawa. Kusa da su ya karasa ya zauna, itako deejah tana kwance kan tabarmar da ke shimfiďe a ďakin Hajjan. "Sannu Hadiza." Yace mata da kulawa. Kai zalla ta gyaďa mishi, idanunta a rufe. Tsura mata ido yayi naďan lokaci, yana so ya mata tambaya ya rasa ta yadda zai fara. Ganin haka Habiba ta ja hanun Fa'i suka fita. Hajja kuma dama tana waje. "Hadiza me ya farune?" Ya tambaya. Shiru tayi dan ta rasa me zata ce mishi. "Kin sanshi ne?" Ya sake jefo mata tambayar. Cikin kuka sosai tace "Baban Mahmudu ne." Ras ras, yaji zuciyarshi ya tsinke, kanshi ya mishi wani dumm. Ya jima zaune a wajen yana tufka da warwara dukansu ba mai magana, karshe ya tashi ya fice daga ďakin. D'akinshi ya koma jikinshi duk ya gamayin sanyi. Sam baiyi mamakin abinda yaji daga bakin deejah ba, saima jinjinawa girma da buwayan ubangiji da yakeyi a ranshi. Kama dai yaro da ubanshi yake kama , rashin sani ne yasa aka ga kamar Hamma shehun ya ďauko. Kwance yake cikin rashin abinyi, jin shigowar Hamma shehu ya sashi tashi zaune. "Usman, wacece wnn a gunmu?" Ya tambayeshi tare da tsura mishi ido." "Kanwar muce." Ya bashi amsa lokacin da yake zama kusa dashi. "Kanwarmu as in how, u mean kanwa from same parent?" Ya sake tambayar tashin hankalinshi yana dađa karuwa. "A'a 'yar baffanmu da mukaje wajenka dashi sau biyu." "Huuhh, Thank God." Ya faďa yana sauke nannauyar ajiyar zcy. Sai yanzu ya samu ďan relief tunda ya ganta, sbd ayyanawa da yakeyi, idan ta kasance kanwarshice wacce suka fito ciki ďaya ya ya zaiyi. Daga nan suka shiru duk suka lula duniyar tunani. "Waye Hamma shehu?" "Nine." Ya bashi amsa yana mishi kallon son jin karin bayani. "Ina jn sunan sosai a bakinta, infact ta sanar dani kai zata aura." Sai ya ďanyi shiru na wani lokaci kafin ya sake cewa "Anyi aurenne?" Yana maganar ne amma shi yasan kalar luguden da zcyrshi keyi. "Ranar friday za a ďaura." Ya bashi amsa. Wata irin faďuwar gaba yaji kafin ya buďi baki dakyar ya ce. "Usman, zanso in roke ka gafara kan laifin da na aikata, nasan zuwa yanzu zaka fahimci abunda nake nufi, duk da ba ni na saceta ba tun farko, amma na aikata laifi mai muni a gareku duk da zan iya cewa hakan shi ya haska min hanya na gane munin rayuwar da nakeyi." A hankali ya fara bashi labarin irin rayuwar da yayi da abokanshi, haďuwarsu da Deejah, tsautsayin da ya gifta tsakaninsu har aka samu rabo, ďauketa da sukayi a karo na biyu, gaba ďaya babu abunda ya b'oye mishi. Karshe ya kara da neman gafarar sbd shi ya zamo silar rushewar aurensu. "Kada ka damu ďan uwana, wnn hukuncine na ubangiji, babu wanda ya fi qarfin Qaddara, Allah ne ya shiryar dakai amma ta sanadin Hadiza da Mahmudu, babu mamaki dalili kenan da Allah ya haďa dan ka shiryu ta sanadinsu. Fatana Allah ya dubi nadamar da kayi ya gafarta maka, Allah kuma ya shiryi wad'anda suka b'ata, ya kare mana al'umman musulmi baki ďaya." "Amin, usman, na gode qwarai da gaske. Ni nasan farin cikin da nake ciki a yanzu ,gani ga dangina, abinda na jima shekara da shekaru ina nema, Allah na gode maka." Ya qarashe yana goge kwallar farin cikin da suka surnano mishi. "Shine abin godiya, Allah ya daďa karemu." Shiru ya sake biyo baya kafin ya kuma cewa. "Ina son inga Mahmud, nayi kewarshi sosai." Murmushi Hamma shehu yayi, yace "Yanzu haka ba mamaki yana bayan adda, wlh ni har mamakin soyayyar adda da mahmudu nakeyi, amma yanzu na gano dalili, kullum fa cikin hidiman mahmudu take, tunda suka dawo ya koma wajenta, ashe jininta ne." Ya faďa yana murmushi. Tashi yayi yana cewa "Bari in dubo maka shi." Wani irin dad'ine ya mamaye mishi zcy yau zaisa gudan jininshi a idon shi bayan rabuwarsu na tsawon wata shida. Allah sarki, mahaifa, Allah ne yasan halin da zuciyoyin iyayenshi suka shiga lokacin da ya b'ata da kuma tunani da fargaba, kewa da suka tsinci kansu ciki tsawon shekarunnan da baya tare dasu, tunda yaji dalilinshi mahaifiyarshi ta kamu da hawan jini. Yana cikin tunani su Hamma shehu suka shigo hanunshi rike dana Mahmud. Waro ido yayi yana kallon yanda Mahmudunshi ya kara girma da wayo ga kuma da kafanshi ya shigo. Cikin tsantsan farin ciki ya ďaga shi sama kafin ya rungumeshi kam cikin jikinshi kamar zai maida shi ciki. Wani irin son yaron da qaunarshi da shi da mahaifiyarshi yake daďa fisgarshi. Bai ankara ba sai ga hawaye shar shar suna zubowa. A zuciyarshi sai kirari da yabo yake jerawa ubangiji. Tabbas Allah yana sonshi da ya shiryeshi kuma ya saukaka mishi al'amuranshi. Bai yi tsammani abubuwa zasu zo mishi da sauqi haka ba, ga gane mahaifanshi da yayi ga kuma ďanshi kusa dashi, 'yan uwa da dangi suna kewaye dashi kowa so yake ya nuna mishi qauna. Matsala ďaya zai fiskanta yanzu shine yadda zai yakice son khadijah daga ranshi ko dan farin cikin kaninshi ďan uwanshi mai kaunarshi. Shi kuwa Hamma shehu tsayawa yayi yana kallon ďan uwanshi cikin tausayawa, kamar ya taya shi kukan yakeji. Sassauta rikon da ya mishi ya bawa Mahmud damar kare mishi kallo, yaro da wayonshi sai ya maida kallonshi kan Hamma shehu , ya sake kallon Babanshi, nan ya shiga binsu da kallo idan ya kalli wannan sai ya kalli wancan. Hakan da yakeyi ne yasasu tuntsirewa da dariya dukansu biyu. * * * Gidan Hajja inna dukansu suka haďu sukayi ta hira daga iyayen har yaran. Rarraba idanu yakeyi ko zaiga Deejah amma har aka qare hiran wajen sha biyu na dare bai ganta ba. Ba karya yaji daďin wnn zama da akayi sai jin kanshi yakeyi yanzu ya zama cikakken mutum gashi cikin danginshi da gatanshi. Haka ranan yayi kwanan farin ciki gefe ďaya kuma tunanin makomar soyayyar da yakeyiwa deejah ya addabeshi. Ya sani yakice soyayyarta abu ne mai wahala a gareshi amma zcyrshi na bashi shawarar dole yayi hakan ko don ďan uwanshi. Washegari haka 'yan uwa da makwabta suka ci gaba da shigowa ana murnar dawowarshi, abinci kuma kala kala ake turo mishi, duk wanda zaizo da abinda ya ke riko mishi. * * * Tun daga lokacin da suka haďu walwalan deejah ya kuma raguwa, komai yinshi takeyi a sanyaye tamkar mara lafiya, gaba ďaya ta koma gidan Hajja inna da zama, kuma daga ranar babu wanda ta sake sawa a ido daga shi har Hamma shehu. Duk da son ganinshi da take sonyi amma ta gagara yunkurin aikata hakan. Ta gefenshi ma haka dauriya kawai yakeyi, amma baiki ya qara sata a ido ba. A bakin Fa'iza da Habiba takejin labarin wai har 'yan mata ake kawo mishi ya zab'i duk wacce tayi mishi a aura mishi. A sanyaye cikin tsinkewar zcy, cike da tarin damuwa take tambayarsu "Wa ya zab'a cikin waďanda ake kawo mishi?" "Bai zab'a ba saidai yace su zab'a mishi duk wacce suka ga tayi." Daga nan taja bakinta tayi shiru, tana jin zcyrta kamar zata fashe. Duk wani shirye shiryen da akeyi, ido kawai ta zubawa kowa, duk wani gyara da dabaru da ake mata biyesu kawai takeyi, amma ita tasan abinda takeji a ranta. Tun ana gobe ďaurin aure, ranar da akayi walimah kenan, tun daga wajen taron walimah takejin mummunar faďuwar gaba da tsinkewar zuciya. Kafin a qare walimar ta fara kuka har aka gama kuka takeyi. Ana gamawa matar Babanta ta kirata tayi ta bata baki da nasiha mai ratsa zucy, duk da bata san dalilin kukannata ba. Da dare aka zo akayi rufin amare, inda aka shafe kafafunsu da hannayensu da lalle, tare da feshe su da turare. Abokan wasansu kuwa lalle har fiska sukayi ta shafa musu lallen su kuwa amare sai kuka sukeyi. Washegari tun da safe karfe takwas da rabi aka ďaura aure. Suna cikin ďakinsu sukaji an saki guďa wanda ya tsananta bugun zuciyarta . Tare suka fashe da kuka ita da Fa'i, Habiba da sauran kawayensu suka fara tayasu. Bada jimawa sosai ba taji shigowar su Hamma shehu. Sai guďa ya karu da hayaniya. Kirjinta ta dafe ta haďiye kukan da takeyi sai ajiyar zcy da takeyi. A hankali ta zame ta kwanta tana jin kanta na wani irin sarawa, shi kenan yau kam ta gama tabbatarwa kanta ta rasa Uncle smart. Gashi dai ya dawon , burinshi ya cika na gane danginshi, gata gashi a gida ďaya amma auren da kaninshi aka ďaura ba dashi ba. A hankali ta ďago hanunta tana kallon yatsarta dake sake da zoben da ya bata....... TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *17*&18 *Dedicated to Fasaha group novel members at large.* ~Tana cikin tunani pendonayenta biyu suka shigo, hanunsu ďauke da kwanukan samira. Gaban amaren aka ajiye wnn karo harda na Habiba. Duk da dai sun saba duk abunda aka basu tare da ita suke yi, hakan bai hanasu jin mamakiba. Kallon juna dukansu sukayi ba tare da sunyi magana ba. "Bismillah, ku ci ina zaune ina kallonku." Deejah kamar zata rusa kuka tasa hanu ta buďe kwanon samiran, dafuwar kaxace wacce akayita da ďanyar saiwar bagaruwa. Yatsina fiska tayi tace "Yapendo nidai sai anjima zanci." "Nima." Fa'i ta faďa da sauri. Itako Habiba babu bakin magana sai kunne, wani iri takeji a jikinta, lokaci guda ta tsinci kanta cikin faďuwar gaba. Wani guďan aka kuma saki daga waje wanda ya dada faďar musu dagaba dukansu uku. "Zakuci ko sai na kira muku Hajja inna tazo ta baku da kanta." "A'a zamuci." Suka haďa baki wajen faďa suna kuma buďe kwanukan atare. Saida taga sun cinye tass sun shanye romon kamar yadda ta umarcesu snn ta tattara kwanukan da kasusuwan ta fita dasu. Ruwan wanke hanu da sabulu ďan kamaru aka miko musu suka wanke hannayensu dashi. Wata kanwar Deejah wacce suke hada uba, Hameeda ita ta shigo da gudu har tana haki, take cewa "An ďaura aure uku yau a gidannan." "Uku kuma?" Habiba da ta gama tsarguwa ta tambaya cikin saurin baki. "Eh, mana, Adda deejah, Adda Fa'i da Adda Habiba." Hanu ta ďaura a kanta tace "La haula wala quwwata Illah billah." Sai kuma tayi saurin sauqe hanun ta jawo Hamida kusa da ita tana zare mata ido. "Ke ki faďa min gaskiya wlh ko in miki dukan tsiya yanzunnan, ko kuma in haďa ki da Hamma shehu , ba ya hana ku karya ba." "Wlh, harda Hamma shehu da ya Manga da Yaya Ibrahima." Ya Manga sunan da suke kiran Smart kenan tun da ya dawo gidan wato (Babban yaya.) Ibrahima kuma shine wanda ya auri Fa'i. Dam dam kirjin Deejah ya buga, shi kenan ta faru ta qare ta rasa shi har abada tun da gashi har an ďaura mishi aure da kanwarta Habiba. Ita ya zab'a kenan. Zcyarta tayi mata tambayar. Ta kuma sake cewa "Ko dai su baba ne suka zab'a mishi ita." Duk yadda taso ta daure kasawa tayi, take taji jiri na kwasarta daga zaune, idonta ya fara gani dishi dishi. Da sauri ta koma kan gadon ta kwanta ta juya musu baya, hawaye na ta aikin ambaliya a fiskarta, suko Fa'i da Habiba, jin abin sukayi kamar tatsuniya ko a mafarki sbd haka suka saki baki da hanci suna bin Hamida da kallo kamar zasu gano gaskiyar lamarin a fiskarta. Itako Hamida ko a jikinta bata ma lura da yanayin da suke ciki ba ta mike ta fita tana rera waka tare da tafa hannayenta. Shiru ďakin ya ďauka tamkar babu kowa a ciki. "Kai, bari inje inji gaskiyar maganar." Cewar Fa'i tana mikewa. "Ku fito kuyi wanka." suka tsinkayo muryar goggonsu dake tsaye daga bakin kofa. "Deejah, tashi maza kuje kuyi wanka." Ta sake faďa tana kallon bayan Deejah. "Inajin tayi bacci fa." Cewar Fa'i. "Taso ta Habiba, maza tun kafin ruwan ya huce." Tashinta ta shiga yi itako tayi likimo tamkar mai baccin dagaske. "Idan kika bari na shigo ďakinnan baza ki ji daďina ba Deejah." Ta sake faďa a kufule. A hankali ta tashi ta zauna tare da lalub'o gyale ta yafa akanta ta jawoshi sosai ya rufe mata fiska. Sumi sumi suka fita dukansu, ita Fa'i tayi hanyar ban ďakin Adda, ita kuwa Deejah nasu na yaran gidan ta shiga sai kuma Habiba da aka turata na Dadayi. Ruwan lalle ne wanda aka wadata shi da turare mai daďin kamshi. Gaba ďaya ya buďaďe bayan gidan da kamshi. Wankan sukayi amma dukansu tunani ne fal cikin ransu, bama kamar Habiba da ta rasa gane takammamen abinda take tunani. Fa'i ce ta fara fitowa ta shiga ďakin adda. Saida ta je kusa dab da dab da addan ta ce ta yi qasa da muryarta "Adda, Hamida tace harda Habiba aka ďaurawa aure, wata aura." "Nima ban sani ba, Fa'i, yanzu nima na samu labari, koma menene zamuji daga baya, tafi ďakinku ki shirya an kai muku kayan sawanku a can." Jinjina kai tayi ta tashi ta fita. Sabbin kaya aka ajiye musu dukansu uku, abin sai mamaki yake basu. Yarsu kanwar Hamma Atiku ita suka samu a cikin ďakin. Batayi nauyin baki ba itama ta jefa mata tambayar da tayiwa Adda. Daga Deejah har Habiban kirjinsu bugawa yakeyi suna jiran amsa. Amsai ďayace itama batasan da wanda aka ďaura auren ba. Cike suke cikin ďakin da kawayensu da wasu daga cikin dangi 'yan mata sai hayaniya ke tashi ana ta shewa , Habiba da Deejah dai daurewa kawai sukeyi suna biye musu amma sam hankulansu basa jikkunansu. Abincin rana aka kawo musu, gefe guda kuma fruits ne, Ayaba, yankakkun abarba da kuma pear cikin babban tray. Dake su a can waďannan fruits ďin kamar abun banxa ne a wajensu basu wani damu dashi ba, sai bakin da suka zozzo daga wasu garuruwa ne suke ta marmarinsu. ~Bayan sallar la'asar hidindimu suka karu sbd shirye shirye kai amarya da sukeyi, Fa'iza kaďai za a kai a ranar, masu kiďan gargajiya na fulani ma sun iso suka fara aikinsu a kofar gidan, 'yanmata da samari sai cashewa sukeyi, yan kallo kuwa suna ta bawa ido abinci. Ganin raguwar jama a cikin gidan yasa ta leka, ta kira yaro ta aikeshi ya kira mata yusufa. Bada jimawa ba yusufa ya iso. Tambayarshi tayi ko da mutane a ďakinshi yace babu kowa, kulle ďakinma yayi ya fita. "Bani keyn ďakin." Tace dashi. Cikin aljihunshi ya zura hanu ya ďauka ya mika mata. Har ya fara tafiya, sai kuma tace mishi ya jirata su fita tare. Ciki ta koma dan ďauko babbar mayafi ta samu Habiba na ta rusa kuka dan yanzu kam ta tabbatar da itama auren akayi mata. "Ba kece da kuka ba Habiba, nice da kuka." Ta faďi hakan cikin zcyrta tana bin habiban da kallo. Ita ko Fa'iza sai aikin lallashi takeyi, tanajin kamar ta tayata kukan. A sulale suka fita ba tare da an lura da fitannasu ba, har cikin ďakin ya rakata kafin ya fita ya jawo mata kofa. Zama tayi a bakin gadonshi tana kallon zoben dake maqale a yatsar hanunta. "Uncle smart." Ta faďa a hankali kamar mai raďa. Tsabar yanda takejin wani irin zafi a zcyrta, kukan da takeso ta zo tayi a cikin ďakinma ya gagareta. Tunanin haďuwarsu tun farko ta farayi har zuwa lokacin da suka rabu, ta koma tunanin ganinshi da tayi a matsayin ďan uwanta, gashi yanzu kuma ya zama mijin kanwarta. Wani irin sanyi taji ya fara shigarta, kafin ta ankara taji sanyi sosai na shiga jikinta, hakan yasata jawo bargon yusufa ta kwanta tare da lullub'e dukkan jikinta. Tana nan kwance taji an turo kofar a hankali. A zatonta yusufa ne ya shigo shi yasa bata ďago ba. Idanunta a rufe tace "Yusufa wai da gaskene harda ya manga aka ďaura auren?" Jin shiru bai amsaba yasata ďagowa ta kalleshi. Karaf suka haďa ido dashi yana tsaye ya zuba hannayenshi cikin aljihun light brown half jumper dake jikinshi. Zuciyarta ne ya bada damm, ta fara tunanin me ya shigo dashi ďakin. Amsa ta bawa kanta cewar baisan tana ciki bane. Mayar da kanta tayi cikin bargo ta lullub'e kan. A hankali ya tako ya karasa gaban gadon tare da durqusawa kan rug ďin dake tsakiyar ďakin. Yaye bargon yayi, yana kare mata kallo, sosai yaga ramar da tayi. Zcyrta ce ta tsananta bugu lokacin da ta jishi kusa da ita hakan ya sata rintse idanunta da karfi. "Baki da kirki mummy." Taji muryarshi cikin kunnuwanta, wanda ya ratsa dukan jijiyoyi na jikinta. A hankali ta buďe idonta tana kallonshi ta kasa yi mishi magana. "Bayan rabuwar watannu shida, na dawo cikin nasara sbd na gane iyayena da yan uwana cikin sauqi, cikin sa a ya kasance, swthrt ďina da mom ďinshi duk suna cikin dangina, suma na ganosu ba tare da shan wahala ba kamar yadda na zata, amma abin mamaki kina gani na sai kika saki jiki kika kwanta kika rufe ido da gangan dan kada ki kalleni sbd aurenki ya kusa ko?" Haushi maganarshi ta bata, wai ta rufe ido da gangan, wato ma yana nufin bai san sumewa tayi ba, kuma dan baisan halin da zcyrta ke ciki bane yake faďar haka. "Kuma tsabar ki tabbatar mini baki damu dani ba shine ko ki nemi ki sake ganina duk kokarin da nayi dan na samu ganinki amma kikayi ta min rowar fiskarki. Ga babbar kyauta da na samu, na samu mata, nima yanzu na zama magidanci amma ko tayani murna bakiyi ba." Wani kululun bakin cikine ya tokareta, bata san sanda ta ďago ta banka mishi harara ba. Wato har shi da bakinshi yake ce mata ya samu wata mata kuma yana nufin ta taya shi murna. Dariyar da yayi ne ya sata fashewa da kukan da ita kanta batasan yaya akayi yazo mata ba. Take ya hađiye dariyar ya kuma cewa "To meye abin kuka kuma daga fađan gaskiya?" "Dan Allah ka fita ka kyaleni bana son damuwa, kaje can ka samu amaryar taka tunda kasan ni ďinma yanzu matar aurece." Ta faďa cikin matsanancin kuka da zafin kishi. "Wait, what are u talking about, wace amarya kuma zan samu bayan gaki kusa dani, wani auren kuma kike magana bayan nawa dake kanki . ko yau ďinma baki son ganina ne, dan Allah mummy laifin me na miki kike min irin wnn horon?" Ya karashe maganar yana marairaicewa kama qaramin yaro. Galala ta saki baki tana kallonshi kamar taga sabon halitta. Hure mata idanun yayi yace "What." "Uncle smart wa aka aurawa Hamma shehu, bana ji dashi aka ďaura auren ba?" Ta faďa tana mikewa zaune. Tashi yayi daga inda yake durkushe ya dawo kusa da ita yana kallonta cikin ido, saida taji kunya ta kawar da nata idon. "Nidai kamar kafin mu rabu nace miki zan dawo ne a matsayin daddyn Mahmud ba Uncle smart ba." Sbd tana so taji kan zancen sai tayi saurin cewa "To daddyn Mahmud." Murmusawa yayi kafin yace "Habiba aka aurawa shehu ni kuma aka bani matata." Ya karashe yana ďaga mata gira. Wani sanyin dadi ne taji yana ratsata, tuni zazzab'in da ta fara ji taji ya tafi, lokaci guda taji kunyarshi ya rufeta ta sunkuyar da kanta tana murmushin farin ciki dan kam bazata iya b'oye wnn farin cikin da ta tsinci kanta ciki ba. Yatsar hanunta mai zoben ya kamo ya haďa da nashi mai zoben azurfan da ta bashi yana kallo. A hankali ya saukewa yatsannata peck, wanda yayi shocking ďinta, snn ya maida hankalinshi ga zanen lallen da aka zana mata ja da bak'i. "Wa ya miki wnn abun?" Ya tambaya yana bin zanen da yatsanshi. "Surayya." Ta amsa ba tare da ta kalleshi ba. "Yayi kyau sosai, ina sonshi." Ya kare maganarshi yana binta da kallo. "Me ya faru ne naga kin rame sosai." "Kaima ai ka rame." Ta faďa yayin da ta ďaho tana kallonshi. "Tsakani da Allah rashinku kusa da ni ya ramar dani, ke fa?" Kawar da maganar tayi ta hanyar jefa mishi tata tambayar "Ya akayi kuka hađu da su Baba?" Muskutawa yayi ya sauke kwakkwarar ajiyar zcy....... *Dan Allah fans ku tausaya min, ku rika yi min uzuri, wlh turawa ta pcn nan yana bani wahala, mutanene da yawa kowa yanaso, idan nace zan biye turawan bazan samun daman typing da posting akai akai ba, ku rika cigiya a grp, dan Allah grp members kuma ku rika taimakawa kuna bawa masu nema, shine zaman taren * *Ina yinku ina kaunarku irin sosai d'innan, ku huta lafiya.* *F.O.W* * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* * Impacting Valuable knowledge and Entertainment is our concern * *18* *Sadaukarwa ga dukkan masoyan nvl ďin Tashin hankali, duk inda kuke.* *Allah ya raba mu da tashin hankali.* *_Flash Back_* ~Lokacin da smart ya kai kanshi ga hukuma, sosai abin ya basu mamaki, jin cewa shi ďin kungurmin ďan fashi da makami ne ya kuma kawo kanshi dan a hukuntashi. La'akari da cewar da yayi yayi nadamar ayyukan da ya aikata a baya ne yasashi mika kanshi, kuma yana da niyyar gina tsaftatacciyar rayuwa bayan ya karb'i hukuncin da ya dace dashi, hakan yasa suka maida hankulansu gareshi suka kuma yarda cewa ba wata muguwar nufi ne ya sashi tukaransu haka ba. Da taimakonshi aka kama manyansu kasancewar ya gama sanin dukkan sirrinsu. Ta hanyar manyan akayi ta bi har aka gane sauran 'yan ta'addan waďanda suke wasu garuruwa duk da dai da farko an sha wuya kafin suka amsa laifinsu saida suka ci azaba, ganin za a halakasu ne yasa su faďin inda sauran suke. Anyi nasarar cafke kashi tamanin daga cikinsu, sai ďaiďaikunsu ne suka tsira. Yawancinsu da sukayi arba da smart ba karamar kaďuwa sukayi ba, dan sun shafe labarinshi a tarihin rayuwarsu, sun yi tsammanin ya daďe a lahira. Duk da kaďuwar da sukayi bai hana scorpion da Nass nuna jin daďin ganinshi a raye ba duk da suna cikin hali na *tashin hankalin* cafkesu da akayi dan kona gidan smart da akayi ba karakin kaďa su yayi ba, tun da lokacin basu gama jimamin mutuwar abokinsu billy ba. Su suke faďa mishi cewar Mark ďaya daga cikinsu shi yazo gidanshi ya koma ya faďawa ogansu abinda yaji yana faďawa khadijah, sanadiyyar hakan suka yanke konashi daga shi har khadijan sbd gudun tonuwar asirinsu. Saida aka kona gidan kafin aka sanar da su scorpion halin da ake ciki sbd tunanin kada su sani da wuri su b'ata musu plan ta hanyar sanar dashi. Mark shi ya jagoranci kona gidan smart, sbd haka scorpion ya fakeshi ya harbe shi lkacin da suka fita wani operation, ba tare da an fahimci shi ya aikata hakan ba, sai Nass kawai da yasan komai. Suma scorpion ba a wani sha wahala dasu ba suka amsa laifinsu sbd haka aka shigar dasu kotu domin yanke musu hukuncin da ya dace dasu. Nunasu da akayi a network news ne yasa 'Yan uwan adda suka ga kamar Hamma shehu ne a cikin su sbd haka ba b'ata lokaci aka wakilta wanda zai je ya sanar da iyayensu. Babu wanda yayi tunanin kiran layin shehu daga cikinsu, shi kuma dama ko ya kira ba shiga zaiyi ba indai ba dace yayi suna wajen service ba, shi yasa basu communicating ba har suka tafi can abuja. Ranar da aka shiga kotu domin yanke hukunci Allah yasa sun riga sunje domin su tabbatar da abunda aka sanar dasu, su biyar suka je, biyu daga ciki kawunan su Hamma shehunne. Suna ganin smart suka fahimci cewar ba shehu bane duk da kamar da suke dashi, sbd shi smart ya ďanfi shehu haske da faďi, snn yana da wani bakin ďigo ta gefen idonshi. Amma take suka fahimci cewar ďansune da ya b'ata shekaru ishirin da bakwai da suka shuďe a lokacin yana ďan shekara biyar. Babu b'ata lokaci suka sanar da alqali abunda yake tafe dasu, cewa ďaya daga cikin b'arayin ďansu ne da ya b'ata tun yana da shekaru biyar, bayan an kammala yanke musu hukunci. Kwanaki biyu aka kara snn aka sake wani zaman inda aka nemi smart da kanshi da ya faďi yadda ya fara wnn harka. Take ya sanar dasu cewa shima ya tashi ya ganshi ne cikin harkar nan ya basu labarin yanda suka taso a gurin ogansu. Koda aka nemi ogansu karyatawa yayi da cewa da girmanshi ya kawo kanshi sbd kada a sake kama shi da laifin satar yaran mutane. Da ďaďaya aka nemi sauran b'arayin inda yawanci kamar yanda smart ya faďa haka suka faďa sai wasu daga cikinsu ne suka ce da girmansu suka shiga harkar. Hakan yasa aka qara musu sati biyu kafinnan anyi kwakkwaran bincike. Dawowarsu Hamma shehu kawai suka sanarwa. Bayan sati biyunne Hamma shehu suka koma tare da bbn deejah da kuma kawunsu guda ďaya. Ganin Hamma shehu ya tabbatar musu da cewa da gaske smart ďansu ne sbd haka aka tilasta ogansu ya bayyana yanda akayi ya samesu. Saida yasha bakar wuya kafin yayi admitting cewa sato shi yayi a wani kauyen Sardauna local government, sauran ma haka yayi ta lissafo garuruwan da ya ďauko su, anan Nass da Scorpion suka san cewa su 'yan Maiduguri ne, amma daga kauyuka mabambanta. Tsabar farin ciki smart har kuka yayi da yaga danginshi sunzo nemanshi da kansu, bai gushe ba kullum cikin godewa Allah yakeyi da baiwar da yayi mishi na samun shiriya dana gane iyayenshi. Tun daga nan aka shiga sanarwa kan duk wanda yasan ďanshi ya bata cikin waďancan shekaru yazo ya duba ko zai gane ďanshi. Hakan kuwa akayi mutane daga gurare daban daban sukayi ta zuwa, wasu sun gane 'ya'yansu, wasu kuma basu samu nasu ba. Cikin masu zuwa har da iyayen Scorpion da Nass, farin ciki sukayi tayi na gane danginsu. Saidai kam sunyi kukan rashin Billy ba kađan ba, da shima yaga wannan abin farin ciki. Da yake akwai hukunci akansu basu tafi tare da iyayensu ba nan suka barsu sai wa'adin da aka ďiban musu ya cika, bayan haka kuma duk wanda basu manta satar da suka mishi sun bayar da credit card ďinsu, dan a cire kuďaďe a mayarwa waďanda rabonsu ya rantse, fashin da sukayi a kan hanyoyi kuma sun roki jama'a waďanda abun ya shafa da su yafe musu. Mutanen da suka sato suka ajiye a gidajensu suna musu bauta duk anbi an sallamesu, kowa ya kama gabanshi. Manyan oganninsu su aka yankewa hukuncin ďaurin rai da rai sbd munanan b'arna da sukayi ta aikatawa, barinsu a doron kasa haďari ne, makamansu da an bi an kwashe. Saida suka kwashi watanni shida cikin gidan yari da horo mai tsanani duk da na smart da ďan sauki tun da shi ya kawo kanshi. Cikin ikon Allah wa'adinsu ya cika aka sallami waďanda aka ga nadama a tare dasu, su kuma kangararrun aka ci gaba da tsaresu, wađanda suka gudu ba a kamasu ba kuma ana kan nemansu. Hamma shehu da kawunsu su sukaje suka ďauko shi, saida suka kwana uku a jalingo ya huta, sosai yaga gata da kulawa wajen dangin mahaifiyarshi , kafin suka kamo hanyar dorofi. Ranar ta zamo babbar rana kuma ranar farin ciki a gareshi, sbd yau zai sanya mahaifiyarshi da sauran 'yan uwanshi a idonshi. Shima yau zai zama kamar ko wani ďa mai 'yanci. Bayan haka karin farin cikin shi shine kasancewar garinsu ďaya da khadijanshi, bazai sha wahalar nemota ba, gashi yaga iyayenshi, yasan idan ita rabonshi ce zai sameta tunda shima yanzu da gatan shi, babu batun fargabar za a binciki iyayenshi. Su kuma nan dorofi babu wanda yasan da zancen an gano Mahmud, saniyar da aka yanka ana ta sadaka dashi, duk sunyi tsammanin ko a cikin hidiman biki ne, snn an sanar dasu dai suna da babban bako da zai zo daga jalingo, shi yasa sukayi shiri sosai na tarbanshi. Wnn bazatanne ya jawo sumewar adda da ta ganshi, sbd duk da ta jima rabonta dashi, ya girma amma hakan bai hanata gane shine Mahmudunta ba da ta ganshi. ~ Ajiyar zuciya suka sauqe gaba ďayan su kafin ya ci gaba da cewa. "Khadijah, duk lokacin da na ďauka a gidan yari kullum kuna raina, ban tab'a mantawa da tunaninku ba, burina kullum na ganni a tare daku. Sai gashi cikin ikon Allah, Allah ya bayyana min ku cikin sauqi ba tare da nasha wahala ba. "Khadijah ina alfahari daku, kune silar kyamatar sana'ata, kune silar gano iyayena, banyi tsammani zanyi rayuwar farin ciki ba in har babu ku a tare dani. Bazan gakiya da yiwa kanina ďan uwa rabin jikina usman addu'a ba dan yayi min sadaukarwa mai muhimmanci a rayuwata, na godewa Allah da ba ciki ďaya muka fito dake ba, da ban san yanda rayuwata zata kasance ba. Na godewa Allah da ya bani ďan uwa mai kaunata da kuma fahimtar damuwata. Wlh Khadija ranar da yace min saura kwanaki kaďan a ďaura muku aura ji nayi kamar kaina ya kwance, jun kaina bnake kamar bani da cikakken hankali, komawa nayi tamkar wani mara lafiya. Duk abinda nakeyi cikin karfin hali kawai nakeyi, aAllah kaďai yasan alin da zuciyata ke ciki. Addu'a nakeyi ba dare ba rana, Allah ya zab'a min abinda yafi alkhairi. Kwatsam anzo ďaurin aure duk da dai dama ance min dahar dani cikin angwayen ban nemi sanin wacece amaryar ba sbd nasan ni da kaina na basu zab'i. Allah maji rokon bawa sai naji da khadijata aka ďaura auren. Wlh mummy tsabar farin ciki saida na zubar da qwalla. Babu abunda zan cewa shehu, babu abinda zan saka mishi da shi sai addu'ar Allah ya biya shi da aljanna mafificiya. "Amin." Tace tana share hawayen farin cikin da suka surnano mata, a yanzu jinta take yi sakayau, bata da wata sauran damuwa, hankalinta ya kwanta, a hankali farin ciki yake maye mata gurbin bakin cikin da take tare dashi. D'ago hab'arta yayi yana kallon cikin idanunta. "Allah yasa wnn hawayen na farin ciki ne." Gyad'a mishi kai kawai idanunta a ru fe dan baza ta iya jurar kallon kurillar da yake mata ba. Share mata hawayen yayi tass kafin ya kuma cewa "Dan Allah mummy buďe idanunki ki kalleni kuma ki bar kukan hakanan." A hankali take buďewa kamar tana gudun kada taga wani abin tsoro. Langab'e kanshi yayi kamar karamin yaro yace "Mummy bani labarin bayan rabuwar mu." Kanta ta kawar gefe kafin tace a sanyaye "Sai mun sake haďuwa kaga yanzu magriba tayi." Ajiyar zcy mai karfi ya sauke yace Allah ya nuna mana. Daga nan kuma aka shiga gardamar yanda za a fita daga ďakin danshi yace tare zasu fita, ita kuma tace bazata iya wnn abun kunyar ba saidai ta fara fita ko shi ya fara. Toh, ni dai nace koma wanene zai fara fita Wnn kuma ku ta dama dan nikanm sallah zanje inyi kar lokaci ya k'ure...... Bayan sallar magriba dukansu sun hallara a ďakin baban su Hamma shehu , amaren da Angwayen sai iyayensu. Nan iyayensu suka yi musu nasiha mai shiga jiki snn suka yi musu bayanin yadda akayi al'amarin ya juye, a takaice Allah baiyi Deejah matar shehu bace. Ita kuwa Habiba hakuri aka bata na yanke hukuncin da sukayi ba tare da saninta ba, duk da cewa da amincewar mahaifinta akayi komai. Sai a snn suka san cewa Mahmud ďan Mahmudu ne. Sosai sukayi mamaki da kara girmama al'amarin ubangiji. Adda kam har kuka tayi, tana tuna dagewan da tayi tana yiwa wanda ya lalata musu deejah munanan addu'o'i, ashe ďan cikinta takeyiwa. Nanma dan mijinta yana taka mata birki da cewa ta yarda da kaddara, kuma ta daina yiwa ďan wani munanan addu'o'i kada ta manta itama tana da nata 'ya'yan bata san kaddarar da zai iya faďa musu ba... A ranta take cewa ba banza ba mahmudu ya shiga ranta sosai a she jininta ne, duk da cewa sunan shi da kamanninshi ma sun taka muhimmiyar rawa wajen kara mata son yaron. Ya manga kam da sun haďa ido da khadijanshi sai ya sakar mata murmushi, itako kunya kamar ta nitse, gani take kamar kowa yana kallonsu. Saida akayi kiran sallar isha'i duk suka watse. * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* * Impacting Valuable knowledge and Entertainment is our concern. * *19*&20 *Dedicated to Haj. Aisha T. Yamel (Mmn Mima)* ~Mamaki bai bar zuciyoyinsu ba na yadda akayi tuntuni khadija bata tab'a kawo musu zancen smart ba, kodon kamanninshi da 'yan gidansu. Karshe matar babanta tayi mata tambayar dake cin zcyrta nan kuma deejah ta sanar da ita cewa itama sai ranar da zasu rabu na karshe ya bayyana mata asalin kammaninshi, kuma ita tsorata tayi sai take tunanin kamar idanunta ne basu gani dadai ba. Dangin gidan ango ne suka zo d'aukar amaryarsu, abokan ango kuwa suna kofar gida tare da kawayen amarya, suna ta gwabzawa kan maganar kud'in fitar da amarya. Itako amarya dama tun da Magriba aka kaita gidanta fikin rakiyar matar kawunta da goggonsu Mmn Habiba. Wata daga cikin cousins dinsu aka lullub'e da sunan itace amaryar aka sata a mota sai kuka irin ta amare takeyi kamar gaske. Amarya ko dama ta riga ta gama shan kukanta tun kafin a tafi da ita. Harda su Habiba da Deejah cikin 'yan zuwa kai amarya. Hayaniyar mutane da gud'a kawai kakeji yake tashi, a gidan amaryar. Kujeru na plastic aka jera a kofar gida aka sa kid'e kid'e na zamani samari suna ta cashewa. Wnn na tarban amarya ne. 'yan kallo ma ba barsu a baya ba sunje bawa idanunsu abinci. Su Deejah kam suna ciki tare da amarya, sai kakar amarya ta gefen adda, wato kanwar Maman addan da aka barsu tare. Kusan kwana akayi ana cashewa na murnar zuwan amarya. Nan suka kwana kasancewar babu jama'a duk sun koma gida sai washe gari kuma za a dawo a ci gaba da shagali. Washe gari aka ci gaba da shagulgulan biki, su Deejah da Habiba duk a takure suke sbd igiyoyin da ke kansu babu dama su shiga cikin kawaye ayi hidima dasu sai a cikin gida. Girke girke akeyi kala kala, kasancewar har saniya aka yanka, nama birjik sai sarrafa shi akeyi. Abinci kuwa rabawa akayi tayi gida gida, wadanda suka shigo ma suci rabonsu. Yamma nayi akayi bud'an kai, ana gamawa kuma aka shiga fitan angwanci. kafin magriba aka gama, manya suka fara watsewa. Biki aka hada a wani fili na musamman da aka tanada sbd hakan. Angwaye da kawayen amarya, da kuma yan uwa da abokan arziki ake hallara a gurin, a gayyaci mawaka kowa suzo su baje basirarsu. ~"Adda deejah nikam fa zanje gurin dinner dinnan." "Zuwa kai." Deejah ta bawa Habiba amsa da sauri." Kwashewa sauran kawayen sukayi da dariya daya daga cikinsu tace. "Mudai babu ruwanmu idan mazajenku suka ganku." "Dama bamuce da ruwanku ba ai." Cewar deejah yayin da take gyara d'aurin d'ankwalinta. Ba karya sunsha kyau ba kad'an ba. Suna fitowa kofar gida inda abokan ango suke jiransu, su wuce, saiga yusufa. Make shi Deejah tayi a kafad'a tana cewa kai kuma daga ina, ko tare zamuje ? " "Zanje amma dai yanzu aiko ni akayi." "Waya aiko ka ?" "Ya manga." Dumm taji zcyrta yayi, rabonta dashi tun jiya da suka rabu da yamma. Allah yasa ba hanata zuwa zaiyi ba. "Wai ki biyo ni muje gida tare yanzu." Juyawa tayi tana neman Habiba, can ta hangota zata shiga mota, ta kwala mata kira. Hanyar gida suka kama suna hira. Can tace "Me yace maka yusufa kafin ya aiko ka ? " Dan ita sam hankalinta bai kwanta da kiran ba. "Ya tambaye nine har yanzu ba a gama bikin ba ne, ni kuma nace mishi ba a gama ba dan yau za a yi ajo. Shine ya tambayeni yanda akeyi na fad'a mishi." Katse shi da cewa "Sai kuma yace kazo ka kirani." "Eh mana." Ya amsa mata cikin nuna gajiyawa da tambayoyin da take jera mishi. "Anya Habiba, za a barmu muje kuwa ? " Ta juya tana tambayar Habiba cikin shakku " "Kayya watakila tare zakuje ma, dan naga shima kamar ya yi shirin zuwa bikinne." Ajiyar zcy ta sauke tana d'an jin relief. Tun kafin su karasa isa kofar gidan suka hango Hamma shehu da uncle smart tsaye a kofar dakin Hamma shehu, dukansu sanye suke da rigunan sanyi masu kauri kamar na yusufa. Lokaci guda Habiba tayi wani irin diriricewa, dan har yanzu shock da ta shiga na maganar aurenta bai gama saketa ba, baza tace bata son Hamma shehu saidai bata taba kawowa ranta cewa zata aureshi ba dan dan uwa kuma mijin 'yar uwarta ta daukeshi. Duk da su din abokan wasa ne, kuma sosai suke raha idan sun had'u, amma yanzu sosai takejin kunyarshi. Gaishesu sukayi dukansu biyu a tare, suka kuma kama hanya zasu shige gida. "Khadijah." Ta tsinkayo muryar shi yana kiranta. Cakk ta tsaya, yayin da Habiba tayi saurin shigewa cikin gida. Barin wajen Hamma shehu yayi dan yasan ba lallai bane ta yarda ta je yana wajen sbd kunya. A hankali ta fara takowa tana zuwa wajenshi, yayin da ya zuba mata ido yana kallon yanda take takawa daddaya a hankaliv kamar bata da jini a jiki. Tana karasowa ya wani hade rai ya daure fiska, ya kama gyalenda ta yafa ta sama, yace "Ina kika kai min auren ? " Da mamaki ta dago ta kalleshi, saidai yanayin fiskarshi ya tsoratata yanda taga yayi kicin kicin. Shiru tayi tayi kasa da kanta, zcyrt na dokawa dan zata iya cewa bata tab'a ganin ya daure fiska haka ba. Juyawa yayi ya shige dakin shehu ya barta tsaye anan gurin tana tunanin binshi zatayi ko kuma tayi wucewarta. A sanyaye tabi bayanshi ta tsaya tayi sallama daga bakin kofa. Amsawa yayi tare da bata izinin shiga. A dari dari ta shiga ta zauna gefen three sittern da ke cikin dakin a darare. "Dawo nan ki zauna." Ya umurceta yana nuna mata kusa dashi kan kujerar. Kusan a tsorace ta zauna tana maimaita kalmar ina kika kai min aure ? Ta kamar yaya, me yake nufi da ina ta kai mishi aure. "Khadijah, ina kika fito ? " Ya sake jefo maya wata tambayar. Muryarta na rawa tace "Gidan Fa'i." Amma can kasan zcyrta tana jin haushin takurata da yakeson yi dan taga alamun hakan daga gareshi. "Wa ya baki izinin zuwa gidan ? " "Ikon Allah." Tace a ranta, yayin da take ta lankwasa yatsun hanunta. Kura mata ido yayi yana bin kwalliyar fiskarta da kallo. Hanu yasa ya lakaci janbakin da tasa a bakinta. "Wnn duk wa 'yan bikin kika yiwa kenan ? " Jin bata tanka ba yace "Ya ina ta magana kin min shiru." Girgiza kanta tayi alamar a'a. "Yanzu khadija kin kyauta min kenan, kin kama hanya kin tafi ba tare da sanina ba, snn kika kwana kika wuni baki tunani Mahmud bama balle babanshi, bayan haka a matsayinki na matar aure ji kwalliyar da kikayi zakije ki nunawa wasu mazan, dubi gyalen da kika yafa, ina mutunci anan." Har yanzu fiskarshi babu walwala yake maganar. "Kayi hakuri." Ta iya cewa kamar zatayi kuka, can kasan zcyrta tana jin cewar tayi ba daidai ba. "Khadijah, ina da kishi sosai, dan Allah kada ki kara irin haka bana so, bazan iya jurar ganinki cikin wasu mazan da kwalliya irin haka ba, ki ga gyalen da kika yafa fa." Ya sake maimaitawa yana jan gyalen. Wato ma gyalen shi yafi bashi hausjhi kenan, shi yasa ya saya mata manyan hijabai lokacin da suke Bauchi. Ta ayyana hakan a ranta. Hakurin dai ta sake bashi, dan bata da abin da zata ce mishi. Take kuma taji fitanma ya fice mata arai. Jin baice komai ba ta tashi zata fita daga dakin. "Ina zakije kuma ? " Wayyo Allah, ji tayi kamar ta rusa kuka, itafa yanzu damuwarta batso wani yasan cewa tana cikin dakin. "Zo ki zuba min abinci." Taji shi ya sake cewa. Sabon salo, ko tunda ya dawo wa yake zuba mishi oho. Bata ida tunaninta ba taji ya sake cewa . "Ko baki shirya fara dutynki daga yanzu bane ? " Ba tare da tayi magana ba ta dawo ta zuba mishi abincin tana jinta duk ta takura. "Zauna muci." Ya kuma cewa yana kallon yadda tabi ta takura kanta. "Na koshi." Tace da sauri. "To zo ki zauna idan na gama sai ki shiga da kwanukan." Ya fada yana nuna mata kusa dashi. Babu yadda ta iya haka ta dawo ta zauna har yaci ya gama ya wanke hanunshi, kafin ta yunkura taga ya fara hada kan kwanukan da kanshi ya tura gefe ya ajiye . "Kinyi sallah." Kai kawai ta gyada mishi tana jiran taji kuma ta ina zai sake bullo mata. "Kina jin bacci ? " Ya kuma tambayarta. Da sauri ta gyada mishi kanta dan ya barta ta tafi. "Ayya, nayi tsammanin bakyajine ki tayani hira, tunda kinaji kuma ga wurin kwanciya hau ki kwanta." "Dan mannin hauka." Tace a ranta. Rau rau tayi kamar zatayi kuka tace "Dan Allah uncle smart kayi hakuri, zan shiga gida in kwanta wlh na fasa zuwa bikin." "Na sani ai, dama zuwa biki kam dole ki fasa, cikin gida kuma jama'a sunyi yawa zasu takuramin ke, ni kuma bana son hakan, kwanta abinki anan kinji." "Mahmudu zanje in gani." ta fada cikin saurin baki. Kallon gefen ido ya mata kafin yace "Irin kamar kin damu dashi dinnan, inace tun jiya kika tafi kika barshi ko waiwayoshi bakiyi ba, yau dinma ba don na aika a kiraki ba watakila sai jibi zaki dawo." "A'a gobe da safe ne." Ta fadi hakan dason kare kanta. "You see." Yace yana wara hannayenshi, kafin ya ci gaba da cewa "Ki bari gobe da safen kya ganshi dan yanzu kam na tabbata yayi bacci." "Hamma shehu." Ta fada da sauri ganin ya je yana kokarin kulle kofar dakin. "Tun shekaran jiya ya tattara ya barmin dakin ko kinga alamar kayanshi anan." Shiru tayi tana zare idanu tare da tunani ta yanda zata b'ullo mishi ya barta ta tafi. "Hiran zamuyi kenan, ya fada yana kwanciya kan kafarta bayan ya maidata ta zauna, murmushi dauke a fiskarshi. Tsabar rudewa da tunanin irin kallon da za a mata idan ta kwana a dakin yasata cewa "Nikam uncle smart bakasan Kunya bane ? " ""Ba na kashe wnn suna ba." "Toh, daddyn Mahmud dan Allah ka barni na shiga gida, wlh za a ce bani da kunya." Yadda tayi maganar ya bashi dariya, dan har wani marairaicewa takeyi. "Allah mummy saidai ace baki da kunya, amma yau anan zaki kwana." Kuka ta rushe dashi harda shessheka, shiko ya dage sai kallon yanda take rusa kuka yakeyi, a ranshi kuma yanajin bazai fasa abinda yayi niyya ba. "Baiwar Allah, kuka kikeyi ? " Ya tamabaya yana leka fiskarta. Shure shure ta farayi da kafafunta tana ture kanshi fdaga jikinta tana kuma ci gaba da kukanta. "Dakata to kiji." Ya fada yana mata dariya. Shiru tayi tana share hawayenta ganin ya tashi zaune, duk a tunaninta bude mata kofar zaiyi. "Mummy da kin daina wahalar da kanki, ki bar zubar min da hawayennan, dan laifi kikayi min kuma ya zama dole in hukunta ki. Tashi tayi tsam taje ta tsaya a bakin kofar, ko zai tausaya mata ya bude. Amma abin haushi sai gani tayi ya haye gado ya kwanta yana kare mata kallo. Gajiya tayi da tsayuwar ta koma gun kujerar ta durkusa tare da kifa kanta a kai. A hakan barci ya sureta. Saida ya tabbatar da tayi baccin ya lallab'a hankali yaje ya zare gyalen jikinta snn ya daga ta ya maidata kan gadon. Shiri kwanciya yayi yazo ya tofe ta da addu'o'i kafin ya kwanta kusa da ita ya lullub'a musu bargo. *Asubah ta gari Khadijan uncle smart* *F.O.W * * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* * Impacting valuable knowledge and Entertainment is our concern. * *20* *Sakon gaisuwa gareku masoya, A duk inda kuke.* *Mom Faisal* *Mom Eiman* *Amina Jaji* *Azeezat mijinyawa* *Nablah* Da sauran wad'anda ban ambata b *Fasaha grp 3* Allah ya bar qauna, ina alfahari daku. ~Kiraye kirayen sallah da ake ta kwad'awa a masallatai suka shiga dodon kunnenta, hakan yayi sanadiyyar farkawarta daga bacci bakinta dauke da addu'a. Dube dube ta farayi lokacin da ta tashi ta zauna. Lokaci guda haske ya gauraye dakin hakan ya bata damar ganinshi zaune kan sallaya, rike da casbaha. Tsura mishi ido tayi, ita dai har yanzu bata daina mamakin rikon ibadanshi ba, kamar wanda ya taso a gidan masu cikakken tarbiya. Murmushi ya sakar mata yace "Kawar amarya kin tashi ? Ya gajiyar biki.? " Kamar an tsikareta ta mike ta fara neman gyalenta ta yafa snn ta nufi kofar dakin, luckily ta jita a bude. Ba tare da ta waiwayo ba ta bude ta fita da sauri kamar ana hankada ta. Cikin gida ta nufa tana sand'a kamar wata munafuka. Jin motsi yasata zaran buta tayi cikin bayan gida. Tana fitowa tayi alwala ta shige dakin Matar babanta, gaba daya a tsarge take, gani take kamar kowa yasan inda ta kwana. Tana makale cikin dakin ta ki fitowa, sai noke noke takeyi. Saida taji ana tambayar Habiba snn tayi wuff ta fito duk a tunaninta Habiba zata fada musu ne. Saida ta bi iyaye da yayyu da gaisuwa snn suka koma ciki tare da Habiba. "Adda Deejah, jiya nayi ta jiranki baki dawo ba har nayi bacci." Ba tare da ta kalleta ba tace "Nayi tsammanin kinyi bacci da wuri ne shi yasa da na shigo na wuce dakin Dadayi na kwanta, tunda nasan dakinmu a cike yake." "Uhmmm." Kawai Habiba tace ta tsuke bakinta tayi shiru. Tsabar tsarguwa sai ta gagara hakura saida ta tambayeta. "Meye ? " "Ba komai." Ta bata amsa tana murmushi. Gidan bikin da bata koma ba kenan, hasalima ko gidan Hajja tsoron zuwa take, kada ya kuma cewa tayi wani laifin, kuma tasan ita ba iya zuwa wani tambayarshi zatayi ba. An kare biki lafiya, mutane sun fara watsewa dan su ba yanzu zasu tare ba, sai nan da wata guda, sbd a bawa iyayen Habiba damar shiryawa. Itama Habiban shirin tafiya tayi zasu tafi tare sa mamanta, har yanzu dai itakam basu samu kebewa da angonnata ba, dan dukansu jin avin sukeyi wani iri. Deejah ji takeyi kamar ta bisu amma ba damar hakan. Tambayar da goggonta ta mata game da kayakin da ta bari a can, tana cewa ko ta turo mata su, shi ya bata damar amsawa cikin zumudi cewa Zata zo ta dauka da kanta, dan tana tunanin idan ta fadi kayanta zata dauka babu mai hanata. Ji take kamar ta hana Habiba tafiya, dan tasan kewar Fa'i dole ya dameta, da su biyu ne cikin daki, idan Habiba tazo su zama uku, yanzu kuwa duk zasu watse su barta. Kamar zatayi kuka lokacin da su Habiba sukazo tafiya, har kofar gida ta rakasu duk jikinta a sanyaye. Allah ya kiyaye hanya sauran mutanen gidan suke ta musu. Yayin da Deejah da Habiba suka kebe suna kuskus dinsu ba tare da ana jin abinda suke cewa ba. "Habiba wuce mu tafi dan kunce hirarku baya karewa in kun hadu." "Saura kadan dai goggo." cewar Deejah. "A, to da alama Habiba dai so take a biyo ta da kayanta kawai." A zabure Habiba ta juya tana Adda deejah sai kinzo. Duka mutanen gurin dariya suke mata harda su uncle Smart da Hamma shehu, Ali, yusufa da sauran wadanda suka fito dan yin sallama da goggonsu. Kanta a kasa ta wuce ta fara tafiya, goggonta ta mara mata baya zuwa gurin machine din da ke jiransu. Suna hada ido tayi saurin shigewa gida har tana hadawa da gudu. Dariya yayi a zcyrshi yana girgiza kai, ya lura wnn kunya a jininsu yake. Tunda gashi Mamanshi ma har yanzu ta ki yarda ta saki jiki dashi. Koda sau nawa zai shiga wajenta saidai tayi ta kallonshi a sace, bata yarda ta saki jiki suyi hira wai ita kunyar dan fari, kamar yadda Hamma shehu ya fada mishi. Tun daga lokacin suka shiga wasan buya dashi, in taji muryarshi a cikin gida makalewa takeyi a cikin daki har sai ta tabbatar ya tafi. Hakama koda tana tsakar gida ne taji alamun zai shigo shigewarta daki takeyi har sai ya gama abunda yakeyi ya fita. Mahmud kam har yanzu yana wajen kakarshi, sam bai damu da uwar ba, sai kara shagwab'ashi adda takeyi duk da a yanzu takan rage nuna mishi kulawa a cikin mutane, sbd shi d'an d'an farinta ne, amma in su biyu ne shi yasan irin gatan da yakesha. Cikin kwanakin aka tayar da gini kusa da na shehu duk cikin anguwar ne, room and palour, toilet sai kitchen, dsb'anin na Hamma shehu, da akayi two bedroom, ko wane daki da toilet a ciki, snn ga na waje sbd bak'i, kitchen da store . Kamar yadda ta saba, tunda Fa'i ta yi aure ta karb'i shara da gyaran d'akin adda. Haka yauma ta shiga bayan sun gaisa, ta fara tattara d'akin kamar yadda ta saba. Tana cikn sharan ta tsinkayo sallamarshi, lokacin kuma adda ta shiga tana fitar da kayan mahmud masu datti tana fitarwa. Kofar d'akin ya tsaya ya doka sallama, dukansu biyu suka amsa ciki ciki. Bai damu da hakan ba ya kutsa kanshi ya shigo ciki. Gaisheda Adda ya farayi kafin itama ta gaisheshi kanta a sunkuye. Kallonta yakeyi a ranshi yana kitsa irin tsiyar da zai tsula mata, yaga karshen kunyarsu daga ita har adda. Gyara zamanshi yayi ya fara jan adda da hira,duk da yasan dukansu biyu jira suke ya fita su ci gaba da abinda sukeyi. Ganin bata amsashi ba, yace, "Adda kayan mahmud kike fitarwa ne." Shiru tayi kamar bata jishi ba. "Adda surkuwarki shara take miki ne ? " Cikin kosawa da surutanshi tace "Nikam deejah 'yata ce ba surukuwata ba." "Kawo in tayaki sharan nima in samu ladan." Ya fada lokacin da yasa hanunshi ya riko tsintsiyar har da hadawa da hanunta. Durkushewa tayi a gurin ta dukar da kanta yayin da adda kuma ta fita da sauri har tana tuntub'e da bakin kofar. "Ka gani ko ? " Deejah ta fada tana harararshi. "Me na gani to, ni banga komai ba." Ya fada yana wani irin murmushi na rainin hankali. "Dan Allah ka fita aiki nakeyi." Hade ranshi yayi yace "Bazan fita ba, badai ni kike gudu ba, yau kwana nawa rabon da in sa ki a idona ? " "Kayi hakuri nidai kafita." "To sakarmin tsintsiyar inyi sharan ko mu share tare." Da sauri ta sakar mishi tsintsiyar ta mike zata fita, ya tareta "Zo kiyi sharanki, amma dole zaki karb'i hukunci dadai da abunda kika aikata, babu yafiya kuma." Yana gama fad'in haka ya bata peck a kumatunta ya fita ya barta da salati. Ita kadai ta fara magana. "A d'akin addan ? Lallai na tabbata baka da kunya , kuma idan banyi hankali ba, wata rana sai ka bani kunya a idon mutane, Tabd'i." Ta karashe tana rike hab'a da zare idanu. A haka ta gama gyara d'akin tana tana jinjina abinda ya mata a ranta. Adda kuwa bata kuma shigowa ba saida taga Deejah ta fita snn ta shiga d'akin. Tun daga ranar take taka tsantsan sai ta tabbatar ya shigo ya gaida mutanen gidan ya tafi kafin itama ta fito ta kama aiyukanta. Gyara kuwa tana shansu daga wajen matar babanta, Hajja ma ba a barta a baya ba. Madaran shanu shi take fara karyawa dashi ko wace safiya, wani lokacin har dare bata akeyi tasha tare da zuma mai kyau. Tea da kayan yaji yaji kanumfari yawanci kuma da zuma ake hadawa, wnn dama sun saba shan tea ko da rana ne sbd yanayin sanyi da suke dashi, basu cika shan ruwan sanyi ba. Snn ko zagawa zasuyi da ruwan zafi suke amfani, shi yasa basa rabo da wuta a murhu, da ruwa a flask. Ita kuma Hajja kullum dare sai ta bata fura da nono tasha sbd ta murmure, kasusuwan da suka fito su rufu. Duk lokacin da deejah tayi mata mitar ta gaji ko tace mata koshi, sai tace "So kike akaiki gidan miji jiki duk kasusuwa ? " ~Fitowarta kenan daga gida zata shiga gidan Hajja inna, tana ta zuba sauri gudun kada ya ganta, duk da tana kyautata zaton sun fita da Hamma shehu dan yanzu tare suke zuwa shagon Hamma shehu, dan tuni ya sayar da motarshi ya bawa shehu kudin yana saro musu kaya suna sayarwa. "Yan mata." Ta jiyo muyarshi ya daki dodon kunnenta saida ta razana. Tare suke da Hamma shehu ga dukkan alamu fita zasuyi. Gaishesu tayi a dakile duk da cewa shi Hamma shehu sun gaisa dashi da safe. Zata wuce yace "Mummy dan Allah kawo min Mahmud na ganshi kafin mu fita yau na shiga ban ganshi ba, kuma na tambayi ada bata amsa min ba." "Ni ? " Ta tambaya tana nuna kanta tana zare ido. "To da waye in ba ke ba." Ya fad'a da mamakin razanar da ya bayyana a fiskarta. "Ya manga ka barta bazata iya ba." Cewar Hamma shehu. "Kamar yaya bazata iya ba kuma ? " Ya tambaya yana maida kallonshi ga Hamma shehu. "Kunya takeji, kasan ko a gidan ba wani kulashi takeyi ba, bazata iya zuwa ta dauko shi ta kawo maka ba." "What ? Kada kace min ita ma irin abinda adda takemin take mishi.? Yana dariya ya amsa mishi da "Ai hakan al'adace, in har batayi bama ta nuna mishi kulawa a idon mutane zagi zatasha, ace bata da kunya." "Ai kuwa akwai cutarwa a ciki wlh, ni dai bazan yarda da hakanba, idan ni anyi min bazan bari ayiwa yarona ba." Yana fada ya maida kallonshi inda take yaga wayam ta gudu. Maganar Hamma shehu yasa ya sake maida hankalinshi gareshi inda ya ke cewa "Kuma ku d'in aka fi so ba, saidai baza a iya bayyanawa bane." "Ban yarda da wnn so ba, wani irin so ne zaka so mutum bazaka nuna mishi ba." Haka ya ci gaba da mitarshi suna tafiya yana ta zuba mita shidai wnn al'ada bai mishi ba. Aiko washegari tun karfe takwas da rabi aka ankara mahmud baya gida. Gidajen makwabta aka fara bi ana nemanshi, amma har aka karad'e gidajen babu shi babu alamun shi. Wasa wasa fa, aka fara cewa Mahmud ya b'ata, Dadayi, Adda, da Addayi, Hajja inna duka zama ya gagaresu, ko wacce ta zari lullub'i ta kama hanya, babu mai sauraren wata a cikinsu, sauran yaran ma duk an baza su neman Mahmud. Amaryar Baffansu babba, da Deejah kawai aka bari, wacce tayi karfin halin d'aura girki Aiki takeyi amma sam hankalinta baya jikinta, sai maimaita La haula wa laa kuwwata take tayi, dan Malamin islamiyyarsu ya tab'a ce musu, idan aka nemi mutum aka rasa, ko da ya fad'a mummunan hanu ne idan ana yawaita karanta mishi laa haula wala kuwwata, Allah zai kawo mishi agaji da mafita , saidai in dama mai kararren kwana ne. Har ta gama girki, babu labarin Mahmud. Wanka ta shiga duk dan ta nuna abin bai dameta ba amma, tanayi tana kuka. Haka ta fito ta d'auro alwala kasancewar azahar ta gabato. Har tayi sallah ta idar snn taji sun shigo. Kasa kunne tayi ko zataji cewar an ganoshi, amma sai taji suna cewa zasuyi sallah su ci gaba da nemanshi. Tirkashi, wnn shi ake kira *tashin hankali* Mahmud ya b'ata yaya zatayi da ranta. D'aga hanu tayi zata yi addu'a amma ta rasa abinda zata ce, sai kawai ta rushe da kuka........ * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* * Impacting valuable knowledge and Entertainment is our concern. * *20*&21 *Sakon gaisuwa gareku masoya, A duk inda kuke.* *Mom Faisal* *Mom Eiman* *Amina Jaji* *Azeezat mijinyawa* *Nablah* Da sauran wad'anda ban ambata b *Fasaha grp 3* *Zama Na Amana 2* Allah ya bar qauna, ina alfahari daku. ~Kiraye kirayen sallah da ake ta kwad'awa a masallatai suka shiga dodon kunnenta, hakan yayi sanadiyyar farkawarta daga bacci bakinta dauke da addu'a. Dube dube ta farayi lokacin da ta tashi ta zauna. Lokaci guda haske ya gauraye dakin hakan ya bata damar ganinshi zaune kan sallaya, rike da casbaha. Tsura mishi ido tayi, ita dai har yanzu bata daina mamakin rikon ibadanshi ba, kamar wanda ya taso a gidan masu cikakken tarbiya. Murmushi ya sakar mata yace "Kawar amarya kin tashi ? Ya gajiyar biki.? " Kamar an tsikareta ta mike ta fara neman gyalenta ta yafa snn ta nufi kofar dakin, luckily ta jita a bude. Ba tare da ta waiwayo ba ta bude ta fita da sauri kamar ana hankada ta. Cikin gida ta nufa tana sand'a kamar wata munafuka. Jin motsi yasata zaran buta tayi cikin bayan gida. Tana fitowa tayi alwala ta shige dakin Matar babanta, gaba daya a tsarge take, gani take kamar kowa yasan inda ta kwana. Tana makale cikin dakin ta ki fitowa, sai noke noke takeyi. Saida taji ana tambayar Habiba snn tayi wuff ta fito duk a tunaninta Habiba zata fada musu ne. Saida ta bi iyaye da yayyu da gaisuwa snn suka koma ciki tare da Habiba. "Adda Deejah, jiya nayi ta jiranki baki dawo ba har nayi bacci." Ba tare da ta kalleta ba tace "Nayi tsammanin kinyi bacci da wuri ne shi yasa da na shigo na wuce dakin Dadayi na kwanta, tunda nasan dakinmu a cike yake." "Uhmmm." Kawai Habiba tace ta tsuke bakinta tayi shiru. Tsabar tsarguwa sai ta gagara hakura saida ta tambayeta. "Meye ? " "Ba komai." Ta bata amsa tana murmushi. Gidan bikin da bata koma ba kenan, hasalima ko gidan Hajja tsoron zuwa take, kada ya kuma cewa tayi wani laifin, kuma tasan ita ba iya zuwa wani tambayarshi zatayi ba. An kare biki lafiya, mutane sun fara watsewa dan su ba yanzu zasu tare ba, sai nan da wata guda, sbd a bawa iyayen Habiba damar shiryawa. Itama Habiban shirin tafiya tayi zasu tafi tare sa mamanta, har yanzu dai itakam basu samu kebewa da angonnata ba, dan dukansu jin avin sukeyi wani iri. Deejah ji takeyi kamar ta bisu amma ba damar hakan. Tambayar da goggonta ta mata game da kayakin da ta bari a can, tana cewa ko ta turo mata su, shi ya bata damar amsawa cikin zumudi cewa Zata zo ta dauka da kanta, dan tana tunanin idan ta fadi kayanta zata dauka babu mai hanata. Ji take kamar ta hana Habiba tafiya, dan tasan kewar Fa'i dole ya dameta, da su biyu ne cikin daki, idan Habiba tazo su zama uku, yanzu kuwa duk zasu watse su barta. Kamar zatayi kuka lokacin da su Habiba sukazo tafiya, har kofar gida ta rakasu duk jikinta a sanyaye. Allah ya kiyaye hanya sauran mutanen gidan suke ta musu. Yayin da Deejah da Habiba suka kebe suna kuskus dinsu ba tare da ana jin abinda suke cewa ba. "Habiba wuce mu tafi dan kunce hirarku baya karewa in kun hadu." "Saura kadan dai goggo." cewar Deejah. "A, to da alama Habiba dai so take a biyo ta da kayanta kawai." A zabure Habiba ta juya tana Adda deejah sai kinzo. Duka mutanen gurin dariya suke mata harda su uncle Smart da Hamma shehu, Ali, yusufa da sauran wadanda suka fito dan yin sallama da goggonsu. Kanta a kasa ta wuce ta fara tafiya, goggonta ta mara mata baya zuwa gurin machine din da ke jiransu. Suna hada ido tayi saurin shigewa gida har tana hadawa da gudu. Dariya yayi a zcyrshi yana girgiza kai, ya lura wnn kunya a jininsu yake. Tunda gashi Mamanshi ma har yanzu ta ki yarda ta saki jiki dashi. Koda sau nawa zai shiga wajenta saidai tayi ta kallonshi a sace, bata yarda ta saki jiki suyi hira wai ita kunyar dan fari, kamar yadda Hamma shehu ya fada mishi. Tun daga lokacin suka shiga wasan buya dashi, in taji muryarshi a cikin gida makalewa takeyi a cikin daki har sai ta tabbatar ya tafi. Hakama koda tana tsakar gida ne taji alamun zai shigo shigewarta daki takeyi har sai ya gama abunda yakeyi ya fita. Mahmud kam har yanzu yana wajen kakarshi, sam bai damu da uwar ba, sai kara shagwab'ashi adda takeyi duk da a yanzu takan rage nuna mishi kulawa a cikin mutane, sbd shi d'an d'an farinta ne, amma in su biyu ne shi yasan irin gatan da yakesha. Cikin kwanakin aka tayar da gini kusa da na shehu duk cikin anguwar ne, room and palour, toilet sai kitchen, dsb'anin na Hamma shehu, da akayi two bedroom, ko wane daki da toilet a ciki, snn ga na waje sbd bak'i, kitchen da store . Kamar yadda ta saba, tunda Fa'i ta yi aure ta karb'i shara da gyaran d'akin adda. Haka yauma ta shiga bayan sun gaisa, ta fara tattara d'akin kamar yadda ta saba. Tana cikn sharan ta tsinkayo sallamarshi, lokacin kuma adda ta shiga tana fitar da kayan mahmud masu datti tana fitarwa. Kofar d'akin ya tsaya ya doka sallama, dukansu biyu suka amsa ciki ciki. Bai damu da hakan ba ya kutsa kanshi ya shigo ciki. Gaisheda Adda ya farayi kafin itama ta gaisheshi kanta a sunkuye. Kallonta yakeyi a ranshi yana kitsa irin tsiyar da zai tsula mata, yaga karshen kunyarsu daga ita har adda. Gyara zamanshi yayi ya fara jan adda da hira,duk da yasan dukansu biyu jira suke ya fita su ci gaba da abinda sukeyi. Ganin bata amsashi ba, yace, "Adda kayan mahmud kike fitarwa ne." Shiru tayi kamar bata jishi ba. "Adda surkuwarki shara take miki ne ? " Cikin kosawa da surutanshi tace "Nikam deejah 'yata ce ba surukuwata ba." "Kawo in tayaki sharan nima in samu ladan." Ya fada lokacin da yasa hanunshi ya riko tsintsiyar har da hadawa da hanunta. Durkushewa tayi a gurin ta dukar da kanta yayin da adda kuma ta fita da sauri har tana tuntub'e da bakin kofar. "Ka gani ko ? " Deejah ta fada tana harararshi. "Me na gani to, ni banga komai ba." Ya fada yana wani irin murmushi na rainin hankali. "Dan Allah ka fita aiki nakeyi." Hade ranshi yayi yace "Bazan fita ba, badai ni kike gudu ba, yau kwana nawa rabon da in sa ki a idona ? " "Kayi hakuri nidai kafita." "To sakarmin tsintsiyar inyi sharan ko mu share tare." Da sauri ta sakar mishi tsintsiyar ta mike zata fita, ya tareta "Zo kiyi sharanki, amma dole zaki karb'i hukunci dadai da abunda kika aikata, babu yafiya kuma." Yana gama fad'in haka ya bata peck a kumatunta ya fita ya barta da salati. Ita kadai ta fara magana. "A d'akin addan ? Lallai na tabbata baka da kunya , kuma idan banyi hankali ba, wata rana sai ka bani kunya a idon mutane, Tabd'i." Ta karashe tana rike hab'a da zare idanu. A haka ta gama gyara d'akin tana tana jinjina abinda ya mata a ranta. Adda kuwa bata kuma shigowa ba saida taga Deejah ta fita snn ta shiga d'akin. Tun daga ranar take taka tsantsan sai ta tabbatar ya shigo ya gaida mutanen gidan ya tafi kafin itama ta fito ta kama aiyukanta. Gyara kuwa tana shansu daga wajen matar babanta, Hajja ma ba a barta a baya ba. Madaran shanu shi take fara karyawa dashi ko wace safiya, wani lokacin har dare bata akeyi tasha tare da zuma mai kyau. Tea da kayan yaji yaji kanumfari yawanci kuma da zuma ake hadawa, wnn dama sun saba shan tea ko da rana ne sbd yanayin sanyi da suke dashi, basu cika shan ruwan sanyi ba. Snn ko zagawa zasuyi da ruwan zafi suke amfani, shi yasa basa rabo da wuta a murhu, da ruwa a flask. Ita kuma Hajja kullum dare sai ta bata fura da nono tasha sbd ta murmure, kasusuwan da suka fito su rufu. Duk lokacin da deejah tayi mata mitar ta gaji ko tace mata koshi, sai tace "So kike akaiki gidan miji jiki duk kasusuwa ? " ~Fitowarta kenan daga gida zata shiga gidan Hajja inna, tana ta zuba sauri gudun kada ya ganta, duk da tana kyautata zaton sun fita da Hamma shehu dan yanzu tare suke zuwa shagon Hamma shehu, dan tuni ya sayar da motarshi ya bawa shehu kudin yana saro musu kaya suna sayarwa. "Yan mata." Ta jiyo muyarshi ya daki dodon kunnenta saida ta razana. Tare suke da Hamma shehu ga dukkan alamu fita zasuyi. Gaishesu tayi a dakile duk da cewa shi Hamma shehu sun gaisa dashi da safe. Zata wuce yace "Mummy dan Allah kawo min Mahmud na ganshi kafin mu fita yau na shiga ban ganshi ba, kuma na tambayi ada bata amsa min ba." "Ni ? " Ta tambaya tana nuna kanta tana zare ido. "To da waye in ba ke ba." Ya fad'a da mamakin razanar da ya bayyana a fiskarta. "Ya manga ka barta bazata iya ba." Cewar Hamma shehu. "Kamar yaya bazata iya ba kuma ? " Ya tambaya yana maida kallonshi ga Hamma shehu. "Kunya takeji, kasan ko a gidan ba wani kulashi takeyi ba, bazata iya zuwa ta dauko shi ta kawo maka ba." "What ? Kada kace min ita ma irin abinda adda takemin take mishi.? Yana dariya ya amsa mishi da "Ai hakan al'adace, in har batayi bama ta nuna mishi kulawa a idon mutane zagi zatasha, ace bata da kunya." "Ai kuwa akwai cutarwa a ciki wlh, ni dai bazan yarda da hakanba, idan ni anyi min bazan bari ayiwa yarona ba." Yana fada ya maida kallonshi inda take yaga wayam ta gudu. Maganar Hamma shehu yasa ya sake maida hankalinshi gareshi inda ya ke cewa "Kuma ku d'in aka fi so ba, saidai baza a iya bayyanawa bane." "Ban yarda da wnn so ba, wani irin so ne zaka so mutum bazaka nuna mishi ba." Haka ya ci gaba da mitarshi suna tafiya yana ta zuba mita shidai wnn al'ada bai mishi ba. Aiko washegari tun karfe takwas da rabi aka ankara mahmud baya gida. Gidajen makwabta aka fara bi ana nemanshi, amma har aka karad'e gidajen babu shi babu alamun shi. Wasa wasa fa, aka fara cewa Mahmud ya b'ata, Dadayi, Adda, da Addayi, Hajja inna duka zama ya gagaresu, ko wacce ta zari lullub'i ta kama hanya, babu mai sauraren wata a cikinsu, sauran yaran ma duk an baza su neman Mahmud. Amaryar Baffansu babba, da Deejah kawai aka bari, wacce tayi karfin halin d'aura girki Aiki takeyi amma sam hankalinta baya jikinta, sai maimaita La haula wa laa kuwwata take tayi, dan Malamin islamiyyarsu ya tab'a ce musu, idan aka nemi mutum aka rasa, ko da ya fad'a mummunan hanu ne idan ana yawaita karanta mishi laa haula wala kuwwata, Allah zai kawo mishi agaji da mafita , saidai in dama mai kararren kwana ne. Har ta gama girki, babu labarin Mahmud. Wanka ta shiga duk dan ta nuna abin bai dameta ba amma, tanayi tana kuka. Haka ta fito ta d'auro alwala kasancewar azahar ta gabato. Har tayi sallah ta idar snn taji sun shigo. Kasa kunne tayi ko zataji cewar an ganoshi, amma sai taji suna cewa zasuyi sallah su ci gaba da nemanshi. Tirkashi, wnn shi ake kira *tashin hankali* Mahmud ya b'ata yaya zatayi da ranta. D'aga hanu tayi zata yi addu'a amma ta rasa abinda zata ce, sai kawai ta rushe da kuka......... *F.O.W * * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* *21* *Kuyi hakuri da jina shiru kwana biyu, hakan ya faru ne sakamakon rashin lafiyar da mukayi ni da Nuraini na, amma yanzu alhamdulillah, mun samu sauki sai rashin apetite, bakin nawa sam ba dad'i bana gane taste na abinci, hakan yasa doctor na ya ce, fans su kokarta su sama min Kazaquin, fresh kifiquin, Ovaltine, milk, crate na kwai biyu, in kunga da akwai abinda ya dace a kara ba laifi* *Gital's nvl grp members* *Aminci nvl grp Members* *Fasaha Nvl grp members 1,2,3,4* *Khairat up nvl grp members* *Jeederh nvls grp members* *Zezeen Fasaha.* *Hausa nvls grp* *Hausa Novel* *Hausa Novel 2* *Zauren serdeeyer nvls* Da sauran grps din da ban ambata ba, ina alfahari daku, ina kuma jin dadin comments dinku. *Khadijan Uncle Smart tana gaidaku.* ~Kuka takeyi bilhakk'i, wani irin tsoro yana shigarta, babu abinda zuciyarta ke raya mata illa, mutanen su babanshi da ba a kama bane suka biyo suka d'aukeshi. Wani irin bugawa zuciyarta keyi, take ta kara tausayawa adda, sbd tunani halin da ta shiga lokacin da aka d'auke mata nata d'an. cikin wnn hali taji miryarsu sun shigo. D'an saurarawa tayi ko zataji an ganeshi, amma sai taji suna cewa zasuyi sallah su koma su ci gaba da nemanshi. "Innaa lillahi wa innaa ilaihirraji'un." tace cikin kukan da take hana fitan saitinshi sbd kada a jiyota. Hajja inna ce ta zo zata shiga dan taga halinda da take ciki, ta jiyo shesshekarta. Tausayin deejah ne ya lullub'eta, take taji itama kukan yazo mata. Kokarin daidaita kanta takeyi kafin ta shiga dan ta samu ta lallasheta ta jiyo muryar Mahmud yana cewa "Adda na dawo." Cikin irin maganarshi da bai k'ware ba. Da sauri ta juya ta inda ta jiyo muryarshi, lokacin kuma adda dasu dadayi suke rigerigen fitowa dan su tabbatarwa kansu abunda kunnuwansu suka jiyo. Turus suka tsaya suna kallon Mahmud da babanshi ke rungume dashi, hannunshi daya rike da babban roban bobo. Dayan kuma rike da biscuit. Sauke yaron yayi yana binsu da kallo, da alamar mamaki a fiskarshi. Yana sauke idonshi kan adda ta banka mishi harara ta juya ta shige ciki. Dan murmushi yayi yana shafa kanshi. "Ina ka samoshi Mahmudu ? " Cewar Hajja inna. "Tare muka fita ai adda ta sani." Ya bada amsa yana maida kallonshi kanta. "Ubanka mahmudu, nace, Ubanka. Da ta sani yaushe zata wahalar da kanta ta bar mu mu wahala muna nemanshi." Waro idanunshi yayi kadan yace "Dama nemanshi kukeyi ? " "Ban sani ba d'an nema, Ja'irin yaro." Kusa da ita ya matso yana maida fuskarshi kalar tausayi . "Yi haquri Hajja tsohuwa, ban d'aukeshi dan in baku wahala ba, hasalima adda tana zaune nazo na d'aukeshi, da yake ba kallona takeyi ba, watakila shi yasa bata san na d'aukeshin ba. Tab'are fiskarshi yayi kamar mai shirin yin kuka . "To wai Hajja me yasa take yimin haka ne, idan na shigo bata kallona, idan na gaisheta sai ta amsa ciki ciki kamar bata so, ko wani laifin na mata ban sani ba, ko dai dan ban taso a gurinta ba bata saba dani ba shi yasa take yimin haka." Ya karashe maganarshi a raunane. Ba hajja inna kad'ai ba, sauran matan gidan duka sai da jikinsu yayi sanyi balle kuma adda da yake maganar a kanta. "Yi hakuri Mahmudu, babu laifin da kayi mata, kuma ba don rashin sabo ya satake maka haka ba, al'adarmuce hakan. Idan ta nuna zakewarta a kanka sai a zageta a ce bata da kunya. Dan baka halin da rashinka ya jefata bane, da baka fad'i maganar nan ba." "To, amma hajja al'adar nan tayi tsauri da yawa, akwai cutarwa a ciki, shikenan mutum dan yana d'an fari bazai sake da mahaifiyarshi yayi hira da ita ba, bazai yi shawara da ita ba. Gaskiya tunda ba addinin bane ya kamata a sassauta, irin haka yanasa mutum yaji kamar bashi da gata." Ya fad'a yana langab'e kanshi. "To naji, je ka bata haquri dan ka d'auki alhakinsu da yawa, da ita da Deejatu." D'akin adda ya nufa yayi sallama, ta amsa ciki ciki, ya kutsa kai ya shiga. Zaune take kan Three sittern kwaya d'aya dake cikin d'akin. Mahmud na zaune a gefenta yana cin biscuit d'inshi yana zuba mata surutan shirme. Tun bai isa kusa da ita ba ya durkusa, ya karasa da ja da gwiwa. Daf da ita ta karaso ya d'aura kanshi kan cinyarta. "Adda, ki yafe min, bansan abin zaizo a haka ba da ban d'aukeshi ba, yi hakuri addana." Wani iri taji a ranta, son d'anta na dad'a shiga zuciyarta, hakika kaddara idan yazo maka babu yadda ka iya, ita dai a kullum godewa Allah takeyi da ya azurtata da yara masu biyayya da kaifin hankali, sam basa son b'acin ranta, ga wnn da take ganinshi kamar zai zamo wani irin kangararre tunda a gidan rashin tarbiya ya taso, amma sai ya kasance abin ba haka bane. Godewa Allah takeyi aduk lokacin da tuna irin baiwar da Allah ya mata. Hakika Allah yana jarabtar bayinsa ta hanyoyi daban amma idan mutum yayi hakuri ya kasance mai tawakkali sai hakurinshi ya mishi rana, yarda da kaddarar sai ta zamo mai amfani a gareshi, Allah sai ya musanya mishi da abinda yafi alkhairi. Katse mata tunaninta yayi da cewa "Adda, kiyi hakuri bazan sake ba kinji." A hankali ta d'aga hanunta ta dora a kanshi tace a sanyaye "Ya wuce, Allah yayi maka albarka." Washe baki yayi cikn matsanancin farin ciki Yace "Na gode adda, na godewa Allah da ya sa na dawo gareku dukanku kuna raye, na godewa Allah da ya nuna min ranar da kika samin albarka, Allah ya bar min ku adda." Ya k'arasa yana had'a hannayensu. "Amma kasan ka d'auki alhakin deejah ko ? " "Zan bata hakuri ai adda." "To tashi min a jiki nikam." Yana dariya ya tashi. Shiko mahmud kamar jira yake babanshi ya tashi ya mimmike ya kwanta kan cinyar addan. "Kai tashi ka barta ta huta." Ya fada yana kokarin sa hanu ya d'aga Mahmud. Tare hanunshi adda tayi tana cewa "Kyaleshi, babu ruwanka, kaima babba dakai ka kwanta balleshi." Rausayar da kanshi yayi yana 'yar murmushi, "Nima na manta ne adda, ashe ba'a shiga tsakanin mata da miji." Bata kuma kallonshi ba, sai maida hankalinta tayi kan mahmud dake lumshe ido alamun bacci yakeji. Fita yayi yana jin farin ciki a ranshi, ko ba komai yau dai yayi magana mai d'an tsawo da addanshi, sab'anin da da saidai yayi ta surutunshi ko kallonshi batayi balle ta amsa mishi. Cikin gidan yabi da kallo, ganin babu kowa yayi saurin karasawa kofar d'akin Deejah. Zaune take kan sallaya har yanzu, kanta ta dora kan gadon dake kusa da ita, yanzu ba kukan takeyi ba, amma jikinta har yanzu a sanyaye, duk da taji dawowar Mahmud din. Sallamarshi taji a bakin kofarta, ta amsa a zcyrta bata dago kan ta ba kuma. "Mummy in shigo ? " Ya fad'a lokacin da ya d'aga labulen kofar d'akin. Shiru tayi kamar bata jishi ba, saima runtse idon da tayi. Batayi aune ba tajishi dab da ita yana cewa "Bacci kikeyi a zaune ? " "Neman magana." Tace, cikin zcyrta. Cakk taji ya d'agata, hakan yasata saurin bud'e idonta. "Meye haka Uncle ? " Dariya yayi ya sauketa yana cewa "Sorry, na d'auka bacci kikeyi, zan kwantar da kene kada wuyanki yayi ciwo." Juya kanta tayi ta daina kallon direction din da yake, alamu dai ranta a b'ace. Sunkuyowa yayi yana leka fiskarta. "Mummynmu me ya faru kika yi kuka." Kwafa tayi tsabar kara mata haushi da yayi da wnn tambayar rainin hankali da yayi mata. "Wai kema neman Mahmud d'in kika je ne ? Tab, ammafa kin ban kunya, d'an farin kike nema harda kuka ? " Ya karasa yana rike baki. Harara ta wurga mishi ta sake kawar da kanta. Kusa da ita ya zauna ya jawota jikinshi. "Zo ki fad'a min, me kike cewa da kika fita nemanshi. Kuma ba mamaki harda manya kike tambaya ko anga yaronki, ya b'ata baki ganshi, oh, Khadijatu anyi abin kunya." Kuka ta fashe dsshi tsabar haushi, ta shiga kici kicin kwace jikinta. Cikin dariya yace "Sorry, wasa nake miki na masan ba zaki je nemanshi ba, tunda ba sonshi kikeyi ba, baki damu dashi ba. Sakin baki tayi tana kallonshi. Wai ba sonshi takeyi ba, ta haifi dan kuma ace bata sonshi. D'aure fiskarshi yayi kamar gaske ya kuma cewa "Yes, ko karya na miki kin damu dashi ne, naga tunda nazo gidannan ban tab'a ganinshi a hanunki ba, ban tab'a jin kin kira sunanshi ba, kai nunawa ma kike kamar babu wata alaka dake tsakaninku,wai duk gudun ido da bakin mutane ko , shi yasa ma yaron ko damuwa dake bayayi? amma dake ni kin raina ni lokacin da muke Jos da bauchi har wani cemin kike yaronki, kiran sunanshi kuma a bakinki kamar ke kika rad'a mishi." Kunya ne ya lullub'eta tayi qasa da kanta. Ganin haka yasa ya juyo da ita suna fiskantar juna. "Khadija, don Allah, ki ja yaronnan a jiki, ki dinga bashi kulawar da y kamata uwa ta bawa d'anta, ki nuna mishi ke kika haifeshi, hakan zaisa ya tashi da tausayi da imaninki, ko bayan ranki soyayyarki bazai gushe a zcyrshi ba, haka kuma bazai gaji da yi miki addu'a ba. Wnn abu ba addini bane al'ada ne, ya kamata ki yakiceshi ki zubar, halin mutanen da ne, dan Allah mummy." Ya karishe da sassanyar murya. Shiru ya biyo baya kafin ya kuma cewa . "Ya'yanmu abin alfaharine a idonmu, ya zama wajibi mu nuna wannan cikin tafarkin islama. Dan Allah ki daure ki cire wnn kunya mara tushe balle asali. "Kinji ? " Ya kuma fada kasancewar bata ce mishi komai ba. Gyad'a mishi kai kawai tayi tana sunne kai. Cikin zolaya yace, yanzu kuma a hakan kikayi sallah kina kuka ? Sai kuma ya tab'e baki yace "Hmm, Allah yasa ba'ayi ta kiran sunan Mahmudu cikin sallahn ba." Mikewa tayi ta tashi zata fita ya dawo da ita ta hanyar jawota baya. "Yanzu haka zaki fita babu kunya ido a kumbure da an ganki fa ansan kuka kikayi Mahmuduki ya b'ata ko ? Watakila ma ko abinci baki ci ba, kin barmin ciki da yunwa." Ya karishe maganarshi yana shafa cikinta. Da sauri ta buge hannshi ta fita daga d'akin kamar wacce aka kora, ta barshi tsaye yana mata dariya. ~ *Hamma shehu* Tunda su Habiba suka koma sau d'aya kawai yaje, nanma da yaje hirar da goggonshi sukayi, sai da dare dasu Bashar suka dawo. Shi da Habiba kam sun zama kamar wasu surukan juna, sbd ita sosai take kunyarshi, bata tab'a yarda su had'a ido dashi, duk da shid'in ya kasance abokin wasanta, a da sosai suke sakewa suyi wasa, suyi ta zolayar juna amma yanzu daga ita harshi, basu iyawa. Duk lokacin da ya tuna cewar Habiba ya aura ba Deejah ba, yakanji abun kamar almara. Bai tab'a tunanin akwai wata kaddara,da zata hanashi auren Khadijah ba, amma kwatsam sai gashi d'an uwanshine yake auren ta bashi. Har yanzu soyayyar Deejah ce a ranshi, duk da yasan ya riga ya sadaukarwa d'an uwanshi. duk yanda yaso ya yakice ta a zxyrshi hakan ya gagareshi, Sbd da soyayyarta ya rayu, ya fara sonta tun tana 'yar karamarta, ya fara sonta tun kafin shima kanshi yasan menene son. Duk lokacin da zaiyi ido hud'u da ita sai bugun zcyrshi ya qaru. Shi yasa baya yarda ya kasance tare da ita su biyu, ko da ya manga yana kusa baya jurewa kasancewa kusa da ita sbd yasan ko ta halin yaya fiskarshi da idanunshi zasu fallasa sirrin zcyrshi. Ita kanta Deejan tausayin Hammannata takeyi tare da jin nauyinshi, dan tasan irin son da yake mata, tun tana karamarta yake bata kulawa ta musamman fiye da sauran yan uwanta, hidima yake mata babu gajiyawa, tun bata san so ba shi ya koya mata. Snn duk abubuwan da suka faru da ita baisa ya juya mata baya ba, bai canza mata ba ko kadan, babu abunda ya ragu daga soyayyar da yake nuna mata. Babu abunda yake kashe mata jiki irin idan ta tuna yanda ya nuna damuwarshi sbd wai ya yanke hukunci ba tare da neman amincewarta ba. Wasika musamman ya rubuto mata yana mai bata hakurin sadaukarwa dan uwanshi soyayyarta da yayi, tare da sanar mata dalilanshi nayin hakan. Wato, ganin soyayyar ta a idon dan uwanshi wanda duk kokarinshi da son nuna dauriyarshi ya gagara b'oyewa. Damuwan da yake gani tattare da dan uwanshi, wanda ya sanya baya ko barcin kirki, kuma ya fahimci saboda ita Deejance ya shiga wnn damuwan. Son karfafa zumuncin da ke tsakaninshi da dan uwan shi, sbd su nuna mishi shima yana da nashi gatan, ta hanyar mallaka mishi abunda yakeso muddin bai fi qarfinshi ba. Bayan haka ga Mahmud da ya shiga tsakani, wanda zaiso ya tashi ya ganshi tsakanin iyayenshi biyu. Tabbas Hamma shehu ya cika masoyi na kwarai abun alfahari, fatanta da addu'ar da take mishi a kullum shine ,Allah ya daidaita tsakaninshi da Habiba, ya kuma basu zaman lafiya, da farin ciki mai d'orewa. TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* * Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern. * *22*&23 *Gaisuwa da Fatar alkhairi gareku* *Online Hausa Writers grp Members* *Musan kanmu marubuta* *Hausa nvls social media* *M, F,and J Hausa Nvls* *Cool nvls and kitchen* *Futhatulkhair nvls* *Aisha Hanwa nvls* *Novels world* *Hauwa Sarki Novels* *Maman Ahmad nvls* *Zee and Hussy Nvls* *Dama sauran wad'anda ban ambata ba, kuna da yawa, Allah ya bar qauna.* ~Shirye shiryen biki ya kankama,da ke an kare ginin gidan smart, yayin da aka yanke kai kayan lefen Habiba, wanda a da can na Deejah ne. Dagewa tayi sai ta bisu nguroje, daga can ta d'auko kayanta. "Je ki tambayi mijinki ni babu ruwana." Cewar Dadayi. Ganin da gaske ba barinta za ayi ba sai ta tambayan ya sata ta rubuta note ta bawa kannenta sukai mishi. Bayan ya karanta yace suzo suce mata bai fahimci abunda ta rubuta ba sai tazo da kanta. Suko yara a gaban Dadayi suka isar da saqo, hakan yasa Dadayi ta shiga yi mata fad'a kan zuwa da kantan ai yafi mutunci. Tana zumb'ura baki ta yafa gyalenta ta fita tana tafiya da sauri sauri kamar wata mara gaskiya. Daga bakin kofa ta tsaya bayan tayi sallama, tana cewa gata. Banza ya mata kamar baijita na. "Uncle smart gani." Ta sake cewa tana leka d'akin. "Baza ki iya shigowa bane inzo in shigo dake. Ya ce ba tare da yakalleta ba. Tabd'i gara da da wani a d'akin zata iya shiga amma shi kad'ai kam, Allah ya tsareta, salon ta shiga yayi mata irin na rannan ya sata ta kwana a d'akinshi ya kasheta da kunya. "Dan Allah uncle, gobe za'a kai kayan lefen Hamma shehu, in bisu ? " Ta tambaya daga inda take tsayen. "U r not serious khadijah." Ya fad'a yana mai kallon yanda take leko shi kamar wata bakuwa. "Ayya dai daddyn mahmud." Ta fad'a da kalar tausayi. Murmushi yayi yace "Mhm da yake anyi niyyar cutata harda daddyn mahmud." Itama murmushi tayi ta sake cewa "Inje ? " Mikewa taga yayi ta yi baya da sauri tana raba ido, Ganin itan ya nufa da gaske yasa ta juya a guje ta bar kofar d'akin. Yana tsaye bakin kofar yana kallonta har ta isa kofar gida kafin ta juya ta kalleshi. Da sauri kuma ta fad'a cikin gidan tamkar wacce aka koro. Daga inda yake tsayen wata 'yar tsiririyar dariya ta sub'uce mishi dan ya fahimci abinda ya sa take gudun shiga d'akin. Washe gari kuwa da ita aka tafi dan ta cewa Dadayi ya amince. Kwana guda sukayi, suka dawo banda Deejan da sai lokacin da suka zo tafiya suka nemeta suka rasa. Sai bayan tafiyarsu suka bullo tare da Habiba, ashe d'akin yayansu Basharu suka shiga suka kulle kansu. Kwananta biyu a nguroje, Hamma shehu suka zo tare da Uncle smart. Kasancewar isowar dare sukayi dan basu taso da wuri ba. Suna cikin falon goggo suna cin abinci suka tsinkayo sallamar su. Maraba goggo yake musu cikin farin ciki tare da basu izinin shigowa. Dukansu biyu diriricewa sukayi, ita Deejah ta riga tasan laifinta, ita kuwa Habiba halin da ta tsinci kanta na fad'uwar gaba da kuma tsinkewar zuciya ya sata diriricewan. Ciki suka karaso, suka zauna suna gaisawa da goggo yayin da Smart hankalinshi ke kan Deejah da ke ta d'inne kai. Da kyar Habiba ma ta iya gaishesu. Kafin Deejah tayi magana smart ya rigata . "Mummy Sannu da kokari ko ? " À tsorace ta d'ago ta kalleshi kafin tayi musu sannu d'a zuwa cikin in ina, fiskarta na nuna alamun rashin gaskiya Hamma shehu kawai ya amsa Shiko smart kafita yayi da kaifafan idanunshi, wanda yasa zcyrta tsananta bugawa. Tsilli tsilli ya fara yi da idanunta alamun rashin gaskiya. "Baka san tazo bako Mahmudu ? " Goggo ta tambaya tana tsare ta da ido. "Ta fad'a min goggo." Har ta sauke ajiyar zuciya na samun relief sai kuma ta jishi yana cewa. "Amma ba da izinina tazo ba. " Hararanta goggo tayi tace "Kuma aka ce miki haka akeyi, ki kamo hanya daga dorofi har nguroje bada izinin mijinki ba ? " "Kyaleta goggo, zata karb'i hukunci daidai da laifin ta. " Da sauri ta kalleshi, ya kashe mata ido d'aya yana murmushi, hakan yasata saurin kawar da fiskarta daga kallonshi. Goggo da taga abinda yayi tayi saurin fita. Ba da jimawa ba ta shigo da abinci, tunkan ta karaso suka mik'e dukansu da niyyar karb'arta. Hamma shehu ne ya karb'a ya ajiye tiren Abincin, tasake ficewa ta dawo hanunta d'auke da kwanon sha. Ana ajiyewa Smart ya bud'e kwanon yana cewa. "Ni Wannan zan sha. " Tare da d'aukan ludayi d'aya daga cikin ludunan da ta shigo da su. "Bismillah Usman. " Ya fad'a yana kai damammen fura da nono bakinshi. Mikewa sukayi a tare zasu fita yace "Ku dawo ku zauna." Dukansu biyu a takure suke baranma Habiba da takeji kamar an d'add'aure mata jijiyoyin jikinta kasancewarta guri d'aya da Hamma shehu. "Usman ban aron cikinka gobe zan mayar maka. " Kallonshi shehu yakeyi cikin rashin fahimta "Kafin yace, Me kace ya Manga ? " "Oh, tunani nake da ana bada aron ciki da na karb'i naka na samu na shanye wnn abin, baka san dad'in da nakeji idan ina shanshi ba. " Gimtse dariya suka shiga yi, shi kuwa bai ma kula dasu ba, can ya kuma cewa. "Kasan wani abu Usman ? " Bai jira amsarshi ba yaci gaba da cewa. "Akwai wani gidan fura da nono a jos, ina gaya maka da inji suke markad'a furansu, idan kanasha wani laushi zaka ji yana wucewa sumul babu alamun gudaje ko kad'an. " "Kai Haba ? " Inji shehu. "Wlh kuwa nake fad'a maka." Ya fad'a tare da k'ara kurb'a. "Kuma à kwanon sha suke sayarwa ko ? " Shehu ya tambayeshi. "Umm. " Ya bashi amsa. "Ba mamaki irin wnn kwanon nema." Hamma shehu ya saké tambaya. Shiru yayi ya ci gaba da shan furanshi. "Kyanshi kuma ace kana cikin falo kamar na goggonnan. " Shehu ya kuma fad'a. "Kai ya ina baka labari kana min shiririta Ya fad'a bayan ya d'ago yana kallon shehun da ya kasa rike dariyarshi. Maida kallonshi yayi kan su Deejah yaga duk dariyan sukeyi kasa kasa. "Ha'a wai, me kuke tsammani ne. " Ya tambaya yana binsu da Kallo. Sai kuma ya ja tsaki yace "Kuna da matsala Wlh,kukayi wasa sai in fasa sha ma. " Shima ya k'arashe maganar yana 'yar murmushi, dan sai yanzu ya fahimci abinda yayi. Leka kwanon shan Hamma shehu yayi yaga yasha ya fi rabi, yace "Yi hakuri kada ka fasa ya manga, ai baka sha sosae bama." Kwafa yayi kafin yace "Wato kuna tsammanin santi nakeyi ko, da hankali na sarai labari kawai nake baku." "Sosae ma kuwa. " Hamma shehu ya fada yana ci gaba da dariyarshi. Da gudu Deejah ta shige d'akin Goggo Habiba ta mara mata baya, suka yi ta shan dariyarsu. Saida suka tabbatar Sun gama Sun fita kafin suka fito Suka tattara wajen. Suna zaune suna dariyar ya manga, goggo ta shigo ta samesu. Bata tambayesu dariyar me sukeyi ba ta shiga yiwa Deejah fad'a kan zuwan da tayi ba tare da izinin mijinta ba. K'arshe ta koma yi musu nasiha, tana nuna musu illolli da azabar da mace take jawowa kanta idan ta fita ba tare da sanin mijin ba, sanar da miji zanje wuri kaza bashi yake nufin an yarje miki ba, à à à baki izinin fitan shine babba. K'arshe ta K'are da basu shawarin yadda zasu zauna da mazajensu, su nemi yardarsu cikin aminci, yanda zasu kula da tsabar jikinsu, tsabar muhallinsu, gyara girki, magana cikin tausasawa,gujewa saurin fushi, hakuri, uwa uba Ladabi da biyayya. Washe gari ko da safe suna karyawa Habiba ta kalli Deejah ta tuntsire da dariya, itama Deejah kamar jira take ta fara nata. "Wai lafiya kuke tun jiya kuke ta dariya kamar sabbin kamun hauka ? " Goggo ta tambayesu tana binsu da Kallo. Dariyar suka ci gaba da yi, dakyar suka tsagaita suka shiga bata labarin abunda ya manga yayi. Itama tuni ta fara dariya, har Baffa dake daga cikin d'akinshi sai da ya dara. "Wato kuna gulmar ya manga ko? " Muryar Hamma shehu suka tsinkayo yana fadin hakan, da alamar Shima dariyar yake so yayi. Gimtse dariyar sukayi dukansu biyu suka shiga gaishesu, yayinda smart yake cewa "Goggo yarannan Sun raina ni daga magana fa suka shiga yi min dariya kema Habiba har da biye musu ko ? " Qasa Habiba tayi da kanta tana 'yar murmusawa, ita a dole tana gaban siriki. "Ke kuma ki tashi ki fara shiri tare zamu koma." Ya fad'a yana kallon Deejah. Da sauri ta kalleshi sai kuma ta maida kallonta kan goggonta, suna had'a ido tayi kalar tausayi ko goggonnata zata taimaka tasa baki. Tab'e baki goggo tayi tace "Bakiji abinda Mahmudu yace bane, ko baza ki tafin bane ? " Simi simi ta tashi Habiba na binta a baya suka shiga d'akin su. Jakunkunan da ta dawo dasu daga jos ta fitar, ta fara bubbudewa. Turmin zani, sabulai, man shafawa, da turare ta fitarwa goggonta, ta bawa Habiba kayan kwalliya da mai da turaren itama. Saida taxin da aka nemo shata yazo snn suka fito da kayan, su Hamma shehu suka fitar zuwa gurin motar. Tafe suke cikin motar hirar Hamma shehu da ya manga ke tashi, sai kuma driver dake sa musu baki lokaci lokaci. Itakam Deejah kamar an d'inke mata baki, sai bin guraren takeyi da Kallo kamar wacce bata san hanyar ba. Har ta gaji da dube dubenta ta jingina da jikin kujerar motar tana lumshe ido. Sunyi nisa da tafiya taji kanta jikinshi, da sauri ta bud'e idonta ta ganta kwance kan kafad'ar shi. Zaro ido tayi tace "Laa ilaaha Illallahu, sai kuma ta k'arasa sauran à zcyrta ganin Hamma shehu ya juyo ya kalleta. Kokarin d'aga kanta takeyi ya maidata snn ya d'an rankwafo daf da fiskarta yace cikin murya kasa kasa. "Dama ke mai laifice, ki kara tun baki karb'i hukunci ki ba. " Hamma shehu ko yanda yaga take zura idanunta ne ya bashi dariya, hakan yasashi saurin Kawar da kanshi yana kallon gefe yana dariya k'asa k'asa, tare da jinjina hali irin na d'an uwanshi, abun da yasan shi ko da wasa bazai iya yinshi à gaban wani ba. Wani abu sai girman birni. Tun tana kokarin janye jikinta har ta hakura ta lafe tayi shiru da haka har baccin gaske ya kwasheta ya ya gyara mata kwanciyar à jikinshi har suka isa bata sani ba. Saida ya tasheta, taga kannenta kewaye da mota suna Washe baki, Juyawa tayi taga Hamma shehu da driver suna fitar da Jakunkunan ta. Wani irin kunya taji ya lullub'eta, tayi saurin matsawa daga kusa dashi ta bud'e murfin motar. Saida tasa kafarta d'aya waje kafin ta d'an kalleshi tana keb'e baki tace. "Mara kunya kam bai ji dad'i ba Wlh. " Kamota yayi niyyar yi yana cewa "Waye marar Kunya? " Wuff ta fice tayi hanyar kofar gida da sauri kamar zata kife gudun kada ya cimmata, ya k'ara bata kunya. D'akin Dadayi aka shigar da kayakin ta bita à baya tana kallon kayakin da mamaki kafin ta tambayeta inda ta samosu.. Saida ta fad'a mata bata zauna ba balle ta tsaya dogon bayani ta fita ta wuce d'akin Adda ta gaisheta, haka tabi sauran dakunan ma ta gaishesu kafin ta koma d'akinta. Washegari tare da Dadayi suka ware kayan Mahmudu daban suka d'ura cikin babbar jaka, Kasancewar akwai dinkakku cikin kayan Dadayi ta ware mata na fitar biki. Kayan Mahmudu Dadayi ta kaiwa Adda ta kuma ce abar maganar kayan lefen da za à hadawa Deejah akwai sabbin kayan da Mahmudun ya saya mata masu yawa, duk da haka Adda tace za à bata kud'in ko kuma a saya mata dabbobi ayi mata kiwonsu... *F. O. W * * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* * Impacting Valuable knowledge and Entertainment is our concern * *23* *Yau gaisuwar taku ce.* *A Gidajenmu* *Red Butterfly nvls grp* *Zee &Hussy's nvls* *Melody nvls grp* *Hausa nvls room* *Hausa nvls grps(Na Mmn Aslam* *Novelist* *Hausa nvls books* *Dandalin litattafai* *Matan dai nvl grp* *Foulani Fans* And lots more, Allah ya bar qauna. •• •• •• ~Shirye Shiryen biki aka shiga sosae, baki daga nesa suka fara zuwa, cikin kwanaki biyu gida ya cika dam da Jama'a. Danginsu na Cameroun ma duka Sun Iso, har da abokan Hamma shehu na can. Ana gobe za'a kai amare scorpion da Nas suka Iso. Tarba sosae aka musu duk da akwai wasu bak'in da yawa, kuma ba K'arya sunji dad'in yanda aka karrama su. Har cikin gida suka shiga suka gaisa da su Adda, daga nan suka wuce suka gaida Hajja inna. Labari sukayi tayi na yadda suka samu canjin rayuwa, kowa na fad'ar kalar gata da qaunar da yake samu gun familynshi. Nass, ne cikin tausayawa kanshi, yake fad'in su dai sunyi sa'a da suka samu duka mahaifansu à raye, shi kam ya koma ya samu mahaifiyar shi ta rasu. Sosae suka tayashi jimami, sai kuma suka shiga jimamin rashin d'an uwansu Billy, gara ma su Sun samu Sun shiryu har Sun koma ga mahaifansu, shiko duk da son ganin mahaifinshi da yakeyi Allah bai nufa ba, gashi ta mummunar hanya ya rasa rayuwarshi. Tunin da smart yayiwa Nasir ne yasasu godewa Allah shiryar dasu da yayi kafin ya d'auki rayuwarsu. Raba dare sukayi suna hira duk da gajiyar da suka kwaso. Washe gari aka ci gaba da hidimar buki, inda suke ta yiwa Hamma shehu tambayoyi Kan yanda suke tafiyar da bukukuwansu, shi kuwa yana basu labari . Ranar da aka kai amare Kwana àkayi ana cashewa duk da ango Mahmud Baban Mahmud kam d'an Kallo ya zama, dan ko an kirasu su fito fili saidai ya tsaya kallon masu liki da rawa. 'yan uwa ,kanne da abokan arziki sai liki sukeyi sbd kyakyyawar shirin da sukayiwa wnn rana. Yusufa kam ko shine ango albarka, dan farin cikin dake fiskarshi ba mai b'oyuwa bane. Sunn gayyato mawaka biyu, d'aya daga Cameroun d'aya kuma anan kusa da dorofi yake, (Alh, yahya, da Sanda Boro.) Dukansu mawaka biyun Sun bane basirarsu sosae wajen waqe amare da angwaye. An kusan gamawa aka saki kid'an gargajiya na fulani inda kannen angwaye da amare da kuma suka jeru à Layi suka fara bada step. "Kai Wlh ba za'ayi babu ni ba. " Cewar scorpion, yana mik'ewa daga kan kujerar da suke zaune. Tsakiyar masu rawan ya kutsa ya shiga. Duk a tuñaninshi rawan sauk'i ne dashi, ganin yanda suke taka rawar à jere cikin nitsuwa, su wani jefa k'afar su na dama à tare kafin su juya kuma. Rawar ba k'aramin burgewa yayi ba. Daddagewa yayi Shima zaiyi kamar yanda yaga sunayi, sai dai tun rawannashi baije ko ina ba aka fara yi mishi dariya, sbd ka'rfi da ya dage yake nunawa rawan, ba kamar yanda su suke Juyawa à hankali cikin sakin jiki ba. Ba wani rawan kirki yayi ba, duk yaji ya gaji sai maida numfashi yakeyi. Liki sosae ya tsaya ya musu kafin ya koma gurin zamanshi yana cewa "ashe haka rawan yake da wahala, à haka kuma in ka gani kamar wasa sukeyi." "Wa ya gaya maka babarbare zai iya kwaikwayon fulani cikin sauki." Smart ya fad'a yana mishi dariya. "Kaga rainin da ka jawo mana kuma." Cewar Nas Shima yana nashi dariyar. "Kai tafi can, dan ban shirya bane Kaga banyi da kyau ba, kuma da kake magana ance maka muma zaka iya yin namu ne, ba gwara ni na dan kokarta ba." Scorpion ya bashi amsa yana gyara zamanshi. "Ahaf saidai idan ba ayi na gani ba, kasan bafulatani da sauri d'aukan abu, Sharp brain ne damu." Haka sukayi ta raha tsakaninsu cikin farin ciki da annashuwa aka watse, kowa ya koma masaukinshi. Washegari aka tashi da dafe dafe, masa aka yi da safe sai kunun gyada da kuma tea, ga kuma madaran shanu nan, sai abinda kakeso zaka sha. Da rana kuma, Rice n stew. Tuwon shinkafa, da Tuwon masara, miyan taushe, miyan kuka, da miyar busasshiyar Kub'ewa, nama baja baja Kasancewar shanu biyu aka yanka, ga man shanu ka diba son ranka. Kunun zaki da sob'o. sai rabon abinci akeyi gida gida, wad'anda suka shigo suci. Da yamma kuma akayi bud'an kai dukansu biyu nan cikin gidan. Na Deejah aka fara, kafin akayi na Habiba. Ana gamawa aka shiga daukan hotuna kafin aka shiga fitar angonci. Angwaye sun sha ado da fararen shadda, sunsha babbar riga, suka dora huluna masu adon baki da farin zare, haka ma Mahmud little, exactly irin kayan Daddies dinshi ya saka, sai takalmansu bakake da kuma bakaken agogo da suka daura a hanunsu. Wannan duk aikin Hamma shehu ne, inda ya dinkawa duka kannensu maza light blue shadda, harda kananan yaran gidan. Adda tana daga cikin d'akinta take hango yanda danginta suke nunawa 'ya'yanta gata. Har qwalla tayi sbd farin cikin gajin auren yaranta biyu maza da tayi. Liki akayi ta musu, ana ta daukan hotuna har magriba snn aka watse. Da dare bayan sallar isha'i aka raka angwaye gidajensu inda abokai suka yi musu nasiha kan zaman aure, daga nan suka sake fita, dan ranar ma gidan amare kawayen zasu kwana. Sai washe gari har bayan la'asar bayan sunyi girki, sun gama gyara gidajen snn suka watse. Sai fatan Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a dayyiba. Su scorpion ma a ranar suka tafi bayan sunyiwa deejah kyaututtuka, wanda scorpion sai hakuri yake ta badawa kan abubuwa sun mishi yawa bai samu ya yi kyautar yadda yaso ba, dan wnn alkwari ya daukarwa kanshi, duk yarinyar da smart yaso sai ya mata babban kyauta, gashi shima kuma bikinshi ya kusa saura wata biyu masu zuwa. Cheque na Dubu dari biyar ya bata, shi kuma Nas, cheque na dubu dari. Smart ta bawa, a cewarta ita babu abinda zatayi dashi ya rike ta bashi. Karb'a yayi da nufin zai samu Hamma shehu suyi shawarar abinda ya dace a yi mata da kud'in, saidai bai sanar da ita kudurinshi. ~Bayan kwana uku da bikinsu ta fitar da credit card dinshi da ya tab'a bata lokacin da zai tafi abuja ta mayar mishi tare da kud'ad'en da ya bata, har da wanda yake bata lokacin da suke Jos idan zaiyi tafiya ,dan kad'an tayi amfani dasu. ATM din ya karb'a ya bar mata sauran kud'in yace rike a hanunta, zasu mata amfani dan nata ne ya riga ya bata. ~Gidan Hamma shehu kam saida yayi da gaske ya samu yayi yaki da damuwar dake cin ranshi ya fara jan Habiba a jiki. Ba laifi itama ta fara sakin jiki da shi tunda dama maganar auren su ne ya kawo rashin sakin jikin. Tsakaninsu da Deejah kuma kusan kullum suna tare, dan yawanci idan ta gama aikin da zatayi gidan Deejan take shiga su sha hirarsu, sai mazajensu sun kusa dawowa ta koma, itama Deejan ta kan shiga mata sa'i da lokaci. Sam basu da kewa dan kullum sai kannensu sunzo kasancewar kuma basu da nisa da gida. Mahmud ma kusan kullum sai an kawoshi. Haka kuma kullum suke aika abinci gida idan sun girka, har Hajja inna sa mata sukeyi. Zamansu tsakaninsu da mazajensu kuma lafiya qlau ba a jin kansu. Deejah wani lokacin tausayin smart yake kamata idan taga yana cin cimar su na garin, kasancewar tasan yadda yake a da, tasan cimarshi, amma yanzu komai ya canza. Wani lokacin ma, idan yasa wani abun a bakinshi sai ya yamutsa fiska sbd rashin sabo, amma haka yake kokarin tutturawa kodon ya saba. Yanzu ko machine na kanshi bashi dashi, sai na Hamma shehu da suke amfani dashi tare. Babbar matsalar da ya samu shine k'ona kamfaninshi da 'yan kungiyarsu wad'anda ba a kama ba sukayi. Ya fawwalawa Allah al'amuranshi tare da addu'ar Allah ya takaita mishi ya kawo mishi sauqi, ya kuma kareshi daga sharrinsu dan kona kamfanin ya nuna cewa har yanzu suna bibiyarshi. Baya wasa da sadaqa sbd neman gafara da maganin masifa. Istigfari kuma kullum cikin yinshi yakeyi. ~ Shawara sukayi da Hamma shehu kan kud'ad'en shi da suke Bank. Nan ya bashi shawarar ya nemi gida can cikin Gembu ya koma ya kama sana'a. Saida suka samu iyayensu da shawarar suma suka yi na'am dashi. Kasancewar Hamma Atiku a can yake aiki a matsayin d'ansanda, da ya zo suka sanar dasu shawarar da suka yanke. Nan ya basu tabbacin zai nemawa smart gidan hayan da zai zauna kafin yayi settling ya samu na kanshi. Snn ya sama mishi shago. Take kowa yayi na'am da shawarar. Saura sati bikin scorpion, da Nas, wanda shi zai auri kanwar scorpion,aka had'a bikin gaba d'aya. * * Shirya kayanshi yakeyi cikin travelling bag, kan gobe zai kama hanya, sbd yasan zai kwana biyu a hanya kafin ya isa. Deejah dake gefe tana zaune ta cika tayi fam, dan ta aza mishi rigima kan sai ta bishi. Shiko raina mata hankali yayi da cewa babu inda zata bishi, tunda dai kunya take ji a gansu sun fita tare, dan ko nan da gidansu yace suje tare sai tayi ta nokewa wai ita tana kunyar had'a hanya dashi. Tsakaninshi da Allah wnn hali nata yana bashi haushi dan shi ba haka ya tsara rayuwar su ta kasance cikin kunya da nuku nuku ba. Sau tari yana lura da ita idan sunje gidansu duk zaman da zasuyi a gidan ko d'aga ido batayi ta kalleshi , yi take kamar bata tab'a ganinshi ba, ita wai kunya. Kuka ta fashe dashi tsakaninta da Allah ganin ya gama had'a kaya yana shirin kwanciya. "Wai mummy baza ki bar kukannan ba, sai kanki yayi ciwo ki hanani tafiya goben ko ? " Kara sautin kukan tayi tana bubbuga kafafunta a kasa tamkar karamar yarinya. "Zo ki fad'a min me akayi kike tamin asarar hawayenki haka ? " Bata yi magana ba saidai ta sassauta kukan, tana kuma satar kallonshi dan taga ko kukan nata yayi tasiri a kanshi. Mika hanunshi yayi ya jawota ta zauna kusa da shi yace "Nifa bawai tafiya da ke dinne bana so ba, kije kiyi ta nuna kamar baki sanni ba shine bana so, kuma ma ai naga kunyar fita tare dani kikeyi, tayaya zamuyi tafiya tare kuma ? " "Na daina Daddyn mahmud, Allah kuma idan munje bazanyi kamar ban sanka ba, nan d'inma dan kowa ya sannine, kuma kuskure kadan mutum zaiyi sai ayi ta zaginshi ana cewa baida kunya." D'an karamin tsaki yaja, kafin yace "To ina ruwanki da mutane, ni wlh bana son irin wannan d'abi'a." "Yi hakuri na daina Daddyn Mahmud." Ta fada da sauri. Murmushi yayi mai sauti yace " Wai Daddyn mahmud, sannu mai wayo." Itama murmushin tayi tana sunne kai. "Kwanta to zanyi tunani zuwa goben inga ko akwai yiyuwar tafiya dake din." Ya fad'a cikin dakewa. "Don Allah dai." Ta fada tana had'a hannayenta gu d'aya, ta wani marairaice tayi fiskar tausayi. "Tashi ki had'a kayanki to, yadda baki tayani ba nima bazan tayaki ba." Wani tsalle ta daka tana dariya, "Ko a hakanma na gode." Hada kayan takeyi cikin d'oki da farin ciki, haka kawai taji ranta nason zuwa Maidugurinnan, ita kanta baza ta ce ga takamammen dalili ba. Washe gari kuwa tun asubah suka kama hanya dan ya riga ya sallami mutanen gida, kuma ya sanar musu tare zasu je kawai dai yaja mata raine dan yaga yadda take ta d'okin zuwa tun lokacin tafiyar baiyiba. *Mudai sai muce Allah ya kiyaye hanya Khadijar Mahmud.* * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* * Impacting Valuable knowledge and Entertainment is our concern * *25*&26 *This page is dedicated to my lovely sisters* *Khadijah (Ummi)* *Hameedah* *Zahrah* *I heart u sweet sisters.* ~A razane ya bud'e idanunshi yana kallon Fateema da ke kwance shame shame. "Fateemah ! " Ya kirata da qarfi yayin da yake jijjigata. Take wasu qwalla masu zafin gaske suka kwararo mishi bisa kuncinshi. A zafafe ya maida kallonshi ga mugayen, saidai ga mamakinshi, 'yan sanda ya gani tsaye kan b'arayin, dan sun harbe biyu daga cikinsu, masu bindiga, biyu kuwa suna durkushe a wajen sun d'aga hannayensu sama. Wayarshi da tun d'azu yake ta neman agaji ya d'aga a kid'ime ya kara a kunnenshi dan ko duba mai kiran baiyiba , saida yaji muryar smart, yace "Smart, Fateema." Daga can b'angaren yayi saurin cewa Inna lillahi wa inna ilaihirraji'uun, me ya sameta." Shi kam Naseer tunda yace Fateema yayi hurgi da wayar ya koma kan Fatimar yana kiran sunanta tare da jijjagata. Saida suka iza keyar su, snn biyu daga cikinsu suka dawo suka umarceshi da yad'auketa su tafi asibiti. Duba jikinta ya keyi ko zai ga alamun harbi, amma bai gani ba. Hakan ya bashi tabbacin suma tayi sbd haka yana fita da ita palour ya shimfid'eta ya isa wajen fridge ya bude'. Garin bud'ewa hanunshi ya buge glass cup d'in dake kan fridge d'in ya fad'i ya fashe. Bai kula ba, ya d'auko ruwa ya juya da sauri, taku d'aya yayi ya tsaya tare da yin qara, yana rintse ido sakamakon taka fasasshen glass d'in da yayi wanda sanadiyyar hakan ya haddasa tsargawan wani irin ciwo mai azababben zafi har cikin kwakwalwarshi. Take kuma, jini ya fara fita daga kafan. Polisawan kuwa sukayo kanshi suna duba kafar. Kokacinne kuma Uncle smart da yayan scorpion, (Abubakar) suka shigo cikin *Tashin hankali* mara misaltuwa. Kanshi sukayi dukansu dan basu ma lura da Fatima ba. Ganin yanda jini ya b'ata wajen ya dad'a tayar musu da hankali. Kafar suka shiga dubawa suma. Take Smart yasa hanu ya cisge kwalbar saida Naseer ya dad'a yin qara. "Ina fatimar, me ya sameta ? " Ya tambaya yana share gumin fiskarshi da hanun rigarshi. Yayin da d'aya daga cikin polisawan yake d'aure mishi kafar da d'ankwalin Fatima da ya gani kan kujera. Da hannu ya nuna musu inda take yana Yunkurin tashi , police d'in ya na taimaka mishi. Gudu gudu Abubakar ya qarasa ya sungumi Fatima ya fita da ita a guje, yayin da su kuma suka taimaka mishi suka kaishi gurin motar. D'aya daga cikin polisawan ne yaja motar, smart da d'ayan kuma suka matsu suka zauna a d'aya kujeran. Abubakar da Naseer suna baya sun tallabe Fatima da har yanzu bata san duniyar da take ba. Cikin gaggawa aka karb'esu, aka fara kokarin ceto rayuwar Fatima, yayin da Nass aka shigar sashi thearthre domin d'inke kafarshi sbd ba karamin shiganshi kwalban yayi ba. Sai asuba aka basu tabbacin Faheema kam ta rai yayi halinsa, sanadiyyar shigar bullet biyu jikinta, d'aya a kirjinta d'aya kuma a gefen cikinta, duk a kokarinta na kare scorpion daga harin da aka kawo mishi. A na ukun ne ya ture ta cikin zafin nama, bullet d'in ya sameshi a kafad'a. Ganin dukansu zube ne yasa su saurin barin gidan a tunaninsu sun riga sun gama dasu. Iya rud'ewa, mutuwar Faheema ya rud'a su, ga Umar da har yanzu basu san a wani matsaya yake ba. •• •• •• ~Can gida kuwa haka suka kasance jugum jugum sai kiran waya. Mutanen gidansu Faheema kuwa tuni suna can, kasancewar makotan juna ne gidajennasu. Saida akayi sallar asubah Deejah ta tashi ta shiga d'akinsu tayi alwala ta canza kaya tayi raka'atinil fajr, ta zauna tana azkar. Saida aka tada sallah ta tashi ta bada farali tare da addu'o'i daga nan ta zauna ta zabga tagumi tana tunanin halin zullumin da suke ciki. Tana cikin tunani taji sallamarshi, ta amsa tare da juyawa tana kallon yadda ya shigo a sanyaye. A sanyaye ta tashi ta shige jikinshi ta saki wani marayan kuka. Matseta yayi a jikinshi kamar zai b'allata, ya rasa da kalmar da zaiyi amfani wajen bata baki, dan yana cikin tashin hankali, ga Faheema ta rasu, Umar yana cikin mawuyacin hali, dan kafin su isa shima babu marabinshi da gawa, dan dai har yanzu ba a ce musu ya cika bane. Ga Fatima kwance sai abunda Allah yayi, dan itanma har yanzu bata farfad'o ba. Gwara Naseer an fito dashi bayan anyi mishi d'inki shima d'in har yanzu bacci yake sbd alluran bacci da aka yi mishi. "Da gaske Faheema ta rasu." Ta dawo dashi daga dogon tunanin da ya fad'a. Gyad'a kai yakeyi dakyar ya samu ya iya sarrafa harcensa, yace. "Allah ya karb'i kayansa khadijah, ta koma ga mahallicinmu." "Inna lillahi wa innaa ilaihirra ji'un." Ta fad'a tana juya kanta a kirjinshi. "Kwananta ne ya kare, khadijah, Allah ya rubuta ta wnn hanya zata tafi, kuma lokacinta ne yayi, muma lokacin muke jira,idan ta zo ba jinkirtawa, Fatanmu dai Allah ya d'auki rayuwarmu muna masu imani , ita kuma Allah ya ji kanta, ya kyauta makwancinta, Allah ya bawa sauran lafiya." "Sauran." Ta tambayi kanta, bayan su akwai wasu ma kenan. Tambayarshi taso yi yace "Barin inyi sallah, lokaci na kurewa. Cikin sanyin jiki ta sakeshi ta koma bakin gado ta zauna ta rabka tagumi, lokaci lokaci tana share hawaye. Tana cikin wnn hali ya idar da sallah har yayi addu'o'i ya gama, yace mata zai koma asibiti. Kanta kawai ta iya gyad'a mishi har ya fice, kafin ta tashi ta koma cikin gidan. Bata jima da shiga ba saiga su Zainab, sun shigo suma da nasu kukan. Kamar ana jira aka shigo da gawar Faheema. Take gida ya rikice da kuka, ya tabbata Faheema ta amsa kiran mai duka. wanke ta aka yi aka mata sutura aka sallaceta karshe aka gaita gidan gaskiya. Sai bayan kaita tukun Yagana ta tuna bata ga Fatima . Tambayar zainaba tayi itama tace bata ganta ba, karshe suka dauki wayar Mamansu suka kira layinta dashi. Amma har ya karaci ringing ba'a d'aga ba. Yaya Bukar suka kira dan suji ko Nasir yazo, sai a snn yake shaida musu abunda ya faru. Nan kuma hankula suka dad'a tashi. Ana dawowa daga kaita su zainab yagana, Deejah da kanwar mamansu suka tafi asibitin, kusan tare suka isa dasu Uncle smart. Gurin Nasir suka fara shiga suka dubashi, snn suka tsaya jiran farfad'owar Fatima wanda har yanzu ake fama. Sunkai kusan awa guda a wajen dan itama din har sun fara yi mata kuka kafin daga baya doctor ya fito yace musu ta farfad'o saidai ba'a son hayaniya kusa da ita. Dakyar aka bar Zainab ta shiga, nanma da Fatiman tana ta kiran mamanta ne, ita ta shiga kasancewar Maman bata nan. Kuka sosae ta samu Fatima tanayi hakan yasata karasawa da sassarfa. "Sun kashesu, Aunty Zee, a gabana suka kasheshi." Ta fad'a yayin da take rintse hanun zainab cikin nata. "su wa suka kashe kuma Fati ? " "Ya Nasir da Ya Umar." Ta fad'a cikin matsanancin kuka. "Mafarki kikayi Fati, basu mutuba, dukansu suna raye." Waro ido tayi tana kallon yayarta sai kuma ta shiga girgiza kanta tana cewa "Ba mafarki bane, da gaske sun kashesu, naji karar bindigar, kuma dama sun fad'a sunce sun riga sun kashe Ya Umar." "Ki yarda dani wlh basu mutu ba, dukansu suna cikin asibitinnan." "Ina suke to ? Ya basu shigo ba." Dafata tayi tace "Fati, dukansu basu da lafiya, Tabbas ya umar sun harbeshi da gaske amma bai mutu ba, shi kuma Ya Naseer, glass ne ya soke shi a qafa." Shiru tayi kamar bata yarda ba, daga bisani tace," kaini gurinsu in gansu aunty zee." "Gurin Ya Nasir dai zan kaiki amma Ya umar kam har yanzu ba a barmu mun ganshi ba." "Muje in ganshi." Ta fada dan ta tabbatar da abunda 'yar uwarta take cewa. •• •• •• ~Hamma shehu ne ya kirashi domin yaji ko sun taso. Nan ya sanar mishi da mummunan al'amarin da suka wayi gari dashi, sbd haka sun d'aga tafiyar sai komai ya lafa. Sosae hankalin Hamma shehu ya tashi, baranma da yaji d'an uwanshi yace daga cikin 'yan kungiyarsu wad'anda ba'a kama bane suka biyosu suke neman rayukansu. Bai b'oyewa mutanen gida ba, ya sanar dasu abunda ya faru sbd su tsaya su nemawa musu kariya daga sharrin mugayen, baranma adda da take uwa, addu'ar bakinta zaifi tasiri akan d'anta. Sun shiga tashin hankali suma mutanen gidan ba kad'an ba, amma iyaye mazan sai kwantar musu da hankali sukeyi, suna nuna musu cewar babu abunda zai faru sai abunda Allah ya rubuta musu, wanda wnn kuma babu abunda zai kawar dashi sai ya faru. •• •• •• ~Saida ta shiga ta ganshi har suka yi magana hankalinta ya kwanta, ya kuma tabbatqr mata da d'an uwanta ma yana raye bai mutu ba, kamar yanda su Smart da Ya Bukar suka shaida mishi. Dakyar ta yarda ta bisu gida bayan an bata sallama, nanma saida manya suka sa baki. Isarsu kofar gida ne kuma wani sabon tashin hankali ya shigeta sbd ganin jama'a dankam a kofar gidan. Jikinta ne ya soma rawa, tuni ta fara kuka, "Kuka ce min Ya Umar bai mutu ba, to taruwan me akayi anan ? " Ta fad'a cikin kuka. Duk cikinsu babu wacce ta iya rike kukanta , har suka shiga cikin gida kuka sukeyi babu mai rarrashin wani. Dukansu sun san akwai shaquwa mai qarfi tsakaninta da Faheema, tun yarinta suka taso tare. Rarraba ido takeyi tunda suka shigo gidan tana neman Faheema dan zuwa yanzu ta gama hakikancewa d'an uwanta ne ya rasu. "Ina Heema aunty Yaana ? " Tace daidai lokacin da ta karasa kusa da yayar Faheemar. Fashewa aunty Yaana tayi da kuka tace "Heema babu, ta tafi ta barmu." Wani irin dumm taji kunnuwanta sun mata, duk wani system na jikinta taji ya daina aiki. Yaraf ta saki jiki ta yi zaman dirshan. Kallon aunty yana takeyi ba ko kiftawa, jin abun takeyi tamkar cikin mafarki. Lallai wnn shine ana wata ga wata, wnn shine bazata. Tabbas mutuwar Heema tazo mata a bazata, tunda ko da wasa bata kawota cikin wad'anda take tunanin sun mutn ba, sai gashi kuma ita aka ambata a matsayin wacce suka rasa. To yaushe, abun ya faru ? Me ya faru da ita ? Ciwo tayi ko mutuwar kwaf d'aya tayi ? Ko dai harin da aka kai musu ne yayi ajalinta ? Tambayoyin da zcyrta yake ta wassafa mata kenan ba tare da ta iya bud'ar baki tayi su ba. Ganin yanda ta kafe aunty Yaana da ido, ta zamo kamar bata cikin hayyacinta, yasa Matar Bukar ta zo ta kamata ta fita da ita daga d'akin. Ita dai binta takeyi duk inda tayi da ita, dan ji take kamar kwakwalwarta baya aiki yanda ya kamata. Cikin d'akinsu taje ta ajiyeta inda anan su zainab suke da su Deejah, tare da wasu daga cikin 'yan uwansu. Zuruu tayi tana kallon gu d'aya daga baya kamar an tsikareta ta mike da karfi. Yagana tayi saurin rikota. "Ina zakije Fati ? " Ware murya tayi tace "HEEMAH." Sai kuma ta sulale kasa ta rushe da wani irin kuka mai tab'a zcy....... *F.O.W* * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* * Impacting valuable Knowledge and Entertainment is our concern. * *26* ~"Me kikeyi haka Fati, kamar ba musulma ba ? Musulmi da yarda da kaddara aka sanshi. Idan abu irin haka ya sameki "Innaa lillahi wa Innaa ilaihirraji'uun. Ya kamata ki fad'a ba ihu ba. Kanwar Babansu ce take fad'in hakan. Itako ci gaba tayi da kukanta dan ita kad'ai tasan abunda take ji a zcyrta. Tasan tayi rashi babba, rashin aminiya. Babu abinda yake gifta mata kamar rayuwar da sukayi da Heemanta tun suna yara har lokacin da aure ya rabasu. Shaquwa mai qarfi tsakaninsu, makarantar boko, islamiya, aika, duk tare suke zuwa. Idan d'ayansu bata da lafiya haka d'ayar ma zata kasance sukuku kamar itama bata da lafiyan. Sbd soyayyar da suke wa juna yasa Scorpion baisha wahalar shawo kanta ba, duk da kuwa tana da wanda takeso kafin a ganeshi. A ganinta idan taki wan kawarta kamar bata kyauta mata ba, duk da cewa Fatima da scorpion ba ciki d'aya suka fito ba, uba suka had'a amma akwai fahimtar juna a gidan, babu irin wnn jahilin kishi, yaran gidan duk d'aya ne. Shi yasa tayi ma kawarta wnn hallaci. Allahu akbar, yau gashi mai rabawa ta raba, kakkaifar takobi ta yanke amintaka da soyayyar su, sai addu'a kawai ya rage tsakaninsu. Dole tayi kuka, a yanzu gani take kamar duk wanda ya hanata kuka baya sonta ne, duk wanda yace tabar kuka ma dole ya bata haushi a yadda take jin zcyrta na mata zugi. Saida taci kukanta ma'ishi, fiskarta ya canza kamar ba nata ba, idanun nan sunyi luhu luhu, kafin ta nemi waje ta kwanta tana sauke ajiyar zcy, a ranta kuwa addu'o'i da neman gafara take yi ga aminiyarta. Hankula sun kasu kashi biyu ga marasa lafiya, ga kuma zaman makoki. 'yan tsegumi kuma sai kananan maganganun sukeyi kan iyayen Faheema sun jawo mata ajalinta tunda suka aura mata d'an fashi, dama duk abinda kayi kaima sai an maka, wa ya sani koda ta rayu watakil itama ta haifo d'an fashin. Maganganu dai babu dad'in ji, abunka da halin d'an adam, wani idan bashi abu ya sama ba, babu ruwanshi da kaddara, sai ya iya cewa kai ka jawowa kanka. Cikin kwanaki ukun nan duka kullum sai Hamma shehu ya kira yaji ya suke da kuma masu jiki, wani lokacin har Mahmud yake bawa suyi magana da babanshi, duk da maganan nashi ba sosai bane. Kuma sun dukufa sosae wajen yi musu addu'o'i da nema musu kariya a gun Allah, suma anan Maidugurin ba'a barsu a baya, saukar Qur'ani ake tayi da sadaka, sai dai muce Allah ya karb'a. Zuwa wnn lokacin scorpion ya dawo hayyacinshi saidai ya zama wani sukuku dashi baya magana, abinci ma sai anyi da gaske yake tab'awa, babu abinda yake damun ranshi illa tunanin Faheema, gani yake kamar shi ya ke duk shine sanadin komai. Nadama da Jinjina d'aci da bakin cikin da ya cusawa jama'a da dama, yakeyi. Wad'anda ya rabasu da masoyansu, sbd son zcy ba tare da sun mishi laifin komai. Gashi shi d'aya akayi mishi amma yana jin kamar zai mutu. Allah ya jarabceshi ta hanyar rabashi da abunda yake tsananin so a lokacin da yayi nadama. Ji yake nauyin zunubanshi suna dad'a karuwa akanshi. Wani lokacin saidai aga hawaye na zuba a fiskarshi, lokaci guda ya zabge kamar wanda yayi ciwon shekaru. Smart, 'yan uwanshi da iyayenshi su suke kokarin kwantar mishi da hankali a ko da yaushe. Deejah tsabar yadda ta sa tsoro a ranta da kuma jimamin abunda ya faru yasa ta zama wata iri, har nadamar zuwa da ita smart yakeyi. Ita kuwa gani take kamar suma basu tsira ba, tunda dai gashi duka abokanshi biyu aka kaiwa hari, tana ganin sune na gaba, duk da dai ance mata an kamasu, amma jikinta na bata cewa ba dukansu bane. Kuma tana ganin ko a hanyarsu na komawa zasu iya taresu kamar yadda su scorpion suka tab'a yi musu. Amma kuma duk da haka batayi nadamar biyoshi da tayi ba dan tana tunanin hakan zaifi mata sauki akan idan tana dorofi taji labarin abinda ya faru. Saida akayi sati guda Naseer ya fara taka kafarshi, shi kuma Umar da yake damuwa yayi mishi yawa ya sa jinyarshi karuwa. Sati biyu curr yayi a asibiti kafin aka sallameshi. Dawowar shi gida yasa mutuwar Faheema ya zame mishi sabo, nanma dan gidansu ya dawo ba gidanshi ba. Sati guda suka kara bayan sallamar scorpion kafin sukayi sallama da mutan maiduguri suka kamo hanyar Taraba state, suka barsu da kewa. Nina haka na tattari kayau kayau d'ina na biyosu, sbd d'auko rahoto, muna ta tsilli tsilli da idanu daga ni har Deejah. Allah dai ya dawo damu lafiya. Mun jijjiga mun jigata kafin mu isa dorofi, gani dama bani da juriyan zaman mota, gwara ma Deejan ta fini juriya. Tass suka samu Habiba ta gyara musu gidansu. Kasancewar dawowar dare sukayi, marabtansu kawai sukayi tare da gabatar musu da abincin da akayi musamman dominsu, suka barsu su huta gajiya. ~Kwanansu biyar da dawowa ya tafi cikin Gembu dan ya duba gidan da Hamma Atiku ya sama mishi, da kuma shago. Gidane mai d'auke sashi uku. D'aya na asalin mai gidanne wanda yake shima police ne, abokin aikin Hamma atikun. Part d'aya na Mai gidanne, wanda yake zaune da matarshi da yaranshi uku, sai kanwarshi budurwa Jamila wacce suke kira Jami. K'abilar mambilawa ne su, amma yawanci da fulatanci suke maganarsu. Sai kuma d'aya part d'in wani ne da matarshi da d'ansu d'aya, asalinshi d'an jigawa ne, aikine ya kawo shi cikin Gembun. Kwana biyu yayi a cikin Gembun ya gama dubawa da kuma tsara duk yanda abubuwan zasu kasance kafin ya koma dorofi. Adda bataso barinsu da zaiyi ba saidai babu yanda ta iya, sbd su a can sun saba, yawanci yaransu idan sun girma sun kawo karfi basu cika zama a gida ba, daga masu tafiya karatu, sai wad'anda zasu bar gida sanadiyyar aikin gwamnati, ko kuma masu tafiya wani garin sana'a. Shima Hamma shehu ba wani zama sosae yakeyi a dorofin ba, yafi zama a camaroun inda yake sana'ar saye da sayarwar shi, wani lokacin kuma ya tafi kano. Ali kaninsu kuma yawancin zamanshi a jalingo ne inda yake karatu, yana kuma had'awa da sana'a idan ya samu hutu, zuma yake sayarwa, daga dorofin yake kawowa jalingo. Sai kuma kaninsu mai biwa Ali wanda bai jima da gama secondry schl. ba, shima yakan bi Hamma shehu camaroun ya saro kifi yazo ya sayar, wani lokacin ma shi Hamma shehun yake aike yaje yayi mishi sarin kaya. Yanzu kuma da Smart zai koma Gembu ya fara nashi sana'ar sai suka bashi shawarar ya d'auki kaninnasu da kuma d'aya daga cikin kannen Hamma Atiku su rika tayashi tafiyar da harkar. Hakan ko akayi dan har Hamma Atiku ya samu musu masauki a gidanshi tunda shi smart bashi da gidan kanshi a wajen. ~Ranar da zasu koma cikin Gembu sun tafi ne cike da kewa, san Deejah tsakaninta da Allah ta dage take ta rabza kuka, zata rabu da Babanta, Adda, Dadayi, Hajja Inna kannenta, da sauran 'yan uwa da dangi da sukayi sabo. Ga kuma Habiba da suka qara shaquwa, dukansu biyu ji suke kamar kada su rabu. Karin abin haushinma bata cikin wad'anda zasuyi musu rakiya, sbd laulayi da take fama dashi. Goggo amarya, amaryar baffansu baban su Hamma Atiku, da Adda Rahina, kanwar Hamma Atiku, Hamma shehu, kasancewar yana gari, sai yusufa suka yi rakiyar. Isan yamma sukayi, suka samu an gama furnishing apartment nasun, duk wani abun buqata an saka, har da kayan kitchen, matar Hamma Atiku ta jera mata, dadai masu rufin asiri. Isarsu ba da jimawa ba su Ali dake gidan Hamma Atiku suka kawo musu abincin da Adda Rabi matar Hamma Atikun ta dafa domin tarbarsu. Sai da dare suka koma gidan Hamma Atikun suka kwana, washe gari suka sake dawowa tare da matar shi suka d'an tayata sake gyaran d'an abunda ba za'a rasa ba. Sukam su Hamma shehu da ya manga ba zama suna can kasuwa tare dasu Ali wajen harkar kasuwanci, dan tun jiya kayakinsu suka iso. Daga kasuwan ya jibgo musu tsarabar da zasu koma dashi, ciki har da na Adda da Mahmudunshi. Dukansu biyu kewar Mahmud sukeyi kasancewar zasu yi nesa dashi. Duk da yaso a basu Mahmud Deejance dai ta tubure kan kada ma ya fara bari maganar taje kunnen manya, dan ita a ganinta a bun da kunya, kuma ya kamata suyiwa adda kara da kawaici duba da irin shaquwar da ke tsakaninta da Mahmud d'in. Sai washe gari suka tarkata suka koma aka bar Deejah da kewa, dan shima uncle smart tun safe ya fita, daga rakiya bai dawo ba. Tana zaune cikin falonta tana bin ko ina da kallo, idonta ya sauqa kan wani enlargement hoton da smart tare da Mahmud, sunyi kyau matuqa tsantsan kamanninsu ya bayyana sosai cikin hoton. Dukansu biyu dariya sukeyi, hakan yasata murmusawa tana dad'a qare musu kallo. Can kuma ta sake bin cikin falon da kallo, ita kad'ai tace Allah mai iko. Tunawa da tayi da irin mansions dain da Uncle smart yake rayuwa cikinsu, cikin birane, nanma bata san sauran ba, biyu kawai ta sani. Sai gashi yanxu ya kare a qauye, kuma cikin one bedroom and palour. Dake shid'in mai tawakkali ne jakan sam baya d'aga mishi hankali, nunawa yake yana alfahari da kasancewar shi a haka. Yasha fad'a mata cewa, rayuwarshi a haka, cikin rashin isasshen wadata ya fiye mishi kwanciyar hankali, tunda gashi cikin familynshi, kuma cikin garinshi na haihuwa. Murmushi tayi tana dad'a jinjina al'amari na ubangiji tare da gode mishi bisa ni'imomin da ya yi mata. A hankali ta mike ta fara kewaye apartment d'in nasu, sbd sake tantance yanda gurin yake. Babu abinda yafi burgeta irin d'an madaidaicin kitchen d'in dake had'a da corridor d'insu, sai kuma net d'in da aka kewaye kofar su dashi. Tana tsaye tana bin kitchen d'in da kallo ta jiyo sallamar mace daga kofar net d'in. Amsa sallamar tayi tare da bud'ewa. Wata budurwa ta gani rike da hanun wani d'an karamin yaronda bazai wuce shekaru biyu ba. Kallon yaron tayi tana tuna mahmudunta dan baza wuci sa'o'in juna ba. "Sannu da zuwa." Tace tana matsawa daga hanya sbd budurwar ta samu ta shigo. Shigowa budurwa tayi tana cewa "Yauwa sannu." Cikin falon suka shiga dukansu suka yiwa kansu mazauni kan kujerun dake cikin falon. Saida Deejah ta mikawa yaron hanu tana kiranshi, ya tashi yazo ta d'aga shi ta d'orashi saman cinyarta kafin suka fara gaisawa. "Sunana Jamila, amma ana kira na Jami, yara kuwa suna cemin ainty Jami. Anan gidan nake, ina zaune da yayana da matarshi, sai yaransu uku." "Ayya, ni kuma sunana Hadiza." Deejah ta fad'a a takaice tana murmushi. Ajiye yaron tayi kan kujera ta mike taje ta kawo mata abin motsa baki, ta dawo ta zauna. Zama suka d'anyi shiru na wani d'an lokaci cikin yanayin baqunta, kafin daga bisani Deejah tace "Yanzu akwai yara cikin gidan najishi shiru ? " "Sun tafi makaranta, Mmnsu da Bbnsu kuma duk sun tafi aiki shi yasa kikaji gidan shiru, ni d'in ma dan na qare karatunane cikin kwanan nan na dawo shi yasa kka sameni a gida." "Ayya, Allah ya taimaka." Deejah tace tana wasa da hanun yaron. Ci gaba jami da yi da cewa "Saidai akwai wasu neigbours anan kusa da part d'inki Mmn Ahmad, ta tafi koyon d'inki ne, bata cika zama ba itama." "To fah ya Allah ya had'ani da fad'i ba'a tambayeki ba." Deejah ta tuna hakan a ranta. Shiru suka kumayi na wasu 'yan lokuta kafin Deejah ta d'ago kanta dan ta kalli abokiyar hirar tata. Kurr taga Jami ta kure hoton Uncle smart dake hanyar shiga d'akinsu da ido tana mishi kallon kurilla..... *Toh, jama'a ga fa Deejah sarauniyar 'yan kunya cikin gidan haya, ko yaya rayuwar zata kasance ? "* ** TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* * Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern. * *27*&28 ~Sanye yake da ash coloured suit ya hakimce kan wata farar kujera, bayan shi korayen shuke shuke na furanni masu d'an surkin yellow . Ga dukkan alamu gurin hutawa ne dan da ka ganshi zaka gane yana cikin nishad'i sbd fiskarshi dake d'auke da kayatacciyar murmushi. Sosai taga kayan sun amshe shi, snn ba karamin kyau da kwarjini yayi mata ba. "Wad'annan mutane akwai kyau, har na rasa wanda ya fi kyau tsakanin matar da mijin." Abinda take rayawa a ranta kenan. Niko nace asalin fulanin gembu nefa ba surki, ba kuma muna fulani bane lol. Kallonta ta maida kan Deejah, wanda yayi daidai da ita Deejar ma ta kuma kallon ta suka had'a idanu. Wata 'yar karamar kunya taji ta lullub'e sai tayi kokarin mazewa. Ta gyara zama zatayi halinnata, wato magana, suka tsinkayo sallamar uncle smart a kofar falon. A tare suka amsa sallamar dukansu biyu kuma idanunsu a kanshi. Tsaye yake rike da bakar leda mai d'an girma a hanunshi. Yauma sanye yake da army green coloured suit. Sosae ya dad'a haska fatarshi, fiskarshi cike da annuri, yake bin Deejah da kallo. Ganin haka yasata ajiye yaron dake kan cinyarta ta qarasa kusa da shi a kunyace. Kasa kasa tace "Sannu da dawowa uncle." Tare da kai hanu tana karb'ar ledar hanunshi. Matsowa ya dad'a yi kusa da ita har jikinsu na gogan juna, yana mai shaqan qamshinta tare da d'an lumshe idanu. "Kwalliyar nan tayi min kyau, mummy fad'a min da me zan biya" Rufe idonta tayi da hanunta d'aya tana 'yar dariyar qasa qasa. "Ina kika samo mana yaro ? " Ya sake tambaya a tausashe. "D'an makwabtanmu ne." Ta fad'a da sauri tana nuna inda Jami ke zaune. Kallon gurin yayi suka had'a ido da Jami tayi saurin kawar da idonta. Rab'a shi Deejah take kokarin yi zata fita ya riko hanunta. "Ina zakije kuma ? " "Kitchen." Tace tana nuni da ledar hanunta alamun shi zata kai can. Gyad'a mata kai yayi ya shigo ita kuma ta wuce ta karasa ta ajiye a inda ya dace kafin ta juyo. Rusunawa Jami tayi ta gaisheshi ya amsa hankalinshi na kan yaron. Kusa da yaron ya qarasa ya d'an sunkuya ya shafi kanshi yace. "Ya sunanka small boy." "Junior." Ya bashi amsa. "Good, junior zamu zauna anan tare ko." Maqe kafad'arshi yayi yana kallon auntynshi. "Me yasa junior ? " Da sauri junior ya diro daga kan kujera yanufi gurin auntynshi ganin ta mike tsaye. Da kallo yabi yaron yana murmushi, sbd ya tuna mishi Mahmud d'inshi. "Sai anjima aunty Hadiza." Jami ta fad'a tana riko hanun junior sukayi hanyar kofa. "Na gode, aunty Jami, ki gaida su aunty sai na shigo." *Maiduguri* ~Ma sha, Allah, al'amura sun fara sauqi, saidai rashin Heema a zcyr masoyanta abu ne wanda manta shi zaiyi wuya. Scorpion a yanzu duk ya yi sanyi ya canza kamar ba shine wnn mai kazar kazar d'inba. A koda yaushe Heema na cikin ranshi dan ta zama wata b'angare na rayuwarshi. Sabo ne ea shaquwa wanda suka yishi cikin kankanin lokaci amma jinta yake kamar sun d'ibi shekaru suna tare. A b'angare guda kuma kewar abokinshi wanda abotarsu ya rikid'e ya koma 'yan uwantaka, wato smart ya kasa barinshi. Kasancewar shi a kusa dashi yakan saukaka mishi tunani da damuwa, sbd a ko da yaushe kokari yakeyi ya kwantar mishi da hankali ta hanyar bashi shawarwari masu amfani. Duk a yanzunma kusan kullum sai sun gaisa ya kuma kara da kwantar mishi da hankali amma fa yafi gane suna taren. A b'angaren Naseer kuwa matsaloli biyu ne suka sha kanshi. Na farko , halin da abokinshi yake ciki, sai kuma matsalar fatima, sbd har yanzu bata warware daga damuwar rashi kawarta, amiyarta kuma 'yar uwarta. Sau tari, haka kawai sai yaji ta amsa kira tace mishi Heema ce ta kirata, ko kuwa tayi ta waige waige kamar wata mai neman wani abu. Idan aka tambayeta kuwa sai tace wai "Ba, a ji Heemah ta ce Teemah ba ? " Haka dai yake binta da nasiha da ban haquri qarshe sai da ya had'a da sanar ra iyayenta akatsaya mata da addu'a aka samu sauqin abun. *Gembu* Zaune take cikin d'an madaidaicin kitchen d'inta tana gyaran ganyen kumbi wanda zata yi miyar dare dashi. Aiki takeyi amma a hankali take karanta wasu daga surorin da ta haddace cikin Qur'ani mai girma. Gefe guda kuma stove d'inta ke ci da wuta kad'an kad'an wanda ta d'aura ruwan tuwo. Sallamar Jami ce yasata d'agowa ta kalleta, saida takai aya ta amsa sallamar kafin Jamin ta qaraso cikin kitchen d'in. Bin ko ina takeyi da kallo yanda komai yake tsaf tsaf tana yaba tsafta irin na Deejah. Murmushi Deejah ta sakar mata ita ma ta mayar mata kafin tace. "Sannu da shigowa aunty Jami." "Sannu da aiki aunty Hadiza." Ta bata amsa, tana binta da kallo ganin yanda kwalliyar da tayi na bakin yadin material mai adon furanni kalar ruwan goro ya amshi jikinta, Kasancewarta fara. D'inkin riga da skirt ne sun zana mata d'as a jikinta , ga kuma simple make up data yiwa fiskarta ya dad'a fito da sirrin kyaunta. Uwa uba kamshin turarenta da yakeyi mata dad'i , kusanma abinda ya sa take yawan shigowa wajenta kenan. Ga turaren d'akinta ma kamshinsa dabanne. Suna yawa amfani da turaren wuta ko na tsinke, da room freshner. Amma itakam bata tab'a cin karo da kamshi mai dad'i irin na d'akin Deejah ba. Hhhhh, Jami turaren daga maiduguri ne matattarar kamshi, nima so nake in samu mai turo min na more kamshin jiki da na d'aki. saidai ni nawa na kaduna nake samu. 'Yan maiduguri sunce basu sanni ba. *Gaisuwa ta musamman da jinjina gareku mutan Maiduguri gidan k'amshi, Inayinku sosae wollah* "Aunty Jami zauna mana." Cewar Deejah tana tura mata 'Yar karamar kujerar roba. "Nanma yayi aunty Hadiza." Tace tana dab'ashewa a qasa, kan leda carpet din dake malale a tsakiyar kitchen d'in. Da sauri Deejah tace "A'a wlh, ki tashi ki zauna a saman zaifi dan zaman qasan ba kyau, ga kuma sanyi.." "Ba komai nikam na saba." Tace mata ba tare da wata damuwa ba. "Amma kuma ai babu kyau, mu a gidanmu ba 'a barinmu mu zauna haka a kasa, dole ko akan kujera, ko mu nad'e zani mu zauna akai, ko duk wani abu dai dazai hana sanyi shiga jikinmu dan hakan yana wa macce illah. "Ban sani bane aunty Hadiza, na gode." Tace tare da jawo kujerar ta zauna akai, snn tasa hanu tana tayata tsinke ganyen. Tafasar da taga ruwanta nayi ne yasata tashi ta bud'e robar da ta zuba wankakiyyar farar shinkafarta ta juye cikin tukunyar ta rufe. Attarugun gembu mai kalar yellow ta d'auko kwaya d'aya dan zafi ne dashi, ga kuma kamshi fikin girki, ta had'a da qatuwar albasa qwaya d'aya ta saka cikin wata robar ta wanke. Kafin ta kare wankewa Jami ta jawo 'yar k'aramar turmi da ta gani a kife ta ajiye a gabanta. Ita ta daka mata tsaf, kafin ta kwashe ta saka cikin wata 'yar k'aramar kwanon silver. "Aunty Hadiza kinsan wani abu ? "Kamshin turarenki yana min dad'i wlh, harda na d'akinki." "Allah ? " Tace tana 'yar murmushi kafin ta qara da "zan baki idan na gama." "Yawwa, na gode." Ta fad'a cikin nuna jin dad'inta. "Tun ban bakin ba ? " Ta tambaya tana mata daria." "Ai tunda kikace zaki bani nasan zaki baninne ai." Ta amsa itama tana dariyar. "Ina junior." "Yana wajen aunty Tala(Mamanshi.)" "Yau tun safe bamu had'u da ita ba, gwara Mmn Ahmad ma mun gaisa d'azu." "Eh, wlh, haka itama tace." Shiru yad'an biyo baya, saidai ita Jami duk abinda Deejah takeyi kallonta takeyi a fakaice. Nitsuwar Deejah ba karamin burgeta yakeyi ba. Kamar wacce aka fisgo maganar daga bakinta tace. "Gaskiya aunty Hadiza ba qaramin dacewa kukayi da Uncle ba, dukanku biyu ba baya wajen kyau, ga tsafta zanso inga yaran da zaku haifa." "Hmmmm." Kawai Deejah tace, taci gaba da b'are magginta. "Kuma kin san me ? " Ba tare da ta jira Deejah ta amsa ba tace. "Kina d'aya daga cikin matan da sukayi sa'ar miji, wlh, Uncle, ga kyau, ga nitsuwa, kuma yana sonki sosai. Kinga ni a da bani da sha'awar aure da wuri sai na had'a degree, amma a yanzu inda zan sami miji kamar uncle, wlh aurena zanyi." Kallota Deejah tayi da mamakin furucinta. Ta samu miji kamar uncle, to me kama dashi ko kuma mai irin halinshi ? Ta tambayi kanta da kanta. To koma dai shi karan kansh uncle din take nufi ? Ganin kallon da Deejah take mata ne yasata daburcewa take kuma ta gane b'aramb'aramar da tayi tafara neman hanyar da zata gyara kalamanta da cewa.... * Sunan wani littafi wai sub'ul da baka* *Dakyar na had'a wlh, tun shekaran jiya nayi typing ya goge, gaba d'ayan sai naji jikina y mutu da typing d'in, wnn dimnma inaayi yana hooking.* *F.O.W * * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* * *Impacting Valuable knowledge and entertainment is our concern * *28* ~"Aunty Hadiza, ina ta damunki da surutu ko ? Kiyi hakuri haka nake, ban iya ganin abu inyi shiru ba, halinane." "Ba komai ." Kawai Deejah tace, taci gaba da aikinta, tana kuma kokarin yakice zargin Jami da zcyrta ke neman cusa mata. Ba da jimawa ba Jamin ta tafi, ita kuma ta ci gaba da ayyukanta. Sai kusan magriba ta gama. Saida ta kimtsa kitchen din tsaf ta shiga d'akinta ta d'auko turaren ta tsiyaya mata cikin wata yar madaidaiciyar kwalba, snn ta d'ebo turaren wuta ta kasa kashi uku ta zuzzuba su cikin leda, ta had'a cikin bakar leda, ta fito. Ta cikin kitchen din ta biya ta d'auko 'yar cooler da ta sawa Jami abinci ta fito dashi. Kofar su Jamin ta shiga da sallama. A mutunce suka gaisa da aunty Tala, snn ta ajiyewa Jami cooler a kusa da ita. "Haba aunty Hadiza ,ke kullum sai kin kawo ma mutum abinci, zaki sa na daina shiga kofar ki fa." Murmushi tayi tace "Idan baki shiga bama ni zan shigo ai." Kullin turaren wuta guda ta cire ta mikawa aunty Tala, snn ta ciro guda ta rike a hanunta ta mikawa Jami bakar leda mai d'auke da turaren jiki da na wutan. Godiya sukayi ta mata, har aunty Tala na cewa, ba banza ba taji kamshi ya bud'ad'e part din nasu daga shigowarta, ashe da tsaraba tazo musu. Murmushi kawai tayi ta sallamesu ta fita. Daga nan ta wuce kofar Mmn Ahmad, ta kai mata nata, itama da godiyan ta bita snn ta dawo ta shiga wanka. Kasancewar yanzu baya dawowa da wuri sai karfe tara yake shigowa sbd karatun da yake d'auka a masallaci wajen wani malami, duk bayan sallar isha'i. Film ta kunna Tv yana ta karad'i amma ita sam ba anan hankalinta yake ba. Tunaninta ya tafi ne kan rayuwarta ta baya, kaddarar da ta afkawa rayuwarta, take ta tunani, da yanda Allah ya juya al'amarin ya zamo alkhairi a rayuwarta da na iyayenta. Tabbas ta yarda idan mummunan kaddara ya sameka ka fawwalawa Allah al'amarinka kayi hakuri, yakan juye ya zamo alkhairi a rayuwarka. Gashi yanzu ta sanadiyyar mummunar kaddarar da ta sameta Allah ya bayyano musu da d'an uwansu, kuma masoyinta mijinta a halin yanzu, wanda ko da wasa bata tab'a tunanin hakan ba. A rayuwarta bata tab'a tunanin zata so wani bayan Hamma shehu ba, sai gashi Allah ya juya al'amarinshi cikin kankanin lokaci. Kadddararta shi ya zamo sanadiiyar warakar Adda wacce take a matsayin mahaifiya a gareta. A hankali tunaninta ya gangaro kan zuwansu Maiduguri da abubbuwan da suka faru a can. Tunanin mutuwar Faheema ya ziyarceta lokaci guda. Allahu akbar, rayuwa kenan. D'an adam ba 'a bakin komai yake ba. Yanzu zaka ganshi da lafiyarshi anjima sai kaji yana cikin mawuyacin hali na rashin lafiya, ko kuma ace kwata kwata ma baya raye ya tafi ya bar duniyar.. Duk wanda bai ji tsoron Allah ba yayi asara. Duk wanda ya d'auki duniya da rayuwa da zafi, yayi aikin banza. Share hawayen da suka zubo mata tayi tana jin wani irin tsoron Allah yana shigarta. Ji takeyi kamar kwanakinta sun kare itama. Jinta takeyi kamar mutuwa zaizo ya d'auketa a yanzunnan. Cancakat taji an d'agata kamar wata babyn roba. Tsabar razana wani irin d'auke numfashi tayi harda mimmikewa. A hankali ta sauke numfashinta tana kalmar shahada idanunta a rufe. Shi kanshi smart saida ya tsorata da abinda yaga tayi. Maidata yayi ya kwantar a hankali ya kafa guiwowinshi duka biyu a qasa yana kallon fiskarta, sai motsa baki takeyi tana salati. "Mummy lafiya ? " Sai a snn ta bud'e idanunta tana kallonshi a raunane. "Uncle." Ta kira shi a sanyaye. "Menene ? " Ya sake tambaya. Kokarin yunkurawa takeyi duk jikinta yayi sanyi, ya taimaka mata ta tashi yana kuma binta da kallon son jin qarin bayani. 'Yar murmushi ta sakar mishi tace "Nayi tsammanin na mutu ne fa." "Kamar yaya ? " Ya tambaya da mamaki a fiskarshi. Tunani Faheemah nakeyi da yanayin rayuwa da mutuwa sai kuma naji anyi sama dani shine na kama kalmar shahada ko zan samu na cika dashi a bakina. Dariya ya fashe dashi har ya zauna a qasa yana kallonta. "Allah yayi matsoraciya anan, haka akace miki ake mutuwar ? " Zumb'uro baki tayi ganin irin dariyar da yake mata tace " shine baza kayi sallama ba." "Sallama na nawa kuma, nayi har sau uku ba'a amsa min ba." "To ni na sani ne, tunda ba mutuwar na tab'ayi ba." Tana gama fad'a ta mike tayi cikin d'aki dan had'a mishi ruwan wanka. Shi kuwa sa kallo ya bita yana dariya kasa kasa tare da girgiza kai. Ita kanta saida ta shiga ciki abun ya bata dariya, aiko ta tsaya taci dariyarta ma'ishi kafin ta had'a ruwan wankan ta fito, amma fa sai istigfari take tayi a zcyrta sbd yanda tsoron tunanin mutuwar ya shigeta. Saida suka qare cin abinci yake fad'a mata zainab kanwar scorpion ta kirashi d'azu tace tana ta kiranta bata d'auka ba. Sai a snn ta tuna ta baro wayar a kitchen taje ta d'auko. Maganar business d'inta na kayan kamshi ya mata dan zainaba din ta gaya mishi komai. Nan yake tambayarta wa take ganin zai tsaya mata kan sana'ar . Ba tare da b'ata lokaci ba tace mishi "Yusufa." Bayan shud'ewar wasu 'yan lokuta, ta jefo mishi tambayar dake damunta a zcy. "Uncle dan Allah, mutanen nan duka aka kama ne ko da saura. Kamar bai gane me take nufi ba yace "Wasu mutane kenan." "Wad'anda suka kashe Faheema." "Duka ne." Ya bata amsa a takaice, duk da yasan ba hakan bane, shi dai so yake a bar zancen dan ya fahimci ta sa abin a ranta sosai. "Ina nufin dukansu 'yan kungiyar da suka saura kenan ? " "Eh." Ya kuma bata gajeren amsa. "Amma naji ance su shida kawai aka kama, dama iyakacinsu kenan ? " Sosae ya maida hankalinshi gareta yace "Nikam mummy yaushe kika zama 'yar jarida ne ? " "Hmmm, Uncle ba maganar jarida bane, na ji Fatima tace sunce harda kai suke nema su kashe." "Idan kwanaki na basu qare ba ya suka iya dani khadija, ai ba lokacin kawai suka fara kawo min hari ba, Allah bai basu iko bane. Ko su scorpion da aka ritsasu har cikin gidajensu kinga sun mutu ne ? Faheema da kika ga suka kashe kwananta ne ya kare, kuma Allah ya nufa sune ajalinta, sbd haka ki daina saka tunaninsu a zcyrki su hana ki kwanciyar hankali a banza. Babu mai mutuwa sai lokacinshi yayi." Jinjina kanta tayi amma can kasan ranta tana jina tsoron al'amarin duk lokacin da tunanin hakan ya fad'o mata, gani take kamar mutanen suna tare dasu, kuma zasu iya b'ullowa a ko wani lokaci. Sai washe gari ta kira aunty zainab suka qara tattaunawa kan maganar business d'inta, daga nan ta kira su Fatima ma suka gaggaisa. *2 days later* Tun da ta suka gama karin safe ta fara had'a kayankinsu masu datti tana tarawa gu d'aya. Tana gamawa ta tattara takai ta baya gurin da rijiyar gidan yake. Ganinshi zaune kamar baida niyar fita yasa ta tambayeshi "Uncle yau baza ka fita bane ? " "Ina son sanin abunda kike shirin yi ne tukuna." "Wankin kayanmu zanyi kada su taru suyi yawa." Tabb, wata sabuwa, yace a ranshi. Shi ya ma manta ma da wani abu waishi wanki tsabar gata. A can yana da masu yi mishi, dawowarshi mahaifarshi kuwa saidai yaga an wanko an kawo mishi, wnn aikin d'an uwanshi Hamma shehu ne. Mikewa yayi ya shiga cikin d'akin ba tare da ya yi wata magana ba. Tana ta aikin jan ruwa a rijiya yazo ya tsaya yana kallon kayan da ta tara hannayenshi rike da waist d'inshi. Saida ta gama jan ruwan ta juyo ta ganshi ya canza kayanshi zuwa k'ananan kaya na shan iska. "Me zakayi ? " Ta tambayeshi fiskarta d'auke da mamaki. "Tayaki zanyi ko baki so ? " Ya fad'a yana karasawa gun kayan. Raba kayan kashi biyu yayi, ya fidda nashi daban ya ajiye a gefe. "Da naki zamu fara." "Naka dai." Ta fad'a tana kai hanu kan kayankinshi. "Wanki zamuyi ko musu ? " Ya fad'a yana tsareta da ido yayin da yasa hanu ya dafe kayan. Batayi magana ba, ta koma kan kayanta ta fara jikawa. Ita take wankin farko shi yayi na biyu idan tasa a ruwa na uku ta sake wankewa, sai yayi na karshe yaje ya shanya. Likis yaji hannayenshi sun gaji har wani tsami tsami suke mishi, amma ya dage yaci gaba da tayata suna hirarsu gwanin sha'awa. Can yaji hannayen suna mishi ya d'aga yana dubawa. Kamar wanda aka caccake hanun da allura ko kusa haka yaga hannayen sun b'ubb'ule sunyi ja. Ba wai wanki ne ba iya ba, ko bai tab'a yi ba, rabonshi da wankinne har ya manta, yau kuma da yayi sai ya zame mishi matsala. D'agowan da zatayi ta ganshi yana kallon hannayen, yana tab'e fiska. Kusa dashi ta qarasa kafin taga abunda yake kallo ya sunkuya ya d'auki zani ya nufi gurin shanya tamkar bai ganta ba. Rigarshi ta kamo ta jawoshi kad'an ya dawo baya. "Me ya samu hanun ? " "Ba komai, me kika gani ? " Ya mayar mata da tambayar yana gyara fiskarshi kamar ba yanzu ya gama yamutsa fiskar ba. "Muga hanun to." "Nace miki ba komai, ci gaba da aikinki, idan na gama shanya baki qarasa ba ni dake ne." Ya karasa maganarshi tare da yarfa mata ruwa a fiska. Kallonshi takeyi cikin rashin yarda shi kuma yaqi bari taga hanun. Muryar Jami suka tsinkayo kusa dasu tana cewa . "Uncle ka bari zan tayata mu qarasa." Kallo ta dukansu biyu sukayi dan basu san lokacin da ta iso wajen ba. Abinda basu sani ba shine, ta jima tsaye daga nesa tana hango duk abunda sukeyi. Kafin su ankara har tasa hanu ta riko zanin dake hanunshi ta kuma cewa "Kawo zamu qarasa." Sakar mata zanin yayi da sauri ya koma gun kayanshi da basu fara wankewa ba ya tattara ya tafi dasu. Tsabar yanda abunda Jami tayi ya tab'a Deejah, kasa magana tayi sai kawai ta duka taci gaba da wankinta. Itako Jami ko a jikinta ta fara tayata cikin qwarewa tana kuma janta da hira. Basu wani dad'e sosai ba suka gama , suna tattara containers d'in da sukayi aiki dasu sai ga Ali, qanin smart. Cikin Fara'a ta shiga gaisheshi da tambayar labarin mutan gidan Hamma Atiku d'aya bayan d'aya, kamar dai yadda kuka san gaisuwar Fulani take. Itama Jami ta gaisheshi kafin ya juya ya bar wajen. Kamar ko tana jira tace "Amma wnn qanin uncle ne ko ? " "Uhmm." Kawai Deejah tace mata, a ranta tana cewa, zata fara halin. "Ya naji kika ce mishi Ya Ali ? " "Yayana ne." Tace a takaice. "Dama auren gida kukayi da uncle ? " Bata jira amsartaba ta kuma cewa "Woww, gaskiya Familynku kyawawa ne.".... *Um um fa, qawar 'Yar Baiwa, ki kiyayi ranar da zaki sha marin Deejah babu ruwana, saidai qawarki ta kwaceki duk ranar da kika shiga hanunta.* *Wnn shafin kyautace gareki, 'Yar Baiwa, Gital's Nvl grp, Allah yabar qawancenku da Jami* * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* * Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern. * *29*& ~Ba tare da tace mata komai ba ta gama had'awa ta fara tattarawa. Zuwa yanzu ta fara sabawa da halin Deejah na shariya, wani lokacin zatayi ta zuba mata surutu , ta jera mata tambayoyi amma idan ta tashi amsawa sai ta amsa mata a takaice. Shi yasa bata damuwa dan ta fara sabawa da wnn halin, ita kuwa kasancewarta mai son yawar magana abun sam baya damunta, indai zata nitsu ta saurareta shi kenan ta gama mata komai. Tare suka shigar da kayakin, dadai lokacin da Ali yake fitowa hanunshi dauke da kayan wanshi zai kai mishi wajen wanki. Sallama sukayi ya wuce ita kuma ta shiga ciki yayin da Jami ta wuce part d'insu. Ba yabo ba fallasa tace "Uncle me yasa ka tattara kayakinka baka bari na wanke ba ? " "Gaskiya khadijah, aikin zaiyi yawa, kuma ma sanyin ruwan yayi yawa zai iya cutarwa." Ya bata amsa yana kallon yanayinta, dan ya lura kamar ranta a d'an b'ace yake, duk kokarin b'oyewa kuwa da takeyi saida ya fahimci hakan. "Me ya b'ata miki rai kuma mummy ? " "Ba komai." Ta fad'a tana lafewa cikin kujera. "Indai dan wanki ne, gwara ki saki ranki dan nakin ma baxa ki qara yi da kanki ba." Ya fad'a yana nufar hanyar fita, dan shi sam bai kawo komai game da batun Jami ba. Addu'ar da ta saba yi mishi idan zai fita tayi mishi saidai yau ko 'yar guntuwar rakiyar da takeyi mishi bai samu ba. Bayan fitanshi ta tashi ta kama 'yan aikace aikacen ta tana kokarin yakice tunanin al'amari Jami a ranta. Sai dare Jami ta sake shigo mata sanin cewa maigidan baya dawowa gida sai karfe taran dare. Wayar Deejah dake kan kujera ta sa hanu ta d'auka ta fara danne danne suna hira. Can ta shiga cikin gallery tana kallon pictures. Mostly hotunan mutanen gidansu ne, sai na su aunty Zainab, Faheema, Fateema da ss. Ba hoton da yafi d'aukan hankalinta irin hoton da taga na uncle da Hamma shehu, da kuma Mahmud. Ta jima tana kallon hotunan kafin ta fara sana'ar tata. D'aya bayan d'aya take scrolling din hotunan tana tambayarta game da wad'anda suke ciki. Har tazo kan Hoton Mahmud da Babanayenshi. "Yauwa aunty Hadiza wnn yaron d'an waye ? " Ta fad'a nuna Mahmud, ta sake kallon hotonsu da ke manne jikin bango da babanshi wanda akayi enlarging. Wani duumm, Deejah taji, ta rasa wacce amsa xata bata, ta fad'a mata gaskiya ko ta shareta. Can tace "Dan yayanmune." "Amma uncle yana son yaron sosai, kuma kamarsu har ta b'aci." ""Hmm." Kawai tace. "Ina Babanshi anan ? " Ta sake jefo mata tambayar." "Babu hotonshi anan." Shiru tayi tana sake nazarin yawan kamannin da ta gani tsakanin d'a da uban." Can tace . "Aunty Hadiza, ko yaron uncle ne ? Ina Mamanshi ? " "Wayyo Allahna." Deejah ta fad'a tana numfarfashi, tare da zamewa tana kwanciya kan three sitter. "Me ya faru ? " Jami ta tambayeta. "Kanta ta nuna mata tana rintse idanu kamar gaske. "Sannu, kina da magani ko in kawo miki ? " "Ina dashi." Tace a sanyaye kamar marar lafiyar gaske." "A ina yake in d'auko miki ? " "Barshi kawai, idan na tashi zan d'auko, ina ga ma har da bacci." "Ayya to, yi baccin aunty Hadiza ko zai sakeki, Allah ya sawwake, idan akwai wani damuwa ki kirani kinji." Ta fad'a cikin nuna tausayawa. Kanta ta gyad'a mata tana lumshe idanunta. A sanyaye ta tashi tayi hanyar fita bayan ta ajiye mata wayar tana mata saida safe. Kad'an ta bud'e idanunta tana binta da kallo. Saida ta ida fita snn ta bud'esu tarwai tana sauqe ajiyar zcy. Tunani ta farayi, game da halin Jami. Gaskiya tana ga zcy da shaid'an ne kawai yake raya mata mugun tunani a kan Jami. Amma da alama kamar yadda ta fad'a halin tane yawar magana da yabawa abinda ya mata kyau. Meye laifin wanda ya nuna yana sonka ya damu da damuwarka. Tambayar da zcyrta ta jefo mata kenan. Take ta kuduri niyyar kaucewa duk wata zargi ko mummunan tunani da zcyrta zai raya mata kan Jami. Saida ta yanke wa kanta cewa baza ta sake yarda Jami ta shigo ta sameta a d'akinta dan suyi hira ba, saidai ta rika zuwa kofar su Jamin suyi hiran har da su aunty Tala da Mmn Ahmad kamar yadda taga sunayi, ko dan sbd gujewa tambayoyin Jami. ~ Kamar yadda ta kudurta a ranta kuwa hakan ya kasance dan yanzu da tayi sallar isha'i ta gama dukan addu'ointa take zura rigar sanyinta ta fita hira, gurin su aunty Tala. Sosai kuma take jin dad'in hira da su dan aunty Tala akwai bada dariya. Duk da Jami ake hirar, kuma dukansu sun nuna jin dad'in shiga cikinsu da takeyi a yi hira da ita. Saidai ta fannin gogan fitar hirar tata tazo mishi da wani salo na daban da bai saba da hakan ba. Dalili kuwa shine, muddin ya dawo tana kofarsu Jami, to ko kallonshi batayi. Ba kamar su aunty Tala da Mmn Ahmad ba, da mazajensu na shigowa suke zuwa su marabcesu, idan da abunda suka rike su karb'a musu, wanda ita Deejah a gurin ta tana ganin hakan a matsayin bushewar ido, da rashin kunya. Asalima ita bata nuna alamun tasan ya dawo. Koda kuwa yana rike da abu a hanunshine saidai Jami sarkin karambani taje ta karb'eshi. Tun yana hana Jamin har ta kai ga idan tazo karb'a yana bata. Ita kuwa Jami babu abinda yake burgeta dashi kamar godiyar da yake yi mata idan ta karb'i abu a hanunshi ta shigar mishi. Duk da godiya halinshi ne, ta sha jin yana cewa aunty Hadiza "Thank u." amma idan ya gode mata jinta takeyi on top. Har takai Aunty Tala tana mata maganar ta tashi taje ga mijinta idan ya dawo, amma ita sam bata iyawa, har sai an watse hiran take komawa part d'insu. Tun yana nuna mata damuwarshi kan hakan har abun yabi jikinshi ya saba. Itako Jami har ya kasance idan taga bai dawo da wuri ba ta rika tambayar Deejah kenan ko lafiya ? Ko kuwa tayi ta matsa mata kan ta kira taji abu da ya hana shi dawowa. Saida Aunty Tala ta fara takawa Jami birki snn ta sassauta nuna damuwarta a kanshi. Dukansu wautarta suke gani amma da yake sun fahimci hakan kamar al'adarsu ce, sai suka barta da halinta. ••• ••• ••• Kamar yanda ya alkawarta wa zcyrta zai nema mata makaranta ta qarasa, Kasancewar shi yaji labarin ta kusa gama sec sch. Kaddara ta fada mata. Hakan kuwa akayi, ya sama mata gurbin karatu a wani sec. Sch. da basu da nisa sosai dashi. Sosai taji dad'in hakan ta kuma nuna murna da jin dad'inta. A kwanakin suka je Dorofi, sukayi ta ziyara. Sati guda sukayi suka wuce Nguroje sukayi kwana biyu kafin suka dawo. Jami kamar Zata d'agata sama sbd murnar dawowarta, wani oyoyon da ta mata saida suka bawa mutanen gidan dariya. Washe gari ta basu tsarabar da ta kawo musu, sai yabawa da godiya suke mata. Bayan dawowarta da kwana biyu Yusufa ya zo Gembu saboda maganar business dinta. Yanda suka tsara abun, shine, za a turo da kayan kamshin daga Maidugurin zuwa jalingo, shi kuma zaije can jalingon ya d'auko daga can ya kawo Gembu. Shago musamman suka bud'e snn tana ajiye wasu a gida. Ba laifi kuma suna samun ciniki dadai gwargwado. ~ Cikin jin dad'i da kwanciyar hankali ta fara zuwa makaranta. Sosai take maida hankalinta kan karatunta. Asubanci takeyi ta d'aura musu brkfast da kuma abincin rana. Idan ta dawo daga makaranta kuma taci abinci ta huta sai ta d'aura na dare, wanda kusan kullum tare da Jami suke aikin. Wani lokacinma idan ganye smart ya kawo kafin ta dawo Jami take gyarawa , dan zuwa yanzu karb'awa uncle kaya a gurin Jami ya zame mata jiki saidai idan bata ga shigowarshi ba. Shi kuma dama duk bayan sallar azahar yake dawowa gida ya d'an tab'a bacci zuwa la'asar ya koma gurin kasuwancinsa. Mutunci sosai akeyi tsakanin Jami da Deejah. Turare jiki da na d'aki kuwa kyautansu take musu basai sun saya ba. Aunty Tala ko har talla take kai mata gurin aikinta, wani lokacin har gida ake zuwa saye, dan ba karya ana yin had'in babu ha'inci. ••• ••• ••• Yau farin ciki suka tashi dashi saboda samun labarin haihuwar Habiba. Murna Deejah takeyi ko ita ta haihu iyakaci. Abu d'aya ya mata cikas, makaranta. Sai ana jibi suna suka kama hanya, har da Jami da tace itama zata bisu, dakyar wanta ya yarda ya barta. Aiko taga karamci da mutuntawa a gurin mitan dorofi, su Habiba da Fa'i kuwa sun sha surutu da tambayoyi. Da yake fa'i ma gwana ce wajen surutu sai ta samu abokiyar yi. Sosai ta sake a cikinsu kamar dama can ta sansu. Mamaki tayi matuka da taji cewar Mahmud d'an Deejah ne. Ba karamin jinjina zurfin cikin Deejah tayi a ranta ba, sbd ko da wasa bata tab'a nuna mata alamun hakan ba. Saidai fa tayi mamaki kasancewar ganin sabbin ma'aurata takeyi musu amma taji har suna da kamar Mahmud. Lallai Uncle ya cika namijin da kowacce mace zatayi burin kasancewa dashi, dan indai ta Deejah ce dunkum d'innan wacce kunya yayi wa katutu da wannan tarairaya tuni ya kau. Take taji kima da darajar uncle smart ya qaru a idanunta, har tana ganin samun miji mai irin halinshi zaiyi wuya. Mahmud kuma wani ji dashi takeyi kamar ta had'iyeshi, sai wani nan nan takeyi dashi. Tun yana kin sakin jiki da ita har ya fara sakewa. Son da take nunawa Mahmud ya bata matsayi na musamman a gurin mutanen gidan harma da uban gayyan. Deejah kuwa dama tasan Jami maisonta ne da duk wani abu da ya danganceta, sbd haka mutuncin Jami ya dad'a karuwa a idanunta. Kwanaki hud'u sukayi suka dawo inda ita kuma Habiba aka wuce da ita nguroje wankan gida. Yarinya dai taci sunan Hajja inna (Fad'imatu.) Itama kuma Hajjan suke ce mata. Komawarsu da wata guda Fa'i ma ta haihu. Wnn karo ita da matar Hamma Atiku suka tafi. Shi kuma smart sun tafi cotonou sarin kaya. Yadda Jami ta nuna damuwar rashin ganin uncle da Deejah ta kira ta, dan tasan ba tare suka tafi ba. Abun sosai ya sosa ran Deejah, saidai bata nuna mata hakan ba, ta dai sanar da ita shima yayi tafiya ne. Hira sosai sukayi tayi tana ta tambayar Deejah mutanen gida d'aya bayan d'aya, tana kuma cewa a gaishesu, har cewa tayi idan zata dawo ta zo mata da Mahmudu. Amsa mata da to kawai Deejah tayi amma tasan ko da wasa bazata fara ce musu su bata Mahmud ta tafi dashi ba. ••• ••• ••• Kamar yanda lokaci yake gudu , haka cikin iko da hikima na Ubangiji Deejah ta fara zana jarabawar fita daga makaranta. Alla Alla takeyi ta gama zana jarabawar ta dan ta samu zama da lokaci ta takawa Jami birki kan shisshigewa uncle da takeyi, sbd ganin abunnata yana so ya wuce gona da iri. Ita kuwa Jami zuwa yanzu babu abinda yake sata nishad'i irin taganta kusa da uncle, shi yasa ma yanzu ko irin karar da takeyi idan ya dawo ta fita ta basu wuri ta daina. Saidai shi d'in ya shige cikin d'aki ya barsu a palour, ko kuma ya fita. A ranar da zasu rubuta last paper kuwa zumud'i da kewar classmates d'inta ne, suka had'u suka tarar mata tun da safiya. Cewa takeyi yau dai sai an ganta kawai dan zata tsaya tayi bankwana sosai da mates d'inta. Shima smart ce mishi tayi kada yazo d'aukarta zata dawo idan ta qare abunda takeyi. Ciwon kan daya kawo mata farmakine ya taka mayta birki, gaba d'aya taji ta kasa samun nitsuwa. Hotunan da sukeyi ma kala biyu kawai ta tsaya akayi da ita ta sallamesu ta kamo hanyar gida. Wani irin mummunar fad'uwar gaba da *Tashin hankali* taji sun shige ta lokaci guda sbd tsinkayo muryar Uncle smart da Jami da tayi a cikin kitchen d'inta dadai lokacin da tasa hanu zata bude kofar net d'in da aka kewaye kofarsu dashi. Kokarin qaryata kunnuwanta takeyi amma hakan ya gagara sbd yanda takejin muryoyinsu ke ratsa dodon kunnuwanta. Babu tantama muryan macen na Jamice, saidai bata jin abinda suke cewa. Wani irin jirine taji yana neman kada ita saida ta dafa jikin kofar ta tsaya........ *F.O.W * * TASHIN HANKALI * *Written by :Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* * Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern. * *30* ~Cikin qarin *Tashin hankali* ta jinginu da jikin bango sbd jin shiru da tayi. Zuba ido tayi taga fitowar Jami tare da tunanin irin matakin da ya kamata ta d'auka. Abin mamaki babu alamun Jami, bata fito ba kuma ta daina jin maganarsu. Take zcyrta ta fara ayyano mata munanan tunani game da dukansu biyu. Kanta ne ya dad'a sarawa zucyarta na wani irin bugawa da qarfi fatt, fatt, fatt. Runtse idanunta da suka soye tayi dan ko kad'an bata ji alamun kuka ba balle akai ga tunanin samun sassauci. Wani irin quna zcyrta keyi, yana kuma dad'a ingizata cikin munanan tunanuka. Dole ta d'au mataki kan Jami, a yau kuma a yanzu ba sai an d'au lokaci ba, kafin ta koma kan uban gayyar. Lallai ta yarda da maganar da ake cewa makashinka na tare da kai. Wato duk tsawon lokacin da Jami ta d'auka tana nuna mata mutunci ashe zcyrta ba haka abun yake ba, cin amanarta sukeyi da mijinta, d'an uwanta wanda take jin ta yarda dashi fiye da tunanin mai tunani. Wani irin bushewa taji zcyrta tayi, karfi ya fara shigarta, jirin da take ji ya fara sakinta. Question papers da pen d'in dake hanunta ta watsar tayi hanyar kofar gida kamar ana turata. Dube dube ta shiga yi har Allah yasa ta hango wata sharb'eb'iyar bulala. Cikin azama ta qarasa ta d'auka snn ta juyo cikin zafin nama fiye da yanda ta fito. A hankali ta bud'e kofar ba tare da tayi sallama ba, zcyrta na tsananta bugawa. Takalmansu ta tsaya kallon tana jn wani qarin bakin cikin yana shigarta. Lallai wnn shi ake kira *Tashin hankali* Mutane biyu makusantan ta yau su suke cin amanarta. Kutsa kanta tayi cikin falon tana ciza leb'enta na qasa cikin zafin rai. Toh fa yau an tab'o fulani.lol A hankali ta bud'e labulen d'akin, cikin sand'a take takawa zata shiga d'akin, idanunta suka sauqa kan Jami dake kwance cikin kujera, tana karkad'a kafafu, idanunta a lumshe, fiskarta dauke da murmushi. Ga dukkan alamu tayi nisa cikin tunani. Tunanin yanda zata fallasa mishi sirrin zcyrta takeyi, da kuma yanda take hango zata iya samun nasara cikin sauqi, ba tare da tasha wahala ba, tunda dai yanxu sunyi sabo dashi har yana d'an sakar mata. Bayan haka ta b'angaren Deejah tana ganin abu ne mai sauki sbd ta riga da tasan ta da saukin kai, kunya da kuma kawaici. Zai yi wuya ta samu matsala ta b'angarenta har gwara ma uncle d'in tana d'an shakka shakka. Hango yanda idan ta samu karb'uwa zasu kasance cikin rayuwa mai dad'i cike da kwanciyar hankali takeyi shi yake sata yawan sakin murmushi. A yanzu babu abinda take jira irin taga fitowarshi daga cikn d'akin, yau dai tayiwa kanta alkawarin zata bayyana mishi sirrin zuciyarta kafin matarshi ta dawo. Kayan jikinta Deejah tabi da kallo, wani d'an banzan shiga tayi na Matsattsen wando wanda ya fito da dukkan ilahirin shape d'inta. Sai wani d'an qaramin top, da tasa, mai hannayen igiya ya kamata tsaff. Shigar dai kamar mai zuwa club. Hijabinta na uniform ta cire ta wullar, ta rage da riga iya gwiwa da wando na makarantar. Batayi wata wata ba, ta d'aga bulalar ta lafta mata da iyakar qarfinta, wanda yayi sanadiyyar zaburar Jami, tare da sakn wata razananniyar Qara sbd azabar zafin da taji ya shige ta lokaci guda, a bazata. Kafin ta yi wani yunkuri ko ta fahimci abinda ke faruwa, Deejah ta sake takarkarewa ta zabga mata bulalar. Ware murya ta sakeyi ta zunduma ihu tana neman hanyar guduwa. Ita kuwa Deejah cikin zafin rai take jibgarta tsakaninta da Allah ta hanata damar fita. Ganin bazata barta yasa Jami ta fara kokarin kare kanta ta hanyar kaiwa bulalar wawura da nufin kwacewa , amma inaaa, Deejah ta hana ta samun damar aikata hakan sai ma kara kaimi da takeyi wajen tsalawa hannayennata bulalar. Uncle smart da ke cikin bacci, ya farka ba shiri sbd jin ihun da Jami ke yi duk da bai tabbatar da wa ke ihun ba. Jin karar bugu da yayi yaki karewa yasashi fitowa daga d'akin a sukwane. Abunda ya gani ne yayi bala'in kulle mishi kai da bashi mamaki. Khadijah mai sanyin hali da saukin kai, yau ita ke jibgar kawarta, abokiyar hirarta. To me ya had'asu haka ? " Cikin azama ya qarasa ya rike bulalar da Deejah ta d'aga zata sake zabgawa Jami, ta baya. A guje Jami ta bar d'akin, cikin tarin azaba da zugin da takejin duk jikinta nayi mata, dan Deejah dukan hauka tayi mata, duk inda ta samu sauke bulalar kawai take. Cikin huci da zafin zcy Deejah tayi yunkurin kwacewa, amma rikon da yayi mata ya hanata samun damar hakan. "Ka sakeni." Ta fad'a cikin takaici tana kuma dad'a fincikewa daga hanunci. Juyo da ita yayi tana fiskantarshi yace "Me tayi miki ne Khadijah." Wani irin kallon sama da qasa tayi mishi da idanunta da suka rine da b'acin rai. Wandon blue shadda, ne a jikinshi sai farar vest, babu riga. Wani irin tafasa ta sake ji zcyrta nayi. Wai me tayi mata yake tambaya tsabar ya gama raina mata wayo. Irin bai san da zaman Jamin a palourn ba. Ta ayyana hakana zcyrta. Yanayin da ya ganta ciki ba qaramin tsorata shi yayi ba dan zai iya cewa bai tab'a ganin b'acin ranta irin haka. Kallon da take mishi kuwa kallone na tsantsan tsana da kyamata. Cikin kullewar kai ya sake cewa "Me ya farune Khadijah." Kwacewa tayi daga rikon da ya mata cikin zafin rai ta nufi wajen kayanta ta fara had'awa cikin jaka guda. Biyo ta yayi cike da d'imbin mamaki yace "Me kikeyi haka mummy ?" Ko kallonshi batayi ba taci gaba da abinda takeyi tana jin zafin zcyrta yana qaruwa dan ita a tunaninta raina mata hankali yakeyi. Cikin mutuwar jiki ya tsaya yana kallon ikon Allah. Wannan wace iriyar zcy ce da ita, duk da jibgar 'yar mutane da tayi bata huce ba, har ma shirin barin gidan takeyi. To waima me ya had'asu haka ? Har ta gama had'a kayan ta dauki kud'i ta zuba cikin hand bag ta fara jan jakar ba tare da ta sake kallonshi ba. Ita kanta bata gama yanke shawarar inda ya kamata ta nufa ba. Gida can dorofi zata koma, ko kuma gurin goggo zata je. Idan taje kuma me zata ce musu ya had'asu. Gwara taje gurin goggo dai tana ga zaifi da taje dorofi. Da wnn tunanin ta samu qwarin gwiwa ta nufi hanyar fita daga d'akin. Da azama ya fincike jakar daga hanunta har tayi taga taga kamar zata fad'i kasancewar ba wani karfin kirki ne a jikinta ba, ga ciwo, ga b'acin rai, ga kuma tun safe rabonta da abinci. Dukan Jami da ta samu tayi ma tsabar b'acin rai ne ne da zafin zcy. Tarota yayi ta fad'o jikinshi yana binta da kallo. Tamm ta runtse idanunta dan tsakaninta da Allah bata son kallonshi. "Ko ni nayi miki laifi bai kamata ki yanke min hukunci ta hanyar tafiya ki barni ba, balle kuma ni a iya sanina babu abinda nayi miki. Ki tsaya ki sanar dani damuwarki, mu nemi mafita shine abunda ya dace ba tafiya ba. Yanzu ina kike nufin zakije ? Idan kin tafi me zakice yasa ki ka baro d'akin mijinki ? " Wani kallo ta watsa mishi ba tare da shiryawa hakan ba, jikinta har rawa yakeyi tsabar fitina da b'acin rai. "Why is he acting innocent." Ta tambayi zcyrta sbd ganin yanda ya maida kanshi kalar tausayi ga kuma maganganunshi dake nuna alamun kamar bai mata komai ba. Tafin hanunta ya kama yana murzawa, a tasusashe yace. "Mummy dan Allah ba danni ba, ki daina min irin wnn kall, ki sawa zcyrki salama ki nitsu ki fad'a min abunda yake faruwa." Da sauri ta kwace hanunta tana binshi da mummunan kallo, a ranta tana tuna da zata iya babu abinda zai hanata d'udd'ura mishi ashar, in zai samu ma har da kwararan maruka kafin ta bar gidan. Saidai tasan abunda bazata iya bane har abada shi yasa ma take so ta nisanceshi, kafin zcy ya kaita ga aiwatar da mummunan aiki. "Khadijah pls tell me , me ya faru ? " Ya sake tambaya a raunane. "Babu abunda ya faru, tafiya zanyi in barka da Jaminka kuci gaba da rayuwarku kamar yadda kuke so, dan inaga zamana takura muku zaiyi, bazan iya zama dakai ba uncle bayan na gane cewa amanata kukeci." Rass, rass, yaji wani irin tsinkewar zcy. Kar dai Jami gadar zare ta had'a mishi. Badai kashe mishi Aure takeso tayi ba. Tabbas alamu sun nuna haka, idan idanunshi ba qarya sukayi mishi ba, wasu 'Yan iskan dressing ya ganta dasu, sab'anin d'azu da ta shigo da bunjumemen hijabi. Tabd'i lallai ya tabbata Jami shu'uma ce, ya yarda cewa wata macen tafi shaid'an shed'anci. Wani tuquqin b'acin raine ya tokare mishi maqoshi, lokaci guda yanayinshi ya canza. Cikin zallar b'acin rai, muryarshi har wani irin shaqewa yakeyi yace "Yanzu Khadijah zargina kikeyi ? Duk zaman da mukayi dake baki yarda dani ba kenan? Har yanzu baki gama tantance halayena ba ? Nifa khadijah, ni ? Kike zargin ina cin amanarki da Jami ? " Yana maganar ne yana nuna kirjinshi da yatsarshi. "Idan ke baki yarda dani khadijah wa kike tsammanin zai yarda dani ? " Ya karishe maganar muryarshi na cracking. Har zai qara magana sai kuma ya fasa ya juya yad'auki rigar jamfarshi ya saka ya fita a hanzarce , zcyrshi na mishi quna. Kuka mai cin rai ta rushe dashi tare da zamewa tayi zaman dirshan a tsakiyar d'akin. Me hakan yake nufi ? Da gaske babu abunda ke tsakaninsu ko kuma yana so yayi wasa da hankalinta ne ? A b'angaren Jami kuma tunda ta samu ta tsere ta shige d'akinta ta zauna cike da bakin ciki da kuma mamakin abunda Deejah tayi mata. Sam bata tsammaci haka daga gareta ba. Kallon jikinta ta shiga yi cikin tarin takaici, wai kamar Deejah ce tayi mata wnn irin duka, har jikinta yayi rud'u rud'u. Inaa bazai yiyu ba, sai ta rama, ita bata samu cikar burinta ba, a bar ta da tsamin jiki ? Ita a ganinta ma abin kunya ne ace kamar Deejah tayi mata irin wnn duka. Tana ta saqawa da warwarewa taji an bud'e kofar su Deejah. Leqawa tayi ta window ta hango shi ya fito fiskarnan a hade babu alamar annuri ko kad'an. Kad'a kanta ta shigayi tana murmushin mugunta. Yau dai saidai ayi wacce za'ayi amma sai ta rama dukanta. Saida ta tabbatar zuwa yanzu yayi nisa ta fito a sukwane tayi hanyar part din. Ita kuwa Deejah zaune take a qasa ta jingina kanta jikin kujera a palour idanunta a lumshe saidai ita kanta batasan kalar tunanin da takeyi ba. Da qarfi taji an banke kofarsu sai da ta razana ta mike tsaye. Ido hud'u sukayi da Jami dake huci kamar wata zakanya tana nufo ta. Dam, dam, Deejah taji kirjinta na bugawa, sbd yaukam tasan ta shiga tara ba uku ba. Idan a girme ne tasan Jami ta girmeta, idan karfi ne tasan bata isa ta hada karfinta da Jami ba, dan kiranta na karfafa ne. D'azu ma da ta samu ta zaneta ita kanta tasan dan ta shammaceta ne, da bata wane qaniyar kakarta Hajja inna..... *Dan dan dan dan dan dan, Masoyan Deejah ku kawo d'auki in kuka yi jinkiri a karairaya 'yar fulani ba ruwana * * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* * Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern * *31* ~Cikin wani irin bayannanen *tashin hankali* take kallon Jami, a ranta kuwa tunanin hanyar da zata bi ta kare kanta take. Ganin ta kusa isota yasata saurin matsawa baya, cikin zafin nama ta rarumo kwalban turaren wuta ta saita goshinta ta kwad'a mata. Ihu Jami tayi tare da dafe wajen cikin azaba. Cire hanunta ke da wuya ta ga jini. Itako Deejah ganin ta fitar mata jini a jiki wani tsoro ya sake shigarta, gashi babu hanyar guduwa, dan Jami na ta hanyar kofar fita. Wani irin kukan kura Jami tayi ta daka tsalle tayi kan Deejah. Cikin b'arin jiki da zare idanu Deejah ta kauce, zcyrta na dad'a tsinkewa. Bata ankara ba taji ta bugu da jikin T.V stand. Duk da zafin buguwar da tayi bai hanata saurin yunkurawa ba, dabara ya fad'o mata, kamar kiftawar ido ta zare wayar A.V. daga jikin T.V. Jami na karasowa ta kawo mata duka a kafad'a. Batayi wata wata ba ta hard'e wuyan Jami da wayar A.Vn. daidai lokacin da jamin ta sauke mata mari. Cikin zafin nama ta murd'e igiyar a wuyan Jami. Ganin Jamin na kokarin murd'eta tayi saurin komawa ta bayanta hanunta rike da igiyar. Da d'an guntun karfinta da ya rage mata ta daddage tana cije hakora ta jawo igiyar suka zube dukansu biyu a qasa suna maida numfashi. Jami na kokarin fitar da kanta daga cikin igiyar, ita kuwa Deejah sai dad'a tamkewa takeyi dan tasan idan igiyan ya kufce mata kashinta ya bushe. Hhhhhh, Jami kin had'u da muguntar fulani. Mirginawa Jami da niyar hayewa kan Deejah, taji an d'agota. Kan ta ankara sai sauqan tagwayen maruka taji a fiskarta. A gigice ta d'ago, suka yi 4 eyes da uncle smart, fiskar nan a murtuk'e, yayi jajazur. Ganin me cetonta ya shigo ya sata sakin igiyar ta mike dakyar tana maida numfashi. A hankali taja kafafunta ta shige d'aki. Ko ba komai ta d'an ji relief sbd maruka da ta ga ya kwakkwad'a mata. "Me ya dawo dake d'akinnan 'yar iska ? " Kuka ta fashe dashi tana murza wuyanta da ke makale da igiya har yanzu. A hankali ta warware igiyar zcyrta na tsananta bugawa, ga azababben tsoron da ya shige ta ganin yanayin fiskarshi. Kallon wuyanta ta yayi shatin igiyar yayi, a zcyrshi yana godiya ga Allah da ya sa shi tunanin dawowa gida yanzu , ba don haka ba baisan irin b'arnar da zasuyi ba. Dan ya tabbata sai sunyi wa juna illah. A ya dda ya lura, ita Khadijah taurin zcy da zafin rai ne yasa ta iya tsayawa had'a jiki da Jami. Yayin da ita Jami ya lura akwai d'an banzan naci a tare da ita, ba don kuma taurin zcyr Deejah ba ya tabbata sai ta yabawa aya zakinta, dan karfin ba d'aya bane. "Me ya dawo dake ? " Ya sake fad'a tsawace. Cikin kuka tace "kayi haquri uncle, babu abinda na mata fa ta hauni da duka." Wani banzan kallo ya bita dashi snn yace "Babu abinda kika mata ? Ance miki ita d'in mahaukaciya ce da zata hauki da duka babu dalili ? "Me ya shigo da ke d'akinta bata nan in the first place ? Me kika zo yi ? " Kukanta ta ci gaba dayi, bakin ciki goma da ishirin sun had'u mata. To ma me zata ce mishi a yanzu. Wnn damar ta riga ta kubce mata. Kallon takaici ya bita dashi. Wnn idan ya tsaya dukanta ma illatata zaiyi a banza bayan wanda Deejah tayi mata, dan ko ba a fad'a yasan yanda shatin igiyar nan ya fito a wuyarta ba karamin wuya tasha ba, ga fasasshen goshi har ya tasa, ga kuma dukan d'azu. "Ba dake nake ba ? Kin tsaya kukan munafurci, ko sai na nemo brothernki kiyi bayani a gabanshi ? " Hantar cikinta taji tayi wani irin kad'awa, jikinta ya d'au b'ari. Ta shiga tuno warning d'in da aunty Tala take yawan yi mata akanshi, kuma ta sha sanar da ita idan ta kuskura taji wani abu akan haka sai ta sanar da yayanta kuma bazai mata da sauqi ba kan hakan, idan batayi hankali bama maidata gidansu zatayi. Ita kuwa yanzu a rayuwarta babu abinda ta tsana irin komawa gidansu sbd rashin jin dad'i da kwanciyar hankali dake cikin gidan, tunda Allah yayiwa mahaifiyarsu rasuwa, matan baban suka sata a gaba, kullum cikin baain ciki da b'acin rai take Dalili ma kenan da wanta yaje ya d'auko ta daga qauyensu ya dawo da ita wajenshi ya sama mata karatu har ta had'a diploma. Cikin karin sautin kuka ta had'a hannayenta guri guda tare da durkusawa. "Dan Allah uncle kayi haquri, bazan sake ba, ko kofar nan bazan qara zuwa ba tunda bata so." "Better, Kuma ki tabbata idan naga koda kwarzane kad'an a jikin matata u must be in for it." Gyad'a kai tayi tana ci gaba ta kuka kafin ta fice da tarin bakin ciki ga tsamin jiki. Duk maganar da sukeyi tana jiyosu daga cikin d'akin, gaba d'aya jikinta yayi sanyi, sai ta samu kanta da tuhumar kanta da rashin kyautawa uncle d'in nata sbd saurin zarginshi da tayi ba tare da tabbatarwa ba. Kife ya sameta kan gado, ya wuce ta ya shiga toilet ya d'auro alwalan la'asar ya fito. "Bazakiyi sallah bane ? " Abinda yace kenan yana shimfid'a sallaya, dan yana tsoron sake fita ya barsu a gidan su kad'ai. Sumi sumi ta tashi itama ta shige toilet d'in kanta a qasa sbd wata iriyar kunyarshi dake d'awainiya da ita. Yana tsaye har ta fito ta zura hijabinta bata yarda sun had'a idanu ba. Kan sallayar da ya shimfid'a mata ta je ta tsaya ya jasu sallah. Suna idar da sallah ta had'a kai da gwiwa fiskarta yana kallon gefe idanunta suna tsiyayar da hawaye. Bai jima sosai ba ya shafa addu'ar da yayi ya mike yaje ya had'o mata tea. Har ya dawo ya sameta a yadda take kuma har yanzu idanunta basu bar tsiyayar da hawayeba. Kusa da ita ya ajiye kofin tea d'n yana motsawa da cokali ya kalleta. "Wai kukan me kikeyi ne haka ke da duka kuma ke da kuka ? " Share hawayenta ta shiga yi, ita kanta baza tace ga takamammen abinda yake sata kuka ba a yanzu, saidai tasan bata jin dad'in jiki da zcyrta, duk da kuwa ta fahimci uncle d'innata baida wani laifi. So take ma ta bashi haquri kan bahaguwar fahimtar da tayi mishi amma bakinta ya mata nauyi ta kasa aikata hakan. Saidafa duk da haka zataso tasan abinda ya shigo da Jami bata nan kuma har ta jiyosu suna magana. Zata so tasan wace irin magana sukeyi . Tean da ya miko mata tasa hanu ta karb'a ta fara kurb'a kad'an kad'an, badon tana jin dad'inshi ba, sai dan yunwar da ta dameta. Ya jima zaune yana kallon yanda take sha cikin rashin kuzari, ga fiskarta babu alamun walwala, gashi kuma sai kawar da fiska takeyi bata son su had'a idanu. Iska mai zafi ya furzar, snn ya mike a sanyaye ya koma kitchen ya zubo mata abinci, ko ba komai yasan yunwa na d'awainiya da ita, zafin zcy ne kawai ya hanata neman abinci. Yana dawowa ya jiyo ta tana kwarara amai a toilet. Da sauri ya ajiye abincin ya isketa can sai kakarin amai takeyi, ta gama amayar da duka tea din da tasha, sai yunkuri takeyi babu komai a cikin. Saida ya gyara wajen, yana mata sannu snn ya had'a mata ruwan wanka, zcyrshi fal tausayinta. Rawar sanyi ta shiga yi lokacin da ta fito daga wankan. Kwanciya tayi jikinta sai karkarwa yakeyi. Babu yanda baiyi da ita ba su tafi asibiti ta ki, a cewarta murace ta sata amai da ciwon kai, karshe dai magani ya siyo mata ya tilasta ta ta d'anci abinci tasha maganin dakyar kafin ta koma ta kwanta. A ranar dai zaman jinya yayi tayi dukansu zcyoyinsu ba dad'i. ~Jami kuwa tun da ta koma, ta kwanta take ta kukan bakin ciki da takaici. Yaran yayanta sunyi tambaya har sun gaji babu wanda ta kula a cikinsu. Saida auntynta ta dawo ta ganta a haka ta tambayeta, nan ta sharara mata karyar ciwon kai da jiri ke damunta. Ko da ta ga kumburin goshinta kuwa ta tambayeta ce mata tayi, zata fita ne jiri ya kwasheta ta bugu da kofa. Jikinta kuwa bata yarda auntynta ta ta gani ba, dan kada ta binciketa, sai lullub'ewa takeyi cikin hijabi. Har dare Deejah na kwance, saidai zuwa wnn lokacin taji saukin ciwon kan dake damunta, sai rashin kuzari. A sanyaye take komai, ga kuma kunyar uncle da har zuwa yanzu bai barta ba. Sai da ya gama duk abinda yakeyi, kafin yayi shirin kwanciya, a lokacin duk a tunaninshi tayi nisa a bacci sbd yanda tayi lamo ta rufe idanunta. Tofe su yayi da da addu'a ya kwanta tare da rungume ta ta baya. Sassanyar ajiyar zcy ta sauqe, a ranta tana tunanin bazata iya bacci ba tare da ta bashi haqurin laifin da tayi mishi ba. Bai zata ba yaji tace "Uncle kayi haquri dan Allah." Saida ya sauqe ajiyar zcy snn yace. "Bakiyi bacci ba ? " Jin tayi shiru ya sake cewa. "Me akayi ? " "Ni dai kayi haquri." Ta sake cewa a sanyaye. "Yi baccinki ni bakiyi min komai ba." Cikin muryar kuka tace "Uncle, wlh na dad'e ina zargin Jami tana sonka, kuma yau danaji kuna magana a kitchen sai nayi zaton kuna soyayya ne...." Katseta yayi da cewa "Jamin ce tace miki tana sona ? " "Wlh, uncle Jami tana sonka." "Dadainki kenan ai mummy, ke kika nuna mata hakan, ke kika bata kofa, kika nuna mata zata iya son mijinki ba tare da hakan ya dameki ba, ke kika koya mata ta so mijinki snn kuma yanzu kika kamata kikayi ta d'irka kamar kin samu 'yar cikinta, kika shaqeta har kika kusa kashe musu 'ya, ni dai banga laifin Jami ba , kece mai laifi.." Ya fad'a cikin halin ko in kula. Cikin kuka mai sauti da kunan rai tace "To ni kuma me nayi uncle ? " Cike dason kular da ita yace. "Kinyi da yawa Khadijah, Taya kina mace zaki bar wata ta rika yi miki dutynki, Jami fa ita ke wellcoming dina idan na dawo gidannan, ita ke karb'a min abinda na rike, kina kallo ba tare da nuna damuwarki ba, kina cikin gidannan zan shigo ko arzikin kallo bazan samu daga gareki ba, sai Jami ce mai tarba ta, kin nuna mata bakya kishina, baki damu dani ba, son da kike mini bai kai ki nuna min kulawa a cikin mutane ba. Na tabbata hakan hakan shi yasa take tunanin ko ta nuna min so abin bazai wani dameki ba, tunda kedin ba wani sona kikeyi har haka ba... "Wlh, uncle ina sonka." Ta fad'a ba tare da tasan lokacin da maganar ta fito daga bakinta ba. Diff, suka dauke wuta dukansu biyu, ita nata kunyane ya lullub'eta, yayin da shi kuma jin kalmar da bai tab'a ji daga bakinta ba, ya kusa daskarar dashi. A hankali ya juyo da ita wuna suna fiskantar juna. Murya kasa kasa kamar mai rad'a yace . "Me kikace mummy ? Banji da kyau ba." Shiru tayi tana tuna ta yadda zata sake furta mishi wnn kalmar ta so. "Dama na sani, wanda kika fad'a ma sub'utar baki ne, ba wani sona kikeyi ba khadijah, banga amfanin raunata 'yar mutane da kikayi ba dan ta nuna tana sona." Ya fad'a yana janyewa daga rikon da yayi mata....... * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* * Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern. * *32* ~Kankame hanunshi tayi ta dad'a shigewa jikinshi tana kokawa da numfashinta. Ta rasa ta yadda zata sake furta wnn kalma, wanda a yanzu tasan ya zama dole ta furta shi. Shawara take bawa kanta dole fa ta yakice wnn kunyar dake cutar da ita ya cutar da mijinta, tunda dama can ta sani, ya sha nuna mata baya so, kunyar na takurashi yana cutar dashi. Ita kanta wani lokacin takuruwa takeyi da kunyar sbd sai tayi niyyar yin wani abu da zai faranta mishi, sai kunyar ta zo ta lullub'eta ta fasa. Ajiyar zcy take ta saukewa akai akai, sai kuma zcyrta dake harbawa da sauri sauri. "Uncle." Tace sai kuma tayi shiru. "Mummy basai kin wahalar da kanki ba, kiyi baccinki nasan baza ki iya ba, tunda ba har cikin zcyrki bane, fad'a kawai kikayi. Yarje min da kikayi zaki aureni wancan lokacin, nasan tausayina kikaji kawai, bayan haka kina tunanin idan na tafi ba lallai bane in dawo . Aurennnawa da kikayi ma dan ya zo miki a bazata ne. Sbd haka ki kwantar da hankalinki, nidai tunda kika amince kika zauna dani ma na gode. Saidai abinda na sani, duk lokacin da na samu macen da ta kwanta min, zata kuma tarairayeni ta nuna min so ko a gaban waye ne, zan aureta in lallab'a, duk da nasan zai yi wuya in sota kamar yadda nake sonki, zanyi kokarin ganin na kamanta adalci tsakaninku, kinga ke sai ki huta da fitanar da nake miki ko ? " Tunda ya fara maganar zai karo wata bugun zcyrta ya qaru, har numfashinta taji yana wani irin sarkewa. Zumb'uro baki tayi kamar yana kallon fiskarta, tana jin wani irin tukukin bakin ciki nacin zcyrta, kamar ta fashe mishi da kuka take ji. Ga wani azababben kishi dake cin ranta tun bata ma san wacece zai k'aron bama. "To ni uncle yaushe nace bana sonka ? " Ta fad'a cikin rawar murya. "Nima fa bance baki sona ba khadijah, dama ai dole ki soni, tunda ni d'an uwanki ne, jininki ne, kuma uban d'anki, kinga dole akwai so na musulunci da kuma na jini." Ya karishe maganarshi yana kunshe dariyar da ta tuk'oshi, dan sarai yana jin k'arfin bugun zcyrta, ga kuma yanayin yadda tayi maganar muryarta har wani rawa rawa yakeyi, tabbas ko bata fad'a ba yasan kishi ne zalla yakecin zcyrta, kuma ya fahimci cewa ita d'in mai zafin kishi ce, saidai ya san ta hakan zai tunzurata watakil sanadiyyar hakan yaga canji a rayuwar aurensu. Tsinkayo muryarta yayi a sanyaye tana cewa tana cewa. "Uncle, na rantse da Allah, ba son 'yan uwantaka kawai nake maka ba, ina maka so irinna soyayya, ina maka sonda ban tab'a yiwa wani namiji irinshi ba. Uncle zan iya ce maka akanka nasan asalin abinda ake nufi daso. Akanka nasan zafinshi, zaqinshi da kuma d'acinsa. Ina maka irin son da idan na rasaka nima zan iya rasa raina, ina maka sonda nake ganin zcyta baza iya jurar ka had'a ni da wata ba, duk da nasan hakan bai haramta ba, sai dai nasan zcyta baza ta iya d'auka ba. Allah ya d'auki raina da inga wnn ranar da zaka kasance da wata a matsayin matarka." "Subhanallah." Yace yana rufe mata baki. "Na yarda mummy basai kin mana fatar mutuwa ba, sbd nasan idan kin mutu binki zanyi, idan kuma ban mutu zan zamo mara amfani, I luv u so very much khadijah, ni kaina bazan iya kwatanta irin qaunar da nake miki ba. Abinda na sani dai, ke ta dabance, ina jinki cikin zcy da gangar jikina, ina qaunarki fiye da tunanin mai tunani. Kina da matsayi mai girma a cikin a zcyta. I cherish u my Deejah." Wani irin azababben farin ciki ne ya lullub'e Deejah kamar yanda shima yake jin kanshi a yau. Ya tabbata yakai Deejah maqura tunda har ta iya furta mishi wad'annan kalaman fatanshi dai Allah yasa zata canza salon zamansu. Niko nace Hmm, uncle sa'a kayi a cikin duhu take shi yasa ta saki baki take ta suburbud'a maka kalamai badan haka ba hmmm Dad'a shigewa jikinshi tayi cikin shauqi, yayin da shima ya rungumeta kamar zai maida ta ciki, bai ankara ba yaji lips d'inta kan nashi. To sabon salo. Hmmm, idan ana sallah ba'a magana. Ranar dai kam Uncle yaga salo duk da dai ba wani isasshen lafiya ne da ita ba amma ta shayar dashi mamaki. Aiko hatta Jami saida ta samu rabon albarka balle kuma ita 'yar albarkan. Washe gari kuwa duk da ta tashi gata nan ne sbd muran da ya takurat ga kuma jiri jirin da takeji hakan bai hanata shiga kitchen ba. Da taimakonshi suka had'a breakfast, dukan su zcyoyinsu wasai ,sai nishad'i suke ji. Bata haqura ba kuwa sai da ta tambayeshi maganar me sukeyi da Jami cikin kitchen d'inta. Saida yaci dariyarshi son ranshi yana ta zolayar ta, mummy kishi. Ita dai da bata ga abun dariya a wajen ba, had'e fiskarta tayi ta nitsu ta bashi hankalinta tana jiran gamsasshen bayani. Ganin taci serious ne ya sashi barin dariyan ya shiga yi mata bayani. Shima shiganshi kenan, ya shiga kitchen ya ajiye cefane, kafin ya fito yaji ta yi sallama tare da tura kofar. A kofar kitchen ta tsaya ta gaisheshi, daganan ta ce mishi tayi tsamanin Aunty Hadiza ta dawo. Shi kuma yace mata ba ita bace shima yanzu shigowarshi. Shine fa ta tambayeshi ko da wani abunda yake buqata ta ganshi a kitchen. Yace mata babu komai. Sai kuma ta sake cewa ko akwai abunda zata taimakawa aunty Hadiza dashi kafin ta dawo. Nanma yace mata babu yayi hanyar ficewa dan bacci ne sosai a idanunshi, kasancewar ya riga ya saba lokacin baccinshine bayan sallar azahar, ya tashi da la'asar. Daga nan yayi shigewarshi ciki yayi kwanciyarshi, baisan kuma abunda ya faru daga baya ba, sai ihunta da ya tashe shi a bacci. Amma abunda ya bashi mamaki shine ganinta da yayi da English wears instead of qaton hijabin da ta shigo dashi. Sai yanzu hankalin Deejah ta dad'a kwaciya dan ta tabbatarwa kanta uncle d'inta baisan nufin Jami akanshi ba, kuma ta kuduri niyar dad'a nisanta da ita. Daga ranar saidai aunty Tala ta leqo su gaisa, tun tana zuwa da nufin gaisheta da jiki dan da farko ce mata tayi bata jin dad'in jikinta shi yasa bata shigowa part d'insu, har lokacin tana zolayarsu da Jami cewar ciwon nasu na kawaye ne. Hardai ta fahimci kwata kwata yanzu Deejahn bata son shiga part d'insu ne, kuma taga Jami ma bata zuwa gurin Deejan sbd haka tayi tunanin ko Deejan ma ta gano abinda ta jima tana hangowa a tare da Jamine game da Uncle smart, sbd haka ta zuba musu ido kawai. Saidai suna gaisawa da Deejah, kuma Deejah bata fasa yi mata kyautar turaren wuta da Humrah ba yadda ta saba duk lokacin da sukayi sabon sari. Tsakaninta da Jami kuwa ko kallo bata isheta ba, idan sun had'u. Ita Jami ba qaramin mamaki Deejah take bata ba, dan sam ba haka ta tsammaci Deejan ba, tana mata ganin marar wayo, gani take kamar zata samu abunda ta keso cikin sauki tunda taga Deejan kunyace da ita ga kawaici, ga kuma sanyin hali, abun hanunta kuma bai rufe mata ido ba. Ko kad'an a zcyrta bata da niyyar cutar da ita, ita dai burinta ta samu uncle yasota koda rabin sonda yakewa Deejah ne tasamu, ita dai ace itama uncle mijinta ne, shine damuwarta. Hhhh, baki da hankali Jami, uffan abun hanunta bai rufe mata ido ba, uncle kam ya rufe mata ido, zata iya yi miki kyautar komai banda na uncle. Kuma abunda baki sani ba, su fulani akwai kunya, kawaici, da haquri amma basa jurar raini. Sbd haka ki kiyaye Kawar Kakus da 'yar Baiwa. Ko islamiyar da suka suka shiga na asabar da lahadi suke zuwa tare, yanzu daban daban suke tafiya, kuma ko sunje babu mai kula wata tsakaninsu har su dawo. A wnn d'an tsakanin zamansu ya canza salo, dan sosai take kokarin yakice kunya ta nuna mishi salon nata soyayyar, shi ko jinshi yake kamar sabon ango. English wears d'in da yake saya mata take kin sawa, yanzu su suka zama kayan sawarta, cakarewa takeyi a ciki, idan taga ya kusa dawowa, kullum da kalar salon kwalliya da tarairaiyar da take b'ullo mishi dasu. Ai kuwa shikam Jami ba qaramin burgeshi tayi ba, dan tayi mishi maganin kunyar Deejah abunda ya kasa yi cikin shekaru biyu. Har mamaki yake dama duk tasan da wad'annan abubuwa take zaune kamar ba abunda ta sani. Hmm, zo in maka wata gulma uncle. Khadijarka da kake ganin nan. Duk cikin dorofi da kewaye, kai harma cikin Gembu, bayan Mama Deejah da Sadatu, babu wacce ya kaisu sairaren audio novels na Bn Hamza ta waya. Sawa kai wahala ne kawai. Ko yanzu ma sadatu da taje Gembu tana kai mata ziyara kuma tana tura mata novels d'in kala kala. Zumuncinta da mutan Borno kuwa yana nan sai abinda ya qaru, kusan kullum sai saun gaisa, ko ita ta kirasu ko kuma su su kirata. Haka ma mutanen dorofi suna yawan kiransu su gaisa, har da Mahmudu. Cikin kwanakin kuma ya sayi sabuwar machine (Babur) Allah sarki rayuwa, smart din da da yake da motoci na hawa daban daban yau gashi da murna da farin cikin ya sayi machine mai qafa biyu, har da celebrating. Allah ka azurta mu da wadatar zcy. Yawatawa yayi tayi da ita , har filinshi da ya fara ginawa saida ya kaita. qarshe suka yada zango gidan Hamma Atiku. Tunda suka shiga suna gaisawa cikin raha kamar yadda suka saba Adda rabi take ta bin Deejah da kallon nazari. Cikin zolaya tace. "Deejah ni zan fara albishir a dorofi ko kun rigani ? " "Albishir na me kuma ? " Ta tambaya cikin rashin fahimta. "Na abunda kuke b'oyewan na ganoshi ko baku fad'a ba." Ta fad'a tana mata hararar wasa. "To me kuma muke b'oyewa ? "cewar uncle smart. "Kun fini sani ai, ni dai ku fad'a min idan baku rigani ba inyi musu albishir, dan nasan goro na na musamman ne. Zuwan danayi kwanaki ma su Dadayi sai tambaya sukeyi ko an samu nace musu babu ashe kekam kina hanya." Kallon juna sukayi, kafin uncle yace "Yi min bayani yadda zan fahimta dan nikam ban gane maganarki ba Rabi." "Kin shiga uku Deejah, har da ya mangan ma b'oye mishi kikayi." Ta fad'a tana rike bakinta alamun mamaki. Zuwa yanxu kwakwalwar Deejah ya fara hasaso mata abunda adda Rabi take nufi, ta fara gano inda ta dosa. Inko haka ne da itama kanta ta cancanci goron albishir daga gareta ba mutanen dorofi kawai ba. Bazata manta ba zuwanta na qarshe Fa'i take ce mata, wai ko tana shan magani ne, dan tana makaranta, ga yaransu duk sunyi wayo ita ba labari. Itama kanta abun na damunta saidai ganin uban gayyan ko maganar bai tab'a kawo mata ba yasa bata wani d'aga hankalinta ba. Har tunani take watakil Mahmudu ne kawai rabon ta a duniya, idan ta tuna hakan tana godewa Allah da bai basu damar zubar da cikinshi ba, ko ba komai in ta ganshi dai zataji shi d'in jininta, d'anta da ta haifa a cikinta. "Mummy wai tunanin me kikeyi ne ? " Ta jiyo muryarshi yana tambaya. Firgigit tayi kamar wacce aka tasa a bacci tana binsu da kallo. "kyaleta ya Manga, tsabar rashin gaskiyane ke damunta, idan ba haka ba, Allah ya maka kyauta mai muhimmanci haka ta b'oye bata fad'a ba. Wlh Deejah cikine da ke, ko na miki qarya ki musa ? " Ta karashe zancenta tana banka mata wata hararar. "Wai, tsaya Rabi, cikin haihuwa kike nufi ko menene ? " Ya tambaya cikin zumud'i dason jin qarin bayani. Dariya ta kece dashi tace "Ka tambayeta wlh ciki ne da ita na haihuwa." Kallon Deejah yayi wacce itama shi d'in take kallo, dan ganin reaction d'inshi, tana kuma lissafa kwanakin da suka tsallaketa na al'ada, tana kuma tunanin changes da take ji a jikinta. Ko muran da ya addabeta nan ma ya isheta babban shaida , dan haka tayi ta fama dashi a cikin Mahmudu. "Me yasa kika b'oye min wnn abun farin cikin Khadijah." Ya fad'a idanunshi cike taff da qwalla yana kokarin maida su. Muryarta na rawa tace "Nima fa bansani ba uncle." Kamo hanunta yayi ya mikar da ita bayan ya tashi tsaye yace, "Ina dawowa Rabi, zan kawo miki goron albishir d'inki." Daga nan yajata suka fita. Hankalinshi bai kwanta ba saida ya kaita asibiti aka tabbatar mishi da hakan. Farin cikin da ya nuna har ya bawa Deejah mamaki da tausayi, dan ita tana tunanin ko bai damu da haihuwar bane. A nashi b'angaren kuma bawai bai damun bane yanaso, saidai tunda bai samu ba yana ganin nuna damuwan butulci ne tunda Allah ya azurtashi da Mahmudu watakila shine kad'ai rabonshi a duniya. Kyautar da yayi wa Adda Rabi kuwa ba qaramin mamaki yabata ba, sai addu'a take ta mishi Allah ya inganta, ya raba Deejah da abinda ke cikin lafiya....... *Kun jini shiru kwana biyu, Rashin lafiya nayi, amma yanzu Alhamdulillah na samu sauqi, Godiya da gaisuwa mai tarin yawa ga wad'anda suka kira ni domin jin lafiyata na gode qwarai Allah ya bar zumunci* *LYSM* * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* * Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern. * *33* ~Kulawa da riritawa kuwa Deejah tana ganinsu tamkar akanta aka fara ciki. Gefe d'aya kuwa ya dage da gininshi dan yana so inda hali ya kammala su koma kafin ta haihu. Mutanen dorofi kuwa tuni Adda Rabi ta fesa musu kowa sai murna yakeyi, da fatan Allah ya raba lafiya. Zuwan da zatayi dorofi ma kasancewar ta kare makarantar, hanawa sukayi sukace ta bari sai ta haihu dan hanyar bashi da kyau. Kasuwancinsu kuwa Alhamdulillah yana tafiya yanda ya kamata, dukansu biyu suna samu daidai gwargwado. Yusufa na iya kokarin na ganin ya kare dukiyar yayarshi, wanda hakan yasa ba qaramin alfahari takeyi dashi ba, dama kuma akwai fahimtar juna sosai tsakaninsu tun basu mallaki hankalin kansu ba, duk da shine abokin fad'anta a gidan, sbd kasancewarsu sak'o da sak'uwa. Cikin ikon Allah cikin Deejah ya girma har ya shiga watan haihuwa. A lokacinne kuma Adda Rabi itama ta haihu, inda ta qara haihuwar 'ya mace. Yanzu yaranta hud'u kenan, mata uku namiji d'aya. Sau biyu Deejah taje gidan mai jego, daganan yace sai ranar suna sbd nauyin da tayi. Ana gobe suna da safe yana fita, Ali yace mishi mutanen dorofi sun iso jiya da dare. Gidan Hamma Atiku yaje ya tarar da su Adda, Dadayi, goggo amarya, Habiba, Fa'i, goggonsu Mmn Habiba, an zo harda Mahmudu. Sun jima tare dasu suna ta hirar yaushe gamo, daga baya da yazo tafiya ya d'auki Mahmud ya tafi dashi. Deejah tana zaune ta jiyo muryar yaro yana surutu kamar na Mahmudunta. A hankali ta tashi ta leka, aiko taga shi d'inne. Kallonshi takeyi fiskarta d'auke da murmushi na farin cikin ganinshi. Saida ta leqa bayansu taga babu kowa daga shi sai babanshi ne ta kamo d'anta ta rungume tana shafa kanshi. Tayi missing d'inshi ba kad'an, haka kuma ba qaramin dad'in ganinshi tayi ba . Uncle smart dake tsaye yana kallonsu, dariya yayi a ranshi yana cewa, mai hali dai baya fasa halinshi, sbd ganin lek'e lek'en da tayi kafin ta marabci yaron. Wato inda da wani yazo dai, sai tayi petending kamar bata damu dashi ba. Yana makale jikinta taja shi suka qarasa cikin falon suka zauna. Bayan sun zauna ta fara tambayarshi da wa suka zo, nan yaro ya fara zuba mata bayani, yana lissafa mata wad'anda suka zo tare. Rass maganarshi take fita, ga wayo, kammaninshi kuwa sai dad'a fitowa yakeyi da na babanshi. Wani sanyin dad'i takeji na ganin gudan jininta bayan lokutan da ta d'auka bata ganshi ba. Ji take inama adda zata bar musu shi su zauna tare. Hanunshi taji ya d'ora a kan cikinta. "Adda cikinki na ciwo ne, naga yayi qato ? " Ya tambayeta da fulatanci. Shiru tayi tana kallonshi ta rasa ma me zata ce mishi. Babanshi ne ya kamo shi yana dariya. "Ba nace maka sunanta mummy ba, kai kowa adda ne ? " "Na manta ne." Ya ce snn ya sake cewa cikinta na ciwo ne ? " "Cwthrt qani zaka samu, kwanannan mummy zata haifo maka wani baby." "D'an qarami kaman na adda Rabi ? " Yaron ya kuma tambaya. "Eh, ashe ka gane." "Yeh, yeh, yeh, Allahu akbar, Allahu sammad." Ya fad'a yana tsalle da dariya. Suma dariyar sukeyi. "Wa ya koya maka Allahussamad ? " Babanshi ya tambayeshi. "Ina zuwa Islamiyyar su adda Ummi ai a gurin muke karatu." Shafa kanshi yayi yace "Gud boy, nima zaka koya min karatun ? " "Eh, amma sai kace min Ustaz. Haka muke kiran malaminmu, idan kana kirana ustaz zan rika koya maka karatu kullum." "Toh , ustaz Mahmud, koya min." "To sauka qasa ka zauna, mu a kasa kan taburma muke zama, ustaz d'inmu kuma a kan benci." D'an juye juye yayi, sai ya kuma kallon babanshi. "Ku gidanku baku da benci sai kujera, mukam a gidanmu akwai." "To zauna kan kujerar sai ka koya min karatun ko ? " Cewar Baban. Gyara zamanshi yayi kan kujerar yayin da Baban ya sauqa qasa ya zauna ya lankwashe kafafu Irinna masu d'aukar karatu. Daga Alifun, Ba'un ya fara mishi yana amsawa, har suka gama. Suka koma Fatiha, suka gama, Sai yace Baban yayi shi kad'ai. Shi kuwa ya dage yayi ta karantawa. "Attakbeer." Cewar Mahmud. "Allahu akbar." Baban ya amsa mishi. Ya kuma cewa . "Altakbeer." "Allahu akbar." "Allahu ssamad zakace yanzu kam." Ya fad'a yana zumb'uro baki. "To Allahu ssamad. Ya fad'a yana mishi dariya. Yawwa mun gama mu karanta attahiyaatu. Tahiya suka karanta, daga nan yayi addu'a yace an tashi karatu sai gobe. Dukansu kallon sha'awa da alfahari suke bin d'annasu dashi. "Ke kam mummy bazan koya miki karatun ba, tunda baki ce min ustaz ba. Ya fad'a yana nuna maman. Kadin tayi magana yace. "Tea zansha." Kokarin mikewa takeyi ya dakatar da ita, yaje ya had'a mishi tea d'in. Sosai suka ji dad'in zuwan yaron dan ya d'ebe musu kewanshi da surutunshi, sai sasu dariya yake tayi, hakan yasa ko kasuwa babannashi bai je. Fa'i da Habiba ne suka zo tare da Yusufa da ya rakosu. Murnan ganin juna sukayi tayi sai lokacin ya fita ya basu guri, shi kuma Mahmudu ya makalewa Kawunshi yusufa. Su aunty Tala da Mmn Ahmad suka shigo suka gaisa da baqinta, anan suka ga Mahmud. Sai a ranar Jami ma ta shigo jin Fa'i na ta tambayar ina take. Bata wani jima ba, suka gaisa, ta fita. Su sukayi mata girkin da zatayi suna hiransu cikn raha da annashuwa. Abinci mai yawa suka dafa ta zuba nasu adda a cikin babban cooler. Tare suka tafi gidan Hamma Atiku, nan ta zauna sukayi ta hira da su addayi har dare. Abun dariya abun mamaki wai har yanzu adda bata sakin jiki da Deejah, a dole ita matar d'an farinta. Sai dare yazo ya tafi dasu tare da Mahmudu. Washegari suna ma a can suka wuni, har dare yazo suka tafi. Su adda sunso tafiya washegarin suna ya dakatar dasu kan shima yana shirin tarewa sabon gidanshi, su bari suga tarewarsu kafin su tafi. Tun ranar da suka zo kuma Mahmud yana wajensu. A cikin kwanaki biyun da suke shirye shiryen tarewar nan suka shaqu sosai da Mahmud har suna jin kamar a bar musu shi. Saidai kam sun jinjinawa adda da kokari dan yana ji da kiriniya ga surutu, baya gajiya sam da magana, komai ya gani sai yayi tambaya. Ana gobe zasu tare, Deejah tana zaune kan filo a tsakiyar falonsu, haka kawai take jin jikinta a sanyaye, komai baya mata dad'i a ranar. Zaune take sai yamutsa fiska take tayi. Uncle smart da ya shigo tare da Mahmud yake tambayarta cikin zolaya. "Kuka zakiyi ne mummy." Kamar kuwa jira take ta gyad'a kanta a shagwab'e tana cewa "Wlh, haka nake ji kamar inyi kukan, saidai yaki zuwa." "Kukan dai yaki zuwa ? Bakiyi niya badai mummy." "Hmm, kawai tace tayi shiru, ita kad,'ai tasan abunda takeji. "Ko dai abun yazo ne ? " Ya sake tambaya. "Babu abunda yazo, jikinne kawai nake jinshi ba dad'i." "Waye ne yazo Daddy ? " Mahmudu ya tambaya yana kallon babanshi. kallonshi yayi shima ya shafa kanshi, bai bashi amsa ba ya maida hankalinshi ga Deejah. "Ko zamu je asibitine ? " "Um, um." Kawai tace, ta yunkura ta mike tana yamutsa fiska, ta shige kitchen. Binta Mahmud yayi cikin kitchen d'in yana ta zuba mata surutu da tambayoyi, ita kuwa tana wiki ne kawai, amma ta rasa gane takammamen damuwarta. Har ta kammala ayyukanta suka fito, tana yin komai cikin qarfin hali ne dan taga yadda uncle smart ya maida hankalinshi sosai kanta. Ganin canjin yanayinnata ne kamar taji sauki har ta sake suna hira tayiwa Mahmudu wanka itama tayi, yasashi shirin fita. Nan kuma Mahmudu ya d'afe mishi lallai sai ya kaishi gurin addanshi. "My boy ka zauna ka taya mummy hira ni ba gurin su adda zanje ba." Maqe kafad'a yayi "Nikam adda." Ya fad'a yana narke fiskar shi zaiyi kuka. "Uncle ka tafi dashi, kar ka tafi ya dameni da kuka." "Zo muje." Yace yana fita. "Yeh, yeh, yeh." Ya fad'a yana dariya tare da d'aga hannayenshi biyu duka sama. Saida ya gama tsallenshi yace "Allahu akbar, Allahussamad, Mummy sai na dawo." Har ya fita ya sake dawowa. "Mummy me zan sayo miki, sha ka hura, ko biscuit ko Bobo, wanne kikeso ? " Kallonshi takeyi cikin wani irin yanayin da bazata iya fassara me takeji a lokacin ba. Kusa da ita ya matso ya kwantar da kanshi jikinta. "Mummy kar kiyi kuka, zan dawo, kuma zan saya miki duka ko ? Kinji ? " Ya fad'a da alamar rarrashi. Dariya tayi ta shafa kanshi snn ta sumbaci goshinshi, tace "A dawo lafiya Ustaz." "Idan kun gama soyayyar sai kazo muje ko." Cewar babanshi da tun d'azu yake tsaye yana kallonsu cikin sha'awa. Da gudu yaje ya kama hanun baban ya sake waigowa ya kalli maman, yace "bye bye mummy." "Bye bye." Itama tace tana d'aga mishi hanu. Saida suka fita ta sauke hanunta tana jin soyayyar d'anta cikin zcyrta. Gidan Hamma Atiku suka nufa, sauri yake yaje ya samu Hamma shehun da ya qira shi yace mishi ya shigo Gembu yana shagonshi, yana so su had'u kafin ya qarasa gidan Hamma Atikun. Dadai sun isa kofar gidan tsayar da machine yake cewa mahmud . Zan saukeka ka shiga ciki, anjima zan dawo mu koma gurin mummy ko ? " Gyad'a mishi kai yayi cikin zumud'in zai shiga wajen addanshi. "Ka gaida adda, sai na dawo ko ? " Yace dadai lokacin da yake sauqeshi daga kan machine d'in . Ihun kiran sunan shi da yaji anyi ne yasashi waigawa da sauri, babu shakka muryar yusufa yaji ya kirashi da karfi kuma cikin muryar *Tashin hankali.* Saidai kafin yasan me ke faruwa yaci wani qara kamar bindiga, sai wucewar abu yaji, kafin ya ankara yaga Mahmudu yana langab'ewa zai zube qasa. A zabure ya sauqo daga kan Machine d'in ya tallaboshi, gaba d'aya jini ya gama wankewa Mahmudu d'in cikin d'an kankanin lokaci. "Innaa lillahi wa innaa ilaihirraji'uun, Allahumma ajirnii fii musiibatin wa akhalifinii khairan minhu." Abinda ya ke maimaitawa kenan cikin rauni da rawar murya, gaba d'aya yana nema ya fita hayyacinshi. Yusufa ne ya qaraso da gudu, yayin da wasu mutane suka mara mishi ba. Cikin zafin nama ya karb'e mahmud daga janun babanshi wanda a halin yanzu ya zamo kamar mutum mutumi. Shi yusufan ma babu abinda ya tab'uka illah rungume yaron da yayi ya fashe da wani irin kuka mai cin rai. Wani dattijo ne ya sa hannu ya b'amb'are Mahmudu a jikin yusufa dakyar ya shiga duba shi. Ga dukkan alamu Mahmudu kam rai yayi halinshi. Shi ko yusufa karb'ar yaron da akayi a hanunshi yasashi zabura ya mike ya shiga surutai cikin fitar hayyaci. "Tanan suka fito, ina kallonsu suka saita bindiga suka harbeshi, harbeshi sukayi wlh, kuma sun gudu, suna harbeshi suka ja motarsu suka gudu, na gansu da ido na, wlh sun gudu..... * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* * Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern * *34* ~Surutai yakeyi na fitar hayyaci yana nuna hanyar da yaga sunbi. Rirrikeshi wasu matasa sukayi suna bashi baki. Shi kuwa Baban mahmud yana durkushe a gurin sai bin hanunshi da jinin mahmud ya b'ata yakeyi da kallo tamkar mai son karanto wani abu. Wasu mutane biyu ne suka d'agoshi suka ajiye kan dakalin kofar gidan. Wani makocin Hamma atiku kuma ya kira wayar Hamma atikun yana fad'a mishi abunda ya faru. Jin mutumin yana cewa yaron ya mutu ne, yusufa ya juyo a zabure yana kallon Mahmudun dake kwance lifeless a hanun dattijon. "Kai dan baku da tausayi sai kucewa adda mahmudu ya mutu, haka zaku fad'awa adda Deejah ma ? Kun tabbatar ya mutun ne ? " Ya fad'a yana zaro idanu, da gani kasan ba cikin hayyacinshi ya ke ba. Ambatar adda Deejah da yusufa yayi ne yasa uncle smart mikewa yana jin zuciyar shi na tsinkewa. Take tunanin shi da hankalinshi suka dawo gangar jikinshi. Kan mahmudu ya nufa yana qare mishi kallo. Ko shakka babu Mahmudu bashi da rai. "Kaima ka yarda ya mutunne ya manga ? " Cewar yusufa ,ganin yayannashi yana girgiza kai tare da kwararowar wasu hawaye a fiskarshi. Cikin zafin nama ya wafce mahmudu daga hanun dattijon yana cewa "In Allah ya yarda adda, Deejah baza taga wnn *tashin hankalin* ba. Ya isa haka, abun zaiyi mata yawa. A sukwane ya juya ya bar wajen rike da yaron a hanunshi wuyanshi na reto bai damu da hakan ba. Ganin ana faman karb'an yaro yasashi tub'e takalman kafanshi ya ruga da gudu, yana cewa "Asibiti zan kaishi." Wani ne yabi bayanshi da machine yace mishi. "Hau in kaiku asibitin." Da sauri ya hau yana cewa "Yauwa d'an uwa kaima ka gane bai mutunba kenan." Daga nan kuma ya daddage sai tofe mahmudu yakeyi da addu'a a cewarshi bai mutu ba yana da rai. Tunanin yadda zai sanar da Deejah wnn labari ya shigayi. Tausayinta ya cika mishi zcy, ga kuma halin da take ciki. Tunano yanda yau take tayi yayi, ya karkad'a kanshi. Tsakanin uwa da d'a, tabbas jikinta ya bata akwai abinda zai faru shi yasa duk tazama wata iri. Dole ma yasan yadda zaiyi tazo tayi wa d'anta kallon karshe. Da wnn tunani ya samu kwarin gwiwar mikewa ya hau machine d'inshi yana tafe bakinshi d'auke da addu'a. A kofar gidan yayi parking , saida daidaita kanshi ya shiga. Duk da dai idan ka kalleshi sosai zaka gane yana cikin damuwa. Da sallama ya shiga, ya sameta tana zaune a inda suka barta ta tsurawa waje d'aya ido. D'agowa tayi ta kalleshi a sanyaye tace "Har ka dawo, ina mahmudun ? " "Yana wajen adda." Ya bata amsa ba tare da ya yarda sun had'a idanu ba. "A can zai kwana ? " Ta sake tambaya. Zcyrshi sai bugawa takeyi, ya dake yace, "a'a, na barshi canne nazo dubaki." Ya karasa maganar yana zama a qasa ya kamo kafafunta yana matsawa. Idonshi na kan kafafun duk gudun kada su had'a idanu ta gane wani abu. "Ya na ganki kamar har yanzu bakijin dad'in jikin." 'Yar karamar tsaki taja. "Wlh, uncle yau d'innan kam ina jina wata iri, ko mutuwa zanyi ne oho ? " "Saurin kallonta yayi sai kuma ya maida kanshi kasa. "Daga jin jikinki wani iri sai mutuwa ? " Tashi muje asibiti a duba min ke." "Allah uncle bana son zuwa asibitinnan." "Tashi muje gidan Atiku to." "Yauwa, anjima sai ka d'auko mu ba." Ta fad'a tana mikewa. Binta da kallo yakeyi cikin tausayawa, yayinda ita kuma tana tafiya ne kawai jikin duk yayi mata nauyi. Hijabinta ta d'auko ta zura suka fito. Tafe suke babu mai magana cikinsu har suka iso kofar gidan. D'an nesa kad'an da jama'a yayi parking. Saukowa tayi jikinta a sanyaye. D'ago kan da zatayi ta hango mutane zaune da butoci suna alwala. Hamma shehu ta fara gani sai Mijin aunty Tala, gefenshi kuma Hamma Atiku. Take jikinta ya d'au b'ari, amma bakinta ya mata nauyi ta gagara magana. Yusufa ta hango ya had'a kai da gwiwa. Kallon uncle smart tayi wanda yayi saurin kawar dakai shima yana kallon jama'an tamkar baisan abunda yake faruwa ba. Ganin ta da rikice ya sashi riko hanunta suka bi gefe suka shiga cikin gidan. Tana kutsa kanta cikin falon ta ji sautin kukan matan dake cikin falon. Zcyarta ya shiga dokawa tana tunanin wanda ya rasu a cikin gidan. Cakk ta tsaya tana binsu da kallo, su adda da makotan su adda Rabi ta gani a falon, bata gama tantance su ba balle ta gane wad'anda basa ciki. Adda da tunda aka shigo da gawar Mahmud jikinta ya rika b'ari saida aka riketa, tana zaune jingine da jikin gini. Suna had'a ido da Deejah tayi saurin kawar da kanta tana rufe fiskarta da hijabin jikinta. Qarasowa deejah tayi sosai cikin falon ta zauna tsakanin Fa'i da Habiba tana bin jama'an falon da kallo. Dadayi ce da goggo amarya basa wajen , to wace ta rasu a cikinsu. Dukansu babu wacce ta ke marmarin kallonta, kuma babu wacce ta mata magana a cikinsu. Ba da jimawa ba, su Dadayi suka fito daga d'ayan d'akin gidan. Gurin Adda Dadayi ta nufa yayin da Goggo amarya ta fita. Ita dai binsu da kallo takeyi, taga Dadayi ta riko hanun adda suka shiga cikin d'akin. Daddafa qasa tayi ta tashi ta bisu a baya dan ta ganewa kanta abunda yake faruwa. Abinda kunnuwanta suka jiyo mata adda take fad'a cikin kuka ne yasata jin wani shegen jiri na kwasanta tayi saurin dafe gini. "Allah yafuma Mahmudu." Abinda taji adda take fad'a kenan. Sunan da basu tab'a ji ta kira ba, sai dai tace "B'ingel d'o." (Yaronnan.)" "Dadayi." Deejah tace cikin rawar murya, ta kasa qarasa maganar da takeso tayi. Adda ce ta juyo tazo kusa da ita ta kamo hanunta kam ta jawo zuwa gaban gawar Mahmud. Yana kwance cikin likkafani, fiskarshi kamar ka kira shi ya amsa. "Kizo ki yafe mishi Deejah, ya tafi ya barmu." Adda take fad'a cikin matsanancin kuka. Bugun zcyrta ne ya qaru da tayi arba da fiskar d'anta amatsayin matacce. Yaron da d'azu suka rabu yana ce mata kada tayi kuka zai sayo mata, sha ka hura da biscuit da Bobo . Yaron da ya fita daga falonta yana tsallen tsallenshi, yana d'aga mata hanu. Amon muryarshi take jiyowa a yanzu yana mata bye bye mummy. Qura mishi ido tayi ko kiftawa babu, har su Hamma shehu suka shigo. Babanshi da baffanunshi ne suka shigo suka tsuguna dukansu gaban gawar suka shiga yi mishi addu'a. Hanunsu dadayi ta riko suka koma falo. Addu'a sukayi mishi suka rufeshi gaba d'aya suka fito dashi. Mikewa dukansu matan falon sukayi kowacce da addu'a a bakinta lokacin da aka fito dashi. Wani irin juyawa taji d'an cikinta yayi, kasan maranta kuma taji kamar ana tsinkawa. Tuni jini ya tsinke mata ya fara bin kafafunta. Qasa tayi ta durkusa tana rike ciki, idanunta a runtse. Uncle smart da dama hankalinta na kanta tunda suka fito daga d'akin. Tsayawa yayi yana kallonta. Da sauri Habiba da Goggo amarya suka nufi kanta suna mata magana. Ana fita dashi ta tafi luu ta zube jikin goggo amarya. Sai a snn suka ga jinin da ya b'ata mata jiki. "Innaa lillahi wa innaa ilaihirraji uun." Adda ta fad'a dafe da kirjinta da yake matsanancin bugawa. Dadayi kam kuka takeyi haikan kamar zata shid'e. Ganin sun tsaya koke koke ne ya sashi qarasowa ya d'auketa ya fita da ita a sukwane. Fa'i da goggo amarya suka mara mishi baya sauran kam kukan *Tashin hankalin* da ya samesu sukeyi da tausayawa Deejah. Asibiti aka kaita, haka aka kai Mahmudu makwancinshi ba tare da Babanshi ba kasancewar magriba ta kusa. Tiyata aka shiga da ita ganin bata cikin hayyacinta gashi jini yaqi tsayawa. Sun jima zaune cikin alhini har masu kai mahmud suka zo asibitin suka samesu. Yusufa kam har idanu sun kumbura sbd kukan da yasha. Sai bayan isha'i aka fito da baby mace mai kama da uwarta sak. Ko kallon ta baban baiyiba sai tambayar Deejah yakeyi. Su goggo amarya ne suka karb'eta suma basu iya nuna farin cikinsu ba sbd halin da suke ciki. Ba da jimawa ba aka fito da ita aka kaita ward. Haka suka yi ta zaman jiran farfad'owarta cikin fargaba. Sai wajen karfe goman dare ta farfad'o, nanma babu wanda tayiwa magana, kallo ta bisu dashi d'aya bayan d'aya. Duk sannun da suke mata babu wanda ta amsawa. A haka doctor yazo ya duba ta yana tambayarta ko akwai inda yake mata ciwo. Batayi magana ba sai nuni da tayi mishi da kanta da cikinta. Allurai ya had'a ya zuba cikin drip d'in da aka sa mata. Kusan sha d'aya sauran mutanen suka koma gida aka bar Dadayi da Uncle smart a gurinta dan yaki tafiya. Washegari kuwa saida aka sa mata qarin jini sbd tayi losing sosai. Aunty Tala da Mmn Ahmad kusan anan suka wuni. Jami kuwa saida tayi girkin rana ta kawo asibitin tayi musu gaisuwa da fatan samun lafiya wa Deejah. Sosai Jami taji mutuwar Mahmudu, tayi kuka kuwa sosai, dan ba qarya yaron ya shiga ranta. Cikin kwana biyu saida tasha qarin jini leda uku, kuma har lokacin bata yiwa kowa magana saidai ta bisu da ido. Ko zuwan su babanta ma duk gaisuwar da suke mata da ido da kai take amsa musu har abun ya soma damunsu. Nasiha sukai ta mata kan yarda da kaddara , ita dai binsu da ido kawai takeyi. Addu'a suke mata sosai ganin kamar har lokacin bata cikin hayyacinta. A cikin 'yan kwanakin smart duk ya rame ya lalace, abinci ma sai su Hamma shehu sun matsa mishi yakeci. Ita ma Deejan sai anyi da gaske take tab'a ruwan tea ko indomie ko kuma koko. Tsakaninta da babynta kuma sai in zata shayar da ita. Kwananta hud'u a asibitin mutanen maiduguri suka iso. Zainaba kanwar scorpion da scorpion da amaryarshi kanwar Faheema mai suna Raheema, sai Nass da Fatima da 'yarsu mai sunan Deejah (khadijah) Dan dukansu biyu alkawari suka d'aukarwa kansu Zasu yi mata mai suna idan Allah ya azurtasu da 'ya mace. Sai kuma yaya Bukar. Zuwansu Fatima ne aka fara ganin canji, domin Fatima na ganinta ta gagara haqura ta fashe da kuka, itama take aka ga ta fara sharar kwalla. Babu wanda ya hanata sbd suma rashin kukannata na damunsu, ita batayi kuka ba kuma ba magana. Kuka sukayi tayi dasu Fatima, su Dadayi suna tayasu. Cikin kuka Fatima tace "Allah zai saka mana, in sha Allahu Allah sai toni asirin munafukan da suka kashe mana shi, zasu shiga hanu da yardar ubangiji." Cakk ta tsaya da kukan ta d'ago tana kallon uncke smart da ke tsaye ya hard'e hannayenshi a kirji yana kallonsu , su nass, ta kuma bi da kallo kafin ta sake maida kallonta gareshi. Cikin disasshiyar muryarta tace..... * TASHIN HANKALI * *Written by:Mmn Abduljalal* *Fasaha Online Writers* * Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern. * *35* ~"Dama kasheshi akayi ? " Jinjina kanta tayi tana share hawayenta. "Ni dama jikina ya bani suna bibiyanmu, na sani basu qare ba akwai saura, sun kashe minshi, saura mu kuma." "In sha Allah bazasu sake samun nasara ba, bazasu sake kashe kowa ba, kiyi hakuri aunty Khadijah." Cewar zainaba. "Aunty zainab na jima ina ji a jikina baza su barmu ba." "Kiyi haquri." Ta sake katse ta. Ko ba komai yaji dad'in maganan da tayi yau, sbd rashin maganar ba qaramin damunshi yakeyi ba Zamewa tayi a hankali ta kwanta idanunta suna ta tsiyayar da hawaye. Ta ma rasa wani irin rad'ad'i take ji a zcyrta. Magunguna da addu'o'i da kakansu scorpion ya bayar aka kawowa smart, suka bashi tare da bayanin yadda zai aiwatar dasu. Magunguna ne na tsarin jiki har da maganin bindiga. Bai tsaya wasa ba ya ci gaba da amfani dasu sbd yasan shi ake hari ba Mahmud ba, abin dai ya sauqa ta kansshi ne kawai, kuma yana da tabbacin indai suka san bashi suka harbe ba sai sun dawo mishi. Kwananta shida aka sallameta daga asibiti, ta koma gidan Hamma shehu. Ranar suna kuwa babu wani hidima sai abinci da aka daddafa akayi ta rabawa sadaka. 'Yan gaisuwa sai zuwa sukeyi na cikin Gembun, daga dorofi, nguroje, 'yan sunkani dangin maman Deejah, da 'yan Jalingo da yawancinsu dangin adda ne. Bayan suna da kwana uku sukayi parking ya bar gidan su aunty Tala. Suma kuma suna zuwa duba Deejah can gidan Hamma atiku. A ranar su adda sukaje suka ga gidan, suka kama hanyar komawa dorofi. Sosai adda tasha kuka da ta tuna tazo tare da Mahmudu gashi tana komawa ita ba tare dashi ba, kuma sun rabu kenan har abada. Goggo kawai aka bari tare dasu, kasancewar adda Rabin ma jego takeyi, kuma babu damar a tafi da Deejah sbd aikin jikinta. Sai kuma su Fatima da har yanzu suna nan basu tafi ba. Ranar da yayi parking kuwa a ranar mutanen nashi suka zo mishi. Saidai sun taki rashin sa'an samunshi. Gaba d'aya mutanen gidan suka fiffitar suna tambayarsu uncle smart. Jami da tun shigowarsu taji tayi saurin shigewa cikin toilet ta kulle ta turawa yayanta dake night duty text message. Tana jin uban tsawar da suke ta dakawa Baban Ahmad kan ya nuna musu inda smart yake. Daga cikin bayan gidan taji an bud'e kofar d'akin ta aka shigo. Jikinta sai b'ari yakeyu, tsabar tsoro saida ta saki fitsari a jiki. Dudduba d'akin sukayi ganin duka yara ne a ciki suka fita suka bud'e d'akin aunty Tala. Nan itama sukayi ta bud'a mata wuta bayan sun kwace wayarta, sun d'ibi abubuwa masu muhimmanci cikin d'akin. Qarshe dai tasa Baban Ahmad sukayi kan sai ya nuna musu inda smart yake ko su kasheshi. Maman Ahmad sai kuka takeyi tana rokonsu haka suka iza keyarshi suka fita dashi. Tsoro ne ya cika Jami tana tunanin yanda zatayi. Can ta shiga dialling nambar Deejah, tana shiga amma bata d'auka. Wayar a silent take dan smart ne yasata a silent kafin ya tafi, sbd kada a tasheta tana bacci. Tunowa tayi ta tab'a d'aukar nambarshi cikin wayar Deejah, hakan yasa ta shiga searching tana fatar Allah yasa ta sameshi. Ringing biyu tayi taji an d'aga. Sallama yayi da muryar bacci. Tayi saurin cewa "Uncle." Bayan ta sauke ajiyar zcy. Ware ido yayi yana mamakin mai kiranshi cikin darennan kuma muryar mace. "Uncle, Jami ce ,suna nemanka zasu kasheka ka b'uya kafin suzo, suna zuwa da Baban Ahmad, sunce zasu kasheshi idan bai kaisu inda kake ba." Ta fad'a sauri sauri." "Nagode." Kawai ya iya cewa ya kashe wayar. Tashin su Scorpion yayi ya fad'a musu abinda Jami ta fad'a mishi. Inda abin yazo musu da sauqi babu mata a gidan su kad'ai ne, matan duk suna gidan Hamma atiku. Kiran wayar Hamma Atiku yayi, nan yace mishi suna tare da yayan Jami ya qirasu ta gaya musu,suna kan hanyarsu na zuwa gidan, saidai suyi taka tsantsan dasu kafin su iso. dama kuma cikin 'yan kwanakinnan binciken da sukeyi kenan kan wad'anda suka kashe Mahmudu, dan shi da kanshi smart d'in ya basu tabbacin zasu dawo muddin sun tabbatar da ba shi ya mutu ba, sbd yana da yakinin shi suke nema ba Mahmudu ba. Fita sukayi suka lab'e a wani lungu na cikin gidan ta baya, bayan sun bar kofofin a bud'e amma sun ja sun rufe basu kulle bane. Ba da jimawa suka iso, da motocinsu har biyu. Baban Ahmad shine a gaba suna biye dashi a baya. Da hasken waya suke amfani suna haska hanya. Biyu daga cikinsu kuwa suna kofar gida, suna musu gadi, shida suka shiga daga ciki, biyu suka tsaya bakin kofar falon suna muzurai. Baban ahmad kam jikinshi sai b'ari yakeyi yana karanto duk addu'ar da tazo bakinshi. Shi dai kam yau yaga *tashin hankalin* da bai tab'a gani ba a rayuwarshi. Ta bayansu suka lab'ab'a da dabaransu ta tsofin 'yan fashi suka samu suka rapke biyu dake bakin qofa suka murd'e, tare da toshe musu baki. Smart kuwa yayi saurin saka key ya kulle kofar falon da sauran suke ciki. Suko suna bin d'akuna suna bankad'awa cikin zafin nama da zafin zuciya ,yau dai suna gani ba makawa burinsu zai cika kan smart. Motsi kulle kofar suka ji daga waje wasunsu suka nufo bakin kofar. Bindigogin hanun biyu na kofar dakin suka kwace. Da iya qarfin da Allah ya jore musu suka rika jibgar 'yan iska, suma dagewa sukayi suna kokarin ramawa. Abinda yayi musu cikas rashin bindiga a hanunsu. Su kuma gashi sun karb'e amma basu yi amfani da su ba. Nuna musu bindigar scorpion yayi yana muzurai tare da basu umarnin tsayawa guri guda idan ba haka ba ya harbesu. Take suka daidaita nitsuwarsu. Ana cikin haka kuma suka ji musayar wuta a waje, tsakanin su Hamma atiku da masu gadin kofar gida. Suko na ciki kokarin balle kofar sukeyi. Cikin sa'a suka samu suka b'alla kofar, suka shiga sakin bullet, abin mamaki babu wanda bullet d'in yayi wa illah a cikinsu. Saima su da scorpion ya harbe mutum biyu a qafa. Baban Ahmad kam tunda yaga sun fita ya makale cikin d'akin, yana ta rarraba idanu. Daga wajen suka shigo suka had'a su suka tattara bayan sunyi nasarar amshe bindigogin hannayensu. Saida komai ya lafa, an tafi dasu kafin suka shiga suka tarar da Baban ahmad, yayi wani zuru zuru dashi. A gidan ya kwana, sai washegari yayi sammakon komawa gida. Kwanaki biyu mutasn Borno suka qara suka koma aka bar Deejah da kewa, dan kam suna kokarin d'ebe mata kewa sosai. Yanzu daga ita sai babynta wacce taci sunan mahaifiyarta, (Hafsat) suna kiranta Walida. Sai matar Hamma atiku sai kuma goggo dake kula dasu, kasancewar dukansu biyu jegon sukeyi. Yusufa ma yana kokarin shigowa akai akai gurin yayarshi. Ba karamin tausaya mata yakeyi ba, tunda Mahmud ya rasu, gata dama can yadda rayuwa tayi ta juyi da ita. ~zaune take kan gado ta mimmike kafafu tana shayar da Walida, gefe guda kuma rigunan jarirai ne masi kyau guda biyu, da huluna biyu, set na pant d'in jarirai, sai socks mai guda uku cikin leda. Jami ce ta kawo mata su, tare da rokanta gafara kan abunda ya faru tsakaninsu. Duk da da tana jin haushin abinda Deejah tayi mata, amma zuwa yanzu ta zubar da komai, tun rasuwar Mahmud taji jikinta yayi sanyi da yanayin rayuwa, gashi kuma lokaci guda sukayi parking suka bar musu gidan, sai taji jikinta ya dad'a sanyi, ga kuma al'amarin da ya tsoratata game da wadanda suka zo neman wanda suke gaba akanshi zasu kashe. Da badon kwananshi na gaba ba, da shima yanzu ya zama tarihi. To itama ta gefen Deejah kasancewar tana cikin hali na alhini, ko da Jami ta nemi gafarar ta bata yi wani jinkirin yafe mata ba, itama har ta nemi gafarar Jamin, sun tab'a hira duk da dai ba wani sakewa suka yi sosai kamar da ba. Saidai a yanzu ganin kima da darajar Jami takeyi tunda taji cewar ita ta qira Uncle d'inta ta fad'a mishi makasanshi suna zuwa gareshi. Hakan ya nuna mata cewar duk abinda sukayi mata baisa tayi fushi ta goge nambobinsu a wayarta ba tunda itama taga missed call d'inta washe gari, duk da cewar bata san lokacin da Jamin ta d'au nambar Uncle d'inba, amma ita dai a yanzu d'aukar ya mata amfani. Ta'aziyar da ta qara yi mata na Mahmud da yanda tayi ta nuna alhininta game da rasuwar yaron ya kuma d'ago mata damuwar da take kokarin dannewa. Sharar kwalla takeyi kad'an kad'an tana tuno rayuwar da sukayi da yaron a cikin 'yan kwanakin da sukayi tare. Har ya qaraso kusa da ita ya zauna hankalinta baije kanshi ba sbd ta lula duniyar tunani. Babbar yatsarshi yasa yana share mata hawayen fiskarta, hakan ya ankarar da ita wanzuwarshi a wajen. A hankali ta kwantar da kanta a kafad'arshi tana jin zcyrta na dad'a karyewa. Kallon fiskarta yakeyi cikin tausayawa, sosai take bashi tausayi, bama shi kad'ai ba, mutane da dama, sbd ta gamu da jarrabawa kalakala a rayuwa. Shafa kanta yayi snn ya kewaya hannayenshi jikinta, ya kwanto ta jikinshi. A tausashe ya fara mata magana. "Mummy, har yanzu baki daina yiwa Mahmud kuka ba ? Wnn ba gatan da ya kamata uwa tayi d'anta idan ta rasa shi ba kenan khadijah. Haquri zakiyi ki fawwalawa Allah al'amarinshi. Ki tuna Allahn da ya bamu shi shi ya d'aukeshi kuma yafi mu sanshi kuma shi yasan dalilin yin hakan. Yawan kukanki yana nuna kamar kina fushi da hukuncin Allah ne. Kada ki manta cewa ni fa akaso kashewa, da yake shine mai kararren kwana abun ya sauqa a kanshi. Ko kina tsammanin idan Mahmud ya girma yaji labarin ta yadda aka sameshi zaiji dad'i, ko yayi alfahari damu a matsayin iyayenshi, tunda kinsan dole sai an fad'a mishi, sbd irin haka baya b'oyuwa. Kukanki yana nuna min cewa da ni ne na mutu irin gatan da zakiyi min kenan, kiyi ta kuka ki manta da addu'a, hakan kuma ba dad'i zai min ba a matsayinki na masoyiyata. Dan Allah mummy ki cire damuwa a ranki, ki sawa ranki cewa Allah ya kawo Mahmud cikin rayuwarmu na lokaci kankani ya nuna kanshi, ya kuma yi sanadin shiryuwar mahaifinshi ya tafine, dama can Allah baiyi mai tsawon rai bane. Nasan abun da ciwo amma ya zamuyi, hakuri ya kamata muyi mu godewa Allah, da ya bamu Mahmud ya d'aukeshi kuma ya qara yi mana wata kyautar a dadai lokacin da muka rasa Mahmud." A sanyaye ta gyad'a kanta tana had'iye kukan da take ji yana taho mata. Shima kanshi ji yake kamar ya tayata kukan sbd ba qaramin dukanshi mutuwar Mahmud yayi ba, gefe d'aya kuma ga tausayin mahaifiyar mahmud d'in. Suna cikin haka goggo tayi sallama, hakan yasa tayi saurin yunkurawa ta tashi daga jikinshi. D'aukar Walida yayi yana kallomta tare da godewa Allah bisa wnn kyauta da yayi mishi. A haka suka gaisa da goggo daga bisani yayi musu sallama ya fita. Zama goggo tayi tana d'an jan Deejah da hira, sbd ta lura da kukan da tayi, fiskarta ya nuna, kad'an kad'an take jefa mata nasiha cikin hirar tasu. ~ Watan goggo guda a gidan Hamma Atiku ta tattara ta koma Nguroje ta barsu da kewa, daga kula da Deejah ya koma hanun Adda Rabi matar Hamma Atiku. Saida ta cika watanni uku ta koma gidanta, bayan an had'ata da Hameeda dan ta rika taimaka mata. Sadaka kuwa kullum ne sai sunyi da fatar Allah yakai ladan wa Mahmudu. Har rijiya yatona a kofar gida mutane suna d'iban ruwa a matsayi sadaqatul Jariya wa Mahmudu. *Five years later* ~Deejah na gani sanye da baqin swiss lace mai adon green flower, ta d'ora babban hijabi kanta, kafarta sanye da takalma kalar hijabin mai d'an madaidaicin tudu. Tayi kyau ta qara haske, tayi qiba ba sosai ba, da ganinta kasan tana cikin kwanciyar hankali da nitsuwa. Walida ce a gefenta ta rike hanunta tana tsallen tsallenta na yara, yarinya mai kama da mamanta, kyakkyawa da ita son kowa, tana ciikn shiga mai kyau da d'aukan hankali, kanta sanye da d'an madaidaicin hijabi wanda ya dace da kayan jikinta. Daga gefenta Uncle smart ne rike da yaro d'an wata hud'u mai kama dashi, mai sunan Hamma shehu, wanda Deejah ta haifa daga baya bayannan. Sai Yusuf dake biye dasu a baya rike da hannayen yara biyu, d'an shekara hud'u da 'yar shekara uku. Shi namijin d'an Hamma shehu ne mai sunan Uncle smart Mahmud, wanda suke qira Amir. Sai macen kuma 'yar Deejah ce ta biyu mai sunan Adda, wacce suke kira da Ummi, ita kuwa sakk take kama da ubanta. Sai Hamma shehu da yake gaba ga dukkan alamu shine jagorar tafiyar. Wani qaton guri na gani sukanufa wanda akayi fencing d'inshi, shanukai ne cike taff a wajen. Bayani Hamma shehu yakeyi musu kan dukan wnn shanayen arzikin Deejah ne, wanda ya saya mata da kud'in sadakinta da kuma wanda smart ya bata ta mayar mishi shi kuma ya damka ma Hamma shehu kan yayi mata abinda yaga ya kamata dasu. Shine fa ya saya mata shanukai ya bayar ana kiwata mata su ba tare da ta sani ba har suka hayayyafa suka yi yawa haka. Sai gurin raguna duka natane suma kiwata su akeyi. Mamaki ne ya cika Deejah ganin irin dukiyar da Allah ya mallaka mata. Bata san sanda ta fara sharar qwallah ba. Take ta yanke shawarar a bawa yaranta , yaran Hamma shehu da yaran Hamma Atiku kowa d'add'aya. Iyayenta kam tasan suna da nasu saidai ta kyautata musu ta wani fannin, wnn kuma suna iyakar kokarinsu dukansu biyu. Gefe guda kuma ga sana'arta na kayan kamshi sai dad'a bunqasa yakeyi, zumuncinsu da mutan Borno kuma sai abunda ya qaru. Deejah dai ta zama Hajiya khadija sbd a yadda suka yanke shawara cikin wnn shekarar zata sauqe farali tare da babansu da babanta da adda, wata shekarar kuma su Uncle smart, Hamma shehu da Dadayi sai goggo amarya. Baban Hamma atiku tun wancan shekara sukaje tare da uwargidanshi Mmnsu Hamma atiku, saidai muce Allah ya karb'i ibada. Gidansu gaba d'aya sun canza tsarinshi ya zama ginin zamani, sun gyara gidan babu bambanci har gidan Hajja inna tsohuwa, yaran gidan kowa da irin gudunmuwar da ya bayar wajen gyara gidan iyayennasu. ••• ••• ••• ~Cike suke cikin falon Hajja inna tsohuwa, sun sata a tsakiya sai raha ake tayi cikin farin ciki. A wnn rana Hajja tana cikin wani irin farin ciki ne marar misaltuwa saboda ganin taruwan jikokinnata kusan dukansu. Bikin yusufa a kayi wanda aka had'a dana kanwarshi Hameeda. Shine dalilin had'uwarsu a dorofi, zuwa wnn lokacin jama'ar biki sun fashe kowa ya koma gidanshi saura yaran da jikokin gidanne suka rage. Su Ali da sukayi aure wancan shekara kowa yazo da nashi iyalin. Su Scorpion ma duk sunzo bikin. Jami ma kanta ba'a barta a baya ba, duk da yanzu tana auren wani d'an qabilarsu, d'an asalin qauyen Tamnya. Yaronta d'aya. Basharu d'an goggo ne ya shigo, cikin zolaya yake cewa. "Wannan taro haka ko wasiyya Hajja take bayarwa ne ? Ni dai kawai ki lissafa min duk inda kikasan kin b'oye dukiyarki sbd kada ki mutu musha wahalar nema." "Kayya, Basharu am, da mutuwar zata zo ta d'aukeni ma da naji dad'i, wannan taron duka jikoki da 'ya'yansu ne me zan jira tunda Allah ya nuna mini wannan duka. Daga nan ta fara lissafa kawayenta da 'yan uwanta wad'anda suka mutu tana musu addu'ar Allah yaji kansu harda kukanta. Dariya suka shiga yi mata, Ali yace "Kuma fa yanzu maganar da takeyi da zata ga mutuwar guduwa fa zatayi." "Kai gadanga ka fita idona, shekarun da nayi a duniya daga ku har iyayenku ban yi tsammanin akwai mai yinshi ba, to meye kuma abun guduwa." "In sha Allahu ma Hajja sai ta rike Mahmudu na kafin ta mutu ko Hajja ? Cewar Yusufa." "To rasa kunya, ni ko yanzu na mutu na gode wa Allah, fatanmu dai idan mutuwar tazo Allah yasa mu cika da imani...." "Amin... Suka amsa dukansu .... *Alhamdulillah* Anan na kawo qarshen littafina Tashin hankali. Allah ya gafarta min kurakuran da na yi a ciki. *Sadaukarwa* Gareku 'yan uwa rabin jiki Umar Mu'azu (Hammana) Umar A Umar (Ya Maimuri) Jamila Sulaiman(My Jamil.) Nafeesat Abdussalam (Sweet sister) Late Rasheedat Abdussalam (Lovely sister) Auwal Aliyu Salim Aliyu (senior) Muhammad kabeer Abdussalam (Bobbos) Isma'il Abdussalam(Magaj) Abbas Abdussalam (Amir) Nafi'u Abdussalam (Little) *Gaisuwa da jinjinan ban girma gareku* Rahama Rufa'i Nalele (Auntyn luv) Haleema Auwal (Mmn Aisha) Maryam A. I Gital (Ummyn Beauty) Hauwa S Zaria(Mmn Uswan.) Zainab Bugaje (Zezen Fasaha) Hauwa Abdullahi sarki (Auta) khairat Up (Ahlam) Ummin Weedyan. Hussaina Khamis. Zainab Shuaibu (Zabsha) Fasaha Tana alfahari daku. *Ina alfahari daku* Masoya a duk inda kuke dan kuna da yawa baza ku lissafu ba kun san kanku. Allah ya bar qauna. *Tukuici ne gareku* Members na Fasaha nvl group. 1,2,3,4. Zama na amana 2 Allah ya bar mu tare. *Taku mai burin faranta muku* Mmn Abduljalal

BTemplates.com

Popular Posts